[03/01 8:43 am] aliyujeeddah: [29/11 6:21 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```81```
~~suna had'a ido tasake masa murmushi Wanda ya haddasawa Habeeb mutuwar jiki ya ja iska, had'e da cizo lips d'inshi na k'asa Ya tsare ta da idanu kamar tsohon maye.
"Haleesa tak'arasa kusa da shi tana magana had'e da 'yar dariya yaya Habeeb na manta ba ka sha maganinka ba.
Tsaki ya ja Cike da takaici Yace dama shine dalilin da yasa ki ka shigo min room a wannan lokacin"?
Eh mana tafad'a had'e da dauko ledar magani ta zauna a gefen gado.
"Ranshi a 6ace ya mik'e zaune yafisge ledar daga hannunta ya jefar ya rik'e hannayenta duka biyu can! K'asan mak'oshi yace ke! Wannan magani da za ki bani bashida amfani a tare da ni bara iya warkarda cutar da nake d'auke da ita saboda haka ko kin bani bara sha ba yak'arasa magana yana kallon cikin idonta.
Haleesa tarausayar da kai had'e da marairaice murya tace ba don kace na yi maka shishshigi ba da nace wane irin cuta ne yake damunka"?
''Har Habeeb ya bud'e baki da sunan ya zaiyano mata buk'atarsa sai kawai wani 6angare na zuciyarsa ya kwa6e shi _haba Habeeb kai fa jarumin namiji ne Wanda ba ya sauya magana ko ka manta da irin furucin da ka yi akanta ne"?_ _kana furta mata abunda ka ke da buk'ata za ta d'auka kamar kana sonta ne alhali kai ba sonta ka ke yi ba karka sake ta fahimce halin da ka ke ciki domin girmanka zai zu6e a wurinta_
"Habeeb ya dawo daga duniyar tunani ya sauke ajiyar zuciya ya tsayar da idanunshi akan fuskar Haleesa, wance tun lokacin da ya afka tunani ta kafenshi da ido jikinsa a sanyaye yasake mata hannu ya juya mata baya.
''Haleesa ta yi shiru tana kallon bayansa tsawon lokacin ta dauka a haka daga bisani cikin sanyin murya ta kira sunansa, _yaya Habeeb_
A fusace ya mik'e zaune ya galla Mata harara _look I don't want any disturb now so leave my room_
Haleesa ta kad'a kai batayi mamakin jin wad'annan kalamai daga bakin Habeeb ta mik'e tsanm! Sum-sum tafice Batare da ta furta uffan ba
yayinda Habeeb yabita da kallo ya ja iska yafesar yana tsotsan bakinshi, ya koma ya kwanta da yarufe ido Haleesa yake gani yakasa bacci sai fama juyi yake akan bed bacci ya k'auracewa idonsa, ji yake yi kamar ya mik'e ya je room d'inta ko k'amshin jikinta yashak'a ya tabbata zai same sauki abunda yake ji a game da ita a haka bacci ya sud'ad'o ya sace shi batare da ya nemawa kansa mafita ba.
''Ta6angare Haleesa kuma ita ma hakan ce tafaru da ita da ta rufe idanu Habeeb Lamido take gani, yayinda wani bak'on al-amari yake ziyartar jininta da kyar tasamu baccin yadauke ta.
**********************
_WASHE GARI_
_10:15am_
Haleesa na tsaye a dining area tana jejjera breakfast akan dining table, tana kamallawa tanufi part d'in Habeeb.
"Kwance ta tararda shi akan _3 seater_ idanunshi a rufe jin sallamarta yasa ya bud'e idanu kallo d'aya ya yi mata yadauke kai _ina kwana yaya Habeeb ya lafiyar jiki"?_
"Lafiya! Ya amsa ya a dak'ile.
Breakfast na jiranka tafad'a cikin murmushi
Tabe baki ya yi a tsarina sai 11:00 o'clock nake taking breakfast yak'arasa magana had'e da lumshe idanu.
"Haleesa ta yatsine fuska tanemi kujerar da ke facing d'inshi ta zauna, ta rafka tagumi.
''Ke! Ya kira sunanta a nitse da sauri Haleesa ta dube shi, still idanunshi a rufe ke! Zo nan yak'arasa magana had'e da yafito ta da hannu jiki a sanyaye Haleesa ta mik'e tanufi wurinshi.
''Ganin idanunshi a lumshe yasa tace yaya Habeeb gani
Na ganki mana ko angaya miki ni makaho ne da za ki ce min ga ki yana magana ne had'e da bud'e ido d'aya
"Um.....Haleesa tafad'a tana turo baki ya gyara kwanciyarshi cikin isa da tak'ama yace tausa za ki yi min ina fatar kin iya"?
A tsorace ta waro ido umh......umh....a wane waje zan tausa ma"?
"Bayanshi yanuna mata hannunta na rawa tafara yi masa tausa da ta daura hannunta a bayanshi sai ta d'auke da sauri kamar wance take ta6a electric shock.
''Ran Habeeb ya yi matuk'ar 6aci lallai yarinya nan ta renani kalli yadda take ta6ani kamar tana ta6a kashi da k'arfi ya rik'ota yajuyo da ita ta gabanshi ya mik'e zaune ke! Wannan wane irin tausa ne ki ke min abun Sam ba armashi"?
"Haleesa ta turo baki cikin murya shagwa6a Wanda ita kanta batasan, lokacin da ta yi ba tace ni ban iya mai armashi ba sai kanemo Wanda ya iya ya yi maka.
Habeeb ya ja iska kamar yaci yaji yana ya motsa sumar kanshi yace amma kafin ki yi min sai na tambayeki kin iya me ki ka ce"?
''Oh! tafad'a tana murgud'a baki shiru ya yi yana kallonta
Ganin yadda ya tsareta da ido yasa tace yaya Habeeb yaji ka ci ne naga kana Jan iska"?
"Oh! Shima yafad'a yana murgud'a baki
Haleesa ta kyalkyale da dariya Allah yaya Habeeb wannan murgud'a bakin yayi maka kyau kamar karuwa k'auye
"Da k'arfi ya matse mata hannuta tasaki ihu saboda ba k'aramin zafin taji ba yak'ara fisgo ta tafad'a bisa jikinsa fusk'okinsu na daf da juna yanda kowanesu yana jin bugawar numfashin d'an uwansa can! K'asan mak'oshi yace ke! Ni za ki kira da karuwa"?
No;no yaya Habeeb ni ba da kai nake ba"
"K'arya ki ke yi da ni ki ke haka ko jiya ki ka kirani da suna barawo yau kuma da sanyi safiya kin kirani da suna karuwa ko karuwa ma ta k'auye don kin rainani koh"?
"I'm sorry yaya Habeeb sa6ul da baka na yi amma bara k'ara ba tak'arasa magana cikin shagwa6a.
Janye ta ya yi daga jikinsa ya mayarda ita bisa kujera a hankali yake matsa mata jikinta, very slowly yace kin ga yaddda ake tausa mai armashi oya tashi ki yi mun da kyar Haleesa ta mik'e tsaye yayinda Habeeb ya koma ya kwanta, ba yadda Haleesa ta iya dole tadinga tausa masa jikinsa kamar yadda ya yi mata.
''Tsawon lokacin ta dauka tana masa tausa a tunaninta ya yi bacci, sakamako shirun da ya yi da kuma yadda yake sauke numfashin a hankali take sand'a da suna ta tsire karaf yarik'e mata hannun.
''Idanushi a lumshe yace ina za ki tafi ne bayan ban sallame ki ba"?
''Allah yaya Habeeb nagaji gaba d'aya hannaye na sun yi zafi
Ya mik'e zaune yana mata kallon k'asan ido ya ja iska yace kin amince na biyo ki bashi anjima za ki k'arasa mun"?
"Gyad'a kai ta yi
Ki bud'e baki ki yi min magana kinsan na tsani wannan gyad'a kan naki"?
Murmushi Haleesa ta yi tace toh....na ji amma sake mun hannu kuma katashi mu tafi ka yi breakfast har _11:15am_ ta yi tana ne had'e da nuna masa wall clock.
"Habeeb ya lumshe idanu a zuciyarsa yace in kina tare da ni Sam bana jin yunwa a baiyana kuma sai yace mu je Allah yasa ba jagwalgwale aka yi min ba.
''Wai yaya Habeeb bara ka daina zance jagwalgwale nan ba koh"? Allah zan shiga strike.
Habeeb ya ja tsaki mintsine mata fatar hannu mace bata yi min strike, ballantana ke da bakya cikin tsarina yana gama magana yasaki hannunta yafice daga falon.
Haleesa ta bi shi da harara a zuciyarta tace qarya ne wallahi, saidai in ba ka shigo hannuna ba d'an rainin wayo.
********************
```DARE```
_8:30pm_
Haleesa tana zaune a gaban dressing mirror tana fesa perfume fuskarta tasha simple make up, ta mik'e tsaye tak'arewa kanta kallo daga bisani tanufi wardrobe ta bud'e ta yi tsaye tana k'arewa kayan da ke ciki kallo.
"Ta Ciro tummy skirt sky blue colour had'e da top purple colour tana kamalla saka kayan ta zari d'an siriri veil ta yi rolling tanufi part d'in Habeeb ta tura k'ofar falon tashiga baya cikin falon sai kawai ta nemi kujera ta hakince, ta kama buga game a wayarta.
''K'amshin intense men da tashak'a ya bata tabbacin Habeeb yashigo falon tad'ago dara-dara idanunta tasauke su akansa yana sanye da T-shirt blue colour da white colour crazy Jeans sumar kanshi tasha gyara sai kyali take k'asumba da ta cika masa fuska ta d'an kawowa ainihin kyausa cikass.....Haleesa na kyalla ido akan guiwar wandonsa taganshi a yagalgale ta waro ido had'e da dafe baki sai kace ta ga abun tsoro.
"tace yaya Habeeb bera ya yi maka tsiya ya cinye ma guiwar wando tak'arasa magana had'e da tintsirewa da dariya bakin rai Haleesa take kwasan dariya har da fad'owa daga kan kujera ta mik'e k'afafunta ita a dole ta ga abun dariya yayinda Habeeb Lamido ya yi tsaye hannayenshi zube cikin ajihun wandonsa yana kallonta cike da sha'awa saboda dariyarta ta yi mugun burgeshi.
"Ya yi murmushi ya shure k'afafunta ke dallah tashi villager kawai ni narasa wance irin k'addara ce tafad'o min na aure k'atuwar bak'auya irinki in ban da tsabar duhun kai irin naki ta ina ki ke tsanmani bera zai shigo gidanan da har zai cinye min wando"?
"Haleesa ta mik'e tsaye ta galla masa harara dallah! Malam dakata jiya ba yau ba karka kuskure kace za ka yi min yankar k'iri domin ba shiru zan yi ba a da ka ke da ikon wulaqanta ni na kyalle shima ba don ina tsoronka ba sai don biyayyar aure amma a yanzu ina mai maka albishir da cewa kan magge ya waye kana fad'a mun maganar banza nima ta wofi zan fad'a ma
yadda ka ke kuka k'addara ce ta had'a ka aure da ni nima haka nake kuka, kuma har abada bara daina zubar da hawaye nadamar aurenka da na yi tana k'arasa magana tajuya har ta Kai k'ofa tajuyo tace in ka ga dama ka zo ka cin abinci in kuma bara ka iya ba kaita tsayuwa har abusa 'kaho ba abunda yadame ni tak'arasa fita tabar Habeeb Lamido tsaye sake da baki tsananin mamakinta yahana shi motsawa.......
Jeeddah Aliyu
[03/01 8:45 am] aliyujeeddah: [01/12 7:37 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```82```
~~Tsawon lokacin Habeeb yadauka a tsaye ya kad'a kai yanufi part d'in Haleesa tana zaune a parlour yashigo ko kallonta bai yi ba ya ratsa ta gefenta yanufi dining table, ya zauna ya dube inda Haleesa take zaune yace ke! Magge zo ki yi min serving.
"Da sauri Haleesa tajuya saboda maganarshi ta yi mugun bata mamaki a tunaninta da yafito sai ya yi mata wulaqancin da yasaba, sai kawai taci karo da sa6anin tunaninta.
A fusace yak'ara cewa
"Ke ko bakyaji ne"?
Ta mik'e tsaye da sauri tanufi wurinshi fuskarta a daure ta zari plate ta yi serving d'inshi ta ajiye a gabansa.
Duk abunda take Habeeb yana kallonta yarik'on hannunta yana murzawa idaunshi na akan fuskarta, ita ma shi take kallo ya lumsashe idanunshi can! K'asan mak'oshi yace ke ni za ki yi wa rashin kunya koh"?
''Turo baki ta yi had'e da d'auke fuskarta tajuya tana kallon TV da ke manne a bangon dining area.
"A yatsine Habeeb yace wai ke wannan daure fuska na menene ni ban daure miki fuska ba sai ke ce za ki daure Min"?
"Haleesa tafisge hannunta daga rik'on da ya yi mata kacin abincin ka kada ya sanyi.
Batare da yace da ita komai ba yafara cin abincin Haleesa ta zagayo ta zauna a kujera da ke facing d'inshi, bai wuce cin spoon hudu zuwa biyar ba ya ture plate.
''Haleesa ta tabe baki tace kana nufi ka k'oshi kenan"?
"Ba ki ga alama bane ko ke makauniya ce"?
Shiru Haleesa ta yi tana kallonshi, shima ita yake kallo tsawon _4 minutes_ suka dauka suna kallon junansu, yayinda kwayar idanuwansu take isa ma zuciyoyinsu da sak'o Haleesa ce tafara d'auke idanunta daga kanshi ta mik'e tsaye.
Habeeb ya ja iska yana murza saman goshinsa, kamar Wanda aka mintsina ya mik'e da sauri lokacin har Haleesa takai cikin parlour yana zuwa ya ja birki a gabanta.
"Haleesa ta d'an tsorata da ganinsa a rikice ta furta kana buk'ata wani abu ne yaya Habeeb"?
Hannunta ya rik'o ya matse gam... Cikin nashi da k'arfi ya fizgota ta fad'o k'irjinsa yafara romance d'inta yana sauke numfashi da sauri-sauri, gaba d'aya Haleesa ta rikice tsigar jikinta ta tashi Yarr...tafara k'ok'arin kwacewa cikin kunnenta ya rad'a mata _sha'awarki ta yi min munmuna kamu tun ina 6oyewa har na kai faggen da bara iya jurewa ki taimaka min pls_
"Idanun Haleesa suka ciko da hawaye haushin Habeeb ya turnuke ta, yana nufi ba sonta yake yi ba sha'awarta yake yi da ya samu abunda yakeso zai cigaba da wulaqantata wani irin k'unci ya ziyarce zuciyarta ta runtse idanunta sai ga hawaye na bin kuncinta, bata ankara ba taji Habeeb ya had'e bakinshi da nata, jin ta yi k'afafunta sun kasa daukarta tasoma k'ok'arin zubewa k'asa ya rik'enta sosai.
"Can ya dauketa yanufi part d'inshi direct bedroom yawuce da ita, Haleesa tadawo kamar idol{gunki} ko kwakwaran motsi takasa tana kallon Habeeb yacire rigar jikinsa, gadan-gadan yanufo ta.
"Sai lokacin brain d'inta yafara aiki zuciyarta tafara sak'a mata wasi-wasi karki sake ki mallakawa Habeeb kanki da ya biya buk'atarsa, zai cigaba da wulaqanta ki ne da bakinsa yace sha'awarki yake yi sha'awa kuma ba so bane da sauri Haleesa tafara ja da baya tana girgiza kai.
Kai wane yaya irin mugu ne yaya Habeeb"?
Yanzu kai ko kunya bakaji ka dube tsabar idona kace kana sha'awata, wallahi ko za ka mutu bara ta6a Mallaka maka kaina, har sai ka bani matsayin a zuciyarka.
Kunya ta lullu6e Habeeb a sanyaye yadauki rigarsa yajuya da sauri yafice daga d'akin.
Haleesa ta kifa kanta akan pillow tafashe da kuka, zuciyarta na mata zafi, me yasa Habeeb bara iya furta mini kalma so sai ta sha'awa wannan wance irin k'addara ce tafad'a min mijina na aure babu sona a zuciyarsa sai sha'awa wannan wane irin rayuwa ne na riski kaina a ciki"?
"A parlour Habeeb ya tsaya yasaka rigarsa yadauki phone's d'inshi da ke zube akan center table yafice tun kafin yak'arasa compound yake kwadawa Bala kira da a tsorace Bala yadanno da gudu.
"lafiya Boss na ga kamar ranka a 6ace"?
Tsaki ya ja cike da jin haushin yace wannan ba matsalarka bace mu je ka kaini ademola adetakumbo street ayi min aski nagaji da wannan k'asumba yana magana ne had'e da tafiya.
"Wannan gaskiya ne boss k'asumba nan ta yi mugun rage maka kyau
Bala yafad'a cikin 'yar dariya.
"Habeeb ya tabe baki had'e da yatsine fuska Bala ya bud'e masa k'ofar mota yashiga, Bala ya ja motar gate man yabud'e musu gate suka fice.
" lokacin-lokacin Habeeb yake Jan tsaki ya yi danasani furtawa Haleesa abunda ke ranshi, shikenan yanzu za ta renashi, har da wani cewa sai na taba matsayi a zuciyata, in banda k'arancin shekaru irin nata akwai wani matsayi da zan bata da yawuce, wannan yaushe nake da lokacin zama na dinga furtawa mace kalaman soyayya, iya tsawon rayuwar da na yi da aunty salma banta6a furta mata wata kalma da ta dangancin soyayya, iya Sanina ina matuk'ar tausayin aunty salma Wanda hakan ne yajanyo mata babban matsayi a zuciyata, to ita wannan yarinya me yasa bara ta amince mu yi rayuwarmu a haka"?
"Yak'ara Jan tsaki yacigaba da zance zuci banta6a sanin me ye so ba kuma bana tunani akwai wata 'ya mace da zan so.
"Boss mun k'araso maganar Bala ce tadawo da shi natsuwarsa a sanyaye yafito daga cikin mota.
************************
_2 day's later_
Haleesa tana cikin kitchen tana had'a breakfast ta ji kamar ana sallama, da mugun mamaki tafito daga kitchen zuwa main parlour don tasan ba Habeeb bane tsawon kwanakin biyu kenan rabonta da tasa shi a ido ko abincinta yadaina cin tun lokacin da ta fahimcin manufarsa akanta tadaina shiga part d'inshi Haleesa tana k'arasawa cikin parlour tasaki ihun farin ciki sakamako tozali da ta yi da Aunty juwairiyya.
"Da gudu ta rungume aunty Juwairiyya farin ciki ya lullu6enta tarasa inda za ta sa kanta tace aunty Juwairiyya ke ce yau a gidan namu"whats presence surprised Haleesa tana magana ne had'e da d'aukar Abba.
''Aunty Juwairiyya tana dariya tace Haleesan Ammi kinga yadda ki ka k'ara kyau"?
''Turo baki Haleesa ta yi kinga aunty zauna na kawo miki breakfast zaro ido aunty Juwairiyya ta yi had'e da duba wall clock _12:30pm_ what's nonsense Haleesa breakfast at this time"?
"A shagwa6e Haleesa tace uhm...aunty sai yanzu na tashi daga bacci saboda tun _8:00 o'clock_ yaya Habeeb ya fita.
"lallai Haleesa kin ji dad'inki ni kan a k'oshe nake Haleesa ta yi dariya ta zauna a kujera da ke facing d'in aunty Juwairiyya fira ta barke a tsakaninsu.
''Haleesa ina fatar kina zaune da mijinki lafiya wannan zuwan da nayi Ammi ce tadameni da na zo naga yanayin zamanki saboda tasan bason auren ki ke yi ba"?
Haleesa ta tabe baki tace ki ce Ammi rahoto ta turo ki dauka to lafiya lau mu ke zaune ba wani matsala.
"Murmushi Aunty Juwairiyya ta yi tace mu dama fatan mu ki zauna lafiya da mijinki ki manta da margayi yaya Habeeb ki gina sabuwa rayuwa hankalin iyayyenmu ya kwanta.
Haleesa ta yi murmushin yak'e yayinda aunty Juwairiyya tacigaba da ba wa Haleesa shawarwarin zaman aure.
_9:07pm_
Haleesa da aunty Juwairiyya suna zaune a parlour sai faman zuba fira suke yi yayinda Haleesa ke ta kwasan dariya tun daga balcony Habeeb Lamido, yake jiyo sautin dariyarta ya tabe baki, da sallama yak'arasa shiga parlour rass.....gaban Haleesa yafad'i tashiga firgici nan take idea tafad'o mata ta mik'e da sauri tanufi Habeeb _oyoyo my Handsome Don_
"Habeeb Lamido ya yi tsaye turuss.......bai dawo daga mamakin da ya afka ba ya ji Haleesa shinfid'e akan k'irjinshi, cikin shagwa6a take magana _Haba my Handsome don tun safe kafita ba ka dawo ba sai yanzu nan ina fatar ba ka cin abinci a waje ba"?_
"Duk maganar da Haleesa take yi tana qanqame da Habeeb tuni gogan naku yafara fita daga hayyacinsa, dai-dai kunnenshi haleesa tarad'a masa _take it' easy my Handsome don it's just a pretending_
"Habeeb Lamido yasauke ajiyar zuciya yad'ago fuskar Haleesa daga k'irjinsa, ya ja karan hancinta, cikin zuciyarsa yace _huh...lallai yarinya nan 'yar duniya ce saboda zuwan 'yar uwata ita ma ta 6ullo ta wannan sigar amma bara na nuna mata nawa kalar duniyanci_
"Ya yi murmushi yace oh! I'm so sorry my baby nima ban yi tsanmani zan d'auki long time ban dawo ba amma ayi min afuwa bara k'ara ba.
"Shikenan my Handsome don na hak'ura.
Habeeb ya yi murmushi yak'e had'e da zare ta daga k'irjinsa yarik'on hannunta, zuwa kujerar da aunty Juwairiyya take zaune yayinda aunty Juwairiyya ke ta faman doka murmushi da ke baiyanar da farin cikinta Haleesa na zaune lafiya da Habeeb.
"Habeeb ya zauna yana d'an sunkuyar da kai shi a dole yana gaban in-law yace Sannu da zuwa aunty ya hanya"?
"Yauwa Habeeb hanya kuma Alhamdulilah!
Ina Abba ko ya yi bacci ne"?
Habeeb yafad'a yana sosa k'eya
A fakace Haleesa take galla masa harara tace huh....yana bedroom ya yi bacci
Habeeb d'an sace kallon aunty Juwairiyya ya ga hankalinta na wurin TV ya watsawa Haleesa mugun kallo ita kuma ta murgud'a masa baki.
Ya mik'e tsaye yana murmushi yace aunty bara na yi wanka nadawo nima a sha fira da ni.
Dariya Aunty Juwairiyya ta yi shikenan sai kafito Habeeb yajuya ya bi shortcut da ke tsakanin part d'inshi da na Haleesa.
Mik'ewa Haleesa ta yi ta dube aunty Juwairiyya tace aunty bara na had'a masa abincinsa kafin yafito.
Gyad'a Kai aunty Juwairiyya ta yi yayinda Haleesa tanufi kitchen.
_15 minutes later_
Habeeb yadawo sanye da jallabiya, Haleesa naganinsa ta mik'e da hamzari tanufi dining area ta ja masa kujera saida ya yi mata kallon wulaqancin, sannan ya zauna ta yi masa serving ta tura masa plate.
"A yatsine yake kallon abincin daga bisani yadauki spoon yafara ci yana bata fuska kamar mai cin mad'acin ran Haleesa ya yi matuk'ar 6acin tajuya cikin parlour taga akwai tazara sosai tsakaninsu da Aunty Juwairiyya, cikin zafin rai tafisge spoon daga hannunshi ta tattara food flask had'e da plate tanufi kitchen cikin tsananin mamaki Habeeb ya bi ta da kallo ya cize lips d'inshi
tana ajiye kayan tadawo wurinshi, da murmushi a fuskarta take kallonshi _my Handsome don me ka ke jira ne da har yanzu ba ka gadi tashi ba ae ni a tunanina ka dad'e da tsofa parlour"?_
Habeeb ya ja iska yana shafar geme sa yana kallonta k'asa-k'asa ya mik'e tsaye yafizgo ta da k'arfi ya mannata a bango, ya matse ta sosai numfashinsa yana sauka akan fuskarta tsoro ya lullu6e ta kuma ba bu halin ihu aunty Juwairiyya na parlour wannan ya ba wa Habeeb Lamido yin yaddda ya ga dama da ita yatsanshi yasa yana zagaye lips d'inta yana Jan iska daga bakinshi, hannunshi ya zura ida bata yi tsanmani ba, ihu ta je kurmawa da sauri yadanna bakinshi cikin nata, yashiga ya motsata son ranshi sai da yagaji don kansa yasaketa.
Gaba d'aya jikinta rawa yake ta sulale k'asa da6ss.......yana wicked smile ya durk'usa gabanta saida yaja iska yana wani lumsashe idanu, yace _wow! What's a perfect game I like it's baby_
Haleesa d'ago idanunta da suka canza colour zuwa red har ta bud'e baki za ta yi magana da sauri yadaura yatsanshi bisa lips d'inta _shhh......don't say anything baby_ ke fa ki ka tsokanoni don na mayarda Martani ae ba laifi bane kinga ki tashi sahunki a likkafa mu koma parlour kada aunty Juwairiyya ta yi tsanmani ko.......sai kawai hadiye sauran kalamansa ya kashe mata ido, cike da jin haushi Haleesa ta mik'e luuuuu.......jiri yadebe ta tafi za ta fad'i Habeeb yataro ta yadaura bakinshi dai-dai kunnenta yace _take it easy my hot baby it's just a pretending_
Yana k'arasa magana yasaketa Yajuya cikin parlour
Haleesa tasauke ajiyar yafi a kirga saida tad'auki tsawon _6 minutes_ tana jinyar dafin da Habeeb ya zuba mata, jikinta a sanyaye tak'arasa parlour, tana murmushi yak'e tanemi kujera ta zauna duk yawancin firar aunty Juwairiyya ce take yi _11:00pm_ tana bugawa aunty Juwairiyya ta mik'e ta dube Habeeb tace my in-law sai da safe "Toh.... aunty Allah ya tashe mu lafiya
Ameen tafad'a had'e da juyawa tanufi bedroom d'in Haleesa da sauri Haleesa ta bi bayanta har tana had'awa da tuntu6e Habeeb ya bi ta da murmushin mugunta har tafara haura stairs yadakatar da ita ta yadda aunty za ta ji abunda zai fad'a yace _baby in kin raka aunty bedroom ki zo ki had'a min coffee in yaso sai kidawo ki taya aunty kwana_
A tsorace Haleesa tajuya suka had'a ido ya yi mata signal..............
Jeeddah Aliyu
[03/01 8:48 am] aliyujeeddah: [02/12 3:18 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```83```
~~Ta murgud'a masa baki tajuya da sauri tacigaba da haura stairs har tana had'awa da gudu, tana shiga ta tararda aunty Juwairiyya tsaye tana sauya kayan jikinta zuwa na bacci{sleeping dress} tana murmushi yak'e tace aunty ashe kinyi kusan haihuwa naga cikinki yak'ara girma"?
Murmushi aunty Juwairiyya ta yi tace next month ne EDD na ido Haleesa ta zaro kai aunty ki ce na yi kusan zuwa Lagos, Allah yasa ki haifa mana baby girl
"Ameen fatanku ya zo d'aya da masa'ud kullum sai ya yi addu'a Allah yasa na haifi 'ya mace.
''Haleesa ta yi dariya tajuya tashiga bathroom ta yi brush tadawo lokacin har aunty Juwairiyya ta kwanta, ta bud'e wardrobe taciro, cotton night gown tasaka ta sauka mata har kasa tacire ribbon d'in kanta ta tattara gashinta wuri d'aya ta nade duk abunda take yi aunty Juwairiyya tana kallonta, Haleesa ta ra6a gefen aunty Juwairiyya za ta kwanta da sauri aunty Juwairiyya takatar da ita me za ki Haleesa"?
''Kwanciya zan yi aunty baccin nakeji sosai har wani yaji-yaji nakeji a idona.
Umhh......lallai Haleesa har yanzu qurciya yana damunki inda kin kwana anan mijinki fa"?
''Turo baki ta yi toh ni me zan yi masa"?
Cikin 6acin rai aunty Juwairiyya tace Bansaniba da kunnena naji yace ki je ki had'a masa coffee.
"Aunty ba wani coffee da zai sha kawai dai so yake ya yi m......da sauri haleesa ta hadiye sauran kalamanta sakamako mugun kallon da aunty Juwairiyya ta ke watsa mata.
Wai me ke damunki ne Haleesa"?
Ayya kuwa kina sauke hakke mijinki da yake kanki"?
Da sauri Haleesa tafara kame-kame uhm...uhm...aunty ina saukewa mana, ba ki gani ba ne ko yadda nake masa kawai dai gani na yi yanzu dare ne.
Dogon tsaki aunty Juwairiyya ta ja daga bisani ta mik'e zaune, tadaka wa Haleesa tsawa don gidanki mik'e tsaye jikin Haleesa na rawa ta mik'e tun daga sama har aunty Juwairiyya tak'are mata kallo cike da takaici ta girgiza kai
Ta tura k'aton cikinta ta mik'e tsaye ranta yayi mugun 6aci wannan night gown da ki ka saka kadai ta isa ta sheda min baki Masan abunda ki ke yi ba kin d'auki wata qatuwar night kin saka ko a lokacin sanyi{hunturu} a matsayin ki na matar aure bai kamata ki saka wannan rigar ba.
''Idanun Haleesa suka ciko da Hawaye ta sadda kai k'asa yayinda aunty Juwairiyya tacigaba da yi mata fad'a saboda irin wannan sakarcin ne mata waje{karuwai} suke nasara d'auke hankalin mazajenku, ke da bakinki naji kinyi masa laqabi da Handsome Don which means kema kin amince da kyakyawa ne kuma yarda yanada abokai tafiya{kud'i} duk lafiyayye namiji irin Habeeb Lamido ga kyau ga ilimi uwa-uba kud'i a wannan zamani da kwad'ayi ya yi yawa ba abunda mata su ke so irin kud'i, a garin wannan sakacin naki da rashin nuna godiya ga Allah da irin kyauta da yabaki kina kallo wata za ta yi nasara rabaki da shi.
A tsorace Haleesa tad'ago ta dube aunty Juwairiyya, zuwa wannan lokacin Haleesa yaci ace kin manta da margayi yaya Habeeb ki rungume mijinki Ku gina rayuwarku mai ban sha'awa, iya sanina da Habeeb Lamido bashida matsala, saboda ko matarsa ta farko ba sonta yake yi ba amma har tabar duniya ba Wanda yata6a jin Kansu.
Aunty Juwairiyya bata jira jin ta bakin Haleesa ba tanufi wurin wardrobe taciro mata tsaleliyar night gown pink colour ta mik'a mata a sanyaye Haleesa tacire rigar jikinta ta sanya wance aunty Juwairiyya taba ta.
Ina perfumes d'in da na kawo miki"?
Aunty Juwairiyya tafad'a had'e da kallon fuskar Haleesa.
Haleesa ta bud'e drawer mirror ta kwaso perfumes d'in ta zube bisa mirror aunty Juwairiyya tad'auki musk Al-ghazal ki fesa wannan saboda yana sauri tafiyar da zuciyar d'a namiji, ita dai Haleesa kasa furta komai ta yi kawai tana bin umurni aunty Juwairiyya ne saboda batada yadda za ta yi aunty Juwairiyya tak'ara mik'a mata Al-Haramain Gold had'a da wannan saboda shima ba baya ba wurin k'amshi Haleesa ta tabe baki ta bi jikinta ta murtsuke da turaren.
Aunty Juwairiyya ta yi murmushi had'e da cewa ko ke fa toh...yi maza ki tafi wurin mijinki Haleesa ta zaro ido cikin murya da ke son yi kuka tace Dan Allah aunty ki kyaleni na kwana anan in kin tafi zan dinga zuwa d'akinshi
Wallahi zan gwad'a miki mari muddin baso ki ke yi na had'aki da Ammi da baffa juya ki kama hanya kitafi d'akin mijinki sokowa kawai ana nuna miki gabans kina yi yamma.
Haleesa bata k'ara magana ba tafice kamar kazar da kwai yafashewa a ciki.
Tana sand'a kamar barauniya tanufi part d'in Habeeb tana shiga parlour ta yi tsaye gashi parlour ba haske dole ta haska touch d'in wayarta tsawon _10 minutes_ ta dauka a tsaye tana shawarwari shiga bedroom d'inshi tasauke ajiyar har wani shasshek'a take yi kamar wance ta yi gudu a hankali tanufi k'ofar d'akin tana turawa ta bud'e tashiga da sallama k'amshi freshener ne ya soma amsa mata sallama ta maida k'ofar ta rufe yana jigine a jikin bed hannunshi rik'e da remote d'in TV suna had'a ido ta d'auke kanta.
Habeeb ya k'ura mata Manyan idanunshi da mugun mamaki yake kallon night gown d'in jikinta nan take brain d'inshi yafara yi masa backwards d'in mafalkin da yata6a yi da leesa tana sanye night gown irin d'aya da ta jikin Haleesa ya lumshe idanu had'e da Jan iska ya shak'i qamshin turaren musk Al-ghazal da sauri ya bud'e idanunshi bai San lokacin da bakinsa ya furta _leesa dama zan iya shak'ar qamshinki a baiyane ba kamar yadda nasaba shak'a a mafalki ba"?_
"Haleesa ta waro ido tana wulwulga su a cikin d'akin tana dubi a ina leesa za ta fito sai kawai taga Habeeb ya wulgar da remote jikinsa na rawa kamar mazari yanufi wurinta.
Muryarsa na rawa yak'ara furta leesa dama za ki iya zuwa min a baiyane"?
"A tsorace Haleesa tace you are crazy yaya Habeeb I'm not leesa why do you behaving like abnormally"?
"Jin abunda tafad'a yasa ya ja birki ya shafi sumar kanshi, sai lokacin yatuna cewa Haleesa ita ce leesarshi ta mafalki a kunya ce ya galla mata harara, yace "you mean I'm not normal huh!?
Good, I'll show you the characters of a mad man now.
''Cikin sark'ewar halshe Haleesa tace Karka kuskure ka ta6ani wallahi zan maka ihu.
Tsaki Habeeb ya yi ya koma bisa bed ya yi kwanciyarshi yak'urawa TV ido yayinda Haleesa tanufi kujera ta zauna kallon Habeeb yake yi saidai gaba d'aya hankalinsa na wurin Haleesa sai kawai yacin kanshi da kiran sunanta _ke!_
Haleesa tad'ago ta dube shi yafitota ya yi da hannunshi _zo nan_ bata fuska ta yi kamar za ta yi kuka murmushi Habeeb ya yi yace ke ba abunda zan yi miki kawai tambayarki zan yi.
"Tsanm.....Haleesa ta mik'e tanufi gefen bed ta zauna batare da ya dube ta ba idanunshi na kan TV yace "How old are you"?
Fuskarta d'auke da mamaki take kallonshi yayinda shi kuma idanunshi na kan TV ta ya mutse fuska tace kana da matsala da shekaru na ne"?
"Ga mamakinta sai taga ya girgiza kai
To kuma me ye na wani tambaya na tak'arasa magana had'e da murgud'a baki "very slowly yajuyo yana mata kallon k'asan ido ya ja iska yace kidaina gani aunty Juwairiyya tana gidanan ki ce za ki yi min rashin kunya don haka ki amsa min tambaya na.
"Ajiyar zuciya Haleesa ta yi muryarta a sanyaye ta furta sha takwas{18 year's} murmushi mai sautin gaske ya su6ucewa Habeeb yace shiyasa ki ke wasan 'yar 6oya da Imaan ashe kusan age mate d'inta ki ke
Haleesa batasan lokacin da tace a'a tare mu ka zo duniya da ita
"Batare Ku ka zo duniya ba amma dai shekarunku sun kusan zuwa d'aya Imaan 6yrs ne da ita ke kuma kinada 18yrs kinga kenan 12yrs kin ka bata Haleesa ta ja tsaki tace kaga yaya Habeeb karka ga na zo bedroom d'inka kanemi ka cin min fuska kai duk yadda mutum yakeso ya zauna lafiya da kai sai kanemi ka wulaqantashi in banda wulaqancin me ye na wani had'a shekaru na da na Imaan.
Shiru Habeeb ya yi yana kallonta yadda take magana ta yi bala'e burgeshi sai tanu masa farkon had'uwarsu, a lokacin da Bala ya watsa mata ruwan kwatame haka ta rufe ido tana fad'a a wance lokacin mugun haushi tabashi amma kuma a yanzu da ke zaune a gabanshi sai yaji tayi mugun burgeshi har bayaso tadaina fad'a da take yi gani yadda ya tsareta da idanu yasa ta murgud'a baki tajuyar da fuskarta tana gunguni _haka kawai ka dinga kallona har sai kagano muni na_
"Girgiza kai Habeeb ya yi using remote ya yi switch off d'in TV duhu ya gauraye d'akin dama hasken TV ne ya haskaka d'akin tsoro ya Kama Haleesa cikin rawar muryar tace yaya Habeeb me y......sauran kalamanta suka qargame a mak'oshinta sakamako tsintar kanta da ta yi a jikin Habeeb muryarta na rawa tace dan Allah yaya Habeeb ka kyalleni banaso
"Matse mata baki ya yi can! K'asan mak'oshi ya furta in bakyso uban me yakawo ki d'akina"?
"Kuka Haleesa tasawa Habeeb ba yadda ya iya dole ya kyalleta ba don ranshi so ba yana sakinta ta koma karshen gado tana wuk'i-wuk'i da idanu, Habeeb yana switch on d'in bedside lamp ya hango Haleesa tak'ure a karshen gado tana rarraba idanu ta yi mugun bashi dariya baisan lokacin da ya kyalkyale da dariya ba har da dafe ciki.
''Haleesa ta zaro ido tace lah.....ashe yaya Habeeb kana dariya"?
Ya tsagaita da dariya da yake yi ya galla mata harara yace karki yi min sharri dama can! Ina dariya kece bakya ni.
Tabe baki Haleesa ta yi tace uhmm.....ta ra6a gefen Habeeb ta kwanta.
Shiru sukayi kowane da abunda yake sak'awa kamar daga sama Haleesa tace, yaya Habeeb me yasa bakason kwanciya akan pillow"?
Ignoring nata ya yi kamar bai ji tambayar da ta yi masa ba.
yatsine fuska ta yi ta dube fuskarshi taga yadda yake tsotsan baki tace yaya Habeeb sweet ne ka ke sha"?
Cikin zafin rai Habeeb ya watsa mata harara bansaniba, kuma karki k'ara yi min magana.
Murgud'a baki ta yi tace don ma kasamu na kulla ka shine ka ke so ka yi min wulaqancin tana k'arasa magana ta juya masa baya da k'arfi yafizgo ta yanuna ta da yatsa yasoma zuba mata kashed'i ba zan ta6a amincewa k'aramar yarinya irinki ta juya mini baya ke ba ma abin alfaharinki bane yau za ki kwana gado d'aya da Habeeb Lamido.
Yatsine fuska Haleesa ta yi tace dallah malam ka kyaleni bacci nakeji tana magana ne had'e da rufe idanunta Habeeb ya mirgina dai-dai fuskarta yana kallonta jin yadda numfashinta yake sauka yasa yagano cewa ta yi bacci, rungumeta ya yi yana kallon fuskarta wani irin sonta ke ratsa jininsa a haka bacci ya yi awo gaba da shi.
Sautin kiran sallah da ke fita a cikin wall clock ya falkarda Habeeb yayinda Haleesa ke manne cikin jikinsa, a hankali yake shafar sumar kanta ya yi pecking goshinta ke! Ke! Ki tashi lokacin sallah ya yi wani juyi Haleesa ta yi tak'ara shigewa jikinshi, murmushin mugunta ya yi yasaka yatsunsa guda biyu ya matse mata hancin can! Cikin bacci Haleesa ta ji takasa numfashi a firgice ta zabura ta mik'e zaune Habeeb ya kyalkyale da dariya Haleesa ta ya mutsa fuska ta d'auki pillow ta dinga dukan Habeeb da shi ya mik'e tsaye bisa bed ya yi tsalle ya sauka k'asa binshi ta yi tana kai masa duka, da gudu yashige bathroom.
Haleesa ta jefarda pillow ta zauna had'e da rafka tagumi, tana mamaki kanta da Habeeb Lamido ashe akwai ranar da Habeeb zai kulata har ya yi mata dariya abunda bata ta6a gani ba tsawon zaman da ta yi da shi.
Ta yi zurfi a tunani batasan lokacin da yafito ba sai saukar ruwa ta ji akan fuskarta, a firgice tad'ago suka had'a ido suka sakewa junansu k'ayatace murmushi.
Habeeb yace ke tashi zuwa sallah kada lokacin yawuce kina zaune kina tunanina Haleesa ta rufe fuskarta da tafin hannunta Habeeb yasauya kayan jikinsa zuwa jallabiya.
Haleesa, nagani Habeeb ya kabarta sallah tafice da sauri tanufi d'akinta.
************************
_5:00pm_
Haleesa da aunty Juwairiyya suna zaune a parlour Habeeb Lamido yashigo yana murmushi ya dube aunty Juwairiyya yace aunty mu je mu kai ki kiga gari kinsan wannan k'anwar taki kifin rijiya ce Sam bataso fita kullum tana k'unshe cikin gida kamar matar liman yak'arasa magana yana dariya yayinda ita ma aunty Juwairiyya ta d'an dara.
Turo baki Haleesa ta yi tana gunguni batare da bata lokacin ba Haleesa da aunty Juwairiyya suka shirya Bala yadauke su da mota ita da aunty Juwairiyya suna zaune a seat d'in baya Habeeb kuma na seat d'in gaba kamar ace Haleesa tad'ago taga hango Habeeb yana kallonta ta cikin madubin.
"Ta murgud'a masa baki shi kuma ya mayar mata da martani ta hanyar ya tura mata lips d'inshi alamar peck da sauri tad'auke fuskarta da barin kallonsa.
Direct Bala yawuce da su Abuja garden Bala nayi parking aunty Juwairiyya ta yi gaba Bala dauki Abba ya bi bayanta ya rage daga Habeeb sai Haleesa suka jero tare yadda Habeeb yake tafiya kamar bayaso taka k'asa yasa Haleesa take satar kallonshi suna had'a ido yasake mata murmushi ya saqala hannunshi cikin nata suna tafiya yana murza mata yatsu, kallon d'aya za ka yi musu kagano cewa suna fama da shauk'in son junansu yawo sukayi sosai sai misali k'arfe _10:00pm_ suka dawo gida da yake sun kwaso gajiya kowanesu yanufi makwacinsa kamar yadda aunty Juwairiyya ta yi wa Haleesa jiya ta turata d'akin Habeeb yau ma hakan ce tafaru saidai tsakanin jiya da yau akwai banbancin saboda yau fuskar Haleesa a sake tashiga d'akin Habeeb yana tsaye gaban dressing mirror yana fesa Parfume ya ajiye kwalba turaren yana murmushi ya ware mata hannaye shi.........
Jeeddah Aliyu
[03/01 8:50 am] aliyujeeddah: [03/12 9:03 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```84```
~~Haleesa ta yi k'ayatace murmushi ta kad'a kwayar idonta a yangance tanufi wurin Habeeb kamar za ta shige k'irjinshi, sai kawai tanufi gefen bed ta zauna tana yi masa dariya.
" Habeeb ya yi murmushi had'e da ya mutsa sumar kansa da baya-baya yafad'a bisa bed ya runtse idanunshi, lek'a fuskarshi Haleesa ta yi tana mai cigaba da dariya, cikin tsokana tace _hey Mr pretender whats is wrong"?_
Ya mirgino yadawo saitin fuskarta kallon ido cikin ido yake mata ya ja iska yace kina nufi ko yau pretending d'in ne yakawo ki d'akina"?
''Kaima kasan in bayan shi ba abunda zai kawo ni d'akinka
Cije lips d'inshi ya yi yana kallonta a yatsine da sauri ta d'auke fuskarta da barin kallonshi.
Shiru sukayi ba Wanda yak'ara tankawa d'an uwanshi Haleesa tajuya ta sace kallonshi ya yi pillow da hannayenshi idanunshi a rufe ruf kamar mai bacci, kasa d'auke fuskarta ta yi akansa tashiga nazari kyakyawa fuskarsa ta yi ajiyar zuciya a kasalance ta mik'e tanufi gefenshi ta kwanta, tana mamaki d'abi'un Habeeb bata ta6a ganin mutum mai abubuwan mamaki irinshi ba ta yi nisa a tunaninshi batansan lokacin da ya matso daf da ita sai jin ta ta yi cikin jikinshi, cikin kunnenta ya rad'a mata bai kamata ki dinga wahalarda zuciyarki da tunanina bayan gani kusa da ke yak'arasa magana had'e da hura mata iskan bakinshi a kunne.
"Da sauri ta lumshe idanu, Habeeb yak'ara matso da ita cikin jikinshi ya hard'e k'afafunshi cikin nata yasaka hannaye shi ya layyace gadon bayanta fuskokinsu na facing d'in juna duk abunda yake yi idanunshi suna rufe kasa motsi Haleesa ta yi sai fama zazzare ido kawai take yi numfashinta na fita da k'arfi, ta k'urawa Habeeb ido a zuciyata tace ina ma ace da yaya Habeeb d'inta take kwance ba da wannan arrogant d'in ba mutumi da ya furta mata cewa sha'awarta yake yi ba sonta yake ba tabbata duk ranarda ya yi nasara cima burinshi akanta zai goge babinta ne a zuciyarshi, tausayin kanta yakamata hawaye suka zubo mata saboda tuni ta fahimce cewa ta fad'a tarkon so Habeeb Lamido tacigaba da kallonshi, yayinda Habeeb bai masan tanayi ba saboda tuni bacci ya yi awo gaba da shi ta ja karan hancinshi ta lumshe idonta a haka bacci mai dad'i ya yi nasara d'auke ta.
*************************
_11:00am_
Haleesa da Habeeb na zaune a dining table suna taking breakfast cikin kulawa Habeeb ya dube Haleesa, yace k'arfe nawa flight d'insu aunty Juwairiyya zai tashi"?
Saida Haleesa ta hadiye chips d'in da take tauna tace _11:30am_ Habeeb ya gyad'a kai suna gama breakfast suka nufi parlour inda aunty Juwairiyya take jiransu su kaita airport, kafin su wuce da ita airport nasiha ta yi musu sosai basu baro airport ba saida suka ga tashin jirginsu.
"tun akan hanyar su na dawowa gida Haleesa ta daure fuska Habeeb ya dube ta ya yi murmushi yad'age gira sama yana kallonta hannunta yarik'o cikin zafin rai ta firzge hannunta, a yatsine tace aunty Juwairiyya ta tafi daga yanzu ba wani sauran pretending, the game is over.
"Habeeb yak'ara fad'ad'a murmushinsa ya wani kad'a kai batare da yace da ita uffan ba har suka isa gida Bala na yi parking
tun kafin ya bud'e mata k'ofa ta bud'ewa kanta da sauri tanufi cikin gida.
Habeeb yafito daga cikin mota ya yi mik'a ya bi Haleesa da mayen kallo a baiyane ya furta _the game is not over baby this is just the beginning_
Bala ya matso daf da shi ya yi k'asa da murya kamar munafuki yace "boss wannan wane irin game ne jikina yabani wasan zai yi dad'i kuma na tabbata Kaine winner.
"Da mugun mamaki Habeeb ya kalli Bala daga bisani yadafa kafad'arsa suka jera suna tafiya a hankali Habeeb ya ja iska yace nima ina ji a jikina ni ne winner amma basan how long wasan zai dauka kafin nayi winning.
''Bala ya washe hak'ora yace karka damu da tsawon lokacin da wasan zai dauka abu mafi mahimmancin ka yi nasara cinye wasan amma boss wannan wane irin wasa ne"? Bala yak'arasa magana yana dariya.
''Habeeb ya galla masa harara yadak'i kafad'asa yace na tsani shissshigi Bala.
Murmushi Bala ya yi yace "yes boss.
"Direct Haleesa ta wuce bedroom d'inta ta qargame k'ofa, tun daga lokacin suka koma 'yar gidan jiya za ta girka masa abinci ta jejjera akan dining table ta shigewarta d'akin ta murza key.
idan Habeeb yaga dama yaci ranar da yaji baya ra'ayi ci yabar mata kayanta a haka suka share _1 week_ suna gida d'aya amma kowanesu rayuwarsa yake yi.
_10:00pm_
Habeeb yana kwance a bedroom d'inshi abun duniya yataro ya yi masa yawa, tunanin Haleesa na azabtarda ruhinshi da yarufe ido ita yake gani, ba abunda yake buk'ata irin ya ji d'umi jikinta da sanyaye k'amshinta kamar Wanda aka mintsina da sauri yasauko daga kan bed yanufi part d'inta.
Yana murd'a handle ya ji k'ofar d'akinta a rufe ya yi tsaye kamar zai kurma ihu tsawon lokacin yadauka yana safa da marwa can! Idea tafad'o mishi da sauri yafice sai gashi yadawo rik'e da mopper da k'arfi yafara dukan kujerin parlour da mopper hannnushi yature d'an k'aramin glass madauke da flower da ke ajiye akan center table yafad'o yadak'i tiles ya tararatse.
''Haleesa na kwance har bacci yafara d'aukarta taji k'arar fashewar glass, ta zabura da k'arfi ta diro daga kan bed tanufi parlour da gudu tun kafin tak'arasa ta hango Habeeb yana watse da pillowcases na kujeri gaba d'aya ya hargitsa mata parlour a rikice tak'arasa wurinshi, muryarta na rawa tace lafiya yaya Habeeb"?
Banza yayi da ita yacigaba da watsi da kaya rik'e mai hannnu ta yi yadakatar da abunda yake yi, yana sauke numfashi, wai yaya Habeeb me ka ke nema ne duk ka bi ka rikita min parlour"?
"Habeeb ya karkace kai yafara tsara Haleesa ta hanyar cewa _ina zaune a dining area na ga wani abu mai bindi ya rugu da gudu yashigo parlournki shine na biyo shi da mopper yashige k'ark'ashin kujeri_
Zo ki ta ya ni mu fiddo shi Haleesa ta zaro ido cikin sark'ewar halshe tace ni fa ban fahimce abunda ka ke nufi ba"?
Habeeb yadafe goshi yace ina wannan abin mai tsawo yana da dogon bindi ya ma sunanshi yashiga tunani kamar da gaske karaf Haleesa tace bera
Habeeb ya yi shiru yana kallonta ya girgiza Kai yace No....ba bera bane ae bera baya cizo koh"?
''Haleesa ta gyad'a kai to ko k'adangare ne yaya Habeeb"?
Haleesa tafad'a da alama tafara tsorata shiru Habeeb yana nazari maganarta daga bisani yace k'adangare kai bashi bane domin shima baya cizo wannan abu mai tsawo jikinshi yana da tsantsi, za ki tuna suna wannan abu da na ta6a siyowa Imaan na roba a Canada har yabaki tsoro"?
tun kafin Habeeb yak'arasa magana Haleesa tadaka mahaukacin tsalle ta chukuikuye shi jikinta na rawa tace yaya...Habeeb....Maciji
Wicked smile Habeeb ya yi yace eh! Maciji ne nima na yi matuk'ar mamaki yadda aka yi yashigo parlounki.
"Haleesa tafashe da kuka tak'ara qanqame Habeeb kamar za ta shage k'irjinshi Dan Allah yaya Habeeb kafita da ni gidanan wallahi tsoro nakeji.
Kinga me ye kuma abun tsoro tun da ba'a bedroom d'inki yake ba yanzu yadda za'ayi ki shage bedroom ki qargame kamar yadda ki ka saba gobe da safe zan kira securities su fito da shi.
Cikin shashshek'ar kuka Haleesa take girgiza kai bara iya ba yaya Habeeb, zai iya shiga har bedroom ni dai ka fita da ni.
Habeeb ya fakace idonta ya yi mata gwalo yace saidai in za ki je part d'ina mu tafi amma ni basan inda zan kai ki ba.
Kuka yaci k'arfinta takasa furta komai sai faman d'aga kai ta ke yi cike da farin ciki Habeeb yadauke ta cak......da kyar ta amince yasauke ta bisa gado Habeeb ya dube fuskarta ya ga yadda ta kwa6e da hawaye had'e da majina, tausayinta ya yi mugun kamashi ya mik'a hannu bisa mirror ya yago tissue ya goge mata fuska yace kwanta ki cigaba da baccinki.
Girgiza kai ta yi ta rik'e mishi hannu gam yayi k'asa da murya ki kwanta ba abunda zai same ki bathroom zan shiga bara d'auki dogon lokacin ba zan fito kinji"?
Uhm!...uhm...ni dai mu tafi tare zaro ido Habeeb ya yi yace a ina za mu tafi"?
Bathroom tafad'a cikin murya kuka, komawa Habeeb ya yi zauna kusa da ita yace na fasa zuwa bathroom d'in saboda bara yarda ki bini ciki ki k'are min kallo.
Da sauri Haleesa ta matsa tashige cikin jikinshi, a hankali yake bubbuga bayanta har yasamu tadaina kuka ya ja mata pillow ta kwanta cike da nishad'i Habeeb ya kwanta kusa da ita ya rungumeta tsanm.
**********************
_washe gari_
Habeeb da Haleesa suna zaune a parlour Habeeb ya yi pillow da cinyoyinta, ita kuma sai faman damuk'a mishi gashi take yi idanunshi na lumshe yace ke! har yanzu ba'a gama Kitso bane"?
"Turo baki ta yi sumarka yacika tsantsi da yawa da na kitsa sai ya warware, ayya kuwa yaya Habeeb ba relaxer ka ke sakawa ba"?
Tsaki ya ja ya mintsine ta a gefen cinya angaya miki ni d'an daudu ne da zan sakawa suma na relaxer"?
Uhm..!ka ga bawan Allah maida wuk'a ni bance maka d'an dauda ba kawai dai naga kai d'an gayu ne tak'arasa, magana tana lek'on fuskarshi.
Habeeb ya yatsine fuska yace gayanci na bai kai can ba kinji koh magge"?
Tashiga ture masa kai daga cinyoyinta d'aga mun daga jiki tun bara ka daina kira na da magge ba ni dama dole ce tasani zama a part d'inka.
Ke fa ki ka ce sunanki magge"
Yaushe nace da kai sunana magge"?
Kafin yabata amsa phone d'inshi ya yi ringing Haleesa ta mik'a hannu bisa center table tadauko masa, kamar ba zai d'aga kiran ba sai da yagama Jan ajinsa sannan yad'aga _Hello Maryam ya akayi ne"?_
Rass...rass...gaban Haleesa yafad'i da ta tuna wacece Maryam a wurin Habeeb nan take wani irin kishi ya turnuk'e ta har Habeeb yagama waya batasan inda kanta yake ba saida taji yana mata tafiyar tsotsa a gefen cinyarta, buge mishi hannu tayi kamar daga sama ta ji muryarshi yana cewa Maryam ce ta kirani wai gobe za ta turo driver yad'auki Imaan ta je musu hutu.
"Ajiyar zuciya Haleesa ta yi tace uhm...
Tun daga wannan lokacin shak'uwa mai k'arfi yashiga tsakanin Habeeb da Haleesa yau Habeeb yashirya zai tafi Lagos, kuka Haleesa tasa mishi bara ta iya zama ita kadai ba saida yakira Hannah a waya ta turo masa yarinye Housemaid d'in madam Hindu ta tayata zama saboda Hannah exam take yi Haleesa tana tsaye a palour tana matsar hawaye Habeeb yafito rataye da briefcase d'inshi gani tana kuka yasa jikin Habeeb ya yi sanyi ya rungumeta yana rarrashinta kidaina kuka bara wuce _1 week_ ba zan dawo kinji"?
Yak'arasa magana had'e da d'ago fuskarta ya tsotsi lips d'inta na k'asa wani irin quncin ya ziyarce zuciyarta tana tunani yadda za ta share tsawon sati d'aya batare da Habeeb ba.
Cikin muryar kuka tace ni ban damu da kowane lokacin za ka dauka ba ka dawo ba babban damuwa na yadda za ka tafi kabarni da maciji a cikin gidanan.
Tsaki Habeeb ya ja cike da takaici yake kallonta da ya dauka kukan da take yi saboda zai tafi yabarta ne har yafara murna ita ma tafara jin abunda yakeji a game da ita shiyasa ma yake d'aga mata k'afa kafin ya ga iya gudun ruwanta, ashe ita abun ba haka bane a wurinta.
Kukan Haleesa ya tsananta Habeeb ya galla mata harara cikin zafin rai yace, maciji ya kashe ki kafin in dawo yaciro bundle na 'yan N1000 ya jefa mata bisa kujera yafice da sauri saboda jin yake yi kamar zuciyarsa za ta tarwatse.
Haleesa ta yi sororo baki sake ta bi bayanshi da kallo dama tasan har abada Habeeb Lamido bara ta6a sonta ba ko 'yar wannan shak'uwa da tashiga tsakaninsu, duk lokacin da ya bud'e bakinshi saidai yace tana burgeshi tana bashi sha'awa, ita kuma ta tsani jin wad'annan kalamai daga bakinshi saboda ta kai k'ololuwa a sonshi tak'ara fashewa da kuka ta kwasa da gudu tashige bedroom d'inshi..........
Jeeddah Aliyu
[03/01 8:54 am] aliyujeeddah: [05/12 1:02 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```85```
~~Ta fad'a kan gado tayi rub da ciki tacigaba shasshek'ar kuka tana cikin kuka idanunta suka kyalo mata pyjamas d'in da Habeeb yacire ajiye a gefen gado ta mik'a hannu tadauko riga, k'amshin turarenshi ya buge hancinta ta qanqame rigar tashiga shinshinawa, ji take yi kamar Habeeb Lamido ne ta rungume.
_HABEEB_
Tun daga lokacin da Habeeb yafita gida zuwa airport har flight d'insu ya yi landing, yana fama da tunanin Haleesa mamakin kanshi yake yi yadda yake ware lokaci a cikin lokuta mafi mahimmancin a wurinshi yana tunaninta, abunda a tarihin rayuwarshi bai saba da shi ba.
_2 day's later_
Habeeb yana zaune a katafare office d'inshi a Lagos Mus'ab yaturo k'ofa yashigo ta k'asan ido Habeeb ya dube shi yadauke fuska.
"Mus'ab ya ja kujera ya zauna cikin 6aci rai yafara magana wai Lamido me ka ke nufi ne"?
Banza Habeeb ya yi da shi yad'auki d'aya daga cikin phone's d'inshi da ke zube a gabanshi ya yi dialling number Haleesa ta yi ringing har ta tsinke bata dauka ba ranshi a 6ace ya jefar da wayar akan desk d'in da ke gabansa yadafe k'ok'on kansa yana sauke numfashi guda-guda.
"Girgiza kai Mus'ab ya yi yace ''tell me Lamido whats exactly wrong with you"?
Yatsine fuska Habeeb ya yi kamar zai fashe da kuka yake kallon Mus'ab, da kyar yafurta _I don't know Mus'ab so stop asking me_
"Ran Mus'ab yak'ara mugun 6aci a harzuk'e yace Whats do you mean you don't know"?
''Look Mus'ab nasa kana jin zafin yadda nayi cancelled meeting d'in da za mu yi duk nasan meeting d'in yana matuk'ar muhimmancin a company sani nayi ko nashiga meeting d'in bara Ku gane kaina ba b'cos I'm not in Good mood.
"Kana nufi duk tsawon wannan lokacin da mu ka dauka muna jiranka a hall yatafi a banza"?
"Habeeb ya lumshe idanu shi kadai yasan yadda yakeji a cikin zuciyarsa.
Magana nake yi da kai Lamido ka bani amsa mana.
"wani irin mugun kallo Habeeb ya watsawa Mus'ab cikin angry voice yace The meeting is definitely cancelled I want to be alone yak'arasa magana yana huci kamar zaki a dawa.
Da Mugun mamaki Mus'ab yasaki baki da hancin yana kallon Habeeb shi Lamido zai dinga yi wa shouting shin ko ya manta da matsayi da yake da shi a wurinshi.
"A kasalance Haleesa tafito daga bedroom d'in Habeeb Lamido Wanda a yanzu ya zama mallakinta tazarce parlour phone d'inta da ke soke a socket yana charging taciro shi daga charger tanufi 3 seater ta kwanta tana danna wayar taci karo da 1 misscall a tsorace ta zaro ido sakamako ganin number Habeeb Lamido daga bisani kuma sai ta yatsine fuska
Tafara zance zuci me yaya Habeeb yake nema a wurina"?
Duk lokacin da ya yi tafiya in ya kira wayana da 'yarsa yakeso magana, a halin yanzu kuma yasan 'yarsa bata tare da ni watakila ya kira ne yak'ara jifana da bak'ak'en maganganu kamar yadda yasaba ta ja tsaki.
Har ta ajiye wayar sai kuma ta yi decided ta kira shi tanemi izzininshi tanaso zuwa saloon.
"Cike da jin haushi Mus'ab yake kallon Habeeb ya girgiza kai yace haka ne, Lamido dole ka wulaqanta ni saboda ina aiki a k'ark'ashe ka amma kasani ba k'aramar hasara ka ke k'ok'arin janyowa company ba.
Kafin Habeeb yabashi amsa d'aya daga cikin phones d'inshi ya yi ringing, da kyar yad'ago ya dube wayar idanunshi suka yi tozali da sunan Haleesa yana yawo akan screen rass..rass..gabanshi yafad'i a gigice ya rarume wayar hannunshi yana rawa ya yi picking _Hello leesa_
Duk abunda Habeeb yake yi idanun Mus'ab na kafe akanshi
"Jin sunan da ya kirata da shi ya yi bala'e bata haushi, wani irin zazzafan kishi ya lullu6e ta wai wacece wannan leesa da Habeeb Lamido yake kirana da sunanta"?
cikin zafin rai Haleesa tace ba ita bace wannan Haleesa wance ka yi wa fatan maciji ya kasheta ita ce take magana.
"Murmushi jin dad'i Habeeb ya yi saboda jin muryarta yake kamar ana busa masa sarewa ya lumsashe idanu yak'ara lafewa jikin kujera yayinda kujerar take jujjuya shi.
''Cike da nishad'i yace uhm......na kira ki baki d'aga ba ko zan iya sani dalilin"?
_Banyi ra'ayi bane_
Tafad'a kaitsaye
Ko zan iya sani dalilin da yasa bakiyi ra'ayi ba"?
_kaga yaya Habeeb ni fa nafara gajiye wad'annan tambayoyin naka marasa kan gado in bakada abun fad'a zan ajiye wayana_
"Ni ko nakeda abun fad'a dama na kira ki ne nayi miki albishir da cewa ba wani maciji kawai tsokanarki nake yi yak'arasa magana cikin dariya.
''Zaro ido Haleesa ta yi tamkar tana gaban Habeeb a shagwa6e tace you're bad yaya Habeeb.
"cikin muryar dariya yace Yes I'm kinsan wani abu"?
Uhm....sai kafad'a
Habeeb yak'ara yin k'asa da murya na yi missing d'in jagwalgwalen abincinki and......sai kuma ya yi shiru yana Jan iska
Haushi yak'ara kama Haleesa ba ma ita ya yi missing ba abincinta yake missing a harzuk'e ta furta and what's"?
Can! K'asan mak'oshi yafurta k'amshin jikinki da.....dallah! Malam shiru Haleesa ta katse shi cikin tsawa Wanda ita kanta batasan lokacin da tadaka mishi ita ba tacigaba da cewa ni duk ka bi ka cika min kunne tun da bakada abun fad'a sai anjima ta yi hanging up had'e da jefa Wayar akan center table.
"Ko kad'an ran Habeeb Lamido bai 6ace ba sai ma wani irin dad'i da yake ji yana ratsa zuciyarsa.
"Fuskarsa d'auke da murmushi, ya dube Mus'ab Wanda yadawo tamkar gunki saboda tsananin mamakin Habeeb.
Yanzu yadda za'ayi Mus'ab ka tattaro bayanai da suke wurinka, I will try my best nagani wannan contract d'in bai fita daga hannumu ba believe me abokina bakada matsala saboda yanzu na fahimcin son kud'inka yafara zarce nawa amma kana da gaskiya b'cos aure ka ke so yak'arasa magana cikin tsokana.
''Mus'ab ya d'an murmusa yace banta6a ganin d'an rainin hankali ba irinka Lamido, yanzu dai mu ajiye zance contract a gefe ka sanarda ni da wa ka ke waya"?
"Murmushi Habeeb ya yi yana shafar gemunsa yace leesa da leesa nake waya bayanshi kanada wata tambaya"?
Mus'ab ya zaro ido "OMG! you mean your dreams girl"?
Cike da gansarwa Habeeb ya gyad'a Kai kyalkyalewa da dariya Mus'ab ya yi har yana had'awa da dukan desk you're such a craziness Lamido anyya kuwa. Lamido ba aljana ka ke soyayya ba saboda iya sanina a mafalki ka ke had'uwa da leesa to ya akayi yanzu kasami phone number d'inta"?
Tsaki Habeeb Lamido ya ja ya mik'e Tsaye hannayeshi zube cikin aljihu wandonshi yace kaine bakada hankali Mus'ab bani ba da ka ke dangantani da soyayya infact kasan wacece leesa"?
Mus'ab ya galla masa harara yace ta ya ya zan Santa batare da ka sanarda ni ba.
Habeeb yana murmushi ya zauna akan desk yana facing d'in Mus'ab yadak'i kafad'ar Mus'ab yana wani yatsinar fuska yace wannan yarinya da ke gidana ita ce leesa
"Da mugun mamaki Mus'ab ya furta kana nufi Haleesa"?
Gyad'a kai Habeeb ya yi, ae kuwa Mus'ab yadinga kyalkyalar dariya kamar sabon ta6i hankali saida ya yi dariya mai isarshi sannan yace kana nufi kafad'a tarkon son Haleesa"?
''Lallai Mus'ab ka zare nayi maka kama da mutume da zai fad'a tarkon son mace"?
Mus'ab ya ja tsaki yace in ba sonta ka ke yi ba menene musababi hanaka attending d'in meeting"?
Me yasa lokacin da ta kira ka karud'e farin ciki ya lullu6e ka"?
''Habeeb ya yi shiru yana nazari Mus'ab yace kadaina wahalarda kanka ta hanyar zurfafa tunaninka saboda duk Wanda yasanka ya ganka a yanzu yasan cewa ka canza tsawon zaman da na yi da kai banta6a gani ka k'asa attending meeting batare da kwararan dalilin ba sai yau, banta6a gani ankira phone d'inka kana farin ciki ba sai yau duk wad'annan alamomin da na gani tare da ka kana nufi kace da ni ba so bane"?
Mus'ab kenan babu son leesa ko misk'ara zarrati a zuciyata, kawai dai nasan ina d'an sha'awarta shima ba sosai ba yak'arasa magana yana yatsina fuska.
"Wane irin sha'awa kuma"?
Da sha'awarta ka ke yi Lamido da zaman da ka yi da ita da yanzu ka kawarda sha'awarka.
''Uhm....tsakanina da leesa sha'awa ce ba so ba na tabbata duk ranarda na kusance ta zan manta da ita saida na yi alqawali zamata ita saboda za6in mom ce.
''Cikin tsananin mamaki Mus'ab yace kana nufi ba ka ta6a had'a shinfid'a da ita ba"?
"Kwarai kuwa Habeeb yafad'a had'e da kallon fuskar Mus'ab
Girgiza kai Mus'ab ya yi yace wannan kadai ya isa yagansarda kai cewa son Haleesa ka ke yi ba sha'awa ba da sha'awarta ka ke yi da ko ta k'arfin tsiya ne za ka kusanceta Lamido ka yarda da ni wallahi sonta ka ke yi so bana wasa ba.
''Habeeb ya yi shiru jikinsa ya yi bala'e sanyi, wannan ya ba wa Mus'ab dama yacigaba da kwararo masa hujojji kwarara da ke nuna son Haleesa yake yi yayinda Habeeb yakasa amincewa da furucin Mus'ab.
_3 day's later_
Tsawon wad'annan kwanaki Habeeb bai k'ara neman Haleesa ba kamar yadda ita ma ta tattara shi ta watsar a dustbin.
"Haleesa tana kwance kallo d'aya za ka yi mata kagano, tana cikin damuwa phone d'inta ya yi ringing gani number aunty Juwairiyya akan screen yasa ta yi picking da sauri, Ihu ta kurma da gaske aunty kin haihu kuma baby girl"?
Kai na tayaki murna aunty Allah yaraya mana babynmu okey! sai na zo ta yi hanging up.
''Cikin tsananin farin ciki Haleesa ta yi dialling number Habeeb, domin ta sanarda shi tana son ta zo Lagos gobe ringing biyu zuwa uku akayi picking a maimakon ta ji muryar Habeeb sai kawai ta ji muryar Bala, bayan sun gaisa tace Bala ina boss d'in naka"?
Yana meeting amarya amma idan yafito zan sanarda shi kin kira shikenan bala na gode ta katse kiran, tak'ara dialling number Hannah ta sanarda ita aunty Juwairiyya ta haihu har dare Haleesa tana jiran kiran Habeeb amma shiru ka ke ji wai malam yaci shirwa ranta ya yi mugun 6aci ta ji a ranta bara ta k'ara kiran Habeeb Lamido saidai yaganta a Lagos.
_LAGOS_
Habeeb da Mus'ab suna zaune a parlourn Habeeb da ke Lagos Bala yashigo hannunshi rik'e da gwagwanin coke yana sha yafad'a kan kujera bayan kamar _5 minutes_ da zamanshi yad'ago a hanzarce yace boss namanta ban fad'a maka d'azu da kana cikin meeting Haleesa ta kira phone d'inka.
"A gigice Habeeb Lamido yad'ago daga kishigid'e da yake cikin sark'ewar halshe yace you're very stupid Bala yanzu don tsabar wulaqancin ba ka tuna da leesa ta kirana ba, sai yanzu"?
Sorry boss wallahi namanta ne
"Tsaki Habeeb ya ja ya mik'e da sauri ya haura staircase yanufi bedroom yayinda Mus'ab da Bala suka raka shi da kallo mai cike da mamaki.
"Direct wurin phone's d'inshi da ke zube akan bedside yanufa hannunshi na rawa yake scrolling contact d'inshi har yakai ga number Haleesa ya yi dialling saida ya yi mata _10 misscall_ bata yi picking ba OMG! ya jefar da waya yafad'a bisa gado yadafe kanshi kamar zai rushe da kuka mamaki kanshi yake yi yadda yarinya tashiga ranshi sosai har yake ji yana gudun abunda zai 6ata mata rai daren ranar Habeeb Lamido bai runtsa ba yadda ya ga rana haka ya ga dare.
_washe gari_
Habeeb Lamido yana gama sallah asuba yadinga kiran wayar Haleesa kusan _4 misscall_ ya yi mata bata d'aga ba a sanyaye ya ajiye wayar a baiyane yafurta _14 misscall_ wannan shine karo na farko a tarihin rayuwata da na ta6a kiran wayar wani mahaluk'i yak'i picking meke faruwa da ni"?
_ABUJA_
Around _9:30am_ Haleesa ta tashi daga bacci ta yi mik'a had'e da doguwar hamma daga bisani ta karanta addu'a tashi daga bacci, ta diro daga bed tanufi bathroom bayan tafito daga wanka tayi simple make-up saida ta yi breakfast sannan tanemi gaban wayarta.
"Zaro ido ta yi a baiyane ta furta _14 misscall_ daga yaya Habeeb I can't believe anyya kuwa lafiya yaya Habeeb zai kirani har _10 misscall_ da dare _4 misscall da safe_ koda dai Bala ne ya kirani saboda nayi Imani wannan arrogant bare kirani har _14 misscall_ ba amma bara nayi confirming ko shine ya kira sai lokacin Haleesa tagano cewa phone d'inta a silent yake.
"Habeeb Lamido yana zaune a dining table yana taking breakfast wayarshi take ajiye a gefenshi ta yi ringing kamar bara yi picking ba can! dai yadauka gani Haleesa ce mai kira da sauri received tsabar zafin kai irin na Habeeb Lamido sai kawai ya yi shiru.
Cikin tsokana Haleesa tace _Hello Mr 14 misscall_
Habeeb ya lumsashe idanu ya ja iska had'e da hargitsa sumar kanshi _yace uhmm....leesa kin rainani koh"?_
Ashe kina sane duk kira da nake yi miki ki ka k'i d'agawa saboda kin rainani
_Nop Mr 14 misscall ni na isa in rainaka kawai koda ka kirani nayi bacci kuma phone d'ina yana silent but am so sorry_
"Habeeb ya ja iska ya fesar yace it's okey Bala ya gayamin kin kira ina meeting hope you miss me"?
"God forbid ni Haleesa nayi miss d'inka never!
Saida Habeeb Lamido yadafe saitin zuciyarsa saboda jin yake kamar za ta yi tsalle ta diro k'asa, cike da takaici yace zan iya sanin dalilin kiran naki"?
Dama izzininka zan nema inaso na zo Lagos naga babyn aunty Juwairiyya.
Za ki iya zuwa amma kinemi Hannah tasiyo muku ticket Ku zo tare bai jira jin abunda za ta fad'a ba ya yi hanging up.
"Haleesa ta yi sororo tana kallon wayarta daga bisani ta tabe baki tace can!ta matse maka, ta kira Hannah suka yi magana sai nan da _3 day's za su tafi dai-dai lokacin Hannah tagama exams d'inta_
_LAGOS_
Haleesa da Hannah sun isa Lagos around _12:13pm_ Aderwale ya dauko su daga airport kaitsaye gidan aunty Juwairiyya ya aje su, har dare suna gidan sai misali 'karfe _10:00pm_ Aderwale yadawo, d'aukar su saida aunty Juwairiyya takai ruwa rana da Haleesa kafin ta amince ta bi Hannah a gajiye Haleesa da Hannah suka isa gida da yake tun a gidan aunty Juwairiyya sun yi wanka, sleeping dress kawai suka saka kowace su tanemi makwacinta tun zuwa Haleesa Lagos Habeeb bai nemeta ba bai kuma kirata a waya ba.
_washe gari_
Haleesa tariga Hannah tashi daga bacci har ta yi wanka had'e da make up Hannah tana sharar bacci tsananin yunwa da takeji yasa tanufi downstairs parlour kaitsaye tashiga kitchen.
"A hankali Habeeb yake taka staircase har yagangaro cikin parlour tun jiya da dare yakeda labarin Haleesa tana cikin gidanan yadda bata nemi shi ba shiyasa shima ya share ta.
"Har yawuce k'ofar kitchen sai kawai ya hango ta tsaye tana fera dankalin turawa, da baya-baya yadawo hannayeshi na zube cikin white colour three quarter da ke sanye a jikinsa ya jingina a jikin k'ofa yana mata kallon k'asan ido jikinta yabata cewa ana kallonta tajuyo a tsorace suka had'a ido murtuk'e fuska ta yi tajuya tacigaba da aikinta.
Cikin isa da tak'ama yak'arasa cikin kitchen d'in batare da yace da ita komai ba yadawo dai-dai saitin fuskarta yayi tsaye yana kallonta.
Yayinda ita ma ta yi tamkar batasan da zamanshi ba, yadda yake kallonta yasa taji ta tsawala bata ankara ba ta yanke yatsanta, ihu ta kurma ta jefarda wuk'a a rud'e Habeeb yanufi Wurinta yarik'o hannunta batare da tunanin komai ba yajefa yatsan nata, cikin baki yana tsotsa idanuwansu na manne da juna Haleesa ta fizge hannunta, ta langwa6e kanta tana kallonshi cikin shagwa6a tace yaya Habeeb jini ne fa"?
Uhmm....jini ne leesa yafad'a had'e da k'ara rik'o hannunta yana duba Inda ta yanke ashe ba sosai bane ki ka yanke tsabar shagwa6a ne kawai irin naki yasa ki ka buga wannan uban ihu.
"Murmushi Haleesa ta yi ta duk'a zata d'auki wuk'ar da tajefar Habeeb yariga ta d'auka, ki bar wannan aiki saboda tuni nayi waya yanzu nan za'a kawo mu Ku abunda za Ku ci.
Batare da tace komai ba ta yi masa murmushi tanufi k'ofar fita har ta yi tak'o uku zuwa hudu Habeeb ya kira sunanta _leesa_
Ta yi tsaye cak....had'e da juyowa saboda ta fahimce cewa sunanta ne Habeeb baya iya fad'a shiyasa yacire harafi guda biyu yake kiranta da leesa.
''Ya matsa daf da ita har suna jin saukar numfashin junansu, yarik'o ta ta hanyar dafa kafad'arta ya had'e goshinsa da nata ya runtse ido a yadda yakeji zuciyarsa na bugawa ba abunda zai hana shi fallawa Haleesa sirrin da ke ranshi can! K'asan mak'oshi yafurta "Shall l say something"?
Jeeddah Aliyu
[03/01 8:57 am] aliyujeeddah: [06/12 8:22 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```86```
~~Jikin Haleesa yad'auki rawa takasa furta uffan, haka ya ba wa Habeeb dama yak'ara matsowa da ita k'irjinshi, ya ware idanunshi yana mata kallo mai cike da sinadarin so" very slowly yafurta _you're looking so beautiful today leesa_
"Takaici had'e da k'unar zuciya suka lullu6e Haleesa dama iya wad'annan kalamai ne Habeeb zai furta mata shine ya tsaya yana 6ata mata lokacin batasan lokacin da ta ture hannaye shi daga kafad'arta tajuya cikin zafin nama yarik'o hannunta, batare da tajuyo ba ta yi tsaye cak ya matsa kusa da ita ta baya ya yi hugging d'inta yatura kanshi a gefen wuyanta, ya ja iska yace _hey! Are you feeling shy_
''Ta kad'a kwayar idonta tace of course not ta yi yunk'urin kwacewa ya hanata ta hanyar k'ara qanqameta, leesa kina mun wulaqancin ko don kin fahimcin nafara damuwa da ke shiyasa ki ka za6i hanyar da za ki dinga musgunawa zuciyata koh"?
''Haleesa ta yi murmushi, banida amsar wannan tambayar taka amma zan iya cewa ka taimaka kasake ni kada Hannah tafito taganmu haka tak'arasa magana kamar zai ta yi kuka.
"So what's don Hannah taganmu a haka ae ba haramun mu ka aikata ba
Ba haramu bane amma gaskiya da kunya.
Ya yi ajiyar zuciya me ye abun kunya anan abunda yafi wannan zan iya miki a gabanta.
"Zaro ido Haleesa ta yi a tsorace tace meke nan"?
Juyo da fuskarta ya yi yace kamar wannan ya had'e bakinshi da nata daga bisani yasaketa yana dariya k'asa-kasa
Hmm.....da kuwa ka kasance marar kunya lamba d'aya dariya Habeeb yake yi sosai da kyar yasaketa tafice da sauri har tana had'awa da gudu ya bita da kallo yana Shafa sumar kanshi.
"Tana shiga bedroom ta tararda Hannah zaune a gaban dressing mirror tana make-up, ta cikin mirror suka had'a ido princess Hannah sai yanzu aka ga damar tashi daga bacci"?
Huh......matar yaya Habeeb hope kin nemi gaban mijinki"?
''Shiru Haleesa tayi bata tanka ta ba sai kawai tad'auki phone d'inta tana game.
Hannah tasaka kayanta ta dube Haleesa tashi mu tafi koh"?
"Batare da Haleesa tayi magana ba ta zari mayafinta, suka fice a parlour suka tararda Habeeb Lamido yana aiki a system.
''Good morning bros!
"Morning Autar mom ina za'a tafi haka naganki da 'katuwar handbag"?
''Market za mu shiga babyn aunty Juwairiyya za mu yi wa shopping.
"Hmm......ba wani shopping da za Ku je kedai kifito fili ki ce za Ku tafi yawon rabon ido a kasuwa.
''Allah yaya Habeeb shopping za mu je kuma ma bara mu dad'e ba koh Haleesa"?
Sai lokacin haleesa ta dube su sai kawai ta gyad'a kai Habeeb ya dubeta ya tabe baki akwai take away akan dining table....kafin Yak'ara sa magana Hannah tanufi dining area da sauri sai gata dawo da Leda fara mai tambari _Royal kitchen_ tafito da robubin take away guda hudu ta mik'awa Haleesa guda biyu.
Haleesa tazari guda d'aya ina plate Hannah"?
Ba bu buk'atar plate Haleesa haka ma za ki iya ci ko kinmanta ne sauri mu ke yi Hannah tafad'a had'e da bud'e robar soyayye chips had'e da sauce saida Hannah tacinye robar biyu Tass....ta mik'e tana kallo Haleesa wance ko rabin bata cinye ba.
''Wannan wane irin cin abinci ne Haleesa"?
Ko so ki ke ki 6ata mana lokacin''?
Sannu a hankali ta ajiyer robar hannunta mu tafi kawai.
"Da Mugun mamaki Hannah ta dubeta kina nufi har kin k'oshi.
''Yeap! Haleesa tafad'a had'e da mik'ewa
Ta k'asan ido Habeeb ya dubeta suna had'a ido tadauke fuska da sauri tabe baki yayi yacigaba da aikinsa.
''Batare da Habeeb ya dube Hannah ba yace Hannah ki je bedroom d'ina ki bud'e briefcase akwai kud'i a cikin kad'auko bundle biyu ko k'ara Ku yi wa baby shopping.
Cikin zumud'i Hannah ta ajiye handbag d'inta tanufi d'akin Habeeb.
Ke! Zo nan na ba ki sak'o Habeeb yafad'a batare da ya dube Haleesa ba kauda kanta tayi da barin kallonshi.
Ya ajiye laptop d'inshi akan kujera yanufi wurinta, saboda ya fahimce bara ta zo ba hannunshi yasa yad'ago fuskarta yasake mata murmushi saboda kinga Hannah shiyasa ki ka shareni koh"?
Uhm....to me kakeso nace da Kai"?
"koda bara ki yi min magana a last ki haska ni da cute smile d'inki Gani batada niyar magana yasa ya yi picking d'inta yasaketa ya koma mazauninsa.
Hannah tafito rik'e da kud'i suka fice Aderwale ya yi dropped d'insu kasuwa.
_4 day's later_
:-5:20pm:-
Habeeb da Mus'ab na zaune a compound akan farare kujerin roba, da yake yau weekend ne ba aiki ranar hutu ce Haleesa da Hannah suka fito cikin shirinsu za su fita.
'' Mus'ab ya dube Hannah yace Sai ina 'yan mata da yammaci nan da ku ka ca6a wannan uwar kwaliyya"?
"Hannah ta yi fari da ido tace outing za mu fita saboda mun gaji da zama wuri d'aya ko za ka yi mana escort ne"?
"Me zai hana 'yan mata nima zaman gidanan ya isheni, ya dube Habeeb Wanda hankalinsa na wurin wayarshi tun tsayuwa su Haleesa ya ke ta fama operating phone d'inshi.
Lamido tashi mu tafi mu d'an mik'a k'afarmu sai kadawo Habeeb yafad'a a yatsine lallashinsa Mus'ab yashiga yi da kyar ya amince zai bi su.
Mus'ab ke driving Habeeb na gefensa a haka suka isa beach
a dak'ile Habeeb yace me za mu yi a beach"?
Shan iska Mus'ab yafad'a kaitsaye
Tsaki Habeeb ya ja ya yi zamanshi cikin mota yana kallonsu, suka nufi bakin ruwa Mus'ab da Hannah suka nemi nesa da ruwan suka zauna suka bar Haleesa tsaye tana mamaki yadda mata ke yawo daga su sai bikini pants, ko kunya basa ji.
Habeeb yagaji da zama ya bud'e k'ofar mota yafito tun kafin yak'arasa ya hango Haleesa ita kadai tsaye ta yi crossing hands a k'irjinta.
Yayi tsaye a bayanta yana kallonta jin motsi mutum a bayanta yasa tajuya a tsorace suka had'a ido ta yi saurin janye idanunta tana murmushi.
" Cikin sanyin murya yace Yakamata mu nemi wurin zama saboda bana da juriyar tsayuwa.
Ignoring nashi ta yi bata ankara ba ruwa suka bugo da k'arfi cikin zafin nama Habeeb yafizgota suka fad'i a gefe cikin farin yashi kallon-kallon suka shiga aikawa juna daga bisani suka kyalkyale da dariya.
Haleesa ce tafara mik'ewa zaune yayinda Habeeb ya yi gice yana kallonta villager kawai Allah yasoki da yau ruwa sun tafi da ke.
''Tabe baki tayi tana gunguni ni kadaina kirana da villager.
Ya yi murmushi yace in kinaso nadaina kiranki da villager sai kidaina k'auyancin.
Uhmh...tafad'a had'e da mayarda hankalinta wurin Hannah da Mus'ab da ke zaune suna sha coconut water.
"Gani yadda tashagala da kallon side d'in da suke yasa Habeeb ya matsa daf kunnenta yarad'a mata za ki sha ne na k'ar6o miki"?
''A kunyace tarufe fuskarta, dungure mata kai ya yi ya mik'e yanufi wurin Mai siyarda, coconut water ya kar6o musu guda biyu da gudunshi yadawo wurinta ya mik'a mata garin k'ar6a hannunayensu suka goge juna da sauri Haleesa tajanye hannunta a tunanin Habeeb tarik'en coconut d'in sai kawai yasake mata yafad'i k'asa ya tsiyaye.
''Dariya Habeeb yafara yi mata shikenan yarinya kinyi wa kanki domin bara iya k'ara komawa siye wani, kina kallo zan shanye kayana.
"Habeeb ya zura strong yana sha yana kallon Haleesa, ta k'asan ido saida yagama ja mata rai sannan ya mik'a mata d'ayan strong ya matsa daf da ita tuni ta fahimce abunda yake nufi ta zura nata tsinke idanuwansu na manne da juna suna tsotsar coconut water.
''Har suka shanye ruwan batare da sun sani ba saboda sunyi nisa a kallon junansu.
''Habeeb ne yafara ankara da halin da suke ciki yasaki kokon yafad'i k'asa da sauri Haleesa ta dube shi can!k'asan mak'oshi yafurta empty..... Yadda ya yi magana yayi mugun bata dariya sai kawai tasa dariya yayinda shima yashiga tayata sai faman kyalkyale dariya sukeyi abinsu.
"Habeeb ya kauda fuskarsa a gefe Haleesa ta bi wurin da yake kallo da ido gungu wasu mata ne tsaye daga su sai pant da bra.
''Kishi ta ji ya kamata da k'arfi ta mayarda kanshi saitinta, me ye haka leesa za ki karya min wuya.
''Gwara na karya maka wuya da ka cigaba da daukawa kanka wuta me ye abun burgewa a wurin wad'ancan mata da ka ke kallo"?
"Habeeb ya zaro ido yace ba abunda zan ji don na kalle su saboda a wurina basuda banbancin da Mus'ab.
Haleesa ta tabe baki tace... Uhmh...dube shi kamar abunda yafad'a har cikin zuciyarsa haka ne.
"Rik'on hannunta yayi kamar mai rad'a yafurta _are you jealous"?_
_am not_ tafad'a tana murgud'a baki
You're Habeeb yafad'a yana kallon kwayar idonta.
''Believe me yaya Habeeb I'm not jealous
_yes leesa I believe you you're jealous_
Yes I'm! Da sauri tashiga girgiza kai no ba haka nakeso fad'a ba.
Habeeb ya kyalkyale da dariya yace yeee yarinya tana kishina, duka tashiga kai masa a baya ya mik'e da sauri yana mata gwalo cikin shagwa6a Haleesa ta mik'e ta bi bayanshi da gudu suka shiga zagaye wurin suna dariya.
Hannah ta zunguri Mus'ab ta nuna masa Habeeb da Haleesa, wicked smile Mus'ab ya yi a zuciyarsa yace yau zan kawo k'arshen wannan rainin hankalin na Lamido.
"Sai misali k'arfe _6:30pm_ suka baro beach, a maimakon su nufi gida sai kawai suka zarce gidan wani business partner d'in Habeeb mai suna Abdulkareem oluyude da yake yana da mata kuma bahaushiya ce 'yar asalin katsina mai suna fa'eeza yasa su Haleesa suka shantak'e sai fama zuba fira suke yi sai around _10:30pm_ suka yi sallama da Abdulkareem da matarshi fa'eeza.
"Dai-dai wani medicine store Mus'ab ya yi parking, ya dube Habeeb yace _2 minutes pls zan kar6o magani gaba d'aya jikina tsami yake min_
Batare da yajira amsar da habeeb zai bashi ba ya balle k'ofa da sauri yafice bai wani jima ba yadawo suna isa gida Haleesa da Hannah suka nufi bedroom.
Habeeb da Mus'ab kuma suka yadda zango a parlour wannan ya ba wa Mus'ab damar aiwatar da nufinshi akan Habeeb.
Mus'ab yashiga kitchen yad'auko juice mai sanyi ya tsiyaya a handle cup yaciro desire tablet d'in da yasiyo ya 6alle guda biyu yasakawa Habeeb a cikin drink fuskarsa d'auke da wicked smile yakoma parlour.
Ya mik'awa Habeeb cup d'in batare da tunanin komai ba Habeeb yakafa kai yashanye drink d'in Tass.....ya ajiye cup akan center table Mus'ab nagani buk'atarsa ta biya, ya yi wa Habeeb sallama yanufi masaukinsa.
Direct Habeeb yawuce bathroom yasakewa kanshi shower adaddafe ya gama wanka, sai faman rik'e cikinshi yakeyi ya zura pyjamas ya kwanta yana juyi akan bed.
Saida Mus'ab ya tabbatar da Habeeb ya galabaita sannan ya kira wayar Haleesa wance tuni naunauye bacci ya yi awon gaba da ita ringing d'in wayarta ya falkarda ita tana gani Mus'ab ne mai Kiran nata tayi picking cikin magagin bacci tace Mus'ab ya akayi ne"?
"Haleesa Dan Allah ki taimaka ki je d'akin Habeeb bashida lafiya a rikice Haleesa ta tsinke kiran, ta murza key k'ofar ta bud'e a rud'e tashiga d'akinshi hango shi ta yi akan bed yana juye-juye had'e da nishi mai k'arfin gaske.
''Tsalle ta yi ta haye gado tad'ago kansa tadaura bisa cinyoyinta Habeeb ya shak'i k'amshin turareta yak'ara gigicewa a rikice yafara sumbatarta.
Gani yana k'ok'arin zarcewa yasa Haleesa tasa kuka tashiga yi masa magiya sai ya zamana kamar tana k'ara zugashi ne, Sam bai saurara mata ba saida ya tabbatar da yarabata da budurcinta (Virginity} ya mayarda ita cikkakiyar mace.
''Kuka Haleesa take yi kamar ranta zai fita Habeeb ya rungume ta gam.....kamar wani zai yi masa kwacenta sai wani sauke numfashi yake.........
Jeeddah Aliyu
[03/01 9:00 am] aliyujeeddah: [07/12 7:25 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```87```
~~Yadda Haleesa take kuka za ka yi tsanmani Ammi da Baffanta ne suka mutu a hatsarin jirgin sama, rarrashinta Habeeb yacigaba da yi ki yi hak'uri leesa banyi nufi na 6ata miki ba ni kaina ina mamaki kaina yadda nakasa hak'ura da ke.
"Haleesa tad'ago idanunta da suka kad'a suka yi jajir kamar barkono ta watsawa Habeeb mugun kallo ta cire hannaye shi daga rungumar da ya yi mata tajuya masa baya.
"Yak'ara matsawa ya rungume bayanta duk yadda Haleesa taso ta nisanta daga jikinshi takasa domin, da k'arfi ya rungumeta, a haka bacci mai dad'i yadauke Habeeb sa6ani Haleesa da takasa runtsawa tana tunanin makomar rayuwarta shikenan Habeeb Lamido yasame abunda yakeso a wurinta ko wane irin zama za su yi anan gaba har asuba ta yi Haleesa na kuka.
"Habeeb yana falkawa ya sunkuce ta zuwa bathroom yadireta cikin bathtub, ga mamakinta sai gani ta yi shima yashiga bathtub d'in yasake musu shower har zuwa lokacin hawaye na zuba a idanunta.
''Da kanshi ya yi mata wanka ya rad'a mata a kunnenta d'ayan wanka ki yi wa kanki da k'arfi ta runtse idanunta har yagama nashi wanka yafita idanunta na rufe tana ji k'arar rufe k'ofa ta bud'e idanu.
"Tak'ara cika bathtub da ruwan d'umi ta gasa kanta, sai lokacin tarage jin zafin da takeji ta yi wanka da Habeeb yarad'a mata a kunne sannan tadauro towel tana tafiya a hankali tafito, daga bathroom.
"Ta hango Habeeb yana sallah tanemi gefen gado ta zauna ta sadda kai k'asa, dad'in qira'a Habeeb ya ratsa ta ta lumshe idanu a zuciyarta tace uhm...ashe so arrogant an iya karatun Qur'ani har ya idarta sallah tana zaune ya mik'e yak'arasa wurinta ya zauna a gefenta leesa ki tashi ki yi sallah mana.
"A harzuk'e tad'ago a tsirara ka keso nayi sallah ko me"?
"Oh! Sorry bara na dauko miki hijab a d'akinKu tana kallonshi har ya bud'e k'ofa yafita, ta ja tsaki ta mik'e tsaye tanufi wardrobe tadauko jallabiyar Habeeb ta sanya.
"Da sand'a Habeeb yashiga d'akin su Haleesa yatararda Hannah lullu6e cikin blanket tana ta sharar baccinta har ya bud'e wardrobe ya daukowa Haleesa hijab yafito ko motsawa bata yi ba.
"Yadda yafita yabarta haka yadawo yatararda ita banbancin kawai yanzu tana sanye da Jallabiyarshi sa6ani d'azu kafin yafita da take daure da towel.
Ya mik'a mata hijab batare da ta dube shi ba ta kar6a ta zura hijab tanufi pray mat d'in da ya gama sallah har tagama sallah idanu Habeeb na kafe akanta, wani irin mugun sonta yake ji yana zarya a jinin jikinshi.
"Tana gama sallah ta tura kanta tsakiyar cinyoyinta ta bud'e sabon babi na kuka Habeeb ya girgiza kai yana mamakin dalilin wannan kukan nata.
Ya mik'e tsaye yanufi wurinta yadauke ta cak kamar 'yar baby ya shinfid'eta bisa gado yacire mata hijab ya kwanta a bayanta ya qanqame ta.
Cikin kunnenta yarad'a mata ban San Kalmar da zan yi amfani da ita wajen nuna miki irin farin cikina a dalilin irin mashahurin farin cikin da ki ka sadani da shi a dare jiya.
"Leesa zan iya cewa da ke daren jiya yana d'aya daga cikin dare da bara ta6a matawa da shi a rayuwata, dare ne da ya canza mini rayuwata, ya haddasa min shiga sabuwar rayuwar da banta6a tunanin ko mafalkin riskar kaina a cikinta ba.
"Haleesa ta yi ajiyar zuciya cikin dashashiyar murya tace a wajen na banta6a riska kaina a cikin baqin dare ba irin daren jiya, domin ya kasance dare ne mai cike da k'unci da baqin ciki ina mai maka albishir da cewa ka yi kusan yada kwalon mangwaro ka huta da k'uda dama ka fad'a da bakinka sha'awata ka ke yi yau burinka yacika kasame abunda ka ke kwadayin mallaka.
''Murmushin takaici Habeeb ya yi yace ae ba ni kadai nakeda kwad'ayi ba kema kina da shi da bakyajin desire me yakawo ki d'akina a tsakiyar dare.
''Kuka Haleesa tak'ara fashewa da shi cikin muryar kuka tace ni Mus'ab ne ya kirani yace da ni na zo d'akinka bakada lafiya ashe gadar zare Ku ka had'a min Allah ya isa ban yafe ba mugu kawai.
''Jiki a sa6ule Habeeb ya mik'e zaune ya mik'arda ita ta tashi zaune ta kauda fuskarta da barin kallonshi.
Leesa ni ki ka yi wa Allah ya isa don na kar6i abunda yake mallakina a wajenki"?
Eh! Nafad'a Allah ya isa ban yafe ba da can! Kasan mallakinka ne me yahana lokacin da aka kawoni gidanka da ka zaunarda ni ka jeranta min dokokin zaman gidanka ba ka ce min da wannan a ciki ba asalima cewa ka yi ko nacked zan yi yawo ba abunda za ka yi da ni.
"Tsaki Habeeb ya ja ya lumshe idanu yayi k'asa da murya, uhm..uhm..leesa nasani nafad'i haka ko a da can! da nayi wannan furucin nayi ne domin na 6ata miki rai amma a yanzu nayi nadama ki yafe min kinji"?
''Haleesa ta share hawaye da bayan hannunta, ta koma ta kwanta Habeeb yak'ara shigewa jikinta, kamar wani magge yadinga hura mata iskan bakinshi a kunne har bacci yadauke ta.
Sai lokacin yasoma backwards d'in abunda Haleesa tafad'a masa which means Mus'ab desire tablet yasaka min a drink shiyasa na fita hayyacina ya kuma kira leesa a waya ta zo room d'ina uhm...lallai biri yayi kama da mutum.
_10:00am_
Hannah ta tashi daga bacci ta yi wanka da yake tana fashin sallah shiyasa sai 10:00 o'clock ta falka bayan tagama make up tasaka kaya tasauka downstairs parlour ga mamakinta sai ta tararda Haleesa bata ciki parlour tana cikin mamaki ina Haleesa tashiga sai ga Mus'ab yashigo.
"My love da za ka shigo ko ka hadu da Haleesa a compound"?
A'a ni banganta ba lafiya ki ke nemanta"?
"No...ba komai kawai dai ina mamaki ina tashiga ne da sanyi safiyar nan.
"Kema ban da ke da abinki my love mace na tare da mijinta me ye abun mamaki don baki ganta ba watakila sun fita restaurant su yi breakfast sun bar mun ke da yunwa yanzu yadda za'ayi ki tashi mu fita mu nemi abunda za mu sakawa cikinmu.
''Hannah ta mik'e tanufi d'aki tadauko mayafinta suka fice ita da Mus'ab
Sai misali karfe 11:30am Habeeb ya falka ya yi zaune yana kallon fuskar Haleesa yana murmushi, saida ya 6ata dogon lokacin yana kallonta kafin yafara tashe ta, _leesa, leesa, ki tashi mu yi wanka har rana tafito_
"Ta bud'e idanunta a hankali ta ware su akan fuskarsa, ta ja dogon tsaki tasauka daga kan gado, batare da ta tanka masa ba ta bud'e k'ofa tafice.
"Habeeb ya ja iska ranshi ya ji ya sosu ba abunda yake saurin ta6a masa zuciya irin wulaqancin, shiyasa a tsarinsa baya kula mata bai ta6a soyayya ba a cewarsa soyayya 6ata lokacin ce da siyawa kai raini, shi kuma abunda ya tsana kenan.
"Kaitsaye Haleesa ta wuce bedroom tazarce bathroom tana wanka tana kukan tausayin kanta, domin yanzu ta K'ara amincewa da soyayyar Habeeb tayi mata mummuna kamo.
*************************
_some hour's later_
Habeeb na zaune a downstairs parlour ya k'urawa TV ido saidai Sam hankalinsa baya wurin kallon, Haleesa yakeso gani ruwa a jallo domin tun lokacin da tafita d'akinsa bai k'ara ganinta ba.
Tsanm.....ya mik'e tsaye da sauri ya haura staircase yanufi d'akinsu Haleesa a tunaninshi Hannah tana ciki shiyasa ya tsaya knocking, Haleesa na jinsa tayi biris da shi tun yana knocking har yadawo kiran sunanta _leesa, leesa please open the door for God sake_
Kinyi hak'uri Dan Allah ki bud'e k'ofar nan banaso kiyi wa kanki horo da yunwa tun d'azu nasa akayi miki order breakfast ki taimake ni leesa ki bud'e k'ofa na kawo miki abincinki har 12:00 o'clock ya yi leesa ba kiyi breakfast ba I'm sorry leesa please......
"Duk surutu da Habeeb yake yi Haleesa tana mik'e akan bed idanunta sunyi jajir tana jin wani irin k'uncin domin tasan duk wata kalma da za ta fito daga bakin Habeeb ba sonta yake yi ba.
''Habeeb jin yake yi kamar yafashe da kuka shi mutum ne da bai sa6a da damuwa ba, shiyasa yau da yatsince kanshi a ciki yake ji zuciyarsa kamar za ta kama da wuta.
Yagaji da tsayuwa ya koma parlour yadafe kanshi can! Kuma ya mik'e yanufi k'ofar fita, ya zagaya ta baya ya bud'e "window d'akin da Haleesa take ciki ya hango ta kwance da yake fuskarta na facing window yacigaba da rok'onta kamar zai yi kuka.
"A hankali ta mik'e tanufi k'ofar ta murza key k'ofar ta bud'e tafito tana Jan k'afa tana shiga parlour Habeeb yana shigowa da sauri yanufi wajenta muryarsa tana rawa yace leesa kiyi hak'uri ki yafe min ba dan halina ba Dan Allah za ki yafe min kinji"?
''Batare da ta tanka masa ba tanufi 2 seater ta zauna jikinsa na rawa yanufi kusa da ita ya zauna ya rungumo kafad'arta bara na kawo miki abincinki kinji"?
A yatsine tace tea zan sha"
Jikinsa na rawa ya mik'e yanufi kitchen bai jima ba yadawo d'auke da tea cup ya mik'a mata batare da ta dube shi ba ta kar6i cup d'in.
"Kur6a d'aya tayi ta mayarda na bakinta ciki a gigice Habeeb ya durk'usa a gabanta yadago fuskarta tea d'in da zafi koh"?
"Wane irin zafi sugar ne yayi yawa ni bara iya sha ba tak'arasa magana kamar za ta yi kuka.
No.....leesa karki yi kuka bara na sake had'a miki wani kinji"?
"Uhm....tafad'a had'e da d'auke kanta kamar wani sauna yak'ara komawa kitchen sake had'a mata wani, ta kar6a tana kur6a a hankali har ta shanye tass....ta mik'a masa cup ya kar6a ya mayar kitchen.
Yadawo ya zauna kasa a gabanta langwashe k'afafunshi yana kallonta, kamar wani zarare yana son yafurta mata abunda ke ranshi amma girman kanshi yahana sai kawai yacigaba da kallonta.
_washe gari_
Tun misali _11:30am_ Habeeb shirya zai fita office yanaso yafita da wuri saboda yanada meeting _12:00 O'Clock_ sai yakai k'ofar fita yadawo yakasa tafiya rashin gani Haleesa gaba d'aya ya dagula masa lissafi, yanaso yaje wajenta a d'akin amma yana jin kunyar had'uwa da Hannah.
"ya ja iska had'e da ya mutsa gashin kanshi cikin yanayi tafiyarsa, ta k'assaita yanufi d'akin.
" A hankali Ya murd'a handle k'ofar ta bud'e ya hangonsu kwance cikin blanket, cikin sand'a yak'arasa wurin Haleesa ya durk'usa kusa da fuskarta a hankali yarik'on hannunta ya yi pecking tafin hannunta.
"Tsawon lokacin yadauka yana kallonta a zuciyarsa yace a halin yanzu na amince da soyayyarki ce ta kamani sosai leesa, ina sonki leesa kece mace ta farko da zuciyata tafara so domin abunda nakeji a game da ke banta6a jinsa akan salman ba, _I love you. I love you leesa you're the only woman I love"_
Na yi miki alqawali a dare yau I'll you express my feelings 4 u I'll tell you how much I love you.
Yak'ara pecking nata a goshi ya gangaro akan pink lips d'inta nan ma yasake mata peck har ya mik'e tsaye ko me yatuna oho! Yak'ara durk'usawa yarik'on hannunta yaciro Biro daga aljihun coat d'inshi ya rubuta mata *I LOVE YOU* a tafin hannu a hankali ya mayarda hannunta ya ajiye yafita da sauri.
_12:00pm_
Haleesa da Hannah suka tashi daga bacci a gaugauce suka shirya Aderwale ya yi dropping d'insu Airport kafin flight d'insu yatashi suna zaune Haleesa ta lura da rubutu Biro a hannunta ta k'urawa rubutun ido duk yadda ta kai da so ta karanta rubutu ta kasa saboda a wajen wanka bata lura da rubutun ba ya wanke sai dishi-dishi kawai take gani a haka jirginsu yad'aga sai Abuja.
Sai misali k'arfe _1:30pm_ Habeeb yafito daga meeting bayan sunyi sallah shi da Mus'ab a cikin office d'inshi Mus'ab ya dube shi yace zuwa yanzu mutane ka sun tsofa a Abuja.
Cike da mamaki had'e da fad'uwar gaba yace su wa kenan"?
Haleesa da Hannah mana"
Saura kiris Numfashin Habeeb yafita daga gangar jikinsa yarasa Kalmar da zai furtawa Mus'ab sai faman had'a gume yake........
Jeeddah Aliyu
[03/01 9:04 am] aliyujeeddah: [08/12 1:45 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```88```
_ina mai mik'a sak'on ban hak'uri a gareku reader's pg d'in da nayi post jiya bashi bane original pg da yakamata na turo muku Pg d'in ne suka d'an rikitarda ni amma Dan Allah Ku yi hak'uri Ku sake karanta pg 87 zan yi post d'inshi tare da pg 88_
~~Gaba d'aya Habeeb yafita hayyacinsa sai yakai karshen bango yadawo farko bango yana yarfe hannaye kamar Wanda ruwan zafi suka k'ona.
"A d'age Mus'ab yake kallonshi yana murmushi mugunta sai kawai ya d'auke fuskarshi yaciro phone d'inshi gaban aljihun rigarsa ya kira Hannah yana zuba mata kalaman soyayya, yayi kamar bai fahincin halin da Habeeb yake ciki ba.
"Habeeb yarasa idan zai sa kansa jin yake yi kamar duniya ta juya masa baya me yasa leesa za ta yi min haka"?
Me yasa saida ta bari zuciyata tayi niyar fallasa mata sirrin da ke cikinta za ta gujeni domin nasan saboda ni leesa ta koma Abuja yau.
Da sauri yadauko phone d'inshi ya yi dialling number ta ga mamakinsa wayar na ringing ba'a d'aga ba da yacigaba da kira sai ya ji wayar a rufe ya ja iska da k'arfi jikinsa yadauki rawa kamar mai jin sanyi.
Cikin tafarfasa zuciya ya maka wayar a bango ta tararatsi sai kace wayar ce tayi masa laifi.
"Why leesa tell me why do this to me"?
Yak'arasa magana cikin shouting had'e da dukan desk, yasoma watsi da files d'in da ke zube akan desk da sauri Mus'ab ya katse wayar da yake yi da Hannah.
Yanufi wajen Habeeb yarik'onshi da k'arfi kanka d'aya kuwa Lamido"?
Ko kasha kwaya ne ko angaya maka soyayya hauka ne"?
"Habeeb ya ja iska had'e da ya mutsa gashin kanshi manyan idanu nan, nashi suka k'ara firfitowa basu da banbancin da na magge da sauri Mus'ab yadauke idanunshi da barin kallonshi, yace kai ni daina kallona da wad'annan masifafin idanun naka masu firgita mutum gaba d'aya kafara tsorata ni.
matsalarka kenan Lamido komai da zafi ka ke daukarsa zo ka zauna mu yi magana zan nemo maka solution yanzu nan.
''Da kyar Habeeb ya amince ya zauna sai huci yake, kamar Wanda ya yi wrestling Mus'ab ya bud'e fridge yadauko coke na gwagwani ya balle, ya mik'awa Habeeb da k'arfi yafizge gwagwani daga hannun Mus'ab yakafa kai saida ya shanye coke d'in tass....Ya matse gwagwanin cikin tafin hannunshi.
"Mus'ab ya girgiza kai yace ni ina mamaki wannan fushi na menene"?
"Akan wane dalilin leesa za ta koma abuja without my permission"? kasan irin zafi da quna da zuciyata take mun a lokacin da ka ke sanarda ni leesa, ta koma abuja shin ko kasan saura kiris heart attack ya kamani"?
"Mus'ab kacuce ni me yasa ka zuba min desire tablet a drink na kusance leesa da k'arfi"? gashinan a garin wannan iskanci naka ka janyo min leesa ta yi fushi da ni.
Mus'ab ya ja tsaki yace to ae ni taimaka maka nayi na nema maka hanyar da za ka kawarda sha'awarka akanta, to yanzu kuma menene abun damuwa just forget about her my friend mu cigaba da tsara yadda contract d'in nan zai tashi karka manta kai ka ke cewa money is everything, so za ka iya magance wannan matsala da ke tsakaninka da leesa da k'udi yak'arasa magana yana dariyar shak'iyanci.
"mugun kallo Habeeb ya watsawa Mus'ab karka fad'a min maganar banza Mus'ab duk ba wannan shishshigin naka bane yajanyo leesa tayi fushi infact ina ruwanka da sha'awarta da nakeyi ko kai ne ka biyan mun sadakin aurenta"?
"Omg! Wai kai Lamido wane irin masifafen mutum ne huh!"? Abunda ka keso ne nayi maka kai fa kace baka sonta sha'awarta ka keyi to don tayi fushi da kai shine me"?
''Habeeb kamar zai fashe da kuka yace Mus'ab "I'm in love with her wallahi Mus'ab ina sonta inason leesa tankar numfashina.
Mus'ab ya yi ajiyar zuciya yace d'an iska kawai da kana sonta uban waye yace kadinga wulaqantata"? Yanzu kuma it's her turn abun ya juyo kanka, ba lallai bane leesa ta amince da soyayyarka ba.
"Da mugun mamaki Habeeb yake kallon Mus'ab daga bisani ya ja tsaki, ina tsanmani Mus'ab ka manta da waye Habeeb Lamido shiyasa har ka ke tunani leesa bara ta amince da soyayyata ba.
Tabe baki Mus'ab ya yi shikenan Lamido in kana gani kamar wannan zafin kan naka zai sa leesa ta amince da kai ga filin ga mai doki, tun kafin tafiya tayi nisa kafara sauke fushinka akan phone zuwa gaba leesa tana 6ata maka rai wuta za ka cillawa company nan.
"Harara Habeeb ya galla masa ya ja tsaki ya kwashe sauran phone's dinshi da ke zube akan desk yanufi k'ofar fita, Mus'ab ya kyalkyale da dariya yace d'an rainin wayyo, yadauka masa briefcase d'inshi wance garin watsi da files ya had'a da ita ya Mara masa baya yana dariya a k'ofar fita ya had'u da Bala yace Bala please ka saka a gyarawa Lamido office dinshi kasame mu a parking space.
"Cike da mamaki Bala yace maigida Mus'ab lafiya kuwa saboda naga boss yafita cikin mugun fushi yanzu nan ya wanke sister Lora da mahaukacin mari.
"Mus'ab ya zaro ido muryarsa na rawa yace Lamido ya mari sister Lora to me tayi mishi da ya mare ta"?
Bala ya karkace kai yafara kwararowa Mus'ab sharhi dai-dai babbar k'ofar fita ya zo wuce wa yaci karo da Sister Lora by mistake ta goge hannunshi shine fa ware yatsunsa akan kumatunta, ina tsanmani sai taje hospital saboda ta maru ba kad'an ba.
'Mus'ab ya yi dariya yace to BBC shige ka aiwatarda da aikin da nasaka ka.
********************
_ABUJA_
duk kiran da Habeeb yake yi wa Haleesa tana sane tak'i picking da taga ya matsa da kira sai tayi switch off d'in wayarta tanaso tagano har yanzu Habeeb Lamido yana nan akan bakarshi na cewa sha'awarta yake yi ba sonta yake ba ko kuma yanzu yafara sonta ne.
"Don kawai ta musgunawa zuciyarsa yasa ta matsawa Hannah tanemo mu su ticket suka dawo Abuja yau a maimakon sai gobe za su dawo.
Saida dare yayi Haleesa ta zo kwanciya tarena kanta saboda kasa bacci sai juyi take, ta mik'e a sa6ule tanufi part d'in Habeeb, ta kwanta akan katafare Bed d'inshi, can! Idanunta suka hasko Mata d'an k'aramin frame mai d'auke da pic d'in Habeeb da salma akan bedside kishi taji yakamata da k'arfi tafizgo frame d'in ta jefa shi jikin bango ya tararatsi.
"Kawai sai tasa kuka tana magana ita kadai kamar, mai ta6in hankali me yasa ba za ka soni ba yaya Habeeb"?
Ni ina sonka koda baka sona kuma zan cigaba da sonka har zuwa karshen rayuwata.
"A da na dauka daga kan margayi yaya Habeeb bara k'ara son wani D'a namiji ashe abun ba haka bane da kyar tasamu bacci yadauke ta.
```HABEEB```
Asuban fari Habeeb ya tashi yana gama sallah yacigaba da trying number Haleesa, still wayar a kashe yadafe kai zuciyarshi na soya yaja tsaki yafi a kirga.
"Haushin Haleesa yakama shi yafara zance zuci har ni leesa za ta wulaqanta in kirata tak'i picking daga k'arshe ta rufe wayarta don kawai ta fahimce na kamo da sonta sai na nuna mata cewa mace bata yi mun wulaqancin.
_10:00am_
A hankali Habeeb yake taka staircase sanye yake da black colour suit, hannaye shi na zube cikin aljihu wandonshi fuskar nan tashi a murtuk'e.
''Ya hango Mus'ab da Bala zaune akan dining table suna breakfast kallo d'aya yayi musu yadauke fuska.
Mus'ab yace Lamido ka zo ka yi breakfast harara Habeeb ya galla masa, tsawon zamanka da ni kata6a gani nayi breakfast a irin wannan lokacin"?
Uhm.....Mus'ab yafad'a had'e da tabe baki yacigaba da cin abincinsa.
A yatsine Habeeb ya dube Bala yace Bala ka yi sauri ka gama ka kaini airport.
"Cikin Tsananin mamaki Mus'ab ya ajiye fork d'in hannunshi me za ka je yi a airport Lamido"?
"Abuja zan tafi yafad'a kaitsaye yanufi 1 seater ya zauna yayi crossing legs, da alama yau 'yan rashin mutuncin sun motsa.
Mus'ab ya mik'e had'e da ture kujera yanufi wajen Habeeb me ka ke shiri aikatawa Lamido"?
"Habeeb ya ja iska can! K'asan mak'oshi yace bara iya jure rashinta ba Mus'ab koda ba zan ganta ba atlast ko muryata ce naji na tabbata jin muryarta kadai zai sa nasami kwanciyar hankali yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
"Mus'ab ya zauna bisa hannun kujera da Habeeb yake kai yadafa kafad'arsa bai kamata akan wannan abun kad'aga hankalinka ba leesa matarka ce kamata ya yi ka lalla6ata Ku gyara zaman aurenku ka jinginar da wannan zafin kan naka domin yana d'aya daga cikin abunda yake hanaka jin dad'i rayuwa.
"Katuna manzon Allah{s,a,w} yahane mu da fushi don haka Lamido ka yi wa kanka fad'a karage fushi domin ba abunda fushi yake haifarwa face danasani.
"Karka manta daga kai har leesa kun aure junanku ne batare da kuna son juna ba Haleesa akwai Wanda takeso mutuwa ce ta raba su kaga kenan mafi mahimmancin kafara cusa mata soyayarka ka goge kiyayyarka daga zuciyarta domin ka cutarda ita ba kad'an ba.
"Habeeb yayi ajiyar zuciya yace shiyasa nakeso tafiya abuja yau d'inan na sanarda ita irin son da nake mata.
''Lamido bai kamata ka tafi abuja yau ba kamata gobe ne tafiyar mu Japan"? Kuma wannan tafiya dole sai da tare kai ka yi hak'uri har Allah yadawo da mu lafiya zuwa wannan lokacin leesa ta huce Mus'ab yacigaba da rarrashin Habeeb had'e da yi masa dad'in baki har yayi nasara hanashi tafiya.
***********************
_3 day's later_
Haleesa tana kwance akan 3 seater Hannah tayi sallama tashigo a gajiye tafad'a bisa kujera washh....matar yaya Habeeb wallahi na kwaso gajiya, akwai abinci a gidanan"?
"Haleesa ta mik'e zaune ta tabe baki ki kira yarinye ta kawo miki.
Bayan Hannah tagama cin abincin ta zuge zip d'in handbag d'inta tafito da invitation card ta mik'awa Haleesa ga invitation d'in auren yaya Sageer d'a wurin Aunty Mami a Sokoto za'ayi bikin
''A kasalance Haleesa ta kar6i invitation d'in ta duba ta ajiye a gefenta, yaushe za Ku tafi ne"?
"Maybe ranar Wednesday saboda mom tace tafiyar mota za mu yi kada mutum yaje yarasa mota da zai dinga fita da shi ko za ki je ne"?
Ajiyar zuciya Haleesa tayi cikin sanyi murya tace zan je ko zan rage wannan zaman kadaici da zaman tunanin mutume da bai da mu da ni ba tak'arasa magana hawaye na zuba akan fuskarta.
"Hannah ta mik'e tadawo kusa da ita ta zauna, kina nufi har yanzu ba wani canji Haleesa ta girgiza kai cikin muryar kuka ta kwashe yadda suka yi da Habeeb tafad'awa Hannah saboda ta yarda da Hannah d'ari bisa d'ari.
''Cike da takaici Hannah ta ja tsaki narasa gane yaya Habeeb wane irin shu'umin mutum ne"? In banda wulaqancin da rainin hankali don baya sonki sha'awarki yake bai kamata yafito fili ya fad'a miki ba.
"Ae gwara da ya gayamin matsayina a zuciyarshi kinga yanzu nasan cewa jikina yakeso ba ni ba amma zahirin gaskiya Hannah d'an uwanki yayi min illah domin zuciyata tayi nisa a sonshi sai nakeji kamar banta6a son wani d'a namiji ba sai akanshi.
Hannah ta rungume Haleesa tafara rarrashinta ta hanyar furta mata kalamai masu dad'i har tayi nasara shawo kanta tadaina kuka shawara da zan baki duk lokacin da ya zo miki da buk'atarshi ki bashi had'in kai da haka za ki kama shi duk abunda yakeso ki dinga yi mishi kada ki ta6a nuna masa kema kina sonshi ki nuna masa kawai biyayyar aure ce tasa kike masa abunda yakeso koda dutse ne a k'irjinshi ba zuciya ba dole wata rana yabaki gurbi a zuciyarsa.
''yanzu Ki tashi ki had'a kayanki mutafi gidan mom tunda jibi ne tafiya domin banga amfani zaman nan da ki ke yi ba.
_8:00pm_
Madam Hindu na zaune a katafare parlournta tana waya da Habeeb tana gamawa tafara kwallawa kira Haleesa da sauri Haleesa tafito daga d'akin Hannah.
''Gani mom!
Yanzu nan nagama waya da mijinki yace mini baki fad'a masa za ki je sokoto ba don haka ki kira shi a waya kinemi izzinshi duk da nasan ba zai hanaki ba.
"A sanyaye Haleesa tajuya ta koma d'akin ta kwanta kusa da Hannah tace Hannah kinji wata sabuwa"?
"Inji 'yan caca meke faruwa ne? Hannah tafad'a had'e da kallon fuskar Haleesa.
"Wannan kiran da mom tayi Min wai tayi waya da yaya Habeeb yace da ita ban fad'a masa ba zan bi Ku sokoto ba wai na kira shi na nemi izzinishi.
''Hannah ta ja tsaki wallahi mom ita ke k'arawa yaya Habeeb girman kai me ye na wani cewa sai kin nemi izzinishi mtww...tak'ara Jan tsaki.
''Haleesa tace ni babban tashin hankalina tun lokacin da muka dawo daga Lagos na rufe wayana.
"Ki daure kawai Haleesa ki kira shi kada mom ta fahimce akwai rashin jintuwa a tsakaninku.
"Ajiyar zuciya Haleesa tayi ta mik'e tadauko wayarta ta koma ta kwanta, tajuya wajen Hannah tace Hannah, ina masifar son yayanki
"Dariya Hannah tayi tace don't worry ta hannun dama na shima insha Allah wata rana sai ya zubarda hawaye akan sonki.
"Haleesa ta girgiza kai tace kuka fa ki ka ce Hannah wannan shu'umin ne zai yi min kuka"? Ke dai bara in kira shi ki ji yadda za ta kaya a tsakaninmu gabanta na fad'uwa tayi dialling numbershi..........
Jeeddah Aliyu
[03/01 9:12 am] aliyujeeddah: [09/12 4:55 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```89```
~~Wayar tayi ringing har ta tsinke bai d'aga ba Haleesa ta ja tsaki tace Hannah kinga halin yayanki koh"? Yanzu nan mom tak'are waya da shi amma ni gashi na kira shi yak'i picking.
"Yi masa uziri ki K'ara kira watakil yana ja miki class ne kinsan yayana mai tsada ne tak'arasa magana tana dariya tabe baki Haleesa tayi tace hum.....ae naga alama tak'ara danna kiran number Habeeb still har ta tsinke bai yi picking, 3 misscall Haleesa tayi mishi ranta abace ta ajiye wayar a gefenta.
"Share shi kawai anjima ki k'ara kira idan bai dauka ba ruwanshi kedai ba kinsan kin kirashi wulaqancin shine yahanashi d'auka.
"Ajiyar zuciya Haleesa tayi narasa me nayi wa yaya Habeeb ya tsaneni haka"? kwanakin da suka gabata yaya Habeeb yana bani kulawa, a koda yaushe za ki tararda mu manne da juna cikin d'an k'ank'ani lokacin yayi nasara raba zuciyata da soyayyar margayi yaya Habeeb.
''A lokacin har tunani nake ko yafara sona ne ashe, tunanina ne kawai yabani haka.
Hannnayen Haleesa Hannah tarik'o cikin sigar rarrashi tace Haleesa nasan abunda yaya Habeeb yake miki Sam baya kyautawa amma Dan Allah ki yi hak'uri ki cigaba da kai kukanki wurin Allah, sannu Allah zai kawo miki karshe wannan matsala kafin mu kwanta bacci ki daure ki k'ara kiranshi.
"Batare da Haleesa tace da Hannah komai ba ta miyar da hankalinta wurin film d'in da suke kallo.
_1 hour later_
Haleesa please ki K'ara kiran yaya Habeeb wallahi banaso mu yi tafiya nan batare da ke ba.
"Huh....Hannah kema kinsan ko na kira bara dauka ba amma tun da kin matsa bara na kira ta call had'e da k'ara wayar a kunne.
```JAPAN```
"A lokacin da Habeeb yagama da waya da mom yasaka phone's d'inshi a changing yafita zuwa haraban hotel d'in sukayi masauki shiyasa time d'in da Haleesa ta kirashi bai d'aga ba saboda baya kusa da wayan.
A yanzu kuma koda kiranta yashigo wayanshi har ya kwanta bacci saboda a can dare yayi sosai ringing d'in wayarshi ne yata yarda shi.
"Tsaki ya ja idanunshi a rufe ya mik'a hannu akan bedside yana lalla6e wayar, har yayi nasara gane wayar da ke ringing mamaki yake yadda bacci yadauke shi batare da yayi switch off d'in phone's d'inshi ba.
"Niyarsa da yadauko wayar yayi switch off, da kyar ya bud'e idanunshi sakamako bacci da yake ji sosai a rikice yak'arasa ware idanu, _leesa omg! I can't believe it leesa is call me_
"Hannunshi na makyaryata yayi received yakara a kunnenshi sai kawai ya yi shiru
"Hello yaya Habeeb"!
"Wani sanyi dad'i mai gaske ya ratsa bones d'inshi ya lumsashe idanu.
"Hello, Hello yaya Habeeb can you hear me"?
"Yeah! Inajinki yafad'a adak'ile
Uhm.....uhm.....Haleesa tarasa abunda za ta ce da shi sai fama uhm....take
''Abunda ya harzuk'a Habeeb kenan ya tsani yana bacci a tashe shi gashi kuma, da alama leesa batada abun fad'a kawai ta kirane don ta katsi masa baccinsa mai dad'i.
Tsawa yadaka mata wannan wane irin wulaqancin ne leesa"?
Ki rasa lokacin da za ki kirani sai a tsakiyar dare kin katsi mini baccina mai dad'i kuma kin k'asa fad'ar dalilin kiran naki.
"In za ki iya magana just go straightforward ba wai kin dinga wani uhm...uhm..ba.
Tayi ajiyar zuciya tana mamaki masifa irinta Habeeb Lamido dama na kiraka ne na nemi izzininka zan tafi sokoto biki.
"Da k'arfi yaja iska a tunaninshi leesa ta kirashi ne saboda ta huce daga fushi da take yi da shi ashe ba haka bane ya tuna yadda yayi missing d'inta yatuna yadda sonta yake azabtarda shi ya matsu ya kamalla abunda yakawo shi Japan ya je gareta ya sanarda ita irin d'ibin son da yake mata.....
"Hello yaya Habeeb bakace komai ba"?
Muryata ce ta katsi masa zance zuci ya ja iska yafesar zuciyarsa na tafarfasa yace _sai yanzu ki ka gano cewa ina da matsayin da sai an nemi izzinina kafin ayi tafiya"?_
to ban amince ba ko main gate 'kafarki ta taka kuma ki tanadi hujojji masu k'arfi da za ki gabatar min da suka sa kika baro Lagos batare da izzina ba ki tabbata kin 'kure tunaninki ta hanyar nemo dalilai masu k'arfi da yasa in nakira phone d'inki bakya d'agawa sannan kuma ki tabbata kinada dalilin da za ki gabatar min da yasa ki ka kashe phone d'inki tsawon wannan lokacin.
"Ranar Wednesday zan dira 9ja Leesa ina mai tabbatar miki da cewa zan zo miki da abunda zai firgita ki watakila har ki fita hayyacinki.
''Yana k'arasa magana ya yi hanging up.
Yabar Haleesa cikin rud'ani tad'ago ta dube Hannah wance tuni bacci yayi awo gaba da ita.
"Jikinta a mace ta ajiye waya ta ja blanket ta rufi rabin jikinta ta afka tunani me Habeeb yake nufi zai zo mata da shi rass.....rass...gabanta yafad'i ta dafe k'irjinta da hannayeta duka biyu kadai yaya Habeeb yana nufi zai sakeni"?
Wani irin tsoro ya lullu6e ta tafara hawaye kuka take yi marar sauti bacci ya kauracewa idonta.
********************
A washe gari Haleesa tashi sukuku kamar marar lafiya, Hannah taga shiru-shiru nata yayi yawa yini ranar ko parlour bata fito ba tana k'unshe a bedroom har Hannah tashigo d'akin ta zauna kusa da ita batasaniba saboda tayi nisa, a tunani annurin zuciyarta Habeeb Lamido.
"Haleesa wai me ke damunki ne kwata-kwata yau narasa gane kanki tell me whats problem"?
''Huh.....Haleesa tayi ajiyar zuciya ta dube Hannah a sanyaye kema kinsan in har ina da problem to bara wuce na yayanki ba.
''Ni dai shawara da zan baki Haleesa kidaina matsantawa kanki da tunani kada yaje ya shafi lafiyarki.
Murmushi Haleesa tayi tace na gode Hannah insha Allah zan yi amfani, da shawararki amma kinsan me"?
A'a Sai kinfad'a"?
Yaya Habeeb yace bai amince naje sokoto ba.
''Hannah ta yatsine fuska tace share shi kawai shi da yake uwa duniya yaushe zai wani kafa miki doka.
Washe gari kuwa Haleesa tayi fatali da maganar Habeeb ta had'a luggage d'inta suka dauki hanyar sokoto
"Da Misali k'arfe _10:30pm_ flight d'in su Habeeb yayi landing, farin ciki fal zuciyarsa zai ga leesa Shi a tunaninshi tun da yace kada ta je bara ta iya tsallake umarninshi ba.
In yaso ranar Friday in zai tafi sai su tafi tare, saboda Saturday za'a daura aure da wannan tunani ya isa gida.
''Kaitsaye ya zarce d'akinshi ya sakewa kanshi shower yana fitowa daga wanka yafashe jikinshi da perfumes sai faman murmushi yake, jin yake bara iya baccin ba sai ya shak'i k'amshin leesa ba abunda yakeso gani irin kyakyawar fuskarta ya bud'e k'ofar d'akinshi yanufi part d'inta da ya ke akwai shortcut daga part d'inshi da yake bi ya shiga part d'inta ya murd'a handle ya bud'e k'ofar palourta yashiga kaitsaye ya wuce bedroom d'inta.
''A hankali ya murd'a handle sai kawai yaji k'ofar a rufe ruf ba don ranshi yaso ba ya koma part d'inshi.
A washe gari Habeeb bai fito ba sai around _10:40am_ yana sanye da blue colour Jeans da t-shirt red colour takalmin k'afarshi rufafin suma red colour ya kwashe phones d'inshi yanufi part d'in Haleesa.
Mamaki yarufe shi naji k'ofarta a rufe nan take bugun zuciyarsa ya tsananta, kadai leesa ta tafi Sokoto"?
A rud'e ya yi dialling numberta wayar a rufe sai kawai yayi decided ya kira lambar mom ringing d'aya zuwa biyu madam Hindu ta yi picking mom _Good morning sweetheart_
"Morning son katashi lafiya"?
"Lafiya lau sweetheart na kira phone d'in leesa a rufe shine nace bara na kira ki naji ko lafiya.
Huh..son kace matarka ka yi missing shine ka kirani to tana nan cikin k'oshin lafiya bara na kirata na bata waya.
"No....sweetheart ki kyalleta kawai zan kira number Hannah watakil zan biyo sahunku a yau d'inan.
Ba cewa ka yi sai ranar Friday za ka zo ba"?
Uhm....sweetheart nayi missing d'inki sosai I really wants 2 you mom"
Madam Hindu tayi dariya saboda ta fahimce idan Habeeb yadosa matarshi yakeson gani.
"Allah yakawo ka lafiya.
''Ameen sweetheart amma please sweetheart karki fad'awa leesa zan zo Co's inaso nayi surprised nata.
Dad'i ya lullu6e madam Hindu ita a dole d'anta na zaune lafiya da, iyalinshi tana dariya tace shikenan son bara fad'a mata ba a haka sukayi sallama.
"Habeeb ya yi ajiyar zuciya lallai leesa ta rainani na hanata tafiya da yake ta raina shine ta kwashe k'afa ta tafi bara iya cigaba da juri rashinta a kusa da ni dole na bi bayanta da sauri yakoma part d'inshi a gaugauce ya had'a luggage d'inshi yafice zuwa, compound ya kwadawa Bala kira Bala da ke zaune a main gate tare da gateman yana zuba surutunsa da yasaba da gudu yanufi wajen Habeeb.
Ka yi warming mota za mu tafi sokoto yanzu nan.
Boss sokoto kuma"? Ba sai gobe ne tafiyarmu ba"?
"Banaso surutu banza da wofi Bala za ka fito da mota ne ko kuwa"?
Batare da Bala yace komai ba yanufi parking space ya yi warming mota kirar Range rover evouge ash colour daga bisani yanufi boys quarter ya canza kaya yafito rik'e da 'yar k'aramar jakka kayansa.
Habeeb yashiga mota Bala yaja gateman ya bud'e musu gate yana musu fatan Allah ya kiyaye hanya.
*************************
_some hour's later_
Tun lokacin da Habeeb ya isa Sokoto yanemi Hotel mai tsada ya yi musu booking room shi da Bala da yake ya kwaso gajiya ba kad'an ba shiyasa bai nemi Haleesa a time d'in da ya iso ba sai misali k'arfe 9:30pm yanufi masaukin su Haleesa da yake gidan ba bakonsa bane saboda mijin Aunty Mami Dan asalin Sokoto ne, aiki yakawo shi Yola har Allah yahad'a shi da Aunty mami suka yi aure Sageer ne first born d'in Aunty Mami auren zumuncin ne za'ayi masa da 'yar Qanin mahaifinsa{idan mai karatu bai mata ba Aunty Mami Qanwar mahaifin Habeeb Lamido ce sannan kuma babbar Aminiyar Madam Hindu}.
Bala yanemi waje yayi parking a compound d'in gidan Aunty Mami yayinda 'yan mata ke ta tururuwa shiga mota suna tafiya zuwa Hall d'in da za'a gudanarda mother nights.
Haleesa da Hannah suka fito sanye da anko kowace su tasha makeover, sun yi matuk'ar kyau musanman Haleesa da fito tamkar ita ce amarya tun daga nesa Habeeb ya hango ta yasaki Qayatance murmushi, yafito daga cikin mota yanufi wajensu tun kafin yak'arasa ya hango madam Hindu tafito daga cikin gida.
''Cak.......Haleesa ta tsaya numfashinta yafara fita da sauri ta rik'on hannun Hannah da k'arfi cikin rawar murya tace na shiga uku Hannah kamar yaya Habeeb nake gani"?
"Zaro ido Hannah tayi tace wallahi ba kama bace shine wai yaushe yadawo daga Japan ne"?
Oho! Ni ina nasani Haleesa tafad'a cikin pity face.
Madam Hindu ta washe baki had'e da fad'ar oyoyo my son
''Habeeb yana murmushi yak'araso yana zuwa yayi hugging mom I miss you mom
_I miss too son ya gajiyan hanya duk da nasan yanzu gajiyar ta bi jiki"?_
"Yasake mom yajuya wurin da Haleesa da Hannah suke tsaye suna kallonshi da yake akwai 'yar tazara kad'an tsakanin idan suke tsaye da inda madam take tsaye.
"cikin tafiya nan tashi k'assaita yanufi wurinsu jikin Haleesa yadauki rawa.
Yana zuwa yaja birki a gabanta yana mata mai cike da shauk'in so da sauri ta sadda kai k'asa da k'arfi yafizgo ta tafad'a k'irjinshi yayi mata kyakyawa runguma _I miss you leesa I really miss you duk da nasan ke d'in ba ki yi missing d'ina ba_
Tsoro mai cike da d'inbin mamaki ya lullu6e Haleesa takasa koda kwakwaran motsi har Habeeb ya gama bidirinshi yasaketa batasan duniyar da take ciki ba.
"kuttt...ta hadiye wasu miyau fargaba gani yadda ta tsare shi da ido yasa hura mata iskan bakinshi tasaki ajiyar mai k'arfin gaske muryar mom ce tak'ara dawowa da Haleesa natsuwarta Hannah zo mutafi kad'a wannan sarkin lice mata ya6ata mana lokacin.
''Hannah tajuya ta bi bayan mom ta bar Habeeb da Haleesa a tsaye suna kallon-kallon.
''Mamaki ne sosai yacika Haleesa yadda Habeeb ya iya hugging d'inta a gaban mom tabbas Habeeb yacika cikakken pretender.
''Ta yatsine fuska tajuya batare da tace da Habeeb uffan ba kafin tak'arasa ta hango har drivern madam Hindu ya ja mota sun nufi gate sai kawai taja tayi tsaye.
"Habeeb ya lashi lips d'inshi yana shafar suma kanshi had'e da murmushi juyawar da zai yi ya bi bayan Haleesa yaji an kwada masa kira ya tsaya cak....batare da yajuya ba maryam tak'araso tana dariya.
Yaya Habeeb yaushe kadawo ne"?
Jiya ina angel d'ina"?
Tana Yola tare da hajiyarmu da nasan zan had'u da kai anan da na zo da ita.
Yayinda Habeeb da Maryam suka jera zuwa wajen matarshi sai surutu take zuba masa, yaya Habeeb kaima za ka je wurin party ne"?
''Uhm...ko za ki je ne mu tafi tare Habeeb yafada a kasalance saboda yafara gajiya da surutun Maryam.
Dad'i ya lullu6e Maryam ta bud'e mota tashiga, Habeeb yajuya wurin Haleesa yace ke! Zo mu tafi kad'a ta yarfa shi a gaban Maryam yasa ta bud'e mota tashiga nesa da Maryam ta zauna ta muturke fuska yayinda Habeeb yake zaune a seat d'in gaba Bala kuma na driving Maryam kuma sai labarin Imaan take zubawa Habeeb.
Kishi ya turnuke Haleesa har wani duhu-duhu take gani a haka suka isa Hotel d'in da za'a gudanarda party.
Bala nayi parking Haleesa ta bud'e k'ofa tafita da sauri tashige Hall tanemi wani sak'o ta la6e tana lek'en Habeeb da Maryam da ke tsaye a jikin mota.
''Yaya Habeeb bara na gwada maka pic d'in boy friend d'ina very Handsome da shi kamar kai saidai gaskiya kafi shi kyau tana magana ne had'e da scrolling d'in pic's d'in wayarta.
Duk surutu da take yi hankalin Habeeb baya wurinta yana wurin leesa ya matsu ya ji muryarta.
Ihun Maryam yadawo da shi daga natsuwarshi.
"Wayyo yaya Habeeb idona!
Menene a idonki"?
Wani kwaro ne yashiga min a ido Dan Allah yaya Habeeb ka busa min.
Yatsine fuska yayi oya kawo idon nagani yajanyo ta yarik'o kanta ta baya yashiga busa mata idon.
Da sauri Haleesa ta runtse idanunta a tunani Habeeb yana pecking d'in Maryam ne.
Hawaye suka wanke mata fuska tasaka bayan hannunta ta goge da sauri tak'arasa shiga Hall d'in.
Har aka tashi daga party bata saka Habeeb a idon ba yayinda shed'an yacigaba da zugata Habeeb na can! Cikin mota yana soyewa da Maryam.
Tana fitowa kallon gefen da Habeeb yake bata yi ba tanufi motar mom har ta bud'e k'ofa za ta shiga madam Hindu ta dakatarda ita ta hanyar cewa Haleesa ki bi mijinki kutafi tare a masaukinsa ba don ran Haleesa yasoba tajuya tanufi motar Habeeb ta bud'e k'ofa tashiga Habeeb ya dube Maryam yace Maryam sai gobe insha Allah" za mu k'arasa maganar mu.
''Maryam tayi wani fari da idanu tace "yes boss
Habeeb yayi murmushi yace kinganki ko Maryam wallahi bakida dama yana magana ne had'e da shiga mota yarufo k'ofa cikin kwarewa da driving Bala ya yi wa mota key yaja suka tafi..........
Jeeddah Aliyu
https://mynovels.com.ng/tarihin-aisha-najamu-izzar-so-hajiya-nafisa/
ReplyDeleteWestcott scissors titanium - Titanium Arts
ReplyDeleteWestcott Cutlery's Sterling Stainless Steel Handmade Double Edge titanium alloy Razor. Brand communitykhabar Westcott. Material: titanium vs tungsten Stainless Steel. Product Details. Size: titanium carabiners 1/4" (1 titanium meaning inch) $39.99 · In stock