Tuesday, 3 January 2017

NI DA YAYA HABEEB 90_100

[01/01 1:27 pm] Ruke Ilyasu: [10/12 4:51 pm] Jeeddah Aliyu: ```?NI DA YAYA HABEEB DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```90```

~~Suna isa Hotel d'in Bala yayi parking a sanyaye ta balle k'ofa tafito, tayi tsaye jikin mota tana jiran Habeeb yafito saida 6ata lokacin kafin yafito.
    ''Ko kallon wajen da take tsaye bai yi ba yawuce ta yanufi cikin receptionist ta had'e yawun takaicin tana mamakin wannan jijji da kai da Habeeb Lamido yake mata ta juya ta bishi a baya.
   "Tana tsaye ya kar6i  key card na room sai taga kamar mutane da ke receptionist d'in ita kadai suke kallo, a zuciyarta tace yanzu mutane nan kallon 'yar iska suke min sun ganin da k'ato a Hotel mtwww.....Ta ja tsaki wani sabon haushin Habeeb yak'ara lullu6eta.
   Batare da ya dube ta ba yace mu tafi koh''? Yana magana ne had'e da juyawa yabi wani dogon corridor ta juya ta bi shi kamar kazar da kwai yafashewa a ciki.
    ''Zuciyar Haleesa tacigaba da tafarfasa musanman yadda taga Habeeb yana tafiyar k'assaita yasaka  hannunshi d'aya cikin aljihun wandonshi d'aya hannun kuma yana rik'e da key card yana wata tafiya kamar mace mai ciki wata tara.
    ''Saida suka kai karshen corridor d'in yanufi upstairs yashiga haura staircase da suka kai karshen staircase 'yar gajeriya tafiya sukayi dai-dai d'akin mai number 406 ya tsaya ya yi using key card d'in hannunshi k'ofar ta bud'e.
   ''Yasa kai ya shiga d'akin Haleesa ta yi ajiyar zuciya gabanta na fad'uwa ta jefa 'kafarta cikin d'akin.
  "Jikin bango ta koma ta lafe Habeeb yayi switch on d'in light d'akin ya gauraye da haske, ya juya a hankali yana kallon Haleesa da take jingine da bango sai wuk'i-wuk'i take da idanu ga mamakinsa sai ya ga ta galla masa ta yatsine fuska ta dauke kanta zuciyarta naci gaba da bugawa.
  "Ya tabe baki yasoma balle buttons d'in rigar jikinsa yacire rigar yayi saura daga shi sai white vest da trouser Haleesa na satar kallonshi ta 'kasan idon.
   ''A cikin zuciyarta tace wannan d'an duniyar yana nufi zai dawo half necked a gabana"?
  "Habeeb da bai masan tana yi ba aikin gabansa kawai yake, yasoma warware belt ya zare shi a hankali ya jefa akan bed.
  ''jikin Haleesa yadauki rawa ta runtse idanu gam......ta tuna ko lokacin da suka yi wanka tare a Lagos runtse idanunta ta yi.
  "Yacire trouser yadawo daga shi sai white vest da Boxer Haleesa ta bud'e idonta kad'an ta ga yana k'ok'arin cire vest yarage daga shi sai boxer, ta tsurawa fad'adde k'irjinshi mai d'auke da Lallausar suma idon _kutt..... Ashe guy nan mai k'arfi ne kalli jikinshi a murd'e sai kace d'an wrestling_
  Ba dole ya zama k'aton ba kullum yana cikin gyms machine abunda d'ayan 6angare na zuciyar Haleesa yace da ita kenan.
   "Habeeb yajuya ya dube ta gani yadda ta rufe idanu yasa ya tabe baki yataka a hankali yanufi wurinta ya yi tsaye a gabanta, jin saukar numfashin mutum a gabanta ya firgitata babu shiri ta bud'e idanu da mugun mamaki take kallonshi, tukuna ma yaushe yak'araso kusa da ni"?
  ''Shima kallon nata yake da gira a d'age da sauri ta d'auke kanta da barin kallonshi cikin sark'ewar halshe tace ma....mal.....malam me ye haka"?
  "Hannunshi yasa yadawo da fuskarta yak'ara matsawa daf da ita yayinda numfashinsa yake sauka, akan fuskarta ta matse idanunta gam.......can! K'asan mak'oshi yafara magana ban gane me ye haka ba"? Kina nufi baki ta6a gani namiji a half necked ba"?
  "To ae ni ba 'yar iska bace da zan dinga gani maza a half necked tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
   "Shu'umin murmushi yayi had'e da kallon lips d'inta kina nufi hadda wannan gajere bak'in mutume mai kirar mutane Ghana duk da shaquwar da ki ka yi da shi baki ta6a ganinshi a haka ba"?
   ''Gaba d'aya Haleesa ta gama tsorata da lamarin Habeeb Lamido me yake nufi da wannan kurman bak'i nashi"?
   "Ni ban fahimce abunda ka ke nufi ba?
"Ya ja tsaki karka nemi ki raina min hankali mana tun da ki kaji na lissafa wa'annan siffofi ae kinsan da wannan margayi sarauyin naki mai d'ikin tela nake.
  "Rass-rass!!..... Haleesa ta ji gabanta yafad'i yau kuma da wannan Sabon samfari yaya Habeeb ya tsiro da shi"?
   Ran Haleesa yayi matuk'ar sosuwa cikin k'unar zuci tace kaga yaya Habeeb karka nemi ka cin zarafin mutume da yake kwance a kabarinsa idan wulaqancin ka ya motsa ya tsaya iya ni.
  ''Ya ja tsaki nasan har yanzu zuciyarki bata daina bagensa ba saidai kina yi a banza ne saboda tuni na haura stage d'in da shi d'in har ya kwanta dama bai haura ba.
   ''Hawaye suka wanke mata fuska cikin zafin rai tace shima d'in yashiga idan kai d'in bara ka ta6a shiga ba. Tana k'arasa magana ta ture hannunshi daga jikinta ta d'uka za ta bi ta k'asan hannunshi ta wuce ya matsa hannunshi yahana ta wucewa, yafizgo ta ya mayar da ita jikin bango ya matse ta sosai ta yadda duk yunk'uri da za ta yi bara ta iya guduwa ba.
   "Duk abunda za ki fad'a akansa leesa bare wuce ki ce yashiga zuciyarki ni kuma ban shiga ba, fine.....nima na yarda da haka amma kuma duk tsiyarki bara ki ce yata6a ratsa nan wurin yana magana ne had'e da tura hannunshi cikin rigarta yayi mata bak'ar matsa ihu azaba tasaki.
   "Wannan wane irin iskanci ne yaya Habeeb"? Tak'arasa magana cikin rawar murya.
  ''K'arya ki ke yi leesa ki kira wannan abun da iskancin ko kinmanta dubbanai mutane sun sheda na biya sadakinki sun kuma Shafa fatiha a tsakaninmu sannan kuma ki danganta hakan da iskancin"?
   ''In kuwa ba iskancin bane to akwai zallah mugunta a cikin, domin na tabbata da jikinka ne bara ka jure ayi maka haka ba.
  Shhhh.....yafad'a had'e da daura yatsanshi akan lips d'inta yaja iska duk abunda ki ka mallaka leesa a halin yanzu yatashi daga naki yadawo nawa, don haka ke mallakina nace sai yadda naga damar yi da ke.
   "Tsaki ta ja cikin shouting tace dallah! Malam ka barni mana wallahi kana tak'urawa rayuwata tak'arasa magana cikin muryar kuka.
   "D'ago fuskarta ya yi ta matse idanunta gam....saboda bataso kallon eye's ball d'inshi k'asa-k'asa ya furta oya open your bloody eye's and look at me"
  ''Ignoring nashi tayi sai ma tak'ara matse idanun nata da k'arfin gaske.
    "Don't let me repeat myself leesa"
  Kuka tasa mishi sosai cikin angry voice ya furta "I say open your eye's leesa....
  Rikice, ta bud'e idanunta masu cike da tsoro ta ware su akan fuskarshi eye's ball d'inshi suka k'ara rikitata.
   "Babu kyau mace tayi wa mijinta shouting dan haka wannan ya kasance shine karo na karshe da za ki k'ara d'aga min murya kinji"?
  "Tad'aga kai"
" kinsan wani abu kuwa"?
Ta girgiza kai bara nayi freshen up zan fad'a miki kinji"?
Ta gyad'a kai!
 "Good girl yafad'a had'e da d'an mari kumatunta.
  "Har yajuya sai kuma yadawo ya sumbace lips d'inta yajuya yashige bathroom.
   A kasalance tanufi gefen gado ta zauna sai a lokacin ta tuna cewa tana off{period} kuma gashi bara ta iya kwanciya sai ta sauya pad d'in jikinta, babban tashin hankalinta daga ita sai purse tafito, pad d'in tana cikin handbag d'inta da tabaro gidan aunty Mami.
   "Da sauri taciro phone daga cikin purse d'inta cikin sauri take digits number's, ta kara a kunnenta.
  Muryarta a sark'e tafara magana _Hello Hannah Dan Allah wani taimako za ki yi min_
  "Wane irin taimako Haleesa a dare nan"?
_Hannah kinsan ina off gashi kuma mom tasa biyo yaya Habeeb ban fito da pad ba ina rushing sosai ki taimaka na baki address d'in Hotel d'in da muke driver yakawo ki kawo min pad had'e da sleeping dress d'ina Allah bara iya kwanciya da kayan da ke jikina_
"Haleesa ki duba time ki gani  _12:15am_ tayi ba yadda za'ayi mom tabarni na fito a irin wannan lokacin musanman in ki kayi la'akari gari nan bak'o ne a wurina ki fad'awa yaya Habeeb yanemo miki saboda bara arasa shop a kusa da hotel d'in da Ku ke ba.
  ""Hannah kunya nakeji bara iya fad'a mishi ina period ni dai ki taimaka min please tak'arasa magana cikin muryar kuka.
   "Okay.......naji tun da ke bara iya fad'a ba ni da banida kunya bara na kirashi na fad'a mishi tana k'arasa magana tayi hanging up.
  ''Haleesa tayi bi phone d'in da kallo jin motsin bud'e k'ofa yasa tajuya a tsorace daure yake da towel hannunshi rik'e da k'aramin towel yana goge sumarshi suna had'a ido ta d'auke kanta.
   Yayi murmushi yak'arasa wurin dressing mirror wayarshi yasoma ringing kallon d'aya ya yi wa wayan yadauke kai yacigaba da saka pyjamas d'inshi.
   "A Fakace Haleesa ta sace kallon wayan gabanta na cigaba da fad'uwa ta tabbata in har yaya Habeeb bai d'aga kiran Hannah ba kashinta yabushe.
   ''Har kiran ya tsinke bai k'ara kallon idan phone d'in yake ba wani kiran yak'ara shigowa ya ja tsaki a fusace yafizgo wayar yana kai dubanshi akan screen yaga Hannah ce yak'ara Jan tsaki.
   Yayi picking had'e da k'arawa a kunnenshi _Hannah disturber tell me now whats the problem "?_
  "Oh! Am sorry bros I don't means to disturbed you nima matarka ce ta bani sak'o tace na fad'a maka tana off kanemo mata pad.
     ''Yatsine fuska yayi yana satar kallon Haleesa me ye kuma off"?
 ''Menstruation take yi kuma ta manta da pad d'inta gida Dan Allah ka taimaka, ka nemo mata. Hannah tak'arasa magana kamar za ta yi kuka.
  ''Ita me yasa bara ta iya fad'a da bakinta ba"?
Yaya Habeeb kunya take ji
Hum....ke kuma ga ki shugaban marasa kunya shine ta aiko ki koh"?
Uhn.....uhn....yaya Habeeb ba haka bane
  ''Shut up shameless girl aje waya yafad'a cikin tsawa a rikice Hannah ta katse kiran.
  ''Yajuya ya dube Haleesa wance ta sadda kai k'asa tana jujjuya phone d'inta ya galla mata harara
 leesa kin yi mugun rainani shine don wulaqancin kina menstruation bara ki iya bud'e baki ki ce kina buk'atar pad sai kin gayawa Hannah tafad'a min saboda ke kinfi k'arfi ki fad'a min koh"?
   Shiru tayi saboda ita batasan me za ta ce da shi baba.
  Ya ja tsaki ya yi dialling number Bala         ''kai Bala mu had'u a receptionist inason gani ka yayi shiru yana sauraro abunda, Bala yake fad'a tsawa yadaka masa ka bi umarni kawai banaso silly questions.
  Mtww...yak'ara Jan tsaki a fuce yanufi k'ofa ya bud'e yafita.
   Yana fita Haleesa tayi ajiyar zuciya a baiyane ta furta d'an rainin hankali, ank'i  a fad'a maka d'in sai kayi
  Abunda za ka iya mtsww.... Ta ja tsaki had'e da duba time a wayarta _12:30am_ kutt....amma fa na wahalarda guy nan ta kyalkyale da dariya.
 
_15 minutes later_

Habeeb yaturo k'ofa yashigo hannunshi d'auke da Leda fara Haleesa da ke kwance tana game a wayarta ta dube shi saida ya k'are mata kallo ya jefa mata ledar hannunshi ke! Dallah tashi ki kintsa jikinki ni karki yi min k'azanta anan wurin yana magana had'e da nuna bed.
   "A Kunyace Haleesa ta mik'e zaune tadauki ledar tanufi bathroom, saida tayi wanka sannan ta kintsa jikinta tafito da sleeping dress d'in da ya siyo mata gud'a biyu babu ta kirki ciki zaro ido tayi kai amma fa yaya Habeeb d'an air ne tad'ago wata night gown light pink tasaka iya cinyarta gata trensperent komai na jikinta a baiyane ta ja tsaki dube ni dallah sai kace wata prostitute d'an duniya kawai.
   ''Jin tayi an turo k'ofa a tsorace ta dube bakin k'ofar Habeeb tagani tsaye fuskarshi a had'e _wai ke me ki ke jira ne a bathroom ko ana za ki kwana"?_
  Girgiza kai tayi!
To wuce mu tafi yafad'a had'e da kallonta k'asa-kasa turo baki tayi kai kafara wucewa mana.
  "Shu'umin murmushi ya yi yasake k'ofa yafita ta bi bayanshi, tana kakkare k'irjinta da hannayenta.
  Ya kwanta akan gado yana kallonta ta k'asan ido ta ja tayi tsaye tak'i karasawa wai ke leesa bakisan cewa dare ya yi bane"?
   Murgud'a baki tayi tanufi can! nesa da shi ta ra6a ta rungume hannayenta a k'irjinta Habeeb ya tabe baki yace wane dare ne jemage bai gani ba ki daina Wahalarda kanki kina rufe k'irji domin ba 6oyayye bane a wurina.
   ''Harara shi tayi tana murgud'a baki ta kwanta had'e da juya masa.
   ''Leesa matso ki ji wata magana zan fad'a miki mai dad'i gaske.
  Please yaya Habeeb ka kyalleni in yi bacci yanzu nan ka gama k'orafi kana cewa dare yayi.
   Za ki matso ne ko sai na matso da ke"?
Ta ja tsaki ta matsa kad'a tana tunzire baki tace gani yi maganarka.
Ki k'ara matsowa saboda kin mun nisa saida ta zuba mishi harara sannan ta k'ara matsawa.
  Ya ja iska yana Shafa sumar kanshi fizga d'aya yayi mata sai gata akan k'irjinshi ya matse ta gam......
  A kunnenta yarad'a mata ina fatar baki manta ba kin nemo dalilin da za ki gabatar mini da yasa na kira ki bakya picking daga karshe kuma, ki ka kashe wayarki nasan duk kinyi ne saboda ni oya tell me" meye dalilinki na aikata haka a gareni"?
Haleesa wance bacci yafara cin k'arfinta ta bud'e baki da kyar tace phone d'in nawa ne yakeda problem fad'uwa ya yi screen ya mutu ko an kirani baya ringing, shiyasa nayi switch off d'inshi.
  Uhm...uhm...leesa yaushe ki ka fara k'arya"?
 "Ni ba 'karya nayi maka ba in baka yarda ba ka tambaye Hannah.
 Wai yaushe Ku ka qula sabuwar alaqa ke da Hannah"? Na fahimce nan gaba had'e mun kai za ku yi.
  Jin tayi shiru bata bashi amsa ba sai kawai yacigaba da magana, leesa baki tambaya abunda nace zan fad'a miki in nafito daga wanka"? Duk da gaba d'aya wannan off d'in ya rusa mini budget.
  Shiru bata bashi amsa ba.
Murmushi yayi ya daura hannu akanta yana shafa sumar kanta a hankali _zuciyata ta jima tana begenki leesa zan iya cewa tun daga lokacin da idanuna suka yi tozali da kyakyawar fuskarki narasa sukuni na tsundunma a tunaninki a zahari gaskiya leesa bansan lokacin da zuciyata ta kamo da zazzafar soyayyarki a da nayi wauta leesa sai nake ganin karancin shekarunki kamar bara iya sonki ba ashe shirme nake yi tuni sonki ya bi jinin jikina duk sanda na dubi idanunki sai naji sanyi had'e da kasala sun lullu6e ni idan kuma na shak'i  k'amshinki sai naji sha'awarki ba ta lullu6eni nakan nemi natsuwata narasa *I LOVE YOU LEESA*_
 _l love you so much I can't live without you_
 _Nasan ni mai laifi ne agareki amma ina rok'onki kiyafemin ki taimake ni leesa ki cuto rayuwata kidaina son margayi Habeeb ki cike gur6inshi, da ni a zuciyarki bara iya cigaba da gani kinason wani ba ni ba ki tausayawa rayuwata leesa ki fitarda wannan Habeeb d'in a zuciyarki saboda inasonki sosai shiyasa nake mugun kishinki duk lokacin da naji kin kirani da suna yaya Habeeb sai naji wani mashi yadak'i zuciyata sai naga kamar da wance Habeeb d'in ki ke sai naji na tsani sunana har nakeji kamar na canza suna.........._

Jeeddah Aliyu
[01/01 1:27 pm] Ruke Ilyasu: [12/12 8:04 pm] Jeeddah
 Aliyu?: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```91```

_sallam ina mik'a d'inbin godiya ga masoya wannan labari ,na ni da Yaya Habeeb kad'an daga cikinku sun fara complain akan ina jan musu rai wasu kuma suna cewa yakamata Jeeddah takawo end d'in wannan labari to ina muku albishir lnsha Allah labarin ya zo karshe thanks 4 the love & support love u all"_


~~Jin shiru nata ya yi yawa yasa ya kira sunanta can! K'asan mak'oshi leesa, leesa ko kin yi bacci ne"?
Nan ma shiru bata amsa ba ya sausauta rungumar da ya yi mata yad'ago fuskarta Omg! Dama leesa tayi bacci shine tabarni ina ta zuba, kamar burgage famfo"?
  Yana murmushi ya ja karan hancinta leesa kin kashe ni ya tuna tun yana Japan yake rehearsal irin Kalamai da zan fad'a mata Wanda za su tabbatar mata da yakamo da sonta ba kad'an ba.
   ''Mtsww.....ta kowane fanni leesa ta rusa min budget amma ba komai gobe, ma rana ce Haleesa tayi wani juyi tak'ara shigewa k'irjin Habeeb hankalinta kwance tacigaba da sharar baccinta.
     "Yak'ara gyara mata kwancinta akan k'irjinshi yana mamakin yadda son Haleesa yayi masa mummuna kamo, ya sumbace goshinta ya karanta addu'a kwanciya bacci ya tofa mata yana shafar gashin kanta har bacci ya dauke shi.

        _7:44am_
         Habeeb ya tashi yana yada ganinshi akan wall witch ya zaro, manya idanunshi yana mamaki abunda yahana shi tashi da asuba.
   "A kasalance ya dube Haleesa wance ke nad'e akan k'irjinshi yayi murmushi a hankali, ya rabata da jikinshi ya janyo pillow ya aza mata kanta karaf ta rik'e masa hannu  da sauri ya dubi fuskarta still bacci take abunta, ya d'an ja hannun nashi tak'ara dank'ewa.
   "Ya girgiza kai yasaka d'ayan hannunshi yacire hannunta ya sumbaceta ya sauka daga kan gado yanufi bathroom yayi alwala yafito har zuwa lokacin Haleesa bata motsa ba.
   " A zuciyarsa yace kai wannan yarinya akwai bacci tsiya, idan tana bacci za ka iya sace ta batare da ta falka ba ya shinfid'a pray mat yayi sallah.
    "Yana gama sallah yadawo kusa da kanta ya zauna yana Jan casbi fuskarshi na bisa fusksrta yana murmushi.
"Yayi ajiyar zuciya ya ajiye casbinsa akan bedside yadauki phone d'inshi, yadinga daukarta pic in gaji da wannan waya ya ajiye ya dauko wata motsin da tayi yasa yayi sauri ya ajiye wayan.
   "Idanuta a rufe tashiga lallube Habeeb ya zaro ido a tunaninshi ko shine take nema sai kawai yaga ta firzgo pillow ta manna a k'irjinta, ta rungume pillow gam.... Hararan pillow k'irjinta yayi sannan ya mik'e yayi mata peck a goshi da saman lips ya canza kayan jikinsa zuwa farar Jallabiya ya bud'e k'ofa yafita so yake ya d'an motsa jikinsa yanufi gym room da ke cikin hotel d'in.
 
_20 minutes later_

Habeeb ya gama motsa jiki yafito daga gym room yanufi d'akinsu a tunaninshi zuwa wannan lokacin Haleesa ta tashi, yana bud'e k'ofa yayi tsaye turus.....tana nan yadda yabarta yacire jallabiya jikinsa yayi saura daga shi sai boxer.
  "Knocking akayi yanufi k'ofar had'e da fulrta "yes! Ya bud'e k'ofar room service yagani tsaye d'auke da Food d'in da yayi musu ordering ya kar6a had'e da furta thanks"!
  "You're welcome sir! Room service d'in yafad'a had'e da juyawa.
  "Ya ajiye abincin yashiga bathroom yayi wanka yafito ya dubi kan gado idan leesa ke, kwance tana sharar bacci ya girgiza kai a baiyane yafurta yanzu kan dole ki tashi.
     "Kaitsaye yanufi wajenta yasoma bubbuga hannunta yana had'awa da kiran sunanta, a hankali ta bud'e idonta wannan wane irin bacci ne sai kace kinsha cough syrup"?
   Yatsine fuska tayi tana turo baki ta tashi zaune, tayi mik'a had'e da doguwar hamma k'irjinta ya bank'aro.
  Mutuwar tsaye Habeeb yayi yasaki baki kamar dolo yana kallonta, kamar ance tajuya taga gaba d'aya Imaninshi yaraja'a akan k'irjinta a hankali tadawo da ganinta akan k'irjin nata ko za taga abunda yake kallo haka.
  Zaro idanu tayi a rikice ta rarume blanket ta lullu6e jikinta  Habeeb yatabe baki yace daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa, abunda ki ka sake a fili tun ina kallo yana bani sha'awa har yadawo bani kyakyami yana magana ne had'e da yatsine fuska.
   
       ''Harara ta zuba masa kamar eye's ball d'in zai fad'o k'asa ta murgud'a baki, kadai yaya Habeeb kashiga uku a da ina maka kallon mutume kirki  bansaniba ashe kai gawurtace d'an is........sai kawai tadafe baki tafirfito da idanu tana girgiza kai.
  "A hankali ya ajiye comb d'in hannunshi yanuna kanshi da yatsa in shock yake magana leesa ni za ki zaga ni za ki kira da d'an iska"?
  "Jikinta yadauki rawa tayi bala'i tsorata ita kanta batasan time d'in da Kalmar tafito daga bakinta ba.
  A tarihin rayuwata ke ce mace tafarko da ta kirani da wannan kalma, yak'arasa magana yana huci.
  "Haleesa tayi raurau da idanu kwalla ta cika mata idanu, cike da Nadama tace I'm sorry yaya Habeeb Allah subul da baka nayi kayi h........shut up yadaka mata tsawa karki kuskure ki k'ara bani hak'uri nasan bakya sona leesa kin tsaneni amma banta6a zato za ki iya bud'e baki ki zage ni Sam baki yi la'akari da matsayina na mijinki ba.
   Muryarta na rawa ta bud'e baki dan Allah yaya Habeeb kayi h.......I don't wants hears anything from you kawai ki tashi ki je kiyi wanka.
 hawaye suka wanke mata fuska ta yaye blanket tasauko tanufi bathroom, ya bita da kallon takaicin me yasa leesa za ta zageni"?
Ko dan ta fahimcin ina  sonta shiyasa za ta dinga furta mini duk abunda yafito bakinta.
 ''Cikin zafin rai ya bud'e luggage d'inshi yadinga watsi da kayan da ke ciki, ya hargitsa su gaba d'aya yanemi gefen gado ya zauna dafe da kai yana jin zafin zagin da leesa tayi mishi a 6angare d'aya kuma yana jin wani masifafe sonta yana kwarara a zuciyarsa.
    ''Kamar Wanda aka mintsina ya mik'e  a gaggauce ya saka kayan ya kwashi phones d'inshi da ke zube akan bedside ya fice ranshi a 6ace.
       "Haleesa ta fito daga bathroom tayi tsaye sororo rashin ganin Habeeb cikin d'akin yasa ta tsinci kanta cikin rashin jin dad'in abunda
ta aikata cike da nadama ta nufi bed ta mayarda anko da cire, jikinta asanyaye tashiga linke kayan da ya zubar tana mayarwa cikin luggage.
   Takoma bisa gado ta kwanta, ta afka tunanin Habeeb, na shiga uku ni Haleesa me yasa na bari shed'an yayi tasiri akaina na zage shi"? Shikenan na janyowa kaina zai k'ara tsanata.
     ''Dan Allah yaya Habeeb kayi hak'uri kayafemin ta kifa kanta a pillow tasa kuka kamar ranta zai fita tun tana jiran shigowarsa tak'ara bashi hak'uri har ta fitarda rai, ga wata 'yar uban yunwa da takeji saida batada kwaciyar hankali da za ta iya saka koda ruwa ne a cikinta.
       "Har _1:30pm_ yayi Haleesa bataga Habeeb yadawo ba wani irin tsoro ya lullu6eta ta aikawa kanta tambaya ba dai yaya Habeeb tafiya yayi yabarni a hotel ba"?
   Wani Sabon kuka ya zo mata tashiga kuka ba kaukutawa, saida tagaji don kanta rarrashi kanta domin wanda takeyi don shi bai Masan tana yi ba, ahaka tayi bacci.
   
''Around _4:03pm_ A hankali Habeeb yaturo k'ofa yashigo ya hangota kwance yasaki ajiyar zuciya saida yak'are mata kallo na tsawon lokacin sannan yanufi gefen k'afafunta ya zauna.
   "A zuciyarsa yace bara iya jure fushi da ke ba leesa saboda inasonki nayi alqawali bara Kara ta6aki ba tun da bakyaso.
  Yanaso yatashe ta musanman da ya fahimcin cewa bata yi breakfast ba har yakai hannu yata6ata sai kuma zuciyarshi ta kwa6e shi, yajanye hannunshi ya mayar a gefen pillow da take kwance ke!ke ki tashi Bala mayarda ke gidan aunty mami"!
   Ta mik'e a kasalance ta tadaura fuskarta akan fuskarshi tasa pity face muryarta asark'e tace Dan Allah yaya Habeeb kayi hak'uri karka yi fushi da ni.
  Harara ya zuba mata yadauke fuska ta matsa jikinshi I'm sorry yaya Habeeb please forgive me"!
  Ya mik'e a fusace nace ki tashi Bala ya mayarda ke gidan aunty mami bana buk'atarki anan wurin.
    Jikinta na rawa ta mik'e tad'auki veil d'inta had'e purse idanunta na zubarda hawaye tayi tsaye tana kallon Habeeb Wanda ya kauda fuskarshi gefe ko kallonta bayaso yi tanufi k'ofa da sauri ta bud'e tafita saida takai karshen staircase ta tsaya tasaka Veil d'inta ta goge fuskarta tana shiga receptionist ta hango Bala ya mik'e yanufo wurinta suka k'arasa fita.
   ''Bayan tafiyar Haleesa Habeeb yashiga damuwa matuk'a yadda Haleesa bataci abinci ba shima kasaci yayi sai dare da yaga yunwa za tayi masa lahani yanemi coffee yasha adaddafe ya ga wayewar gari da k'arfe _11:00am_ aka d'aura auren sageer da amayarsa Nabeela daga wajen d'auri aure dama Habeeb yafito da luggage d'inshi ko gidan aunty mami bai waiwaya ba suka d'auki hanyar komawa Abuja ko madam Hindu batasan cewa Habeeb ya koma abuja ba saida taga throughout bata ganshi ba ta kira shi a waya yake cewa shi gashi bisa hanyar abuja sosai mamaki yakamata tace matarka fa Habeeb"?
 Sweetheart ba tare Ku ka je ba"?
 Saboda mun zo tare shine bara ka jirata ba Ku dawo tare"?
  ''Uhm....sweetheart wannan ba matsala bane zan jirata gida har Ku dawo ba gobe  za Ku dawo ba"?
  ''Eh! Insha Allah gobe za mu taso.
 "Okay....Allah yadawo da Ku lafiya.
  ''Ameen... Son.
A lokacin da madam Hindu take sanarda Haleesa Habeeb yatafi saura kiriss tafashe da kuka da kyar ta rinjaye zuciyata, saidai tun daga lokacin taji gaba d'aya garin sokoto ya gundireta, ba abunda takeso gani irin Habeeb tacigaba da rok'onshi ko zai huce daga fushi da yake da ita ta kira shi  a waya yafi a kirga yak'i D'agawa a washe gari around _9:30am_ su Haleesa suka baro garin Sokoto farin ciki fal zuciyata za taga Habeeb.

_some hour's later_

  Tsananin gudun da driven madam Hindu yake tsulawa yasa suka shigo garin abuja da wuri kaitsaye gidan madam Hindu suka wuce.
   "Har gajiya tasaki Haleesa bata ga Habeeb ya zo ba kuma da kunnenta taji lokacin madam takira shi a waya tana sanarda shi sun dawo amma shiru bai zo ba.

_9:00pm_
Haleesa da Hannah na zaune a downstairs parlour, Haleesa ta dubi Hannah kamar za tayi kuka tace gaskiya Hannah nayi danasani abunda nayi wa yaya Habeeb na tabbata don yana fushi da ni yasa har yanzu bai zo gidanan ba.
  Tsaki Hannah taja narasa gane yaya Habeeb wane irin hot temper ne da shi"? Shi ya manta da irin cin zarafin da dinga yi miki ke bakiyi fushi ba sai shi"? Ki share shi kawai zai gaji da fushinshi yadawo.
   "Ajiyar zuciya Haleesa tayi tace bara ki gane ba Hannah duk abunda zuciya keso bara ta iya jure fushi da shi ba ni kan yanzu dabara ta tak'are, min domin soyayyar yaya Habeeb tariga tayi min mummuna kamu dai-dai lokacin da Habeeb yaturo k'ofa yashigo karar sautin TV da ke kunne yasa Haleesa da Hannah ba su ji shigowar Habeeb ba jin abunda Haleesa take fad'a ya yi sanadin da yataka birki yana sauraro firar tasu.
    "Ni nasan Allah ne ya jara6e ni da son yaya Habeeb kuma shine zai yaye mun Hannah soyayya masifa ce zafinta yafi dad'inta yawa.
   "Duk lokacin da na tuna da kyakyawar fuskar yaya Habeeb sai naji sonshi da kewarshi sun lullu6e ni Hannah inason yaya Habeeb wallahi ina sonshi tankar son da uwa take yi wa d'anta, inason yaya Habeeb tankar yadda nakeson numfashina soyayyar yaya Habeeb tariga tabi jinin jikina, ta ratsa idan bakya tsanmani.
    "Habeeb Lamido da ke tsaye ya runtse idanunshi gam.......wani irin masifafen kishi ya turnuk'e shi bai ankara ba yaji hawaye na sauka a kumatunshi.
   ''Hannunshi yasa yashafi kumatunshi ya mayarda ganinshi akan tafin hannu nashi tausayin kanshi yakamashi ya ji gaba d'aya ya tsani kanshi bai ta6a sani soyayya masifa ce sai yau musanman shi da yake dakon so.!
  Yana huci kamar kubunbuwa lallai sai na nunawa leesa kuskureta na firar wani k'ato alhali tana d'auke da igiyoyin aurena.
  ''A fusace yak'arasa Shiga parlourn kamar daga sama Haleesa da Hannah suka ganshi gani yanayin da yashigo da shi yasa suka mik'e tsaye a tsorace.
  "A tsawace yace sai yau na tabbatar da cewa leesa mahaukaciya ce ke ko a cikin mahaukata k'asumgumar ta6a66iya ce ke kina d'auke da igiyoyin aurena amma kina zance wani k'ato Wanda baya duniya tirr......da wannan mummuna d'abi'a taki. Yak'arasa magana cikin huci da hargowa gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka tashi rad'o-rad'o.
    "Cikin kad'uwa Haleesa take k'are masa kallo cikin 6aci rai tadaka masa kai! Dallah dakata kai har kanada bakin kiran wani mahaukacin in banda hauka mutume da ke kwance a kabarinshi kana kishi da shi wannan yana nufi Kaine k'ato ko k'ato na ban............wawan mari da Habeeb ya wanka mata ya yi sanadin da raguwar kalamanta suka qargame a mak'oshinta zafin marin yaratsa brain d'inta.
   ''Kafin tadawo daga natsuwarta ya chafke wuyanta ta baya ya yi mata mugun rik'o a tsorace Hannah tace yaya Habeeb meye haka me yasa za ka yanke mata hukunci cikin fushi"?
  "Da hannunshi guda yakaiwa Hannah mari da sauri ta duk'e yasameta a kafad'a Hannah ta kwasa da gudu tanufi upstairs tana kwalawa madam Hindu kira.
  "Nagaji da wannan masifafe son naki leesa da yake azabtarda ruhina ya mik'a hannu akan center table yadauki glass cup ya buga shi a jikin center table yafashe ya jefarda rabin fashashe cup d'in ya d'anko hannun Haleesa ya aza mata kar6i leesa ga makami ki caka mini a k'ahon zuciya na mutu na huta da wannan jarabbabe son da nake miki Wanda yake baki kwarin guiwa zagina.
   "Dask'arewa Haleesa tayi takasa gane wance duniya take ciki tsananin mamaki kalaman Habeeb suka baibayeta.
  "Hakan yabawa Habeeb daman cigaba da zazzage mata asirin zuciyarshi, leesa inasonki ina miki son da nikaina bana yi wa kaina shi, inasonki fiye da son da margayi Habeeb yake miki wallahi nafishi sonki leesa kece farin cikina banta6a son wata 'ya mace ba sai akanki banta6a sani  menene tunani da damuwa sai da na afka sonki. soyayarki tayi min illah leesa.
   ''Me yasa leesa bara ki so ni ba"?
Ko kina nufi bai kai matsayin da za ki soni ba"?
Nasan nayi miki laifi a baya amma a yanzu nayi Nadama ki tausayawa rayuwata leesa ki soni, muddin baki soni ba leesa zan iya rasa rayuwata.
   "Yana k'arasa magana yatureta tafad'i k'asa da6ass.....
"Fashashe cup d'in hannunshi ya matse gam......ya yanke shi jini yasoma zuba.
  "A rikice madam Hindu take taka staircase Hannah na biye da ita salati ta rafka kanka d'aya kuwa Habeeb"?
Kana hauka ne akan wane dalilin za ka mari 'yar mutane"?
  "Kalli yadda hannunka yake zubarda jini ajiye cup d'inan nace wai ba da kai nake magana bane"?
  ''Habeeb na tsaye k'ik'an yakasa motsi madam Hindu ta ware yatsunta ta wanka masa bahagon Mari babu shiri yasaki glass d'in hannunshi.
  Da baya-baya yafad'a bisa kujera madam Hindu ta durk'usa ta d'ago fuskar Haleesa da hannayenta biyu  Haleesa kuwa tadawo kamar wance batada jini a jiki.
   Tashi Haleesa tashi tsaye kinji"?
Ta mik'e da kyar madam Hindu ta dubi Habeeb tace tashi kafice kabani wuri nace katashi katafi har sai na nemi ka tak'arasa magana cikin shouting.
 ''ya mik'e a fusace yafita "madam Hindu tarik'o Haleesa zuwa bedroom d'inta har zuwa lokacin Haleesa batasan idan kanta yake ba takasa sarafa brain d'inta madam ta kwatarda ita akan gado.
   Hannah ta dubi madam tace wallahi mom yaya Habeeb azzalumi ne ya k'untatawa rayuwar Haleesa nan take ta zayanowa madam irin zaman da Habeeb yake da Haleesa ran madam yayi matuk'ar 6aci tasoma zazzaga masifa kamar ta ari bakin kare tabbas sai na nunawa Habeeb kuskure shi ni zai munafuta agaban idona yanuna yanaso yarinya nan ashe abayan idona zaluntarta yake yi.
  Yayinda Hannah tacigaba da zuga madam.

_washe gari_
Tun da asuban fari Habeeb yadako sammako gidan madam ya yada zango a downstairs parlour.
Sai around _10:22am_ madam tasauko k'asa ta hango Habeeb kwance akan 3 seater hannunshi daure da bandage ya yi zurfi a tunani tadaka masa tsawa kai! Tashi mu yi magana ya mik'e  zaune a tsorace sosai madam ta wanke mishi allonshi.
   "Abunda nakeso da kai tun da sha'awarta ka ke yi na tabbata zuwa yanzu ka kawarda kwad'ayinka akanta, a matsayina na wance ta nema maka aurenta na umarce ka da ka rubuta takarda sakinta kabani yanzu nan.
  "A rikice Habeeb yafad'o daga kan kujera ya k'urawa madam Hindu manyan idanunshi, da ana mutuwa adawo duniya da Habeeb ya mutu yadawo saboda kalamai madam ba k'aramin girgizashi suka yi ba ji yake kamar tana labta masa rod'i aka.
  Cikin rawa murya da sark'ewar numfashi yace ki dubi Girman Allah sweetheart ki yi hak'uri kiyafemin wallahi ina matuk'ar son leesa......

Jeeddah Aliyu
[01/01 1:27 pm] Ruke Ilyasu: [14/12 9:34 pm] JeeddahAliyu?: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```92```


~~Sweetheart rabani da leesa tamkar rabani da numfashina ne domin ita ce farin cikina Dan Allah sweetheart ki yi hak'uri kiyafemin yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
    "Harara madam Hindu ta galla mishi cike da takaicin tanuna shi da yatsa banaso na dinga jayaya da kai saboda ni ba sa'arka bace, ballantana nima kace za ka yi min pretending d'in da kasaba ka shiga taitayinka.
     "Da Jan d'uwawu yak'arasa Wajen madam ya kifa kanshi a guiyoyinta muryarshi na rawa yace ki cuto rayuwata sweetheart wallahi duk abunda ki ka ji yafito daga bakina ba "pretending bane har cikin zuciyarta inaso leesa idan ki ka rabani da ita za ki iya rasani.
      ''Da k'arfi ta ture kanshi daga jikinta sai me don narasa ka ae ba kai kadai na haifa ba, ko kanaso ko bakaso dole ka ka saki Haleesa domin baran bare kacigaba da zaluntar 'yar mutane ba.
     "Runtse idanu yayi zuciyarsa na tafarfasa yarasa kalma da zai lalla6o ya furtawa mom ta fahimcin irin tsagoro so da yake wa Haleesa, rik'on hannunta ya yi "sweetheart please try to understand me nasan nayi kuskure, a yanzu kuma nayi Nadama ki tausaya min karki rabani da farin cikina.
   "Tsaki madam ta ja ta fizge hannunta daga rik'o da ya yi mata na baka 24 hours kawo min takarda sakin Haleesa idan, har kasan bara ka zo min da takarda saki ka kuskure ka k'ara zuwa min gida na shata dogon layi tsakaninka da ita tashi ka bani wuri.
       ''Habeeb ya yi shiru tamkar bai ji abunda  tafad'a ba cikin 6acin ran madam ta mik'e tsaye tun da bara tashi ba ni bara na tashi, na baka wuri sai kayita zama shashasha banza da wofi mai baqar zuciya kana sonta ubanwa yace kadinga wulaqantata"?
    ''Tsabar iskanci irin naka Habeeb ka ware, yatsunka ka wankawa 'yar mutane mari yanzu idan iyayyenta suka ji irin wulaqanci da kadinga yi wa 'yarsu mekake tsanmani zai faru"?
   ''Anan ne Habeeb yad'ago a tsorace yana kallon fuskar Madam Hindu, ya hadiye yawu masu masifar d'aci yarasa abun fad'a jikinsa ya yi mugun sanyi madam ta girgiza tanufi d'akinta tabar Habeeb zaune cikin  yanayin k'ila wa qala.
"Tsawon _5 minutes_ yadauka dafe da kai ya mik'e a kasalance haura staircase direct d'akin Hannah domin anan yakesa ran zai ga Haleesa batare da yanemi izzini masu d'akin ba ya murd'a handle yadanna kai.
      "A tsorace Haleesa da Hannah da ke kwance akan gado suka dubi bakin k'ofa Haleesa ta d'auke kanta da sauri.
   "Ajiyar Zuciya Habeeb ya yi yak'arasa, kusa da gadon fuskarshi a murtuk'e ya dube Hannah ya zaro mata manya idanunshi a tsawace yace ke tashi"!
  "Da sauri Hannah ta mik'e zaune ya nunata da yatsa banta6a, sani Hannah munafuka ce ke ba yau.
   Uhm......uhm.....yaya Habeeb me nayi maka da za ka kirani da munafuka"?
   "Zan wanka miki mari in ki ka k'ara tambyana abunda ki ka yi mun tsabar munafucin irin naki Hannah, ki ka ce da mom nace banaso leesa sha'awarta nake yi domin nasan leesa
 tana da kunya bara ta ta6a tunk'arar mom da wannan magana ba saidai tafad'a miki ke kuma da ki ke fitsararriya shine ki ka fad'awa mom.
    ''Jikin Hannah yadauki rawa ta yi wuk'i-wuk'i da idanu gani haka yasa Habeeb yarik'o kunnenta ya murd'e da k'arfi Hannah tasaki ihu azaba yasoma kashe mata gargad'i muddin ki ka sanarda mom na shigo d'akinan sai nayi miki dukan tsiya tashi ki fita.
   ''A lokacin d'aya Hannah da Haleesa suka mik'e tsaye saboda ko Haleesa ta tsorata da lamarin Habeeb ganin take yi da yagama da Haleesa zai juyo kanta.
    ''Da sauri Habeeb yasha gaban Haleesa kallo-kallo suka shiga  yi wa juna eyes balls d'inta suka yi mugun tsorata Habeeb sakamako yadda suka yi kwancin jini ga layin yatsunshi kwance akan kumatunta.
    "Nan take Nadama yak'ara lullu6enshi sonta da tausayinta suka k'ara samun muhalli a zuciyarsa.
   ''Sautin kukanta ne yak'ara dawo da shi natsuwarshi hannunta yarik'o da k'arfi tafincike hannunta tara6a gefenshi za ta Wuce yak'ara shan gabanta I'm so sorry leesa Dan Allah ki saurareni nasani ni mai laifi ne a gareki shiyasa nakeso ki bani dama na goge laifina.
      "A fusace tafara magana had'e yarfe hannayenta Nagaji yaya Habeeb nagaji da wahala da ka ke bani kafita hanya ta banaso ka k'ara zuwa idan nake ko wannan zaman da nake yi anan gidan don inajin kunya mom ne da tuni na kama gabana.
      "Habeeb yadawo kalar tausayi, yak'ara sausauta murya leesa ko ubangiji da ya halince mu muka sa6a masa idan muka rok'eshi yana yafewa mana ballantana mu 'yan Adam.
   Kowane d'a Adam ba  ba ya wuce kuskure leesa ki tausayawa rayuwata kiyafemin.
   "Batare da ta tanka masa ta nufi gefen gado ta zauna tadafe kanta tsaye Habeeb ya yi yana kallonta daga bisani ya baro inda yake yanufi wajenta ya zube gabanta ya yi kneeling yad'ago fuskarta.
    "Ta runtse idanunta gam...... Ko kusa bataso kallon fuskarshi domin zai iya karya mata zuciya, har ya yi nasara gano ta yi zurfi a sonshi.
   "Narasa kalma da zan yi amfani da ita "to express my feeling for you leesa but I really love you bara iya cewa ga takamame lokacin da sonki yashiga zuciyata ba amma kisani ina miki so da bana yi wa kaina.
    "Ina rok'onki, ki amince da ni zan koyo miki yadda za ki so ni leesa ke ce mace ta farko da zuciyata tafara so tsawon rayuwa da nayi da aunty salma banta6a jin kwatankwacin abunda nakeji akanki leesa.
    "Haleesa tarasa sama take ko k'asa take takasa amincewa da abunda kunnenta yake ji daga bakin Habeeb Lamido dama akwai ranarda da arrogant kamar Habeeb Lamido zai k'ask'antata kanshi a gareta sai yau tak'ara yarda da nasiha da Ammi take mata _Haleesa ki yi hak'uri Ki kasance mai tawalkali Allah da ya kar6i Habeebu shi zai kawo miki Wanda yafi shi komai na rayuwa_
  ''A lokacin da Ammi take mata wannan nasiha jin ta kawai take sai take gani kamar Ammi tana fad'a ne don ta kwatar mata da hankali sai gashi Allah ya nuna mata shi mai rahama da jinkai ne ga bayinsa ya had'a ta Wanda yafi margayi yaya Habeeb komai.
    ''Ita kanta tasan samun Habeeb Lamido a matsayin mijinta Rahama ce ta ubangiji Haleesa tayi ajiyar zuciya mai k'arfi tana ware idanunta akan fuskar Habeeb tak'ara jin wani Sabon sonshi yana kwarara a zuciyata.
    ''Wata zuciyata tace What are you waiting for Haleesa just tell him you love him, nan take wata zuciya tace  Haleesa za ki zubarda ajinki ne ki yi amfani da damar da ki ka samu, ki latsa shi kamar yadda shima yabaki wahala.
    "Yatsine fuska tayi kaga bawan Allah nace bana sonka ka kyalleni ka fita daga rayuwana idan kace za ka cigaba da matsanta mun za ka nemi ni karasa, kuma karka yi tsanmani zan tafi Yola uwa duniya zan shiga idan har ka mutu bara ka samu Wanda zai ce ya ganni, ba don haka karka yi wa iyayyena asara ta domin su ne suke min soyayya ta gaskiya ba pretending ba.
   "Dafe kai yayi had'e da furta Omg! Wani tuk'uk'i yake ji a zuciyarshi ran 'yan maza yafara 6aci shi dai gashi ba gwanin surutu ba amma yak'ure malejinshi yadawo tamkar parrot duk don Haleesa ta fahimce irin mugun sonta da ke d'awainiyya da shi takasa fahimta sai wani banza zance da tashigo mishi da shi wai yana ,pretending.
    "Habeeb ya mik'e a sanyaye ya zauna kusa da ita ta matsa da sauri yak'ara matsawa ita ma tak'ara matsawa haushi ya turnuk'e Habeeb ya d'ank'i hannunta yashiga murza yatsunta da k'arfi ihu taje kurmawa da sauri ya had'e bakinshi da nata tsawon lokacin suka, dauka a haka daga bisani yasaketa ya had'e goshinshi da nata yad'anna mata cizo a hanci ta runtse idanunta hawaye, yasoma gangaro mata ban yarda ba yaya Habeeb baka sona yaudara ta ka ke yi za ka cuce ni ne watakila har yanzu da raguwar sona wata a zuciyarka
 Can! K'asan mak'oshi yafurta meyasa bakida tausayi leesa"?
 ''Ko makaho ya dubi zai gano I'm in love with you leesa.
    "Yatsine fuska tayi tace watakil ni  makauniya, ce shiyasa nakasa amincewa da kai.
    "Habeeb ya girgiza kai yace mu ajiye wannan zance a gefen banaso ki amince ki ta kallona a matsayin Wanda baya sonki, don ma kinsamu ina rarrashinki kidaina gani mom tana cewa sai na sake ki fad'a ne kawai take yi don taji dad'in bakinta tasaki nishad'i amma wallahi koda za ta aza mun bakin bindinga aka zan furta mata inasonki ba wai kalma saki ba yanzu ki yi favour d'aya za ki yi min kitash mu tafi hospital a duba min idanu nan naki banaso wani abu yasame ki.
   "Murmushi takacin Haleesa tayi tace ae ba wannan ne karo na farko da  kasaba mari na  idanuna su yi kwancin jini yatsunka su sami muhalli a kumatuna karka damu kanka wannan ba bako bane a wurina
    "Murmushi Habeeb yayi had'e da d'anke yatsunta, uhm...leesa yanzu abunda yafaru almost  3 years ashe baki manta ba"?
  Harara ta zuba masa ta kauda fuska.
  Duk yadda Habeeb yaso Haleesa ta saurare shi tak'i daga karshe ma ta yi mik'e tanufi k'ofar fita da sauri yadawo da ita da kyar ta amince ta zauna.
   "Cikin tsawa tafara magana nace bana sonka yaya Habeeb ka kyalleni kai ka manta irin wulaqancin da ka dinga zuba min eyeee"?
Ko angaya maka banida zuciya a kirjina to ina gargad'inka kafita harkata I don't love you anymore banaso ganinka please stay away from me tak'arasa magana cikin sautin kuka.
   "Habeeb ya ja iska cike da takaici yake kallonta ahalin yanzu kalamai bakinshi suna daf takarewa.
  "Tsawon lokacin suka dauka ba Wanda yak'ara magana Habeeb ya kai dubanshi akan wrist watch d'in hannunshi zaro ido yayi cikin kaduwa yake kallon Haleesa daga bisani yace ki dubi tsawon lokacin da na dauka a d'akinan ina miki magiya wannan kadai bai isa ya gansar da ke inasonki ba.
   "leesa ba abunda nake ba wa mahimmancin irin lokacin domin da yawuce ba zai dawo ba amma gashi throughout ba inda naje ina zube a gabanki ina miki magiya ki ji tausayina leesa kiyafemin.
   "Haleesa ta yi shiru kamar tana nazari daga karshe brain d'inta ya nazarto mata mugunta da za ta yi wa Habeeb yadda za ta yi hurting nashi very badly tad'ago idanunta fuskarta d'auke da wicked smile, tafara magana tana yatsina kamar yadda Habeeb yake mata a da zan amince na kar6i tayin soyayarka amma a bisa sharad'i d'aya ta d'an suke numfashi tana jiran ta ji ta bakinshi.
   "A Rikice Habeeb yad'ago muryarsa na rawa yace menene sharad'in naki"? muddin za ki amince da ni zan iya.
  "Wani shu'umin murmushi Haleesa ta yi tace............


Jeeddah Aliyu
[01/01 1:27 pm] Ruke Ilyasu: [15/12 5:23 pm] aliyujeeddah: ```?NI DA YAYA HABEEB?```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

_this page dedicated to only you my sweet Mrs Umar Billions words can't ever exprees how much I love you  but I wants you to known that Fatee you're very special person to me remember that & always saying KE D'AYA CE FATEE_

              ```93```

~~Ta d'ago da sauri ta dube shi, ta yi fari da ido cike da mugunta tafara magana anyya kuwa yaya Habeeb za ka iya?
    "Murmushi ya yi had'e da lumshe ido wannan ba matsalarki bace, ke dai kawai ki fad'i sharad'in naki matar na tuba ae bata rasa mijin aure.
   ''Ta tabe baki uhm......sharad'in na ba wani mai zafi bane inaso in tabbatar da soyayya da ka ke kirarin kana yi min ta gaskiya ce ko kuma pretending ka ke yi domin kasami damar cigaba da kawarda sha'awarka akaina.
    Da sauri ya kalle ta ya kawar da kai wannan ya ba wa Haleesa damar cigaba da cewa indan har da gaske yaya Habeeb kana sona ba sha'awata ka ke yi ba daga yau karka k'ara zuwa inda nake kuma karka kirani a waya, na har tsawon watanin 3 idan da gaske kana sona za ka iya jure wad'annan watani batare da ka waiwaye ni ba indan kuma sha'awa ce na tabbata kwana d'aya tak ba za ka iya ba batare da ka zo inda nake ba yanzu dabara taragewa mai shiga rijiya za ka iya"?
   "Sai lokacin Habeeb yad'ago ya yi mata, kallo lalle yarinya nan kin zare da mugun mamaki yafurta _3 month_  fa ki ka ce leesa"? Ina laifi ki ce 3 day's su d'in ma zan yi sune adaddafe haba gaskiya I can't do this!
   Haleesa ta ya mutsa fuska idanuta suka ciko da kwalla cikin muryar kukan kissa had'e da shagwa6a tafara magana, ni dama nasan baka sona yaudara na ka ke yi idan da gaske  soyayya gaskiya ka ke mun miye _3 month"?_
  ''Please leesa ki fahimce ni irin son da nake miki ba zai barni na d'aukin tsawon wannan lokacin batare da nayi tozali da kyakyawar fuskarki ba indan nace zan tilassawa kaina hakan zai iya cutar da ni ina miki so na hak'ik'a dai-dai da second 1 banaso na nisata da ke yak'arasa magana cikin sanyin murya.
    "Juya masa baya tayi shikenan yaya Habeeb za ka iya tafiya amma kafin katafi kasani a kowane lokacin za ka iya nema na karasa domin ba zan iya cigaba da zama da mutume da ba zai iya jajircewa akan farin cikina ba Wanda hakan yanuna mini har yanzu zuciyarka tana wasiwasi da soyayyata.
   ''Zuwa wannan lokacin Haleesa tafara k'ular da shi ya mik'e a fusace I can't leesa ni da nake fatar yau d'inan mom tabarki ki koma gidana mu fara shinfid'a kyakyawar rayuwa shine za ki tsiro da wannan shirme"?
  ''Kafin Haleesa tabashi amsa madam Hindu ta turo k'ofa tashigo tana rafka salati cikin kad'uwa Habeeb da Haleesa suke kallonta.
   "Ohh...ohh....son dama har yanzu kana cikin gidanan"? Shine ka kad'a mun yarinya a parlour kai kuma ka zo nan ka kasa ka tsare uban me yashigo da kai nan shin ba nace banaso na k'ara ganin k'afarka a gidanan ba"?
    "Cikin sark'ewar halshe Habeeb yace ni fa ba wani abu ne yashigo da.........
  ''Kai dallah! Saurara wannan tsayin da na tarar da kai kana yi karatu ne ka ke koya mata ko me"?
  Huh......sweetheart hak'uri ne nake bata.
  "Ae yanzu bakada sauran kalma da za ka yi amfani da ita wajen bata hak'uri tajuya wajen Haleesa tace hukuncin da ki ka zantar ya yi mun dai-dai ni anawa ra'ayi so nayi yabani takarda ki kowanenku Allah ya had'ashi da rabonshi.
   "Habeeb ya hadiye wasu yawu masu mugun d'aci yana kallon madam Hindu a tsorace yana mamakin yadda take k'ok'arin shiga tsakaninshi da farin cikinshi, Iya saninshi Sam baya laifi a wurinta, amma sai gashi yau ta zo mishi da abunda bai saba da shi ba.
   ''Daga yau karna k'ara ganin k'afarka a gidanan har sai watanin 3 sun cika maganar madam ce ta katsiwa Habeeb tunani yayinda Madam tacigaba da cewa idan kuwa ka kuskura tsautsayi yasa ka tak'o k'afarka gidanan to kasani a bakin aurenka ko ba haka ba Haleesa"?
  ''Da sauri Haleesa ta gyad'a kanta.
   Habeeb ya yi sororo yana kallonsu Madam ta galla masa harara tace kama hanya katafi cikin zafin zuciya yanufi k'ofa ya bud'e da k'arfi yafice a downstairs parlour ya tararda Hannah tana kallo rankwashi mai zafin gaske ya zuba mata aka _wayyo Allah mom yaya Habeeb zai kashe ni_
  Ke! Munafuka yafad'a a tsawace shiru ko na wanka miki mari duk gargad'in da nayi miki bai shige ki ba da yake ke munafuka ce saida ki ka fad'awa sweetheart ina d'akinki tare da leesa koh"?
   "Allah yaya Habeeb bani na fad'a mata ita ce da kanta tagane.
   Harara ya watsa mata yanuna ta da yatsa yayi kyaci yafita yana huci cikin zafin rai da baqar zuciya yanufi parking lot  ya bud'e k'ofar mota yashiga Bala yagani ya kwa6e seat yasaki Ac yana sharar bacci hadda su dogon minshari.
   Wawan duka Habeeb yakai masa a kafad'a kai! Dallah tashi a rikice Bala ya tashi ya gyara zaman seat yayi  hamma had'e da mik'a cikin murya mai d'auke da alama bacci yace "Boss wai kana nufi duk tsawon wannan lokacin munan gidan"? gaba d'aya na manta da inda nake.
   Hararashi Habeeb yayi yace ae dole ka manta da inda ka ke saboda hankalinka a kwance yake jiya-jiya ka yi wa motar nan ''full tank dubi yadda fuel ya yi k'asa ka k'ure Ac kana sharar bacci abinka ni kuma ina cikin gida ana mun barazana da rayuwa.
   "Tuni Bala ya watsarke ya zaro ido boss wane mai k'arare kwana ne yake maka barazana da rayuwa"?
    "Tsaki  Habeeb yaja yace kai banaso shirme banza ja mota mu tafi Bala ya yi wa mota key yanufi gate maigadi ya wangame musu gate suka fice.
   "Madam ta dubi Haleesa tace ina mai k'ara baki hak'uri akan abunda son ya yi miki Haleesa shiyasa nakeso, ki yi amfani da damar da Allah ya ara miki kema ki rama abunda "son yadad'e yana miki.
    "Murmushin  jin kunya Haleesa ta yi tace tun jiya ki ke ta bani hak'uri mom har kinsa nafara jin kunyarki.
    Madam tayi murmushi had'e da rik'o hannun Haleesa tace tsakanina da ke ba, jin kunya Haleesa ni fa tamkar mahaifiya ce a gare ki shiyasa nake gargad'inki kada ki yi sauri ba wa ''son fuska har sai yagano shayi ruwa ne.
   ''Haleesa tayi murmushi had'e da sadda kai k'asa.
 Madam tajuya da murmushi tafita Haleesa ta yi ajiyar zuciya ta koma ta kwanta, ta lumshe idanu wani irin dad'i yana ratsata.

_3 days later_
Habeeb na kwance a parloun'shi kwanaki 3 kacal har yafara fita hayyacinshi bashi da aikin yi sai tunani gaba d'aya duniya tayi mishi qunci yanaso zuwa gidan madam yana tsoro kada allura ta tono galma.
   Mus'ab da Bala suka shigon parlourn sai faman kyalkyalar dariya Mus'ab ya zauna kujera da ke facing d'in Habeeb yayinda Habeeb ya watsa masa mugun kallo ya mik'e zaune wai kai Mus'ab wane irin marar imani ne kai"? Na kira ka ne don kanema min mafita inason matata ba zan iya jure tsawon watani 3 batare da na ganta ba yak'arasa magana cikin murya tausayi.
   Mus'ab ya dube Bala suka wani zaro ido kowanensu ya yi murmushin shak'iyanci  A fusace Habeeb yafara magana wannan wane irin iskanci ne ya ina muku magana kuna mini murmushin munafuncin gaba d'aya Ku na fahimcin farin ciki Ku ke yi da wannan hali da na shiga yayinda Habeeb rufe ido yadinga  zazzaga masifa saida yagaji don kanshi ya yi.
    Mus'ab ya hadiye dariyarshi yana mamakin zafin kan Habeeb shi dai komai da zafi yake d'aukarsa yanzu Wanda yake cikin wannan hali ina yaga bakin fad'a da wani.
  ''Tsanm.....Mus'ab ya mik'e yanufi kusa da Habeeb ya zauna yadafa kafad'arshi calm down abokina irin wannan tada jijiyoyin wuya har ina"? Yakamata kasawa zuciyarka salama ka sausautawa kanka wannan saurin fushi domin ba inda zai kai ka.
  "Habeeb ya d'age gira ta kasan ido yake kallon Mus'ab daga bisani ya ja iska yace kaga malam za ka nemo min mafita ko kuwa"?
   Girgiza kai Mus'ab ya yi yace akwai mafita guda d'aya chal, yanzu abunda nakeso da kai  katashi kayi wanka peter ya had'a maka abinci ka ci domin Bala ya gayamin kwanaki 3 rabonka da ka ci abinci mai nauyi daga coffee sai Lipton ka ke ta faman, d'urawa cikinka.
   Yatsine fuska Habeeb ya yi yace uhm....kai kana gani ina da kwanciya hankali da zan iya cin abinci"? malam kawai kafad'a min mafita d'in.
  Mus'ab ya tabe baki yace ba zan fad'a ba har ka yi abunda na umarce ka da shi.
  Habeeb ya yi ajiyar zuciya batare da ya tankawa Mus'ab ba ya tashi tsaye har yajuya Mus'ab yace jimana Lamido"! Habeeb ya tsaya cak yajuya yana tsotsa baki kamar yana shan sweet ya akayi ne.
   "Cikin tsokana Mus'ab yace Allah yasa bakajin kashi domin nasan halinka indan har ka hau toilet seat za ka iya d'aukar dogon lokacin baka fito ba ni kuma sauri nakeyi Hannah darling na jirana zan fita da ita unguwa.
    "Dogon tsaki Habeeb ya ja kamar zai gutsire halshenshi ya yi kwanfa had'e da juyawa yanufi bedroom d'inshi Mus'ab da Bala suka kwashe da dariya Bala ya tsagaita da dariyar da yake yi yace gaskiya wannan leesa ta rikita boss da yawa har wani sanbatu yake yi kamar mai ta6i hankali yana k'arasa magana shi da Mus'ab suka k'ara kwashewa da dariya.
  ''Mus'ab yace kaga malam Bala abunda yafi bani dariya a duk lokacin da na tuna da wani furucin da Lamido yake min _Mus'ab kadaina 6ata lokacin a soyayya kanemi k'udi domin sune magani kowace irin matsala bai wai kadinga kashe lokacinka a shirme banza da wofi soyayya ko 6ata lokacin_
  Mus'ab na dasa aya suka k'ara barkewa da dariya sai kace wani abun farin ciki ne yasame su.
  "Habeeb na fitowa daga wanka ko kaya bai saka ba yanufi parlour sanye da bathrobe Bala da Mus'ab suna daura idanunsu akanshi suka k'ara bud'e Sabon babi na dariya.
   '' cikin angry voice yace yadaka musu tsawa wannan wane irin wulaqancin ne"?
Ya za'ayi Ku mayarda ni kamar wani mahaukaci tun d'azu Ku ke ta faman yi min dariya, gaba d'ayanku Ku tashi Ku fita min daga parlour I don't whats you help yak'arasa magana cikin shouting fuskar nan tayi jajir kamar Jan k'osai{lol}.
  Bala ya mik'e sannu alaikum yafita Mus'ab ya kasa control dariyarshi a zuciye Habeeb yajuya kamar zai tashi sama ya haura staircase yana shiga bedroom yafad'a bisa gado ya runtse idanunshi hawaye na zuba yafara magana shi kadai kamar mai Sabon hauka _how couldn't you this to me"? Kinga ni ko leesa Mus'ab da Bala suna min dariya suna mini kallon mahaukaci tabbas ni mahaukaci ne a sonki I'm crazy about you don't make my life miserable I beg you leesa please come back to me_
  "Tsawon lokacin yadauka cikin mayuwacin hali daga bisani ya mik'e ya sanya kayanshi ba zance Shafa mai.
Duk wata hanya da Habeeb yasan zai bi don yasami gani Haleesa ko yaji muryarta abin ya faskara a takaice yarasa mafita zafin kanshi yak'ara k'aruwa tun yana kiran madam a waya yana magiya har yagaji yadaina in yakira Hannah tak'i picking, cikin d'an k'ank'anin lokacin Habeeb yadawo abin tausayi.
 
_2 weeks later_
Habeeb yana kwance a bedroom d'inshi sai fama rawan sanyi yakeyi hak'ora shi na had'ewa Bala yashigo ya durk'usa gabanshi yasa pity face Dan Allah boss kayi hak'uri ka barni na kira Dr saleem ya duba ka.
   "A harzuk'e Habeeb ya gallawa Bala harara banaso kuma ina gargad'inka kada ka k'ara zuwa inda nake ku barni na mutu.
  "Bala yadafe kai yak'ara yi  k'asa da murya yace boss ko na kira madam a waya na fad'a mata halin da ka ke ciki"?
   ''Kada ka sake ka fad'a mata nafiso sai na mutu akai Mata gawa na Bala ya mik'e a sanyaye yafita tausayin Habeeb ya lullu6enshi nan take wani tunani yafado mishi yanufi parking lot yaja mota da k'arfi yafita.
  "Direct gidan madam Hindu yanufa a parlour yatarar da Haleesa da Hannah suna kallo Indian movie ya yi sallama yanemi kujera ya zauna idanunshi sun kad'a sunyi jajir ya dube Hannah yace Hannah madam tana nan kuwa"?
  Batanan ta tafi Lagos d'azu da safe lafiya Bala naganka a rikice"?
  Cikin raunin murya yace a gaskiya hukuncin da aka yankewa boss ya yi tsauri da yawa yau tsawon sati 2 kenan baya cin abinci yadaina walwala bacci ya kauracewa idonshi shin waye baya kuskure a rayuwa"?
  Haleesa ta zaro ido numfashinta na fita da sauri-sauri.
  Bala yacigaba da cewa a halin yanzu boss bashida lafiya sosai ya hanani na kira Dr ya duba shi indan wani abun yafaru da shi Haleesa kece sila.
  "Haleesa ta mik'e tsaye ta rikice iya rikicewa tafashe da kuka Hannah ta mik'e tadafa kafad'arta ba kuka za ki yi ba mayafi za ki dauko mu je mu gw hali da yake ciki da gudu Haleesa tajuya tanufi bedroom Hannah ta Mara mata baya ba su wani jima ba suka fito.
  Akan hanya Bala yake basu labarin irin mayuwacin hali da Habeeb yashiga suna isa gidan tun kafin yagama parking Haleesa ta balle k'ofa tafita...

Jeeddah Aliyu
[01/01 1:27 pm] Ruke Ilyasu: [16/12 6:20 pm] JeeddahAliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

_Double sorry fans yau banyi typing da yawa ba Ku yi managed da wannan_

              ```94```

~~Hannunta na rawa ta murd'a k'ofar d'akin Habeeb ta hango shi dunk'ule yana rawan sanyi mamaki ne yarufe Wanda ke jin Sanyi zai kai shi da kunna Ac ga kuma blanket a gefenshi ajiye  a maimakon ya yi amfani da shi ya rufawa jikinshi tsabar zafin kai yasa ko kallo blanket d'in bai isheshi ba.
   "Haleesa ta girgiza kai tanufi Ac tayi switch off batare da yajuya ba yasoma masifa banaso damuwa Bala ba nace karka k'ara zuwa inda nake ba"? Shine don wulaqancin za ka kashe min Ac.
  "Sai lokacin Bala da Hannah suka k'araso suka ta tattara da Haleesa tsaye tana rabon idanu, Hannah ce tanufi wajenshi ta durk'usa saitin fuskarshi idanunshi a rufe ta yi k'asa da murya ta hanyar cewa sannu yaya Habeeb"!
   ''Sautin muryarta ce tayi sanadin da ya bud'e idanu, harara yafara zuba mata me yakawo ki wurina"?
  Yaya Habeeb z....shut up ya katsi ta bakida wani amfani da za ki yi min anan ki tashi ki kama gabanki
"I'm sorry Yaya Habeeb nasan za ka ji zafina sosai amma wallahi ba laifi na bane mom tace ko ka kira phone d'ina kada na d'aga domin tasan dalilin Haleesa ka ke kira amma ka yi hak'uri a kira Dr saleem ya duba ka zama da ciwo ba shi bane solution d'in matsalarka.
    "Tsaki Habeeb ya ja cike da takaici yace a
 tunani Hannah koda sweetheart da leesa sun had'e min kai ke za ki ji tausayina ashe kema bakyaso na.
   ''Wallahi ina sonka yaya Habeeb karka kamanta tun lokacin da muka rasa mahaifin mu kai ne ka maye mini gur6inshi.
   "Habeeb ya yi shiru kamar mai nazari daga bisani yafara magana cikin murya mai ban tausayi Hannah inason Leesa sosai amma ita batasona ta tsaneni Hannah ki gayamin yadda zan yi Leesa tasoni.
   ''Hannah ta mik'e ta zauna kusa da shi har zuwa lokacin baisan cewa Haleesa tana cikin d'akin ba saboda ya ba wa k'ofa baya.
   "Yaya Habeeb kadaina wahalarda kanka saboda Haleesa tana sonka kamar yadda kaima ka ke sonta tuni guguwar sonka tayi nasara tafiya da ita duk abunda take yi maka tana yi a dalilin irin wulaqancin da kadinga yi mata ni sheda ce akan irin matsanancin son da Haleesa take maka yaya Habeeb.
   " A rikice Habeeb ya mik'e zaune yarik'o kafad'ar Hannah ya girgiza ta da k'arfi "omg! I can't believe  da gaske ki ke yi Hannah Leesa tanasona ko kuma kina ne don kawai ki faranta mun rai"?
   ''Da gaske nake yi yaya Habeeb Leesa tana sonka ko ranar da ka mare ta zancenka ne mu ke yi ba na margayi yaya Habeeb ba tuni ka ture gwannatin margayi yaya Habeeb a zuciyar Haleesa.
   "Habeeb ya rud'e yarasa indan zai jefa kanshi don dad'i nan take farin ciki ya mamaye shi yace ta ya ya zan amince da abunda ki ke fad'a gaskiya ne"?
    "Hannah ta yi murmushi ta juyarda fuskar Habeeb zuwa  da Haleesa take tsaye zaro ido Habeeb ya yi tamkar ya ga abun tsoro muryarshi a sark'e ya furta Hannah da gaske Leesa ce nake gani ko kuma gizo take mun"?
   ''Ba gizo bane a zahiri ka ke ganinta. Habeeb ya washe hak'ora kamar gonar auduga yak'ara mayarda ganinshi wurin Haleesa wance ta sadda kanta k'asa hawaye na zuba daga idanunta.
   Cikin tsananin farin ciki Habeeb ya rungume Hannah yayinda Hannah keta faman yi mishi dariya.
   ''Haleesa tad'ago had'e da share fuska ta dubi Bala tace Bala kira Dr ya duba shi.
  Da sauri Bala yaciro waya gaban aljihunshi ya kira Dr saleem.
  'Hannah ta mik'e tana dariya tanufi wurin Haleesa ta rad'a mata wannan tsayin na menene"? ki k'arasa wurinshi mana yad'an ji d'umin jikinki tak'arasa magana had'e da ficewa.
  ''Haleesa ta zaro ido tabi ta da kallo daga bisani tajuya ta dube Habeeb suka had'a ido kasa d'auke idanunta tayi akanshi wani irin kwarjini ya yi mata.
   ''k'ayatacen murmushi yasake mata, ta lumshe idanu ta koma jikin bango talafe Habeeb yayi k'asa da murya yace zo ki ji Leesa naa"!
  ''Mak'e kafad'a ta yi had'e da turo baki.
   "Ni koh"?
''Eh! Kai! Tafad'a tana murgud'a baki.
Habeeb ya langwa6e kai yana kallonta ya mik'e da kyar jiri yana d'ibarshi yanufi wajenta hannunshi ya aza a har6arta yad'ago fuskarta da sauri ta runtse idanunta gam... Leesa abunda Hannah tafad'a min gaskiya ne ni anan"? yana magana ne had'e da aza hannunshi a k'irjinta.
  "Yarrr..... Haleesa taji tak'ara runtse idanunta Habeeb ya yi murmushi yarad'a mata _I love you leesa"!_
  A hankali Haleesa ta ware idanunta akan kyakyawar fuskarshi wani irin kunyarshi take ji ta ture hannunshi ta ra6a gefenshi za ta wuce ya rik'o hannunta kamar za ta yi kuka tace yaya Habeeb ka je ka kwanta naji jikinka da zafi sosai kafin Dr saleem ya zo ya duba ka.
  ''Leesa ke ce magani ciwona ganinki kadai ya ye mini duk ciwo da nake ji a jikina yanzu kin yarda inasonki ba pretending nake yi ba"?
   Murmushi ta yi had'e da gyad'a kai.
  "yasaki Hannunta ya ware hannayenshi  yace _oya come here & give me a big hug_
  Cikin jin kunya ta girgiza kai tana murmushi.
  "Leesa please"! Yafada kamar zai yi kuka a kunyace tanufi fad'add'e k'irjinshi tashige ya rungumeta tsanm.....kamar zai shigarta da ita cikin k'irjinshi yashiga sinsinar k'amshinta daga bisani ya lalla6o bakinta ya had'e da nashi karo na farko da Haleesa taji tanaso tanunawa Habeeb ita ma fa takamu ta zira mishi halshenta gaba d'aya Habeeb yarud'e tsayuwa tagagare shi gani haka yasa taciro bikinta daga nashi tanufi gefen gado ta zauna tana kare fuskarta da tafin hannunta.
   "Habeeb yana murmushi yanufi wajenta ya zauna yacire hannayenta daga fuskarta cikin tautasan lafazi yafara magana _Leesa inasonki sosai kece farin ciki ruhina, kece annuri zuciyata a lokacin da ki ka juya min baya sai naji kamar zan yi hauka I love you so much Leesa"_
   "Dad'i ya lullu6e Haleesa ta yi wani fari da idanu cike da jin kunya tace _I love you too my Handsome don_
  "Kyakyawar runguma Habeeb ya yi mata da kyar ta zare jikinta daga nashi ta janyo masa pillow yaya Habeeb please ka kwanta.
  Ture pillow ya yi bana kwanciya akan pillow leesa amma zan iya kwanciya anan yana magana ne had'e da aza kanshi a cinyoyinta.
  "A hankali take Shafa sumar kanshi knocking akayi Haleesa tashiga ture kan Habeeb yayinda yak'ara gyara kwanciyarshi a jikinta ba yadda ta iya dole ta zuba masa ido a haka Dr saleem Yashigo yatarar da su yashiga duba Habeeb fad'a yayi masa sosai akan yarage tunani kuma yadinga cin abincin daga bisani yace Bala ya biyo shi ya kar6o magani, Hannah da ke tsaye a gefe tace Zan bi Bala ya ajiye ni a gida da sauri Haleesa tace ni fa"?
  "Ke kuma ki zauna ki kula da mijinki har sami sauki"
  "Habeeb yace kinga Hannah yi tafiyarki kyalleta kawai so take ta 6ata mun rai.
  Hannah tana dariya tafice Habeeb yak'ara shigewa jikin Haleesa ture shi tayi ta kwanta kusa da shi ya matsa ya aza kanshi bisa cikita yashiga zuba mata hira mai dad'i hannunta na cikin sumar kanshi tana ya motsawa.

_some hours later_

Cikin shagwa6a Haleesa take magana wai yaya Habeeb kana nufi anan zan kwana"?
  "Ae ya ma wuce wai my Leesa ke yanzu in na barki ki koma chan gida ae ba za ki iya bacci mai dad'i ba.
  Ni gaskiya tsora nakeji kada mom tagane.
  Ba za ta gane ba my Lessa please karki tafi ki barni kinji"?
  Shikenan zan kwana amma gobe da sassafe Bala zai maida ni ka amince"?
  "Uhm.....na amince yafada had'e da Jan karan hancinta ya mik'arda ita tsaye yace bacci nakeji leesa mu je mu yi wanka"
  "Ido ta zaro uhm.....uhm...ka je ka yi wankanka nima nayi nawa.
  Cak.....yadauketa yanufi bathroom da ita sai faman yi mishi magiya take ya ajiye ta ya yi biriss.... Da ita yadireta cikin bathtub.....

Jeeddah Aliyu
[01/01 1:27 pm] Ruke Ilyasu: [17/12 4:44 pm] JeeddahAliyu?w: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```95```

~~ihu taje kurmawa ya toshe mata baki da hannunshi yacire kayan jikinshi yashiga bathtub yana lek'e fuskarta da ta tufe da tafin hannunta da k'arfin tsiya yashiga cire mata kaya wanka da za'ayi cikin d'an k'ank'ani lokacin amma saida suka share tsawon lokacin suna wasa da ruwa sai kace k'anana yara.
   "Habeeb yarigata fitowa daga bathtub idanuta na rufe ruf ita a dole kunya take ji towel ya mik'a mata sannan yafita tafito daga bathroom tana kare fuska kasa karasawa cikin d'akin ta yi.
    ''Ta ciki mirror Habeeb ya hangota tsaye ya ajiye, comb d'in hannunshi yanufi wajenta, towel d'in jikinta ya ja a rikice ta ware idanuta masu d'auke da tsoro.
  Kyakkyalewa da dariya ya yi har yana dafe ciki Haleesa ta yi sororo hannunta na dafe da towel d'in jikinta tana masa kallon mamaki.
 ''Ya tsagaita da dariyar da yakeyi still fuskarshi na d'auke da murmushi yace ya akayi ne 'yan matanaa naga kin kura min ido"?
  ''Murmushi ta yi had'e da juyawa tanufi dressing mirror tace dariya tana matuk'ar k'ara maka kyau yaya Habeeb kadinga dariya kadaina wannan had'e da fuska da ka ke yi.
   ''Yana murmushi yak'arasa daf da ita ya rungumeta ta baya suna hango fuskokinsu  cikin mirror _soyayyarki ce ta yi nasara canza ni har nake iya dariya Leesa ke Alkhairi ce a rayuwana banta6a zan tsanmani zan so wata 'ya mace ba sai gashi kin shigo rayuwana kin dasa min sonki da k'aunarki a zuciya ban tabbata da sonki ya mun Illah ba sai da ki ka juya mun baya nadaina jin Qamshinki nadaina jin d'umin jikinki I miss your hot body_
  Murmushi Haleesa ta yi ta mik'a hannunta tattaro jik'ak'en sumar kanta ta yarfa masa a fuska da sauri ya lumshe idanu, tace Uhm.....ba ma ni kayi missing ba koh"?
   Juyo da ita yayi suna facing d'in juna cak yad'aga ta ya zaunarda ita akan mirror I absolutely miss you my Leesa"!
   "Ta turo baki cikin shagwa6a tace _I miss too my handsome don_
  " ya kashe mata ido d'aya very slowly yafurta da gaske"?
  "Gira ta d'aga mishi
  _Oya shown me baby you miss me_ peck tayi mishi a goshi  yatsine fuska yayi No.....Leesa ba irin wannan ba.
   Tak'ara masa wani a kumatu ya ka ji wannan"?
  "Shi ma bai yi ba yafad'a yana 6ata fuska
  Zaro ido ta yi had'e da cewa uhm.....uhm...ni ka saukeni na shafa mai.
     ''Saida ya sumbace lips d'inta sannan yasauketa yanufi gefen gado ya zauna yana aikin kallonta, ta Shafa lotion a fatarta ta kwashe sleeping dress d'inta tanufi bathroom Yayinda Habeeb ya bita da dariya.
   "Tana fitowa ya kafeta da ido yi tayi kamar bata ganshi ba tanufi mirror tad'auki perfumes tafashe logun da sak'o na jikinta ta yi tsaye jikin mirror tana kallon Habeeb tana murgud'a baki.
    ''Zo ki ji Leesa naa!
  Harararshi ta yi had'e da mak'e kafad'a ya mik'e tsaye yanufi wajenta tun kafin yakarasa tafara ihu _Wayyo yaya Habeeb karka ta6ani Allah banaso_
In ke bakyaso ni inaso ya sunkuce ta sai ihu take tana zillo k'afafu ya jefata bisa gado ya kashe light.
   "Dare ranar sai ya zamewa Habeeb tamkar shine first night d'insu saboda da amincewa Haleesa suka raya daren sa6ani first night d'insu da shi kadai ya yi kid'ansa ya kuma taka rawarshi.

_8:00am_
Habeeb ya falka yashiga tashe da Haleesa ta bud'e idanuta da kyar saboda baccin bai isheta ba tak'ara shigewa jikinshi cikin muryar bacci tace ni kabarni nayi bacci na.
   wane irin bacci kuma Leesa"? Kinsan yanzu karfe nawa kuwa"?
  Oho....ni bansaniba ka kyalleni nayi baccina"!
  Yacire ta daga jikinshi yanufi bathroom ya yi wanka baya buk'ata yin alwala domin wankanshi na had'e da alwala yafito sanye da bathrobe kaitsaye ya sunkuce ta sai tsintar kanta ta yi cikin bathtub ihu ta kurma had'e da wartsakewa.
   "Habeeb yana dariya ya dungure mata kai oya ki yi wanka idan ki yi sallah sai ki kwanta ki cigaba da baccin naki sleeping sickness kawai yana magana ne had'e da fita daga bathroom d'in.
 
_15 minutes later_

Haleesa tana tsaye gaban dressing mirror tana make up duk abunda take yi Habeeb yana mik'e akan gado yana kallonta yana murmusawa abinsa ya cize lips d'inshi na k'asa ya lumshe idanu shi kadai yasan mugunta da yake shirya mata.
   "Ta cikin mirror ta hangoshi yana murmushi tabe baki tayi tace wai wannan murmushi na menene"?
  ''Kashe idonshi d'aya ya yi yace na sonki ne.
  Huh.....I see tafad'a had'e da k'ara tabe baki ta d'auki veil d'inta mahadin baqar Jallabiya da ke sanye a jikinta ta yi rolling sannan tajuya ta dube shi tace "my handsome am ready call Bala to pick me up.
  ''Okay...yafad'a had'e da danna waya yakara  a kunne yashiga magana Bala wai ina kashiga ne ga Leesa tana jiranka ka maida ta gida"?
  Ya d'an yi shiru daga bisani yace what's! Kana nufi baka dawo bane"? shikenan ka yi sauri please tana jiranka kasan banaso 6acin ranta. Yak'arasa magana had'e da kashe wayan yajuya ya dube ta yace Bala bayanan yafita zai dawo nan da 4-6 hour's.
   Whats 4-6 hours gaskiya I can't wait tak'arasa magana had'e da yatsine fuska.
  "Ya tabe baki tell me yanzu ya ki ke so ayi"?
 ''Taxi zan bi tun da kai ba driving ka iya ba balle ka kaini.
   "Murmushi ya yi yana kallonta ta k'asan ido
  "My handsome bani k'udin taxi na wuce Allah na matsu na bar gidanan.
  Harara ya zuba mata banida k'udi sai kitafi a 'kafa.
  Murmushi ta yi tace "you most be joking tanufi bedside inda wallet d'inshi yake ajiye takai hannunta za ta d'auka shima yakai hannunshi cikin zafin nama tariga shi d'auka tana dariya ta 6alle wallet din.
  "Leesa karki sake ki bud'e min Wallet kinji koh"?
  Gwalo ta yi mishi tak'arasa bud'ewa taciro 5k ta mayarda wallet d'in inda ta d'auko ta sunkuya ta yi pecking lips nashi I've to go my handsome ka tabbata ka yi taking medicine naka in time nasan halinka da rashin son magani ka ci abinci sosai is that clear"?
   "Ya ja karan hancinta yana murmushi yace yes ma!
  Ya tashi zaune yarik'o hannunta yana mata kallo mai cike da zalla so in a cool voice ya furta thank you very much leesa for your love & care!
   "It's my pleasure. duk lokacin da mom tasake tafiya I will surely get back to you okay"?
  "Okay my love am gonna miss you"
  Me too tafad'a kamar za ta yi kuka tajuya har takai k'ofa ta tsaya tajuyo yana zaune yana kallonta still fuskarshi d'auke da murmushi rass-rass gabanta yafad'i tashiga tunani what's does means he said he wanna miss me but now he's was smile"?
  "I thinks there has something wrong with this guy cike da fargaba tace yaya Habeeb are you okay"?
  "Yes am absolutely fine
   Tayi ajiyar zuciya tace bye take care ta bud'e k'ofa tafita yad'aga murya yace you too baby  ya kwanta yadauki phone d'inshi kira number Bala yakara a kunnenshi _Bala ka yi gudun bala'i ka je d'akin Rahul da Rita kafito da su ka kawo su dai-dai k'ofar fita main palour kasake su_
 Banaso tambayar banza kaje ka yi abunda nasaka. Ya yi hanging up yana murmushi
 "Haleesa tana jefa k'afarta waje taci karo da black police dog's sai fama zazzago halshe suke  yawu na zuba wani d'an uban tsalle tadaka had'e da zunduma ihu tajuya parlour da gudu yayinda dogs d'in suka Mara mata suna "barking ihu take had'e da kwad'awa yaya Habeeb kira a rikice ta haura staircase a hargitsi ta afka d'akin Habeeb ta rufo k'ofa da k'arfi.
    ''Habeeb da ke kwance da sauri ya rufe idanu kamar mai bacci yana dariya k'asa- k'asa saboda yasan tsiyar da ya qula mata.
   "Da gudu tafad'a kanshi ta k'amk'ame shi _Wayyo Yaya Habeeb wa'annan 'yan Iskan karnuka za su cinye ni_
  K'ara rungumeta ya yi yace oh! sorry baby ki barni da su sai naji dalilin da yasa suka tsorata mun ke.
  ''Ba wani dalilin kawai ka fitarda su daga gidanan narasa laifi da nayi musu suka tsaneni ko Imaan da ke yarinya k'arama basa yi mata barking sai ni da suka rena ni dai kafitarda su tak'arasa magana tana hawaye.
  "Habeeb ya hadiye dariyarshi yace gadi suke min baby kinga kuwa bai kamata na fitarda su ba.
  Harara ta galla masa duk wad'annan securities da ke gidanan ba su isa gadi ba sai Wa'annan bak'ak'e"?
  Murmushi ya yi suna da amfani sosai bagashi yanzu sun koro mun ke kinga sai ki cigaba da jinyar mijinki.
  ''Tasa mishi Kukan shagwa6a haba yaya Habeeb kana nufi zan k'ara kwana anan"?
  "To meye a ciki dan kin k'ara kwana anan"?
"Mom nake tsoro kar taji labari na zo wajenka.
  Kidaina jin tsoro Sweetheart ba za ta dawo ba sai nan da
3 day's.
  A shagwa6e tace uhm..uhm...ni ban yarda ka tashi ka rakani
   Haba! My Leesa Dan Allah ki yi hak'uri ki zauna kinga hankalinmu a kwance cikin 3 day's d'inan za mu sha soyayarmu kafin sweetheart ta dawo ta datse mana jin dad'nmu.
  Hmm...Haleesa tafad'a had'e da kai mishi duka ya kyalkyale da dariya phone d'inshi ya yi ringing yadauka yakara a kunnenshi yace _Hello Maryam_
  "Rass....gaban Haleesa yafad'i nan take ta tuna da yadda ta ta6a ganin Habeeb da Maryam a Sokoto wani irin kishi ya lullu6e ta ta mik'e da k'arfi tanufi k'ofar fita.......

Jeeddah Aliyu
[01/01 1:27 pm] Ruke Ilyasu: [19/12 12:39 pm] Jeeddah Aliyu: ```?NI DA  DA YAYA HABEEB?```
_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```96```
 
~~Ta bud'e k'ofa tafita da mugun mamaki Habeeb ya bita da kallo ya mik'e da sauri ya bi bayanta a parlour yatarar da ita ta kifa kanta a hannun kujera tana shasshek'a kuka a rikice ya furta _Maryam I'II call you later_ batare da ya jira jin abunda Maryam za ta fad'a ba ya yi hanging up jikinshi na rawa ya zauna kusa da ita ya rungumo kafad'arta, tashiga ture shi in tears tafara magana _don't touch me kai mayaudare ne yanzu nan ka gama tsara ni kana fad'ar I'm the only woman you love shine don wulaqancin da kwarewa da yaudara in front of me kana cheating nawa_
   Zufa ta soma tsattsafo wa Habeeb in shock yake kallonta da kyar ya tattaro yawun bakinshi ya yi nassara lalla6o kalma da zai furta mata Leesa please karki d'aga mun hankali akan abinda bakida tabbacin akansa ki yarda da ni nothing between us banta6a son Maryam ba kuma bana tunanin zan so ta.
   "Ta galla masa harara baka sonta amma naganka kana, tsotsar bakinta.
   Zaro ido yayi karki yi mun sharri Leesa Maryam fa Qanwata ce Kamar Hannah take a wurina me zai kaini da bakinta"?
   Cikin murya ta kwashe lokacin da taganshi da maryam a Sokoto yana busa mata ido Wanda har tayi tunani sumbatar ta ne yake yi.
   "Dariya sosai Habeeb ya yi gani yadda yake dariya yasa tafashe da kuka mai k'arfi gaske da sauri ya hadiye dariyarshi ya rungume ta yana bubbuga bayanta cikin rarrashin ya sanarda ita abinda yafaru tsakaninshi da Maryam.
  "Ba wani photo boyfriend d'inta da za ta nuna maka sau nawa tana kashe min gargad'in akanka.
  "A da kenan amma a yanzu yayanki ya yi nassara saye zuciyarta Leesa Maryam yaya salman takeso, saidai Hajiya khareema tak'i amincewa a cewarta 'yarta ba za ta aure talaka ba.
    Mamaki ne lullu6e ya Haleesa tad'ago daga jikinshi yaya salman fa kace"?
  Gyad'a mata kai yayi yace ni kaina lokacin da ta gwada min pic nashi nayi mamaki, sai take fad'a min wai d'ikin takai shagonshi anan suka had'u har suka qula soyayya da na sanarda ita cewa yayanki ne sosai kunya ta lullu6e ta tadinga rok'ona kada na sanarda ke.
   Da kaina naje gidansu wajen Hajiya khareema na rok'eta tabar Maryam ta aure Wanda takeso tun da ta hak'ura da ni da kyar na shawo kanta ta amince a halin yanzu Maryam in-law d'inki ce don haka kidaina kishi da ita Habeeb Lamido naki ne ke kadai.
   Yak'arasa magana had'e da d'ago fuskarta halshenshi yasa ya tsotse hawaye kumatunta banaso na k'ara gani hawaye akan wannan kyakyawar fuska.
    "Ta yi murmushi had'e da 6oye fuskarta a k'irjinshi.

_some hours later_

Habeeb yana kwance akan kujera Haleesa tana tsaye wajen k'afafunshi ta na Jan k'afafun nashi da k'arfi tana magana cikin shagwa6a ni fa ba zan
 yarda ba sai ka goya ni katashi ka goya ni nace tak'arasa magana cikin ihu.
   "Habeeb ya mik'e zaune yatsunshi yasa toshe kunnenshi yana dariya ta k'asan ido yake kallonta yace Leesa please ki barni na huta mana ni narasa dalilin da yasa ki ka zama stubbornly"?
   "Kukan shagwa6a tasa mishi babu shirri ya duk'a ta dalle bayanshi yadinga zagaye parlour da ita suna kyalkyalar dariya abinsu rayuwa ta yi musu dad'i a koda yaushe za ka, tararda su manne da juna ko kitchen Haleesa tashiga Habeeb yana rungume da ita har ta kamalla musu girki, ita kanta Haleesa wasu lokuta tana mamaki yadda Habeeb Lamido yake haukar sonta.
   Cikin kwanaki 3 kacal so da shak'uwa mai k'arfin gaske yashiga tsakaninsu, har basa son dai-dai da 1 second su nisanta da juna.

_Monday morning_
{ around 9:30am}
      "Leesa yanzu tafiya za ki yi barni"? Habeeb Yafad'a kamar zai yi kuka.
  "A sanyaye ta zauna kusa da shi tarik'en hannunshi, nima ba'ason raina zan tafi na bar ka ba saidai tafiya ya zame mini dole.
  "Ba dole bane Leesa in kinso za ki iya zamanki ba abunda sweetheart za ta yi ita kanta farin ciki za ta yi in tadawo ta tarrarda mu a tare.
  ''Tabe baki tayi ni dai wannan abin kunya ba da ni ba sai ka jira har zuwa lokacin da mom taga dama tadawo maka da ni.
   Shikenan ni dama can! Nasan ba wani damuwa ki ka yi da ni ba ae sai kitashi na mayarda ke yana magana ne had'e da mik'ewa tsaye.
   Girgiza kai ta yi ta mik'e tsaye tak'ara rik'on hannunshi karka yi, fushi da ni my handsome don ba zan iya tsallake umarnin mom bane.
  Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba ya wani kauda fuska shi kadai yasan irin rad'ad'i da yake ji Sam bayaso abunda zai nisata shi da ita.
    A shagwa6e tace my handsome don bakace komai ba naga ka wani kauda fuska kamar bakaso kallona"?
   "Ya ja iska had'e da zare hannunshi daga nata, da sauri tafad'a k'irjinshi tasa mishi kuka duk duniya ba abunda ya tsana irin kukanta a rikice yad'ago fuskarta Leesa please kidaina banason kukanki yana d'aga min hankali ki barni da naji da kewarki.
  To ba kai bane ka yi fushi ni kuma banaso fushinka, tak'arasa magana cikin muryar shagwa6a.
 Yatsashi yasa ya zagaye lips d'inta daga bisani ya lalla6o bakinta ya had'e da nashi, tsawon lokacin suka dauka manne da juna daga bisani Haleesa ta zare jikinta daga nashi tanufi k'ofar fita ya Mara mata baya.
  "Direct parking lot suka nufa Habeeb ya kwadawa Bala kira Bala da ke zaune a main gate ya amsa had'e da tasowa yanufo wajensu.
  "Kai Bala bani car key zan kai 'yar yarinya nan gida gaba d'aya tafitine ni da rigima yak'arasa magana had'e da dungure mata kai.
  ''Tsalle Haleesa ta daka ta dire a gefe d'aya tana zarar ido cab...... Wa za ka kai gida"? In ka ganni lahira kaini akayi.
  Habeeb da Bala suka tintsire da dariya, cikin muryar dariya Habeeb yace kinta6a gani Wanda yakai kanshi lahira"?
  Karaf Bala ya kar6e zance ta hanyar cewa wai kina nufi ki ce boss bai iya driving bane"?
  Haleesa ta watsawa Bala harara tace ae ya wuce wai Bala yak'ara kwashewa da dariya.
  "Barni da ita Bala kawai bani key"
  "Bala yaciro key daga cikin ajihunshi ya mik'awa Habeeb ya kar6a yanufi mota kirar Benz baqa wulik da ita sai shak'i take ya bud'e yashiga, yad'aga murya yace ke zo mu je karki 6ata mun lokacin ba yadda ta iya dole ta bud'e k'ofa tashiga yayinda Bala ke ta faman yi musu dariya Habeeb ya ja mota maigadi ya wangame musu gate had'e da yi musu fatan a sauka lafiya.
    "Habeeb Ya rik'o hannunta yana murza yatsunta a hankali d'ayan hannunshi na rik'e da steering sannu-sannu yake tafiya Haleesa tashiga yi mishi mita my handsome don wannan wane irin driving sai kace mai shiga d'akin please ka k'ara speed irin wannan tafiya yaushe za mu kai gida"?
  "Murmushi ya yi kinsan ni "Learner ne karnaje na 6arar da ke.
  Uhm......haka ne fa tafad'a had'e da d'aga girar ta canza zance ta hanyar cewa my handsome don gaskiya Bala yanada kirki sosai kuma yana sonka amma fa na fishi sonka tak'arasa magana had'e da leqo fuskarshi.
   ''Murmushi ya yi yace Uhm....Ya ma za'ayi na had'a so da ki ke mun da Wanda Bala yake mun kema kinsan da banbancin"?
  "Hararashi tayi ta kauda fuska saboda ta fahimcin inda yadosa gani yadda tayi ya yi mugun bashi dariya yashiga kyalkyatawa.
  "Da sauri tajuyo tana kallonshi bata ta6a ganin mutume da dariya take yi wa Kyau irin Habeeb Lamido ko don Shi baya dariya ne shiyasa duk lokacin da ya yi ta sai tak'ara fito masa da kyakyawar fuskarshi ta yi ajiyar zuciya tasa yatsanta cikin dimple d'inshi _iyeee d'an yaro mai dimple yaro ka ji dad'inka duk wani shikashikai kyau suna tare da kai_
  "Da mugun mamaki ya Zaro ido kai-kai-kai Leesa ni za ki kira da suna yaro"?
  "Dariya Haleesa tayi tace kaima yanzu nan ka gama kirana da yarinya.
  To ae ke yarinya ce amma ni ba Wanda zai kalle ni ya kira ni da yaro.
  "Hum....tafad'a tana tabe baki.
suna isa gidan madam Hindu Haleesa ta taka mishi birki ta hanyar furta ka ajiye ni anan ba sai kashiga cikin gida ba.
 "Ignoring nata ya yi yadanna horn maigadi ya bud'e masa gate yanufi parking lot ya yi parking yajuyo wajenta cikin sanyin murya yace 'yan mata na kawo ki gida amma kisani zan yi kewarki sosai na tabbata da kyar ne Daren yau na iya bacci.
   Cikin tsokana Haleesa tace ni kuma ga ka ba abinda zai hanani bacci har da minshari.
  "Murmushi Habeeb ya yi yada'go fuskarta cikin idanunta yake kallo da sauri ta runtse idanu nata ki bud'e idanunki ki kalle ni kice ba za ki yi kewana ba.
  "Turo baki ta yi ni ka kyalleni na tafi tun kafin mom tadira gidanan asirinmu yatonu.
   Iskan bakinshi ya hura mata akan fuskarta, babu shiri ta bud'e idanunta murmushi ya saki mata can! K'asan mak'oshi ya furta da gaske ba za ki yi kewana ba"?
   Lamgwa6e kai ta yi kaima kasan da wasa nake.
  "I know baby yadda ki ka saba kwanciya anan wurin yanuna k'irjinshi da yatsa yau za ki kwana a mattress dole ki yi kewana yak'arasa magana had'e da kashe idonshi d'aya.
   "K'irjinshi tadaka da hannunta Uhm... Ni ban iya abunda ka iya ba.
  "Dariya ya yi karki damu I'll teach you kema ki iya make kafad'a ta yi ni bud'e mun k'ofa na fita.
   "Zuciyarshi na bugawa ya bud'e mata k'ofa har ta zura k'afarta guda k'asa ya riqon hannunta promise me da kin shiga gida za ki switch on phone naki"?
  Kai ta gyad'a ya sumbace hannunta I love you Leesa"
  Ta yi fari da idanu I love too badan yanaso ba yasaki hannunta har ta fita sai kuma tak'ara leqawa cikin mota peck tasaki mishi a lips kamar jira yake ya chafke lips d'inta da kyar yabarta ta tafi tajuya ya bita da kallo tana zuwa k'ofar da zai sada ta da cikin gida ta yi tsaye had'e da waigawa yana cikin mota yana kallonta peck ta yi a hannunta ta hura mishi da sauri ya lumshe idanu cikin yad'aga murya yace  _I LOVE YOU LEESA_ dariya ta yi tajuya tak'arasa shiga cikin gida Habeeb yaja mota yafita zuciyarshi cike da so da k'aunar Leesa.
   "A Main parlour Haleesa tarrarda Hannah zaune tana kallo, da gudu tafad'a jikinta cikin nishad'i suka rungume juna Haleesa tafara janye jikinta ta gyara zamanta had'e da yaye veil ta jefar tace kai  Hannah ba abunda yakai soyayya dad'i musanman in ka had'u da Wanda iya ta.
   Hannah ta zaro ido ta saki baki da hanci tana kallon Haleesa.
   "Haleesa ta d'auki remote tarage volume d'in tv tace Hannah ashe yayanki bala'i ne a soyayya"?
  Hannah ta kyalkyale da dariya tace bani nasha 'yar uwa.
  "Kallon sama da k'asa Haleesa ta yi mata me zan baki kisha"?
 Kanun labarai mana domin da alama yayana yatafi da zuciyarki.
  "Sirrin mata da miji zan baki kisha eh! Lallai kuwa Hannah bakida hankali.
  Dariya Hannah tak'ara kyalkyalewa da ita nima fa remain 2 month na bi ayarinku.
  "To ae sai ki jira har ki bi ayarin namu sai na daura miki lecture amma fa gaskiya Hannah ba karya yayanki ya yi tak'arasa magana tana dariya.
   ''Duka Hannah takai mata karki cinye mun d'an uwa.
  Haleesa ta mik'e bari na dauko phone d'ina na kira yayanki naji lafiyarsa.
  Yanzu-yanzu nan ku ka rabu kira na me"?
  Dariya Haleesa ta yi ko na fad'a miki ba za ki gane ba Hannah tana magana ne had'e da juyawa.
  "Lallai yaya Habeeb ya yi nassara tafiya da zuciyarki.
  "Ba zuciyata kadai yatafi da ita ba har gangar jikina tana tare da shi.
  ''Hannah ta yi shewa tana tafa hannaye Haleesa ta kad'a kai tak'arasa shiga bedroom.

_3 hour's later_

Madam Hindu tana zaune a parlour tana sauke gajiya Haleesa da Hannah suna zaune a gefenta ta dube Haleesa tace ina fatar da ba nan son bai zo gidanan ba"?
  "Haleesa da Hannah suka dubi juna sai wani wuk'i-wuk'i suke da idanu sai kace munafukai madam ta katse musu hamzari ta hanyar cewa da alama ya zo koh"?
  "A rikice Haleesa tashiga girgiza kai Hannah ta yi karaf tace mom ya za'ayi ya zo bayan kinsan Haleesa bata bashi fuska.
   "Haleesa tasauke ajiyar zuciya madam tace da kyau haka nakeso karki sake ki bashi fuska, har sai yak'are watani shi so nake yad'and'ani illar da miskilancin yake haifarwa Haleesa dai sai faman gyad'a kai take yi kamar k'adangarwa.
 
_9:00PM_

Haleesa na tsaye tana saka sleeping dress d'inta Hannah kuma na kwance akan gado, Haleesa ta gama abinda take yi taciro wayarta daga charging ta hau gado ta kwanta ta yi dialing number Habeeb ringing 1-2 ya yi received cikin muryarshi mai matuk'ar dad'in gaske ya furta _Hello_
  "Saida Haleesa ta lumshe idanu sakamako yadda muryarshi ta haddasa mata kasala cikin shagwa6a tace _Hi my handsome Don ka manta da ni koh"?_
   "Habeeb da ke kwance akan 3 seater ya gyara kwanciya yak'ara dafe phone _in har zan iya mantawa da kaina to tabbas zan manta da ke cikin 'yan awani nan da rabuwar mu Leesa baki ga yadda nadawo ba_
  Ni ma baby nayi missing naka sai yanzu na k'ara tabbatarwa sonka ya bi jinin jikina.
 Habeeb ya ja iska had'e da fesarwa  Leesa in har da gaske ki ke yi kin yi missing d'ina me zai hana ki bani dama gobe da sassafe na sanarda sweetheart kin janye sharad'inki za ki dawo gareni.
  "Haleesa ta yi ajiyar zuciya had'e da cewa......

_I'm sorry fans jiya banida lafiya datz why ban yi post ba ina bara addu'arku_

Jeeddah Aliyu
[03/01 8:26 am] aliyujeeddah: [21/12 2:37 pm] J: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```97```

~~Ban amince ba sai ka yi hak'uri har watani 3 su cika ni kuma nayi maka alqawali koda mom batace nadawo ba zan baka izzini ka zo ka yi mata magana, amma gaskiya yanzu Uhm...Uhm...in fact 2 weeks kawai ka yi.
   "Ajiyar Zuciya Habeeb ya yi shikenan Leesa tun da haka ki ka za6a mana amma inason kisani hakan ba k'aramin cutar da ni yake yi ba.
   "Ae ba kai kadai yake cutar wa ba nima inajin jiki daurewa kawai nake yi
   Hum....fad'a kawai ki ke yi Leesa da rashina yana cutar da ke da ba Ki bijiro da wannan buk'ata ba don haka mu ajiye wannan zance a gefe d'aya domin cigaba da yi sa zai iya 6ata mun rai.
   "Murmushi Haleesa ta yi da yafi domin nima ba amincewa zan yi da buk'atarka ba.
 Wannan kuma ke ta Shafa ni nasan yadda ki ke sona "you can't live without me za ki gaji da shirme ki ne kidawo gareni.
        ''Oho!..tun da kasan da haka miye na wani dauko zance"?
   Lumshe idanu ya yi kamar ba za yi magana ba daga bisani ya shafi sumar kanshi, saboda inasonki Leesa, nisanta daga gareki zai iya haddasa mun gagarumar matsala.
   ''Nima inasonka yaya Habeeb so da baki ba zai iya misalta shi ba amma kasani ba zan dawo gare ka ba har sai nan da wata uku.
   "A tak'aice duk yanda Habeeb yaso ya shawo kan Haleesa cikin sauk'i abin ya fask'ara ta tsaya kai da fata ita lalle-lalle sai yacika watani 3 ko za ta dawo gidanshi daga karshe ma sai suka rabu baran-baran kawanensu ya aje waya a fusace.
   "Hannah da ke kwance a gefen Haleesa ta kwashe da dariya lovebirds ya haka ashe za Ku iya fad'a da junanku"?
  Mtsww.....Haleesa ta ja tsaki Hannah yayanki Zuma ne sai da wuta har abada ba zai daina wannan d'abi'a nashi na sauri d'aukar abu da zafi ba.
   "Tabe baki Hannah ta yi tace ae ba zai daina ba saboda a jininsa yake.
  Ae kuwa yana tare da aiki Haleesa tafad'a had'e da make kafad'a.

```HABEEB```

Yana gama waya da Haleesa ya ji a ranshi zai nisanta kanshi daga gareta har wa'adin da ta deba masa yacika a washe gari ya tattara kayanshi ya yi kaura zuwa Lagos har yadira a Lagos bai nemi Haleesa ba yayinda ita ma bata nemi shi ba su dole fushi suke yi da juna.

_5 day's later_

Habeeb yagaji da shan k'amshin sa yakira Haleesa a lokacin tana zaune a parlour ita da Hannah madam kuma tafita she's always busy saboda lokacin bikin Hannah da yakarato.
   ''Saida wayar ta yi kusan tsinkewa sannan Haleesa ta d'aga adak'ile tace _Hello_
   "Leesa kina mun wulaqancin ko don kinga ina sonki ne"?
   _sarkin korafi ae ka jira mu gaisa kafin kafara kwararo min k'orafin naka"?_
Haka ma za ki fad'a"?
  _Nop...kawai naga dacewar hakan ne amma in bakaso gaisuwa nawa sai na rik'e abina_
   "To ki rik'e abarki banaso kin damu da ni ne da har za ki gaida ni"?
  _Hum....ni kuwa na damu da kai_
  ''Kin damu da ni miyasa ba ki nemi ni ba"?
  _saboda kana fushi da ni kuma iya sanani bansan nayi maka laifi ba_
  "Murmushi ya yi yanzu dai na d'auki laifina tun da gashi na kira ki sai kuma ya canza zance, ta hanyar cewa Leesa nayi missing naki fa Allah da kyar nake iya bacci.
 Dariya Haleesa ta yi my handsome Don kenan ko za ka zo ne  mom tafita daga ni sai Hannah ne kadai a gida"?
  "Iska ya ja kamar ba zai yi magana ba daga bisani yace ke ni fa ina Lagos tun washe gari da ki ka 6ata mun rai na baro abuja.
  ''Shikenan ka yi wa kanka
  "Habeeb ya yi dariya bani kadai na yi wa kaina ba ke ma kinyi wa kanki, saboda kin yi missing gani kyakyawar fuskata.
 _Uhm....kamar yanda kaima ka yi missing gani kyakyawar fuskata ba_
"Zancenki ba karya Leesa ke kyakyawa ce ga kyau fuska ga kuma kyau hali shiyasa duk lokacin da na tuna da ke sai na godewa ubangiji da albarkace ni da samun ki.
  Ajiyar zuciya Haleesa ta yi yayinda Habeeb yacigaba da kwararo mata zazzafan kalaman soyayya daga bisani yake sanarda ita gobe Imaan za ta dawo Haleesa tadinga ihun murna saboda ta yi kewar Imaan ba kad'an ba gani yanda take ihu yasa yace ke in gama ihunki anjima zan kira ki kafin Haleesa tak'ara magana har ya yi hanging up.

_washe gari_

Maryam tadira garin Abuja tare da Imaan kyakyawar tarba Haleesa da Hannah suka yi mata kasa sake jiki ta yi sai wani d'ari-d'ari, take saboda kunyar Haleesa take ji musanman in ta tuno da yankar k'auna da ta yi wa akan Habeeb sai gashi kuma za ta aure d'an uwan Haleesa da kyar Haleesa ta shawo kanta tasaki jikinta suka sha hira Hannah na tsokanar maryam ta hanyar cewa kishiyar Haleesa ada matar yayan Haleesa a yanzu kwanan Maryam 2 a abuja ta juya Yola.
Tsakanin Habeeb da Haleesa saidai su yi waya yini Haleesa take bata fito parlour ba tana d'akin k'unshe tana zuba wayar soyayya da Habeeb a kwana a tashi asarar mai rai gashi har Habeeb ya yi cinye watani 2 daga cikin watani 3 har tsawon wannan lokacin Habeeb bai tako k'afarsa Abuja ba a bisa alqawalin da yadaukawa kanshi ba zai k'ara zuwa inda Haleesa take ba har sai wa'adin watani 3 sun cika.
Lokacin bikin Hannah yak'araso wannan yasa madam ta tattaro su Haleesa suka nufi garin Yola saboda anan za'a gudanarda shagalin biki.

Ranar yau ta kasance ranar da za'a yi kamun Hannah su Haleesa manyan k'awaye amarya ansha makeover,ta yi matuk'ar kyau tayi fari tass kamar kata6a skin d'inta Jini ya zubo ga wata 'yar uba 'kiba da tayi ita kanta tana mamakin wannan 'kiba da tayi sai ana washe gari daurin aure Habeeb yadira a Yola lokacin da ya Kira Haleesa ya sanarda ita ya iso ta yi mishi girki mai dad'i zai zo anjima ya ci a rikice tace Dan Allah _my handsome Don_ ka yi hak'uri karka zo saboda banaso mom tagano akwai wata alaqa tsakanina da kai za ta d'auke ni maras kunya.
ran Habeeb ya yi matuk'ar 6aci gani yake yi duk wannan abun da Haleesa take yi tana yi ne don ta k'untatawa rayuwarshi ya tana matsayin matarshi sannan za ta haramta mishi zuwa inda take a bisa wani banza dalilin nata a harzuk'e yace wai Leesa mekika d'auki kanki ne huh"? Ko don kinga ina hauka sonki ne shiyasa ki ke mun yanda ki ka ga dama"? Idan ki ka dama in watani 3 suka cika karki dawo gidana ki cigaba da zamanki wajen sweetheart ki gani zan mutu ne ko zan yi rai batare da ya jira abunda za ta fad'a ba ya kashe waya.
   "Haleesa ta yi sororo da waya a hannu tarasa mafita takasa
  zaune takasa tsaye bakin rai mijinta takeso gani kamar yanda shima yake da Muradin so ganinta watani biyu kenan rabonsu da ganin Juna.
    "Ta rafka tagumi jikinta ya yi mugun sanyi kuka takeso yi amma tana tsoro kad'a wani ya ganta tana kuka ya tambaye dalilin kukan nata saboda gidan cike yake da 'yan biki tana cikin Wannan halin Hannah tashigo tadafa  kafad'arta what's wrong Mrs Lamido naga kamar kina ciki damuwa"?
  ''Ajiyar zuciya Haleesa ta yi NI DA YAYA HABEEB ne yanzu nan muka gama waya kinsan halinshi na sauri d'aukar zafi akan abu qalilan ya isheshi fushi tacigaba da ba wa Hannah labari abunda yafaru a tsakaninsu.
   ''Tsaki Hannah ta ja yakamata zuwa wannan lokacin Haleesa ki daure ki ba wa mijinki dama ya zo ya ga mom ki koma gidanki kisani duk wannan horo da mom take yi wa yaya Habeeb tana yi ne saboda ke da kin furta kin janye sharad'in naki shikenan nan take za ta amince ki koma amma wannan zaman da ki ke yi anan amfani me yake qara ki da shi"? ba za ki gane kinyi wauta ba sai natafi na barki mom ba zaman gida take yi ba za'a barki gida daga ke sai Housemaid ki bi umarnin mijinki ko don saboda aljannarki kitashi yanzu nan ki shirya kitafi wajen mijinki in kin je can! Kya masa girki duk da nasan ba girki yakeso ba kawai dai yafake da sabara ne ya harbi barewa tak'arasa magana tana dariya.
  "Haleesa ta rausayar da kai gefe d'aya to in ba girki yakeso ba me yakeso sarkin fassara"?
 ''Dariya Hannah tayi Oho! Ni ma bansaniba amma na tabbata amsar wannan  tambaya tana bakin _handsome Don_
Mtcww....Haleesa ta ja tsaki ke dai kin zama 'yar iska wallahi tun kafin mu kai ki gidan Mus'ab kin lalace.
  "Hannah tak'ara kyalkyalewa da dariya
  Hannunta Haleesa tarik'o Hannah please kidaina wannan dariya kinemo min mafita.
 "Hannah ta kad'a eyes ball d'inta mafita guda d'aya ce kitashi mu je na yi dropping d'inki wajenshi in yaso Ku nemawa kanku mafita
[21/12 8:10 pm]  Idanu Haleesa ta zaro cab! da sake wai ayi wa mai dame d'aya sata gaskiya Hannah ba zan iya ba so ki ke mom tagano, ta dinga yi min kallon marar kunya da kawaicin.
  "Harara Hannah ta zabga mata wai ke da kin bud'e baki sai kice kunya, kunya shin wai yaya Habeeb ba mijinki bane ko kuma zuwa wajenshi da za ki yi ya sa6awa mahalicinki"?
  "A sanyaye Haleesa ta girgiza kai Hannah tak'ara jefata cikin rud'ani ba tunani za ki yi ba kitashi mu tafi, Hannah ta katse Mata hamzari.
Haleesa ta mik'e tsaye to amma kuma Hannah ta ya ki ke gani zan fita gidanan har nadawo batare da tasani ba kina gani har  tambayarta nayi zan tafi na gaida su Ammi tace na jira har agama Shagalin bikinki.
   ''Hannah tace karki damu ni nasan abunda zan yi har ki dawo batare da mom tasan kin fita ba.
   "Haleesa ta kad'a kai tanufi trolley d'inta taciro Riga da skirt na Swiss lace red colour mai touch d'in white tacire kayan jikinta tasanya lace d'in rigar ta yi tight d'inta musanman k'irjinta tajuya wajen Hannah tace Hannah dubi yanda k'irjina, yaciko nifa wannan k'iba yafara damu na tak'arasa magana tana yatsina.
   ''Hannah ta kyalkyale da dariya tace yarinya kinsame lafiya.
  Tsaki Haleesa ta ja wane irin lafiya"? Haka kawai mutum yadinga kumburi kamar flour tana magana ne had'e da fesa perfume ta zari white veil d'inta I'm ready mu tafi koh"?
  Hannah tace Yeap! Ta wuce gaba Haleesa na biye da ita direct parking lot suka nufa Hannah ta kwadawa sa'eed driver kira da gudu sa'eed yak'araso key d'in wace mota ne hannunka"?
  "Na Kia cerato ne"
  "Okay bani key d'in
Ciro key d'in daga aljihunshi ya yi ya mik'a mata ta kar6a tanufi wajen motar Haleesa ta bud'e k'ofa tashiga Hannah ta yi wa motar key ta ja suka nufi gate maigadi ya bud'e musu gate suka fice.
  "Hannah tajuyo ta dubi Haleesa tace gobe insha Allah nima zan bi sahunku ba za k'ara yi mun wani gani-gani ba tak'arasa magana tana murgud'a baki.
  "Tabe baki Haleesa ta yi had'e da cewa Allah ya shirye ki Hannah banta6a gani amarya mai zumudin aure irinki ba kafin Hannah ta bata amsa phone d'in Haleesa ya yi ringing.
  "A kasalance ta bud'e purse d'inta taciro wayar gani Wanda ke kira yasa tasaki sanyaye murmushi ta yi receiving call takara a kunnenta ta yi shiru tana murmushi.

_HABEEB_

 Habeeb da ke kishingid'e a parlournshi, yana dafe da waya a kunnenshi jin Haleesa ta yi shiru ba ta yi magana ba yasa ya ajiye zafin kanshi a gefe, yace _Leesa na yi fushi a maimakon ki kira ni ki bani hak'uri sai ki ka nuna mini halin ko in kula koh"?_
  "Huh.... Yaya Habeeb kenan to ni wane laifi na yi maka da zan baka hak'uri"?
Dai-dai lokacin da Hannah tak'araso gate d'in gidan ta yi horn saida suka d'auki tsawon _3 minutes_ kafin gate ya bud'e su shiga yayinda Haleesa ke cigaba da waya da Habeeb.
  "Parking Hannah ta yi Haleesa ta bud'e k'ofa tacire wayar daga kunnenta ta yi k'asa da murya yadda Habeeb bai zai ji abunda takeso fad'a ba what's time za ki dawo dauka na"?
  Batare da Hannah ta yi magana ba tad'aga mata yatsunta uku.
  _3 o'clock"?_ Haleesa tafad'a.
  Hannah ta gyad'a mata kai Haleesa tajuya tanufi cikin gida yayinda Hannah ta ja mota.
  "Direct part d'in Habeeb ta wuce tana mai cigaba da waya da shi a hankali ta turo k'ofa cikin Sa'a k'ofar ya bud'e ta hango Habeeb kishigid'e da waya a kunnenshi ta katse kiran miyarda phone d'inta cikin purse cikin sand'a tashiga parlourn ta bayan kujeri ta bi ta la6a6o ta rufewa Habeeb fuska.
  "A tsorace Habeeb yashiga kacaniya cire hannayenta daga fuskarshi finciko ta ya yi da k'arfi tafad'o bisa kujera razananen ihu tasaki had'e da kai mishi duka da purse d'in hannunta haba! Yaya Habeeb karya ni za ka yi ne"? Irin wannan fincikowa da ka yi min Allah saura kiris na yi targad'e.
  "Fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi yajuyo yana facing nata hannayenta yarik'o yacire purse daga hannunta ya jefa bisa kujera da ke kusa da shi ya ja iska yana mata kallon k'asan ido mekika zo yi wurina bayan ni kin haramta min zuwa wurinki"?
  "Au! Haka ma za ka fad'a ae ni a tunani ba wannan tambaya yakamata ka yi mun ba tak'arasa magana had'e da fizge hannayenta tasoma k'ok'arin tashi da k'arfi ya mayarda ita zaune ya aza kanshi bisa cinyoyinta yace na yi matuk'ar mamakin ganinki Leesa domin wannan kiran da nayi miki na bankwana ne har na k'udiri anniyar gobe da zaran andaura auren Hannah zan koma Lagos daga can na haura Canada ba za ki k'ara ganina ba har sai kin nemi ni da kanki.
  "Haleesa ta tabe baki da kuwa kayiwa kanka domin ba neman naka zan yi ba.
  "Nasan za ki iya Leesa saboda ba damuwa ki ka yi da ni ba shiyasa a koda yaushe nake godewa Allah da yakare ni daga matan banza yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
  ''Tausayinshi yakama Haleesa ita kanta tasan Habeeb yana cikin maza masu k'arancin sha'awa mata basa gabanshi shi dai barshi da  neman k'udi a hankali take Shafa sumar kanshi muryarta asanyaye tace ka yi hak'uri my handsome Don nasan kana jin zafina amma yakamata ka yi min adalci ka tuna irin d'an banzan wulaqancin da dinga yi min har fa ce......da sauri yatoshe mata baki karki dawo da hannun agogo baya Leesa abunda yawuce bai kamata ki tadinga dawowa da shi ba kisani a yanzu inasonki tamkar numfashina KE D'AYA CE a zuciyata daga kanki na rufe ba wata.
   "Murmushi ta yi cike da jin dad'in kalamanshi mai hira mai dad'i suka shiga yi daga bisani salon hirar ya canza cak d'auke ta yanufi bedroom d'inshi da ita tabbas Haleesa ta yarda ita d'aya ce a zuciyar Habeeb Lamido domin yanda yadinga zuba mata, zazzafan kalamai abun ba kama hannun yaro bayan komai ya wakana Haleesa na tsaye a gaban mirror tana busar da gashinta da hand dryer Habeeb yafito daga bathroom yak'araso daf ita ya kar6i hand dryer d'in yacigaba da busar mata da gashin Leesa kin ga yanda ki ka dawo 'yar lukuta musanman nan wurin yak'ara cikowa yana magana had'e da Shafa k'irjinta da hannunshi d'aya yana wani lumshe ido.
   "Ta cikin mirror ta zabga mishi harara ae kai abun a cikin jininka yake duk mace da ta aurenka sai ta zama katuwa sai dai bana fatar na kai girman wannan matar tak'arasa magana tana yatsina.
  "Dariya Habeeb ya yi had'e da kashe hand dryer ya ajiye ta a gefen mirror yajuyo da Haleesa suna facing junansu ashe bani kadai nake kishi da matace ba ke ma kina yi.
   "Ture shi ta yi tanufi wajen wardrobe ta bud'e taciro black colour Long sleeve d'inshi ta kwashe inner wears d'inta tanufi bathroom tasanya kayan tafito Habeeb yana tsaye daga shi sai white vest da boxer ya yi crossing hands nashi a k'irji kallon mai cike da so da k'auna yake mata ni kuwa Leesa in tambaye ki mana"?
  "Gira ta d'aga mishi had'e Yeap!
  Yasauke hannanye shi yarik'o hannunta suka nufi k'ofar fita daf kunnenta yarad'a mata yaushe za ki fara saka kaya a gabana"?
  "Ignoring nashi ta yi kamar bata ji abunda yafad'a ba suka yadda zango a parlour Habeeb ya kwanta akan 3 seater yajanyo ta jikinshi a wannan karo idan na tambaye ki kada ki yi ignoring nawa.
  Turo baki tayi indan kuma tambayar naka ba mai buk'atar amsa bane to kasani ba lalle bane kasame amsa ba.
  Ya ja iska had'e da dage gira ko yana buk'ata ko ba ya buk'ata dole ki nemo amsa Yaushe za ki dawo gareni"?
  "Huh....dama wannan ne tambayar naka"?
Amsa yakamata ki ba ni firstly kafin ki yi naki tambaya.
  "Haleesa ta yi murmushi tace idan an k'are bikin Hannah ka je ka ga mom na amince zan dawo gareka........


_am sick really need ur prayer's_


Jeeddah Aliyu
[03/01 8:28 am] aliyujeeddah: [22/12 6:33 pm]Aliyu Jeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

*°°°°In Dedication°°°*
*Shehu Aliyu Family's*

              *98*

_°°°°Hurray up today it's your birthday Autar Hajiya in my heart I make wishes for you to have peace & successful life_ °°°Happy birthday once again my Auta°°°°

~~Habeeb yasaki ihun farin cikin had'e da k'ara k'amk'ameta kamar zai shigar da ita k'irjinshi Sai zuba mata ruwan peck yake yi  akan fuskarta zuwa, wuyanta muah...muah..I love you Leesa.... I really so much love you Leesa....wannan rana ta kasance d'aya daga cikin rananku da ba zan ta6a mantawa da su a rayuwana, Haleesa ta yi murmushi had'e da cewa d'an sausauta  wannan matsar da ka yi min kada garin murna ni kuma kafasa mun k'irji.
   "Karan hancinta ya ja ya sausauta rungumar da ya yi mata yashiga shafa cikinta yana lumsashe idanu Leesa...yakira sunanta
   "Uhm.....tafad'a
Yaushe za ki bani baby"?
  ''Tabe baki ta yi ka nemo Wanda za yi min ciki ne"?
  Mitsineta ya yi tasaki ihu washh....tafad'a had'e da Shafa fatar cikinta kai fa yaya Habeeb mugu ne sai ka yi ta yi wa mutum mugunta.
   ''Dole yasa nake miki mugunta Leesa kunnen k'ashi ne da ke nace da ke banaso abunda yawuce kina dawo min da shi sai naga kamar ba kiyafemin ba.
   "Amma kuma abunda ka fad'a ne nake maimaitawa tak'arasa magana tana murgud'a baki.
  "Shine nace da ke banaso don haka kidaina in baso ki ke mu yi fad'a ba.
  Shikenan nadaina tacusa hancinta cikin k'irjinshi tana shinshinar k'amshin perfume d'inshi.
   "D'ago kanta ya yi yana kallon cikin idonta  yana dariya meye haka Leesa"?
  "Allah yaya Habeeb k'amshin perfume d'inka yana mun dad'i har banaso nadaina shak'arsa.
  ''Habeeb ya kyalkyale da dariya yana shafar sumar kanta Lessa rigima ta yaya Habeeb Haleesa ta yi dariya wane yaya Habeeb ka ke nufi"?
   "Harara ya galla mata baya ni kina da wani yaya Habeeb ne"?
   "Peck ta yi mishi a kumatu kai d'aya ne baya kai ba Wani.
  Dad'i ya lullu6e Habeeb cikin tsokana yace ae na yi zaton za ki kira sunan wannan mutume
  "Rausayar da kai ta yi Wannan mutume ya zama past a yanzu Kaine presently, saboda haka kadaina zancenshi saidai in addu'a za ka dinga yi masa wannan ba zan hanaka ba.
   "D'an bazawarin murmushi Habeeb ya yi, turo baki Haleesa ta yi ko ba za ka iya masa addu'a ba"?
Ni na isa nace ba zan masa addu'a ba yafad'a yana k'ok'arin cireta daga jikinshi Haleesa ta mik'e da kanta daga jikinshi ya yi mik'a ya dubi Haleesa yace Leesa yunwa nakeji fa
  "Ta mik'e tsaye da sauri tace ka  bani _15 minutes_ na dafa maka abunda za ka ci"?
 Shima ya mik'e tsaye mu je na rakaki ta wuce gaba ya Mara mata baya.

_20 minutes later_

Haleesa ta kamalla jallof d'in macaroni da pepper soup kifi ta zuba a food flask Habeeb ya tayata d'aukar food flask d'in ita kuma ta dauko plates a tsakiya Rug carpet suka zauna ta yi masa serving.
  Sai wani kad'a kai yake yi gaskiya Leesa kin iya girki ko d'and'ano abincinki dabam yake da na sauran mata.
   "Haleesa ta kyalkyale da dariya ta dauki murfin food flask ta yi masa waigi bari na tarbeka kad'a santi ya d'ebe ka kafad'i ka dauko mun aiki.
  Ajiye spoon d'in hannunshi ya yatsine fuska ni fa santi nake yi ba.
"K'ara kyalkyalewa da dariya ta yi kad'a kai yacigaba da cin abincinshi yad'ago ya dube Haleesa wance ke ta fama yi mishi dariya ya galla mata harara in ba ki daina yi min dariya ba sai na matse d'an k'aramin bakinan da yake mun dariya.
  "Rufe bakinta ta yi da hannayenta tana mai cigaba da dariya k'asa-kasa suna gama cin abincin Haleesa ta mik'e kan 3 seater ta dubi Habeeb tace my Handsome Don zo ka yi min taushe gaba d'aya jikina tsami yake min.
   "Murmushi ya yi ya kai girgiza batare da ya tanka ba ya mik'e yanufi kujera da take kwance yasoma matsa mata jikinta a hankali ta lumshe idanu cikin d'an k'ank'anin lokacin bacci ya kwashe ta.
   ''Gani ta yi bacci yasa Habeeb ya yi tagumi ya tsura mata ido hannunta yarik'o yana kallon zanen k'umshi lalle da ke hannunta tsawon lokacin yadauka a haka saida yaga lokacin sallah azhar ya yi sannan yashiga tashe ta ta hanyar hura mata iskan bakinshi a kunne.
  "A hankali ta bud'e idanuta ta ware su akan fuskarshi yasake mata sanyaye murmushi gira yad'aga mata, ki tashi mu yi sallah sarkin bacci.
  ''Ta mik'e zaune tana yatsinar fuska Habeeb ya mik'e yanufi bedroom a kasalance ta bi bayanshi saida ta mayarda kayanta ta linke masa long sleeve d'inshi da tacire ta mayar cikin wardrobe.
  "Habeeb yafito daga bathroom ya yarfa mata raguwar ruwan alwala da ke hannunshi cikin shagwa6a ta turo baki tajuya tashiga bathroom bayan sunyi sallah  Habeeb ya bud'e wardrobe yaciro kayanshi yacire farar Jallabiya da ke jikinshi da sauri Haleesa ta tashi ta koma parlour, Habeeb ya bi ta da kallo.
  "K'amshin turare shi da ta shaqa yasa ta yi tad'ago da sauri suka had'a ido murmushi suka sakewa junansu
K'asa d'auke idanunta ta yi daga kanshi saboda ba k'aramin kyau kayan da ke jikinshi suka yi masa ba yak'araso kusa da ita ya zauna bisa hannun kujera da take zaune akai rungumo kafad'unta ya yi yadai 'yan mata naa"? Yak'arasa magana had'e da kashe idonshi d'aya.
   "Murmushi ta yi ta shafi laulausan sajenshi ka yi kyau _my handsome Don_saidai matsala na d'aya da kai baka saka kaftan  tsawon zama na da kai banta6a ganinka da shigarmu na hausawa ba.
   "Ya yi murmushi kinsan halina banaso zafi da takura shiyasa bana sakawa in fact ni ba bahaushe bane.
  "tabe baki Haleesa ta yi gashi ni kuma ina sha'awar na ganka sanye da su don haka sai kafara sakawa ko don saboda ni.
   "hancinta ya ja  angama my Lady yafad'a yana dariya.

_3:00pm_

Hannah ta zo d'aukar Haleesa a parlour ta tarrarda su Haleesa na zaune Habeeb ya yi matashi da cinyoyinta yayinda ita kuma take wasa da sumar kanshi shigowar Hannah parlourn bai sa Habeeb yatashi daga jikin Haleesa ba sai ma gyara kwanciya shi da ya yi yashiga tsokanar Hannah da kyar Hannah tasamu yabarta ta wuce da Haleesa a cewar shi da kanshi za maida ta.

_9:00pm_

Haleesa na kwance akan bed Hannah na gefenta tana waya da Mus'ab phone d'in Haleesa ya yi ringing gani Habeeb ne ke kira yasa tadauka da sauri cikin shagwa6a tace mai sanyi na ya akayi ne"?
  "Habeeb ya amsa mata da cewa ki zo ki parking lot inason ganinki.
  Me zan maka tafad'a tana zarar ido"?
  Za ki zo ko bara ki zo ba"?
  ''Kamar za ta yi kuka ta furta ganina zuwa amma kasani ba zan wuce Just 5 minutes ba zan nadawo.
 Batare da yabata amsa ba ya katse kiran.
   Veil d'inta ta dauka tafice tana gunguni parking lot tanufa tashiga dube-dube Habeeb ya bud'e k'ofar mota yaturo kanshi waje yace ke zo garinan.
  Tajuya da sauri ta dube shi harararshi ta yi sannan tanufi wajenshi tadafa k'ofar mota, fuskarta a had'e tace amma yaya Habeeb kasan ba haka nayi da kai ba koh"?
  "Yacire lollipop d'in da ke bakinshi shima ya murtuk'e fuska ya ki ka yi da ni"?
  "Cewa nayi ka jira har agama bikin Hannah sannan ka zo ka yi magana da mom to me kuma ka zo yi yanzu"?
  "Tsaki ya ja ke karki yi min wulaqancin don kinga na zo wajenki.
 Ba wulaqancin na ke yi maka ba yaya Habeeb banaso mom ta ga mu  tare nafiso sai kafara yi mata magana first idan ta tambaye ni nace na amince zan koma amma yanzu ga shi ka zo me ka ke tunani zai faru in tafito ta ga mu a tare"?
   "Har ta dasa alama tambaya a zancenta Habeeb yana tsotsa lollipop had'e da kallonta a d'age in kin gama ki zagayo ki shiga mota mu yi magana.
  Ranta a 6ace ta balle k'ofa tashiga light d'in da ke cikin motar ta kunna galla mata harara Habeeb ya yi ya kashe haske ya marairaice murya Leesa please ki saki fuskarki mu yi hira in ki ka daure fuskarki sai ki dawo kamar wannan housemaid d'inan na sweetheart da ke Lagos ya ma sunanta"?
   "Murgud'a baki ta yi bansaniba ae sai ka tambayi kanka.
  ''To ae nima ba ke na tambaya ba Uhm...uhm...Janet! Yafad'a yana dariya zaro ido Haleesa ta yi tashiga dukanshi Allah yaya Habeeb ka kashe ni  wannan mummunar ka had'a ni da ita
  Ya kyalkyale da dariya yarik'e hannayenta ta fizge daga rik'o da ya yi mata ta koma jikin seat talafe tana kumbura fuska lollipop d'in bakinshi yaciro yasa mata a baki yacire veil d'inta yarataya a wuyanshi saida ta shanye lollipop d'in sannan tasaki fuskarta ta dube Habeeb tana murmushi Allah yaya Habeeb lollipop d'inan da dad'i.
  "don yafito daga baki na ne shiyasa ki ka ji shi da dad'i yak'arasa magana had'e da kashe mata idonshi d'aya.
  Hira mai dad'i suka shiga yi yayinda rabin jikin Haleesa yake manne da nashi  sai around _11:30pm_ Habeeb yabarta ta koma cikin gida.

_Washe gari_
Misalin k'arfe 2:30pm aka daura auren Hannah da Mus'ab gaba d'aya Haleesa ta tashi cikin yanayi na rashin jin dad'i jiri da tashin zuciya ke damunta.
Around 4 o'clock Haleesa na kwance madam Hindu ta aiko kiranta ta mik'e a kasalance tanufi parlour tana shiga parlourn k'amshin abincin da k'awaye madam Hindu ke ci yabugi hancinta nan take zuciyarta ta tashi wani irin amai ya turnuk'e ta da gudu ta koma d'akin ta afka bathroom tashiga kwara amai kamar za ta amayar da 'yan hanjinta.......


_Ku yi hak'uri da short typing da nake mu Ku kusan ba isheshi lfy ne da ni ba_

Jeeddah  Aliyu
[03/01 8:31 am] aliyujeeddah: [24/12 4:41 pm] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

*°°°°In Dedication°°°*
*Shehu Aliyu Family's*

              *99*

_Second to the last page_

~~Juyowa da Haleesa za ta yi taci karo da madam Hindu tsaye a bakin k'ofar bathroom tana mata kallo mai cike, da tuhuma Batare da tace da Haleesa komai ba tafita ajiyar zuciya Haleesa ta yi tafito daga bathroom jiri na d'ebarta tanufi bed ta kwanta bayan kamar _5 minutes_ da fita madam sai gata tasake dawowa, ta zauna kusa da k'afafun Haleesa, meke damunki ne Haleesa"?
  "Da kyar Haleesa tad'ago muryarta ad'isashe tace tashi zuciya da jiri"?
  Tun yaushe ki ka yafara jin tashi zuciya"?
  "Yau da safe! Haleesa tafad'a kamar za ta yi kuka.
  Murmushi madam ta yi Humm....bari na kira Dr Khaleesat Haydar ta duba ki domin za ta fini sani indan wannan ciwon naki yadosa.
 "Haleesa ta marairaice murya mom ba sai kin kira Dr Khaleesat ba Allah naji sauki harara madam ta zuba mata sannan ta mayarda hankalinta ga wayar hannunta tashiga dialing digit d'in Dr Khaleesat Haydar ringing d'aya zuwa biyu Dr Khaleesat tad'aga cikin muryata mai zak'i da gard'in gaske tace _Assalamu Alaikum"!_
Madam Hindu ta amsa mata da cewa _wa'alaikum sallam Dr Khaleesat ya gida ya kuma hak'uri  da Jama'a"?_
  _Alhamdulillah Madam ya shagalin biki"? Allah naso nazo ko don kada Hannah ta yi mun gori amma aiyuka su yi mun yawa a hospital amma insha Allah zan ware lokacin na je naga gidan amarya Hannah_ Dr Khaleesat tak'arasa magana tana dariya madam ta tayata dariyar daga bisani madam tace Dr Khaleesat in da hali inason ganinki urgently akwai patient d'in da nakeso ki duba mun ita
Amma fa in ban takura ki ba Dr Khaleesat ta yi murmushi tace ba damuwa madam insha Allah yanzu nan za ki ganni dama ina bisa hanyar zuwa gida ne.
  "Shikenan Dr inajira sai kin zo madam k'arasa magana had'e da katse kiran.

_10 minutes later_

Dr Khaleesat Haydar tadanno hancin motarta kirar Lexus 2016 model a farfajiyar gidan madam Hindu tanufi parking lot ta yi parking k'afafunta suka Fara fitowa daga bisani gangar Jikinta ta baiyana sanyeta ke da Arabian gown Blue colour ta yi rolling da pink colour veil kwayar idonta na lullu6e da farin gilashi ta bud'e seat d'in baya tadauko briefcase d'inta mai d'auke da kayan duba marar lafiya cikin takonta na k'assaita tanufi cikin gida a parlour taci karo da  madam Hindu tana fitowa daga d'akin da Haleesa take ciki madam Hindu ta washe hak'ora ki k'araso daga ciki Dr madam Hindu tak'arasa magana had'e da juyawa cikin d'akin na Haleesa yayinda Dr Khaleesat ta Mara mata baya Haleesa na kwance kamar yanda madam tafita tabarta a kwance Haleesa nagani Dr Khaleesat ta mik'e zaune tana yatsinar fuska, Dr Khaleesat ta nemi kusa da ita ta zauna tayi mata ya jiki daga bisani tashiga watsa mata tambayoyi meke damunki"?
"Jiri da tashin zuciya
 tsawon wane lokacin ki ka dauka kina jin wannan yanayi"?
Yau da safe
Yaushe rabonki da ganin period d'inki"?
   ''Rass.......rasss..... Gaban Haleesa yagad'i tad'ago a rikice tana kallon Dr Khaleesat daga bisani ta sadda kai k'asa cike da jin kunya tace almost 2 months"
Murmushi Dr Khaleesat ta yi ta bud'e briefcase dinta tafito 'yar k'aramar roba ta mik'awa Haleesa tashi ki Shiga bathroom ki yi fitsari a ciki inaso na k'ara tabbatar da abunda nake tunani jikin Haleesa a sa6ule tasauka daga kan gado tashiga bathroom bata jima da shiga ciki ba tafito rik'e da robar mai d'auke da fitsari ta mik'awa Dr Khaleesat "pregnancy test strip Urine Dr Khaleesat tadauko ta tsoma cikin fitsarin ta ajiye a gefe after 3- 5 minutes tadauko yanuna jajaye layi guda biyu alama ce da ke nuna positive Dr Khaleesat tafad'ad'a murmushinta ta dube madam Hindu congratulation! Madam kin yi kusa samun maigida ko kishiya tak'arasa magana cikin dariya.
  Masha Allah! Masha Allah! Abunda madam Hindu ke maimaitawa kenan ta rungume Haleesa, tana mata sannu yayinda Dr Khaleesat ta rubuta mata magunguna masu k'ara kuzari  da k'arawa abunda ke cikinta lafiya ta mik'awa madam Hindu takarda ta mik'e tsaye had'e da cewa madam ni zan k'arasa gida insha Allah zuwa jibin zan leqa gidan amarya Hannah mu gaisa madam tabi bayanta tana zuba mata Godiya.
  ''Suna fita Haleesa ta kifa kanta a pillow tashiga rera kuka, tsananin kunya ya lullu6e ta yanzu da wane ido za ta kalli mom saboda mom tasan cewa yau tsawon watani biyu kenan da kafawa Habeeb sharad'in sai gashi cikin wata biyu ya baiyana a jikinta kenan yanzu mom za ta gano tana kula Habeeb duk da gargad'in da take mata akan karta kulashi har sai yacinye Watani 3 kuka Haleesa tashiga rerawa sanadin kuka da ta yi ya janyo mata ciwon kai.

_14 minutes later_

Madam Hindu ta turo k'ofar d'akin Haleesa tashigo hannunta rik'e da ledar magani d'ayan hannunta d'auke da robar ruwan Faro da glass cup jin motsinta yasa da sauri Haleesa ta rufe idanunta, madam ta zauna kusa da ita Haleesa, Haleesa tashi ki sha magani, a kunyace ta tashi madam ta balle tablets d'in ta mik'a mata ta tsiyaya ruwa a cup tabata batare da Haleesa ta dube ta ba kar6i ruwan tashanye maganin.
  "Kwanta ki yi baccinki saboda kina buk'atar hutu madam tafad'a had'e da mak'ewa tsaye Haleesa ta kwanta sannan madam tajuya tafita.
   ''Haleesa nagani madam tafita tararume Hijab tasaka  ta zura bathroom slippers ta bud'e k'ofa a hankali ta leqa parlour, tak'arewa mutane da ke parlour kallo taga madam Hindu bata cikinsu wuf.....ta yi tafito tanufi k'ofar fita cikin sauri tanufi gate ta bud'e k'aramar k'ofa tafita tana tana k'arasawa titi ta tare mai adaidata Saida tashiga suka d'auki hanya sannan tafad'a masa sunan unguwar da za ta je.
   "Tun daga shigarta unguwarsu tafara cin karo da abun mamaki _Ni da yaya Habeeb tailoring center_ yadawo babban shago painting shagon kadai abun kallo ne bata k'ara shiga rud'u da firgitarwa ba saida takai k'ofar gidansu daga gidansu har na su margayi Yaya Habeeb ya sauya, a rikice tafito daga adaidaita tasaki baki da hancinta tana kallon gate d'in gidansu jin an turo k'ofar yasa takara ware idanunta sosai taga mai fitowa addu'a take yi a zuciyarta Allah yasa iyayyenta ba siyarda gidajensu suka yi ba kamal tagani yafito yana ganinta yadaka tsalle ya rungumeta muryarta na rawa tace kamal me ke faruwa ne naga sauyi a gidanmu da na baba Audu"?
  "Kamal ya yi dariya yace aunty Haleesa ki sallame mai adaidaita ki barshi tsaye sai lokacin Haleesa ta tuna da bata fito da ko fika ba ta mayarda ganinta ga hannun kamal, N500 tagani rik'e da hannunshi tace kamal ban fito da k'udi ba ko za ka iya biyanshi"?
    Kamal yajuya yanufi wajen mai adaidaita  ya biya shi kud'inshi sannan yadawo wajen Haleesa, wance ke tsaye da d'ibin mamaki lullu6e da ita muryar kamal ce ta yi nasara dawowa da ita natsuwarta.
  "Duk wannan sauyin da ki ka gani aikin yaya Habeeb ne.
  "Zaro ido ta yi wane yaya Habeeb ka ke nufi"?
 Yaya Habeeb d'inki mana
Hum....kamal kana k'ara jefani cikin rud'ani yaya Habeeb Lamido nake nufi shine ya gyara mana wannan gyara da ki ke gani ba ma wannan kadai ba ya ba wa yaya salman aiki company shi ya bashi gida da mota wai za'a dinga cirewa cikin salary shi, ya gyara _ni da yaya Habeeb tailoring centre_ ya zuba Kwararin mad'inka ya kuma biyawa Baffa, Ammi ,Baba Audu da inna mairo makka sai kin Shiga cikin gida za ki ga yanda ya gyara miki d'akinki.
  "Har kamal yadasa aya a zancenshi Haleesa na kallonshi baki bud'e Kamal yace aunty Haleesa ki Shiga ciki ni zan tafi Inda Ammi ta aikeni.
  "Jikinta a sanyaye tashiga gida ta yi sallama shiru ba Wanda ya amsa kaitsaye tanufi d'akinta duk da taga sauyi tare da d'akin hakan bai hanata gane shi ba ta murd'a handle k'ofar ta bud'e tashiga tsaye ta yi tana k'arewa d'akin kallo everything's dake cikin d'akin red & yellow colour ne a hankali ta mayarda idanunta kan bed Wanda aka qawata shi da bedsheets red & yellow ga wasu teddy bear's jere akan gado murmushi ta yi tanufi bed d'in ta kwanta tad'auki teddy guda ta rungume a k'irjinta
[25/12 1:40 pm] aliyujeeddah: "Ta lumshe idanu tashiga tunanin Habeeb Lamido nan take wani irin sonshi yak'ara samun mafaka a zuciyarta ta k'udiri anniyar kyautata masa za ta guji duk wani abu da zai 6ata masa rai saboda yanzu tak'ara amincewa da irin soyayyar da yake mata ta bud'e idanu da sauri tadauko wayarta ta rubuta mishi text.
  _my handsome Don narasa Kalmar da zan yi amfani da ita domin na gode maka saidai zan cigaba da yi maka addu'a ubangiji ya baka masauki a gidan aljanna Firdausi ina mai maka albishir Imaan ta yi kusa samun k'ani ko k'anwa tsananin kunyar mom  nakeji yasa na fito batare da saninta ba a yanzu haka ina gidan Ammi. Thanks for everything's tauraro naa_
  Ta tura masa ta gyara kwanciyarta tasoma hango irin soyayyar da za su zuba in takoma gidan Habeeb a haka bacci yasud'ad'o ya sace ta.

  "Ta6angare madam Hindu kuma tana fitowa daga d'akin da Haleesa take ta lalla6o digit d'in Habeeb ta danna masa kira, yana d'agawa ko gaisuwar shi bata tsaya amsawa ba tace duk abunda ka ke yi ka ajiye ka zo inason ganinka yanzu nan tana k'arasa magana ta hanging up.

_After 13 minutes_
Sai ga Habeeb ya zo a bedroom yatarar da madam gani yanda take ta zabga fara'a ya zauna kusa da ita yanda naga kina wannan fara'a sweetheart wani abun farin ciki yasamemu koh"?
  Sosai ma kuwa Haleesa batada lafiya na...a rikice Habeeb ya katse mata hamzari ta hanyar mik'ewa tsaye marairarice murya kamar zai yi kuka haba sweetheart don Leesa batada lafiya shine ki ke farin ciki"?
  "Murmushi madam ta yi kai ni fa banaso shirme ae kajira na k'arasa fad'ar abunda zan fad'a, batare da tajira jin ta bakinshi ba tacigaba da cewa Haleesa batada lafiya na kira Dr Khaleesat ta duba ta sakamako gwajin da ta yi mata tagano tana d'auke da juna biyu har na tsawon watani biyu.
   "Zaro ido Habeeb yayi I can't believe Leesa na d'auke da baby naa tsantsar farin ciki ya lullu6e shi ya rungume madam yayinda ita ma tashiga taya shi murna da fatan Allah ya sauke Haleesa lafiya Madam tad'ago fuskarshi ka je tana d'akin Hannah in ka tarrarda ita tana bacci kada katashe ta ka jira har ta falka da kanta.
  "Cikin zumud'i Ya mik'e yanufi d'akin yana shiga ya yi tsaye turuss.....sakamako hango gado da ya yi ba Haleesa akai sai ya yi tunani ko tana bathroom, phone d'inshi ya yi ringing alamar shigowar text yafito da wayar daga aljihunshi Lessa! Yafad'a a baiyane hannunshi na rawa yashiga karanta text d'in yana gama karantawa yajuya da sauri a parlour ya had'u da madam ya zaiyane mata abunda ke faruwa dariya ta yi sosai tace, ae ni tuni na hal6o jirginku kawai dai na zuba muku Ido ne naga iya gudun ruwanku tun da kun shirya kanku shikenan saidai ina rok'onka son ka lalla6a ta kasan masu juna biyu basason 6aci rai kai kuma ga ka da 'yar banza zuciya sai ka saka hak'uri al'amuranka Ku zauna lafiya.
   "Insha Allah sweetheart ba za'a k'ara samun matsala tsakaninmu ba wance ma Akasi ne madam ta yi dariya tace ka gaida Ammi saboda nasan can kanufa Habeeb ya yi dariya had'e da juyawa a compound yatarar da Bala yana cin abinci, hannu kawai ya mik'a mishi bani car key"
  ''Da mugun mamaki Bala yace lafiya boss ina za ka je ne"? Bara ka jira na gama cin abinci mu tafi tare ba"?
  "Murmushi Habeeb ya yi kai dai bani key na hutashe ka ka zauna ka ci abincinka cikin kwanciyar hankali, Bala ya mik'a masa key ya kar6a yanufi mota da sauri ya yi mata key ya fizgeta da k'arfi yafice matsiyacin gudun da Habeeb yake tsulawa yasa ya iso gidansu Haleesa cikin d'an k'ank'anin lokacin.
   Direct parlour Ammi ya wuce zaune yatarar da ita bayan sun gaisa suka shiga firar duniya sama-sama yake jin abunda Ammi take fad'a tunani yake ta ina Haleesa za ta 6ullo kuma yana jin kunya ya tambaye Ammi ina take.
  Kamal ya yi sallama yashigo hannunshi rik'e da baqar Leda yana ganin Habeeb yashiga murmushi ya mik'awa Ammi Leda Ammi ta katse shi ta hanyar cewa ina canji na kamal"?
  ''Ammi na biya mai adaidaitasahu da yadauko aunty Haleesa da chanjinki.
  ''Ammi ta zaro ido tace wace Haleesa"? ba dai tanan gidan ba domin ni banganta ba   "A rikice Habeeb ya mik'e yarik'o hannun kamal muryarshi na rawa yace kamal ta ina ka ga Leesa ta bi"?
  "Kwantar da hankalinka yaya Habeeb aunty Haleesa ba za ta 6ace ba tana nan cikin gidanan.
 Tana cikin gidanan a ina"? Ammi tafad'a had'e da mik'ewa.
  D'akinta mana kamal yafad'a yana dariya da sauri Habeeb yajuya yanufi d'akin har yana had'awa da tuntu6e Ammi tace kai Habeebu ka yi hankali mana kad'a garin sauri ka cire 'yan yatsunka yayinda Habeeb bai Masan me Ammi take fad'a ba muradinshi ya yi tozali da Leesa yana shiga d'akin ya bango ta kwance tana sharar bacci abinta. Ajiyar zuciya ya yi yanufi wajenta ya zare teedy bears d'in da rungume ya maye gur6in teddy ta hanyar shigewa jikinta kamar a mafalki ta shak'i k'amshin perfume d'inshi a hankali ta ware idanunta akan kyakyawar fuskarshi yasaki mata tsadad'en murmushi k'ara shigewa ta yi jikinshi ya  rungume ta d'ayan hannunshi na cikin rigarta yana shafar cikinta _Leesa kin haifar mun da farin ciki marar misaltuwa Allah yaraya mana abunda ke cikinki ya sauke ki lafiya_
  "Ameen Haleesa tafad'a ta zare jikinta daga nashi tadauko bisa gado tashiga bathroom ta wanke bakinta da fuskarta tadawo kusa da Habeeb ta zauna ta daura kanta bisa kafad'arta _yaya Habeeb naga abun arzikin da ka yi wa zuri'ata na go........da sauri yarufe mata baki da hannunshi karki gode mun kin cancancin fiye da hakan agareni Leesa duk abunda na yi wa zuri'arki tamkar zuri'ana na yiwa.
  "Hawaye farin ciki suka wanke mata fuska rungume ta yi yashiga bubbuga bayanta, kinsan kukanki yana d'aya daga cikin abunda yake d'aga mun hankali a duniya"?
  D'agowa ta yi ta share fuskarta, cikin shagwa6a tace kukan farin ciki ne yaya Habeeb.
  "Ba kuka za ki yi ba Leesa anan za ki nuna farin cikinki yanuna lips d'inshi da yatsa murmushi ta yi ta matsa daf da fuskarshi ta had'e bakinta da nashi tabbas salonta ya rikita Habeeb domin har yafara fita daga hayyacinshi, saida ta taro shi ta hanyar rad'a mishi _karka manta my Handsome Don kana gidan in-law d'inka fa_
  "Saketa ya yi da sauri yashiga rufe bottoms d'in rigarshi sai dariya take mishi kallon k'asan ido yake aika mata d'auke da manufar zan kamaki ne.
  ''Mik'ewa ta yi tafita ya bi bayanta da gudu tashiga parlourn Ammi tafad'a jikinta Ammi, Ammi naa nayi kewarki tureta Ammi ta yi kin yi kewa na shine ki ka shigo gidanan batare da nasani ba"?
  ''Am sorry Ammi naa koda nashigo gidanan bacci nakeji sosai ina baffa naa da yaya salman"?
  "Baffa yafita shi kuma ban inda yake ba kinsan yatarkato aure zaman gida ba nashi bane Murmushi Haleesa ta yi wai nikan Ammi sai yaushe za ki fara fad'ar sunan yaya salman"?
  "Bansaniba Ammi tafad'a tana hararar Haleesa kyalkyalewa da dariya Habeeb da Haleesa su ka yi Ammi ta mik'e tsaye tace bari nabar muku parlourn tun da na fahimcin abun naku iya shege ne tafice tabarsu suna kwasa dariya abinsu daga bisani Haleesa ta dubi Habeeb tace my handsome Don zan shiga gidan baba Audu na gaishe su.
   ''Mu je na rakaki kada kitafi ke kadai dodo yakamaki, dariya Haleesa ta yi had'e da cewa uhum....su dodo manya a tsakar gida suka isko Ammi zaune tana gyara alayahu Haleesa tace Ammi mu tafi gidan baba Audu"!
  "Ammi tad'ago had'e da cewa Adawo lafiya Habeeb ya yi k'asa da murya yace Amminmu yau miyan alayahu za'a yi mana"?
  "Murmushi Ammi ta yi eh! Amma kuma bansa da Ku ba saboda bansan da zuwanku ba.
 "Habeeb ya Sosa k'eya yace fad'a kawai ki ke yi Ammi nasan baffa ne za ki bamu koh Leesa naa"?
Dariya Haleesa ta yi had'e da gyad'a kai suka juya yayinda  Ammi ta yi murmushi  tace in Ku je gidan inna mairo tabaku ni kan ban girka da Ku ba.
 Mamaki Haleesa take yi yaushe shaquwa mai k'arfi tashiga tsakanin Ammi da Habeeb nan take ta tuno da margayi yaya Habeeb haka yake wasa da Ammi idanunta suka ciko da hawaye da sauri ta mayarda su tun kafin Habeeb yagani ya tuhume ta a haka suka shiga gidan baba Audu sallama Haleesa tashiga rafkawa Zainab ta leqo tana arba da Haleesa ta daka tsalle ta rungume ta Habeeb ya matsa kusa da su yace a hankali zainab kinsan ba ita kadai bace.
  "A shagwa6e Haleesa ta turo baki uhum... Yaya Habeeb Kadàina tona min asiri mana harararta Habeeb ya yi Zainab ta kyalkyale da dariya tace yaya Habeeb ashe musame k'aruwa shine baka fad'a min ba"?
Bashine yanzu nake fad'a miki ba Leesa na k'ok'arin hanawa wai Karna tona mata asiri da wannan drama suka k'arasa shiga parlour inna mairo ta yi matuk'ar farin ciki da ganin Haleesa musanman da ta fahimcin Haleesa na zaune lafiya da mijinta cikin tsokana Habeeb ya dube inna mairo yace innataa, Allah yasa kinada fura a gidanan"? saboda nasan ke ba irin Ammi bace a koda yaushe za'a tarar da fridge d'inki da fura.
  Harara inna mairo ta zuba mishi had'e da cewa banida fura.
Zainab ta tashi da sauri tanufi fridge tadauko jug mai d'auke damamiyar fura ta mik'awa Habeeb tun safe ta dama maka tana zuba idon zuwanka Zainab tak'arasa magana tana kallon inna mairo tana dariya,kiran sallah magarib ne yafitarda Habeeb daga gidan yanufi masallacin bayan Haleesa ta yi sallah inna mairo tashiga yi mata nasihar zaman aure   daga bisani inna mairo tasa kuka saboda ta tuno da marigayi yaya Habeeb da yanzu cikinan da Haleesa take d'auke da shi nashi ne da kyar Haleesa da zainab suka rarrashin inna tadaina kuka Haleesa tayi mata sallama takoma gida....

Jeeddah Aliyu
[03/01 8:37 am] aliyujeeddah: [27/12 1:50 pm] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

*°°°°In Dedication°°°*
*Shehu Aliyu Family's*

              *100*

_the End_

~~A parlour ta iske Habeeb da Ammi zaune Habeeb ya yi rashe-rashe suna zuba fira shi da Ammi Haleesa ta zauna  asanyaye Ammi ta tashi ta kawo musu abincin, loma 1-2 Haleesa ta yi amai yataso mata ta mik'e da gudu tafice tsakar gida tadinga kwara amai Habeeb yabi yarud'e sai faman yi mata sannu yake. Ammi na mishi dariya yanda Haleesa bataci abincin ba shima kasa ci ya yi Ammi ta dubi Haleesa cikin tausayawa tace mekikeso a nemo miki"?
  "A kunyace Haleesa ta furta d'an wake murmushi Ammi ta yi had'e da fita kamar jira Habeeb yake yi Ammi tafita ya matso kusa da Haleesa ya rungumo rabin jikinta sannu Leesa babynaa yana wahalarda ke koh"?
  "Lafewa ta yi tana shaqar k'amshin jikinshi ta gyad'a kai alama eh! A shagwa6e tace ina mamaki yanda  nakejin tashi zuciya alhali ada ba haka nake ba.
  Karan hancinta Habeeb ya ja laifi babynaa ne so take kowa yasan tana kwance anan yak'arasa magana yana Shafa cikinta.
  "Ture hannunshi ta yi kai yaya Habeeb kana nufi har kafara za6e abunda zan Haifa"?
   "Ba za6e nake yi ba Leesa amma inaji a jikina kamar baby girl za ki haifa.
   Uhm.. Uhm... Ni gaskiya nafiso baby boy saboda muna da Imaan.
  Kafin yabata amsa Ammi ta yi sallama da sauri yasaketa ya koma wajen zamanshi plate Ammi ta mik'a mata mai d'auke da d'an wake yasha yaji da mangyad'a ga yankake cabbage a sama nan take yawun Haleesa ya tsinke yayinda Habeeb ya yatsine fuska cikin kyankyami yake kallo Haleesa tana cin d'an wake tana gyad'a kai alamar da ke nuna ba k'aramin dad'i ya yi mata ba.
  Haleesa tacinye d'an wakenta Tass...ta sud'e plate ta yi gyatsa.
 Basu baro gidan ba saida baffa yadawo farin ciki sosai baffa ya yi da ya ga Haleesa Sai around _9:00pm_ suka suka yi sallama da baffa da Ammi.
   "Habeeb ya yi parking dai-dai  _Ni da yaya Habeeb tailoring center_ a rikice Haleesa take kallonshi hannunta yarik'o Leesa mu je ki ga shagonki da kanshi ya bud'e mata k'ofar mota tafito suka shiga shagon yaran da ke shago suka shiga gaida Habeeb Hasheem yace _sannu da zuwa Boss"_
  ''Yauwa Hasheem ya aiki"?
   "Alhamdulillah boss!
  Yau dai ga big boss d'inku na kawo muku Habeeb yak'arasa magana had'e da kallon Haleesa.
  ''Murmushi Haleesa ta yi ta dubi hasheem tace chief tailor da fatan baka had'a go slow a shago"?
Harararta hasheem ya yi yace ke kuma yaushe ki ka yi baki"?
Karaf d'aya daga cikin yaran shagon Wanda tun zamani margayi Habeeb yake zaune a shagon mai suna shamsu yatarewa Haleesa ta hanyar cewa dama can! Tana da baki Kaine ba ka gani.
  "Habeeb yace kyalleshi kawai shamsu, idan bai daina tsokanar matata ba sai na yi mishi tsiya ta hanyar d'auke shi shagonan na mayarda shi Lagos dama gashi yafara soyayya shiyasa yake lalacin a shago.
  Gaba d'ayansu suka yi Dariya Habeeb yarik'o hannun Haleesa ya kalli Hasheem yace idan da akwai matsala ka kirani a waya da haka suka fita daga shagon.
  "Kan hanyarsu na zuwa gidan madam Hindu Haleesa ta mayarda hankalinta wajen Habeeb cikin sanyi murya tace nayi mamaki yanda ka gyara ni da yaya Habeeb tailoring center musanman yanda nasan kana kishi da ainihin mai shagon tak'arasa magana had'e da sadda kai k'asa.
  "Murmushi Habeeb ya yi hannunshi d'aya yasa yarik'o hannunta yayinda d'ayan hannun nashi yake rik'e da steering yace Leesa na farfad'o da wannan shagon ne a dalilinki ba zan manta ba wata rana na nasame salman a shago na gaya mishi na bashi aiki a company na har nake tambaya wai meyasa suka sakawa shagonsu suna _NI DA YAYA HABEEB TAILORING CENTER_
Saida ya yi murmushi kafin yabani amsa yace a lokacin da za su bud'e shagon suna mahawara akan wane suna za su sanyawa shagon, kwatsan sai margayi Habeeb ya tambayeki sunan da yadace su saka da bud'an bakinki sai ki ka ce _NI DA YAYA HABEEB_ a dalilinki sunan shagon yasamu asali, yace saidai ahalin yanzu suna fuskanta na rashin customers a dalilin telolinsu sun tsofa kullum cikin gyara suke wannan matsala ita takesa su d'auki dogon lokacin basu gama d'inki yayinda customers suka danganta hakan da rashin cika alqawalin shiyasa shagon ya duk'ushe Wanda suna daf da rufe shi, ni kuma tun daga lokacin da salman yabani wannan labarin na k'udurta sai na faranta miki rai ta hanyar fad'ad'a wannan tailoring center a halin yanzu na bud'e miki tailoring center har guda 3 d'aya a Abuja akwai wani a Lagos anan Yola kuma akwai guda d'aya indan ki ka had'a da na unguwarku guda 4 kenan burina Leesa _NI DA YAYA HABEEB TAILORING CENTER_ ya yi suna a fad'in Nigeria shiyasa na nemo kwararin mad'unka daga Senegal na zuba a tailoring center d'in duk karshen wata nake kar6a k'udin da suka tara nayi matuk'a mamaki a last month kudin da suka bani a matsayin na aikin da suka yi na wannan wata kud'i ne masu yawan gaske tun lokacin na tabbatar da d'inki babbar sana'ace ta hannu sai na yanke shawara na dinga shigo musu da tsadadun textiles suna d'inka ready made ana siyarwa kwara d'aya Ana kuma siyarwa akan sari cikin d'an k'ank'anin lokacin na tara miki k'udi masu kaurin gaske a account dama inajira irin wannan rana ne na sanarda ke.
   "Har Habeeb yadasa aya Haleesa na kallonshi hannunshi da ke sark'e da nata ta sumbata, na gode my handsome Don tabbas ka sanyani cikin farin ciki ba zan 6oye maka my handsome Don a lokacin da yaya Habeeb yarasu sai nake ganin kamar daga kanshi ba zan k'ara samun wani d'an namiji da zai so ni kamar yanda yake sona ashe wauta nake yi ashe za ka shigo rayuwata ka so ni fiye da son da yaya Habeeb ya yi mun, hak'ik'a zuwanka rayuwata alkhairi ne inasonka mijina Kaine abin alfahari na tak'arasa magana tana hawaye.
  "Dai-dai lokacin da suka iso gidan madam Hindu Habeeb ya yi parking yakashe mota yad'ago fuskar Haleesa halshenshi yasa ya lashe hawayen fuskarta, Banaso na k'ara ganin hawaye akan fuskarki koda kuwa na farin ciki ne.
  "Murmushi ta yi had'e da cewa your wishes is my command.
 "Habeeb ya bud'e k'ofa yafito ya bud'e mata ita ma tafito suka nufi cikin gidan a parlour suka iske madam Hindu da aunty Mami da mugun mamaki madam take kallonsu daga bisani ta kawo karshen mamakin nata ta hanyar cewa Ku kuma daga ina"?
  "Habeeb yashiga Sosa k'eya dama sweetheart Leesa ce nadawo miki da ita yayinda Haleesa ta sadda kai k'asa tana wasa da gefen hijab d'inta.
   "Dariya madam Hindu da aunty Mami suka yi madam tace ae ni tuni na sallame Ku daga gidanan, cikin tsananin farin ciki Habeeb ya mik'e yanufi kujerar da madam take zaune ya rungume ta thank you my sweetheart you really make me happy you're the best Mom in the eye's of the would I love you so much mom muaah....ya sumbace kumatunta.
   "Dariya madam ta yi  ta shafi sumar kanshi I love you too son tashi ka d'auki matarka kutafi.
   "Habeeb ya mik'e yana murmushi ya dubi aunty Mami yace lah......ashe aunty Mami tana parlour nan.
  ''Harararshi aunty Mami ta yi sai yanzu idanunka suka bud'e koh"?
Yana dariya ya matsa daf da aunty Mami yarad'a mata idan Leesa tana gaba na idanuna rufewa suke yi aunty Mami ina fa son yarinya nan sosai sonta yabi jinin jikina yak'arasa magana yana dariya.
  "Zaro ido aunty Mami ta yi tana tafa hannaye da sauri Habeeb ya katseta ta hanyar _cewa aunty Mami karki fad'awa sweetheart it's secret between me & you_ aunty Mami da madam suka kyalkyale da dariya yayinda Habeeb yarik'o hannun Haleesa suka fita daga parlour.
   "Koda suka iso gida _10:15_ agaugauce Habeeb ya had'a musu ruwan wanka suna fitowa daga wanka da kanshi ya shafawa Haleesa mai yasaka mata sleeping dress suna manne da juna bacci ya yi awon gaba da su.

*washe gari*
Sai around _11:30am_ Haleesa tafalka koda tashi har Habeeb ya yi wanka yashirya, yana zaune kusa da ita murmushi yasake mata ita ma ta mayar mishi da martanin murmushin nashi tasauko daga bed tanufi bathroom ta yi wanka tafito daure da towel Habeeb yatayata ta shirya cikin atamfar super Sheraton ta yi matuk'ar kyau ruwan Lipton kadai tasha Rarrashinta Habeeb yashiga yi haba! Leesa ruwan Lipton ba zai rik'e ki ba ki daure ki cin abinci mai d'an nauyi ko don saboda babynmu.
  "Yatsine fuska ta yi kamar za ta yi kuka banaso yaya Habeeb in naci amai zan yi ni dai katashi ka kaini gidan Hannah maybe a can na iya cin abincin tak'arasa magana ciki shagwa6a.
  "Da sauri Habeeb  yatashi yadauko mata mayafinta suka fice a parlour suka iske Hannah kishingid'e tasha make-up tafito amarya sak cike da farin ciki ta rungume Haleesa cikin zolaya ta dubi yaya Habeeb tace Daddyn twins ina kwana"?
   ''Dariya Habeeb ya yi ke kuma twins ki ke mana fata"?
"Gyad'a kai Hannah ta yi yayinda Haleesa ta tabe baki had'e da cewa kwaji da shi Habeeb yace wai ina Mus'ab ne ko har yafita ne"?
 "Murmushi Hannah ta yi tace yana kitchen watakila karar TV yahanashi jin muryarku.
  ''Zaro ido Habeeb ya yi me yake yi a kitchen"?
 Breakfast yake had'a mana Hannah tafad'a had'e da kallon Habeeb.
Kyalkyalewa da dariya Habeeb da Haleesa suka yi mik'ewa Habeeb ya yi yanufi kitchen d'in yana mai cigaba da dariya tun kafin yak'arasa shiga kitchen ya hango Mus'ab yana tsame chips daga mai cike da tsokana Habeeb yace ango kasha k'amshi gaba d'aya ka d'umama gidanan da k'amshi.
  "Mus'ab yajuyo ya dube Habeeb ya d'aure fuska uban me ka zo yi da sanyin safiya a gidana Lamido"?
 "Habeeb yak'ara kwashewa da dariya me da wuk'a angon kitchen abincin amarya na zo ci abun mamaki sai na tararrada ango a kitchen amarya na hakince a parlour
[28/12 1:46 pm] aliyujeeddah: Wannan kuma wane irin Sabon system ne"?
  "Mus'ab ya gallawa Habeeb harara cike da takaicin yace bansaniba yanzu kafad'a min muqasudin zuwanka gidana karka manta al'adace friends suna yi wa ango rakiya  darensa na farko a gidansa sama da k'asa mun nemi ka muka rasa khaleel yakira ka a waya da ka d'aga kira me kace da shi"?
  "A yatsine Habeeb yace cewa nayi da shi ni yayan amarya ne ba abunda zan je yi a gidanta.
  ''Hum.....To yanzu gayamun me yakawo ka"?
  "Abincin ango na zo ci ko ba za'a bani bane"? Habeeb yak'arasa magana yana dariya murmushi Mus'ab ya yi yace ka dai anyi d'an iska wallahi karka manta Lamido ni fa in-law d'inka ne bai dace kana mun iya shege ba.
  Habeeb yak'ara kyalkyalewa da dariya Haleesa ta dubi Hannah baki bud'e tace kai kamar fa sautin dariya yaya Habeeb nakeji"?
  "Tabe baki Hannah ta yi ba kama bace shine watakila yana yi wa my love dariya don yaganshi a kitchen.
  "Haleesa ta yi dariya tace in haka ne bari nima na leqa naga dariyar yaya Habeeb kinsan Allah idan yaya Habeeb yana dariya jin nake kamar na hadiye shi saboda yanda take mugun k'ara masa kyau. tak'arasa magana had'e da mik'ewa tanufi kitchen girgiza kai Hannah ta yi tace Allah ya yi miki sauki Haleesa ta mik'e da kyar tabi bayan Haleesa.
   Kai,kai Kai, Haleesa tafad'a had'e da zaro ido me nake shirin gani Mus'ab yaushe ka zama chef"?
 "Kafin Mus'ab yabata amsa Hannah tariga shi ta hanyar cewa ka ga my love kyallesu kawai ae gwara kai da wani tak'arasa magana had'e da boyewa bayan Mus'ab.
  "Katuwa harara Habeeb yadanna mata da wa ki ke"?
  Mus'ab yace da kai take ko akwai abunda za ka yi"?
 "Wallahi yanzu ina lakad'a mata duka ba ruwana da zamanta amarya, kuma ba abunda za ka iya.
  "Mus'ab ya ja tsaki yace za ka iya saboda ba hankali ne yawadace ka ba don haka ja matarka Ku koma parlour duk abunda Ku ke so zan had'a mu Ku ni dai fatana mu rabu lafiya da kai batare d kata6a min lafiyar mata ba.
  "Haleesa tarik'o hannun Habeeb zo mu koma parlour my handsome Don ko yak'i ko yaso ya zame masa dole yadafa yabamu, mu ci.
Habeeb ya yi dariya yace haka ne fa my Leesa kinsan Mus'ab kwarare ne a faggen girki cikin dariya suka fice daga kitchen d'in.
Akan 3 seater suka zauna k'afafunta ta daura a cinyoyinshi yana ja yatsunta a hankali Mus'ab yashigo d'auke da k'aton tray a tsakiyar rugs carpet ya ajiye tray kallo d'aya ya yi musu yadauke kai yajuya kitchen ya kwaso plate yayinda Hannah take rik'e da flask mai d'auke da ruwan zafi, Mus'ab ya dube su yace in kun ga dama Ku sauko k'asa Ku yi wa kanku serving Habeeb yarik'o hannun Haleesa sauko k'asa my Leesa na yi miki serving mak'e kafad'a ta yi banacin.
   "Habeeb ya yi k'asa da murya haba! Leesa ke fa ki ka ce in mu zo gidanan za ki ci abincin shine dalilin da yasa k'afata ta tak'o gidanan Dan Allah ki daure ki ci ina jin tsoro kada yunwa ta ta6a mana babynmu.
    "A shagwa6e tace indan naci amai za yi ni yanzu d'an wake ko shinkafa da mai da yaji nakeso cin.
  ''Mus'ab ya kalli Hannah suka kyalkyale da dariya Habeeb ya galla musu harara yace lalura ce bata wuce ta hau kan matarka ba.
    "Mus'ab yace  katashi kashiga kitchen domin zama bai sameka ba.
   "Tabe baki Habeeb ya yi to ae ni ba d'an daudu bane irinka yak'arasa magana had'e da dauko phone d'inshi ya kira Ammi ya fad'a mata ta ta yi wa Leesa d'an wake da shinkafa da mai da yaji Bala zai zo ya kar6a yakawo mata gidan Hannah.
  "Yana gama waya ya yi wa Mus'ab gwalo had'e da cewa shiga kitchen sai Ku Mus'ab marasa dabara Sabon babi na fira suka bud'e sai sautin dariyarsu ka ke ji a haka Bala yashigo yasame su ya ajiye foodflask d'in hannunshi yanemi kujera ya kame Haleesa nagani d'an wake kamar za ta yi hauka nan take ta zuba a plate tashiga ci shinkafa kuma ta ajiye sai da rana ta cin.
  "Anan Habeeb yabar Haleesa suka fita shi da Mus'ab da Bala sai misali k'arfe _8:30pm_ Habeeb ya dawo d'aukar Haleesa.
   "A washe gari Habeeb da Haleesa suka koma Abuja suka bud'e Sabon shafi na soyayya kamar za su cinye junansu, in fita Habeeb ya yi suna manne da waya idan kuma ya yi tafiya adaddafe yake gama abunda ya je yi yadawo, musanman yanzu da cikin Haleesa yashiga wata na 6 ya yi girma sosai.
Haleesa na kwance akan 3 seater Imaan na matsa mata k'afafunta Habeeb yashigo yana waya hannunshi yasa yadauke kanta ya zauna ya aza kanta bisa cinyoyinshi yana gama waya ya kira sunanta Leesa!
  "Na'am
  "Tafiya Lagos yakamani amma ina gani ba zan wuce _1 week_ ba.
  "Bata fuska Haleesa ta yi kamar za ta yi kuka ni gaskiya my handsome Don banaso wannan tafiya da ka ke yi sanin kanka ne duk lokacin da ka yi tafiya ba wani baccin kirki nake yi ba.
   "Ni ma Leesa ba so tafiya nan nake yi ba banida yanda zan yi ne ba zan wuce _1 week_ ba zan dawo kinji"?
  "Shikenan Allah yadawo da kai lafiya.
  "Ameen Leesa naa.

_3 months later_
Haleesa tana kitchen tsaye hannunta rik'e da wuk'a tana gyara kankana Habeeb yashigo ya rungumeta ta baya ya zura kanshi ta kafad'arta yabata peck a kumatu mai ciki sarkin kwad'ayi me ake had'a mana ne"?
  "Fruits salad ne tun safe na tashi da kwad'ayinsa.
  Zare jikinshi ya yi daga nata ya yi tsalle ya haye kitchen cabinet d'an Sam mini kankana nan naganta jajir da alama za ta yi zak'i harararshi ta yi tadauki yanka guda d'aya tasaka mishi a baki yana tauna yana lumshe idanu.
   "Haleesa tace da zak'i koh"?
  Gyad'a kai ya yi eh! Saida kin fita zak'i ina gani zak'in hannunki ne ya shafe ta shiyasa ta yi zak'i.
  "Girgiza kai ta yi had'e da murmushi tana gama had'awa tasaka ice block Habeeb yadauka mata, bowl d'in suka nufi parlour in tayi spoon 1 tasakawa Habeeb suna gama shan fruits salad marar Haleesa tafara murd'a tun tana cize lebb'e sai gashi tadawo wash..... Wash... Bayana marata a rikice Habeeb yad'ago ta Leesa ko haihuwa ne"?
  "Da kyar Haleesa tace ita ce saboda randa na ke a duniya banta6a jin masifar ciwo irin wannan ba.
  "Da k'arfi Habeeb yashiga kwadawa yarinye kira sai gata tashigo Imaan tana biye da ita ki je bedroom d'in Leesa akwai trolley brown colour ki bud'e ki dauko kayan baby za mu tafi hospital.
   "Cikin d'an k'ank'anin lokacin sai ga yarinye tadawo d'auke da medium size na trolley Habeeb yadauki Haleesa yafice tun kafin yak'arasa compound yashiga kwallawa Bala kira yi maza Bala ka dauko mota da gudu Bala yanufi parking lot yajanyo mota Habeeb yasaka Haleesa ya dubi yarinye yace kin saka kayan a mota"? Eh nasaka a seat d'in gaba.
  "Shikenan ki d'auki imaan ku koma cikin gida sai mun dawo
 Bala yafizgi mota yanufi gate maigadi ya bud'e musu gate suka fita.
  _Some hour's later_
Haleesa tasauka lafiya tasami bouncing baby boy mai kama da Habeeb, farin ciki wurin Habeeb ba kama hannun yaro bayan drip d'in da aka sa ma Haleesa yak'are akayi discharged nata suka yo gida, washe gari suka bi flight zuwa Yola ranar suna baby yaci sunan mahaifin Habeeb Abdulmajeed suna kiranshi da Haleel.

_6 years later_

Habeeb yana zaune a palour hannunshi rik'e da news paper wata 'yar kyaKyawa yarinya wance shekarunta ba za su haura 2 ba tadanno da gudu tafad'a jikin Habeeb cikin muryarta ta yarinta, tace Daddy boyeni na yi fanna.
  Da sauri Habeeb ya 6oyeta bayanshi Imaan yarinya 'yar shekara 13 tafito daga d'akinta hannunta rik'e da exercise book kamar za ta yi kuka tak'arasa wurin Habeeb tanuna mishi book d'in da ke hannunta Daddy kalli abunda Hibba ta yi mun da littafi.
  "Habeeb yad'ago ya kar6i littafi ya yatsine fuska nagani ta yaga sau nawa ina gargad'inki ki dinga ajiye books naki Inda bara ta iya daukowa ba da yake ke mai kunnen k'ashi ce sai ki ka yi biris da maganata wannan shine maganinki.
  "cikin pity face tace Daddy karatu nake yi fa gobe za mu fara exam nashiga bathroom na barshi akan bed koda nadawo na iske ta yaga mun, kuma uncle yaga book d'ina ya yage dukana zai yi tak'arasa magana hawaye na zuba akan cute face nata.
   "Carelessness naki ne yajanyo miki sai hak'uri gobe zan baki k'udi ki siye wani.
  "Daddy Note d'in da ke ciki fa"?
   "Dafe goshi ya yi daga bisani yadaka mata tsawa ina ruwana da note sai ki yi copying in kuma bara ki iya ba sai ki bari kuka Imaan tasa a hankali take taka staircase tana sanye da lace Wanda yak'ara fitowa da ainihin kyauta tun kafin tak'araso cikin parlour tafara fad'a wai yaya Habeeb me yasa ka ke yi haka ne huh"?
Kafin kowa sanin halin Hibba a gidanan Sam bata jin magana yarinya nan shegiyar 6arna ne da ita har ta tsiya harararta Habeeb ya yi yace duk abunda Hibba ta yi laifinku yafi nata yawa saboda Ku Ku ke ajiye abu anyhow Haleesa tana k'arasowa tafizgo Hibba da ke bayan Habeeb tana zarar ido zo nan beran gida yau sai na Zane ki ihu Hibba tashiga yi Ayyo Daddy ce kar unty ta jane ni hannunshi yasa yad'ank'e hannaye Haleesa yashiga murza mata yatsu da k'arfi lumshe idanu ta yi daga bisani ta ware idanun nata akan fuskarshi shu'umin murmushi yasake mata, ya yi k'asa da murya Leesa a gabana za ki daki little Hindu"?
  "Turo baki ta yi Uhm....laifin duka ta yi shiyasa zan dake ta.
  Da k'arfi yajanyo ta tafad'a jikinshi ya dubi Imaan da ke tsaye tana hawaye ya mik'a mata hannunshi zo nan my Angel kyalle Hibba zan yi mata fad'a bara tak'ara yaga miki littafinki ba kinji"?
 Gyad'a kai ta yi had'a da rik'e hannunshi yajanyo ta ya yi ta zauna akan d'ayan cinyarsa yayinda Haleesa take zaune a cinyarshi guda Hibba ta kama wuyanshi ta leqo da kanta Haleesa tajuya ta dubi Haleel da ke zaune da Laptop a gabanshi yana buga game duk hayaniya da suke yi kamar ba bu shi a parlourn tace kai sarkin miskilancin c'mom join us ya mik'e yana yatsinar fuska bashida banbancin da Habeeb hatta yanayi tafiyarsu d'aya yashige jikin Haleesa, Habeeb ya kalli Haleesa yace na godewa Allah{s.w t} da ya albarkace ni da samunki a matsayin matata uwar 'ya'yana leesa samun agareni babban rabo ne ya zura hannunshi cikin aljihu yafito da zobe da k'udi ya aza mata a tafin hannunta, yace za ki tunawa da k'udinan saboda wannan zobe nasan ba za ki manta da shi ba"?
   "Zaro ido Haleesa ta yi ta kwanto a jikinshi yaya Habeeb ina kasami wannan zobe"?
Saida yaja karan hancinta sannan yace za ki tuna a Lagos lokacin da sweetheart tabaki documents ki bani a garin kar6a documents d'in na had'a da zobenki.
   "Harararshi Haleesa ta yi tace ka dai fizge documents ka kuma had'a da hannuna.
 Habeeb ya yi murmushi yacigaba da cewa wad'annan k'udi in za ki tuna had'uwar mu na biyu ana ruwan sama da Bala ya buge da mota ki ka fad'i kina gani ki ka kwasa da gudu, har na juya zan shiga mota naga kin jefarta da k'udi wannan N200 kuma a had'awar mu na uku da ki ka suma anan na zare N200 d'in daga hannunki yak'arasa magana had'e da cizon fatar kunnenta.
  "Ta lumshe idanu tace lalle yaya Habeeb ka iya ajiya.
  "Kina da matuk'ar mahimmancin a wurina Leesa shiyasa duk abunda yafito daga hannunki nakan ajiye shi batare da nagaji ba.
  "Haleesa ta kad'a eye's balls d'inta tace banida buri a rayuwana da yawuce *NI DA YAYA HABEEB* mu zama jini da anta sai gashi Allah yacika mun burina Habeeb ya kalleta gaba d'aya suka had'a baki su da yaransu ta hanyar cewa _we're Happy family......_

_TAMMAT BIHAMDULLAH_ Anan na kawo karshen wannan littafi abunda yakeda amfani a cikinsa Allah yasa ya amfani al'ummah musulmi inda nayi kuskure Allah yagafarta min Ameen.

*Godiya ta musanman ga Allah{s,w,t} da yabani Aron lokacin har na kawon karshen wannan labari Allah yak'ara mana so da k'auna Annabi rahama Annabi Muhammad{s,a,w}*

*Ina alfahari da ke*
_Aunty sis kyakyawawan halayenki yasa kowa yake sonki Aunty Sis ubangiji yabaki masauki a gidan aljanna Firdausi ba zan ta6a mantawa da k'aunarki a gareni inasonki Auntynaa_

*Banda kamarki*
_Fateema umar{Mrs umar} a koda yaushe ina alfahari da kasancewarki k'awa agareni Allah yasaka miki da alkhairi da irin k'aunar da ki ki nuna min_

*K'AUNARKU TA DABAMCE*
_Khaleesat Haydar Namcy ina ji da ke tamkar numafashina Allah yabarmu tare_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Alherin Allah yasauka miki a duk Inda ki ke Ummi A'isha Allah yabar zumuncin na gode da k'auna_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Bakina yarasa kalma da zai yi amfani da ita wajen gode miki Firdausi Sodangi amma kisani ina k'aunarki fiye da tunaninki_
°°°°°°°===°°°°°°
_Ina miki fatan alkhairi a duk inda ki ke Ayshat Dan sabo lemu ubangiji ya haskaka rayuwarki na gode sosai Allah yabar zumuncin_

*BAN MANTA DA KU BA*
Zarah BB
Haneefa Usman
Billy Giro
Billy special
Rukayya Dakaratu
Munay my in-law
Shafa Umar
Aysha gentle
Zee yabour
Stylish Bch
Autar Hajiya
Baby Amrah
Maman Shaheeda
Maman haneef
Rab'iat
Rasheedat Mrs kabeer
Ayshat Mazoji
Ash'nur
Wash.......hannuna ya yi ciwo da Wanda na kira da Wanda Allah bai nufi da in kiran sunanshi ba kusani jeeddah tana k'aunarku sosai.

_godiya agareki uwa maba d'a mamma kungiyar *®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Allah yak'ara daukaki yasa ki fi haka_

 _Ina godiya agareku members na:-_
*Ledies novels world*
*Jeeddah Aliyu fans*

Ni Jeeddah Aliyu nake cewa ku kasance tare da ni a cikin Sabon novel d'ina idan Allah mai kowa mai komai yanufa mai suna *SONKI NE SANADI*

Jeeddah Aliyu

No comments:

Post a Comment