Tuesday, 3 January 2017

NI DA YAYA 71_80

[31/12/2016 9:57 am] aliyujeeddah: [16/11 7:04 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```71```

_this page is dedicated 2 u *Firdausi Sodangi* thanks 4 the love & care_


~~Da sauri Haleesa ta sada kai k'asa Hannah tacigaba da cewa yaya Habeeb kai dai bara kadaina irin wannan zuwa bazata naka, mutum bai kwana da kai ba saidai kawai ya waye gari ya ganka.
       ''Habeeb Lamido ya yatsine fuska cike da isa da ji da kai yace gidana ne ina da right da zan shigo a duk lokacin da naga dama ke me ye matsalarki da hakan''?
   Hannah ta kyalkyale da dariya maida wuk'a big bros daga magana sai cibi yazama k'aro kai fa d'an kaifi ne tak'arasa magana had'e da shot d'in ball ta gangara akan table ta shige rami ta daka tsalle had'e da ihu tajuya wurin Haleesa da ke tsaye kamar an shuka ta tayi mata gwalo _yes I'm the winner you are loser matar yaya Habeeb_
  Haleesa ta kwa6e fuska kamar za ta yi kuka cikin muryarta mai sanyi tace _Humm.....dole ki zama winner tun da ni ba iya wa nayi ba amma ki jira ranar da duk na kware u will be loser_
Hannah ta yi dariya tana magana had'e da kallon fuskar Habeeb Lamido no way matar yaya Habeeb bara ki ta6a iya yi min game ko mijiki da yake mayye snooker da kyar yake dokeni.
    ''Habeeb Lamido ya yi murmushi ya lumshe ido daga bisani ya ware su akan Hannah yace ko za mu gwada ne''?
   ''Hannah ta zaro ido cab! A'a ba shirya buga wasa da kai ba
Habeeb ya tabe baki karki ji mamaki ki yi min game saboda na kwana biyu ban yi wasan ba.
   ''Hannah tace ba wani nan wayo ka ke so yi min ka ramawa matarka game d'in da nayi mata.
Habeeb Lamido ya yi ignoring nata kamar bai ji abunda tafad'a Yajuya wurin Bala yace _Bala please put the racket_
''Yes Boss Bala yafad'a had'e da k'arasa wa wurin snooker table ya tattara balls ya yi arranged d'insu.
  ''Habeeb Lamido ya matsa daf da Haleesa cikin voice d'inshi mai masifar tsorata Haleesa yace ke bani stick hannunta na rawa garin mik'a masa hannunta ya goge nashi a lokacin d'aya suka ji wani irin electric shock ya ja hannaye su Haleesa batasan lokacin da tasaki stick d'in k'asa cikin rawan murya tace am sorry yaya Habeeb tana magana ne had'e da sunkuyawa k'asa yayin da shima Habeeb Lamido ya d'uka ya d'auki stick dai-dai ta kai hannunta again hannaye su suka sake had'ewa kallon da ya yi mata yasa ta yi sauri janye hannunta, ta mik'e da sauri.
Hannah da ke tsaye tana kallonsu tasaki murmushi, Wanda ita kadai tasan manufarsa   Habeeb yana shot d'in ball tashige rami Haleesa batasan lokacin da ta daka tsalle had'e da furta _yes_ kallon da Habeeb ya watsa mata yasaka ta jin kunya ta sunkuyar da kai Habeeb ya yi winning Haleesa tadinga yi ma Hannah dariya''
"Harara Hannah ta galla Mata had'e da cewa da nayi niyya na koya miki har ki kware tun da ki ka yi min dariya na fasa.
''Habeeb ya tabe ya matsa wurin Haleesa ba zato ba tsanmani Haleesa ta ji yadank'o hannunta ya yi k'asa da murya kamar mai rad'a zo na koyo miki ki huta da wannan 'yar tsarko gaban Haleesa yafad'i 'yan hanjinta suka kad'a ta rikice Habeeb rik'o hannunta suka k'arasa wurin snooker table ya yi bayanta yadaura kanshi a kafad'a ta Hannah ta zaro ido tana kallon iko Allah a zuciyarta tace _huh...lallai yaya Habeeb cikkake d'an wasa ne so yake yanuna min lafiya qalau yake zaune da Haleesa bara na zuba ido naga yadda wasa nashi zai k'are_            
     ''Tsoro ya lullu6e Haleesa ji take kamar tasaki fitsari daf da kunnenta yakai bakinshi yarad'a mata _hold this stick please_
Ka sa motsi ta yi yarik'o hannunta aza bisa Stick ya saita ball yana bugawa ball d'in yashige rami Hannah tasaki ihu had'e da tafi phone d'in Habeeb da ke rik'e a hannun Bala ya yi ''ringing da saur Bala ya mik'a masa yasake Haleesa ya kar6e wayan had'e da juyawa cikin gida.
 Haleesa takasa kwakwaran motsi Hannah ta dafa ta, tace Haleesa tuni na fahimce inda yaya Habeeb ya dosa saidai abunda ya rikita ni me yake nufi da wannan pretending da yake yi.
Haleesa ta yi rau-rau da idanu tace kada wannan ya baki mamaki domin haka ya ke nunawa a gaban mutane idan mu ka kadaita daga ni sai shi bathroom slippers yafi ni a wurinshi.
  ''Ba abunda zan ce da ke Haleesa illah nace da ke ki yi hankuri Allah yana tare da masu hankuri.
Haleesa ta share hawaye da suka zubo mata tace hankuri ya zama dole saboda da amincewa ta iyayye na suka aura masa ni ba dole aka yi min ba.
  "Tausayinta Yakama Hannah ta ji kamar ta tayata kukan da take yi saida bara ta iya ba saboda za ta karyawa Haleesa zuciya, sai kawai tarik'o hannunta suka shiga cikin gida.
Bayan su yi wanka had'e da breakfast da yake Hannah _11:00am_ take ta lectures hakan ne yabata dama kafin ta wuce school tashiga part d'in yaya Habeeb, zaune ta tarar da shi a sitting room _Sannu da hutawa yaya Habeeb_
  "Yauwa ya aka yi baki tafi school ba ko yau bakida lectures ne"?
Hannah ta zauna akan kujera da ke facing d'inshi tace ina da amma sai _11:00 o'clock_ dama yaya Habeeb zuwa na yi na d'an baka shawara akan irin yanayi zamanka da Haleesa ta d'an numfasa wani mugun kallo Habeeb ya watsa mata had'e da cewa inajinki"
A ganina yaya Habeeb a bisa ra'ayinka mom ta nema maka auren Haleesa bai kamata ki dinga nunawa duniya kana son Haleesa amma idan Ku ka kad'aita ka nuna mata tsantsa k'iyayya wannan zalinci ne yaya Habeeb kuma ba halika bane infact me ka ke tunani zai faru idan mom tasan irin abunda ke wakana a tsakaninku"?
Cikin zafin rai Habeeb yadaka mata tsawa ya kuma nuna ta da yatsa banaso iskanci banza da wofi Hannah yaushe ki ka yi shekaru da za ki bani shawara ina gargad'inki da ki fita daga harka gidana banaso sa ido kuma karki sake na ji wannan magana taje kunnen mom infact ba laifi ki bane, laifin wannan munafuka ne da ta yi zaune ta zaiyane miki sirrin zaman aure mu tashi ki bani wuri yafad'a kamar zai daketa da gudu Hannah tafita.
"Ya ja tsoki yafara zance zuci ni yarinya nan zata ta wulaqanta yanzu duk, wannan pretending da nake yi ya tashi a banza tabbas sai na nuna mata kuskure ta na fad'awa Hannah sirrin zaman mu.
   "Cikin zafin rai ya mik'e yanufi part d'in Haleesa.
    ''Haleesa na zaune akan kujera hannunta rik'e da remote tana chanza channel ta ji Habeeb Lamido ya fisgo ta da k'arfi ya matsi mata wuya cikin k'auk'ausar murya mai cike da gargad'i yafara magana........

Jeeddah Aliyu
[31/12/2016 9:59 am] aliyujeeddah: [17/11 5:59 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```72```

~~Ashe ke munafuka ce bansaniba har ni za ki fallasa, ko don kin ga ina d'aga miki k'afa shin kin manta da gargad'i da nayi miki"?
    ''Ki bud'e kunnenki da kyau ki saurare ni yana magana had'e da murd'e mata, kunne muddin ki ka sake wannan magana ya je kunne mom wallahi sai na wulaqanta ki kala wulaqanci da ba ki ta6a gani a tarihi rayuwarki.
  Tsanani zafin rik'o da ya yi mata yasa takasa ko da motsi, sai hawaye ke zuba daga idanunta abu gwanin ban tausayi da kyar ta bud'e baki muryar ta baya fita sosai tace _me na yi maka yaya Habeeb me yasa ka za6i ka hukunta ni bisa laifi da banida masaniya akai"?_
   ''Rufe min baki kafin na wanka miki mari banta6a sani miye 6aci rai sai da na hadu da ke tun daga lokacin da ki ka shigo rayuwata ta chanza, narasa sukuni banta6a tsanar wata 'ya mace sai akanki banta6a kwanciya bacci ya k'auracewa idanuwa na sai da na hadu da ke
''shin wannan kadai bai ishe ki ba har sai kin jagorance raba tsakanina da mahaifiyata"?
Ya ja iska ya fesar zuciyarshi na tafarfasa yacigaba da cewa ina matuk'ar son mahaifiya ta had'e da farin cikinta dalili da yasa kenan na amince na aure ki nake kuma pretending as muna zaman lafiya duk ina yi ne saboda mahaifiya ta, sai ga shi cikin d'an k'ank'ani lokacin kinaso ki rusa min budget'' ki had'ani da ita''
 ke kanki kisan _you're not my type_ wannan abu da ki ka aikata yau yak'ara min tsanarki yana gama magana ya saketa had'e da hankad'e ta ta yi tagal-tagal tafad'a bisa kujera yak'ara dank'o wuyanta karki kuskure ki K'ara kuskure fad'awa Hannah sirrin zaman mu, sake aikata hakan yana nufi za ki rasa sauran farin ciki da yai saura a tare da ke, yasake mata rankwashi tasaki ihun azaba ji take kamar kwakwalwa ta zai fita yanuna ta da yatsa cikin tsawa yace _I'm warning you don't do that mistake again_ yajuya azafafe ya shige part d'inshi.
   ''Tsawon lokacin Haleesa tadauka hannunta dafe da kanta tun daga wuyanta har izuwa zuciyarta rad'ad'i suke mata ji take kamar ta hadiye zuciya, ta mutu ko za ta huta da wannan d'ibin bakin ciki da Habeeb Lamido yake guma mata.
   Takifa kanta a hannun kujera tafashe da kuka mai tsunma zuciya kuka taci mai isar ta daga bisani tashige bedroom" wahalalle bacci ya yi awo gaba da ita.
*******************
_some hour's later_
Haleesa na zaune a parlounta idanuta sunyi luhu-luhu sakamako kukan da ta ci har yanzu mamaki take me Hannah ta je tafad'a wa Habeeb Lamido har da yazo ya yi mata wannan mummuna cin zarafi iya saninta batasan tafad'i wata magana akan irin zama da sukeyi asalima ita ce tafara dauko maganar.
Tak'ara gyara zamanta had'e da rafka tagumi tacigaba zance zuci in kuwa Hannah ta je ta gayawa yaya Habeeb wani abu Wanda ni ban fad'a ba da kuwa ta cuce ni zan jira dawowarta tafad'a min abunda ta sanarda shi da ya harzuk'a shi ya iya rufe idanu ya zazzaga min rashin mutunci, duk da dama halinsa ne rashin mutunci da rashin sanin daraja d'an Adam.
   Haleesa na cikin wannan yanayi Hannah ta yi sallama cike da gajiya tafad'a kan kujera _matar yaya Habeeb ya kadaici"?_
  ''Murmushi yak'e Haleesa ta yi tace huh...ba kin tafi kin barni ba
Hmm.... Bari kawai matar yaya Habeeb ni kaina na matsu na kamalla karatu nan na huta da wahala.
_Ni kuwa Hannah kina bani mamaki kwata-kwata remain 3 months ki zana final exam miye kuma abin damuwa"?_
Cab.....ni gani 3 months nakeyi tamkar 3 year's ke ni fa na matsu na ganni gidan yaya Mus'ab tak'arasa magana had'e da mik'ewa tashiga kitchen tadawo hannunta d'auke da plate.
Haleesa ta galla mata  harara kin Shiga uku Hannah bakida zance sai na aure Sai kinyin auren kidawo kina danasani a da kafin zuwan wannan lokacin banida zance da yawuce irin wannan da ki ke yi ashe buri na ba zai cika ba, mutuwa tashiga tsakanina da farin cikina kaddara ta jefo ni gidan mutume da a kullum yake min barazana rabani da raguwa farin ciki da yai saura a tare da ni narasa me ki ka fad'a masa d'azu da safe da ya 6ata masa rai iya sanina ban gaya miki wata mummuna magana akansa.
  ''Hannah ta dire spoon d'in hannunta fuskarta d'auke da tsantsan damuwa tace kina nufi ki ce kema yaya Habeeb ya yi miki gargad'i da yai min"?
   ''Haleesa ta tabe ta koma jikin kujera ta kwanta had'e da lumshe idanu zuciyarta na mata rad'ad'i.
    ''Hannah ta yi ajiyar zuciya daga bisani ta kwashe yadda ta yi da yaya Habeeb da kuma gargad'i da ya yi mata tafad'awa Haleesa
  Ajiyar zuciya Haleesa ta yi tace _please Hannah na rok'e ki da kada ki sanar da mom wannan zance zan cigaba da zama da yaya Habeeb har izuwa lokacin da Allah zai yanke min wahala_
  Hannah ta ja tsoki cike da tausayi Haleesa tace kema matar yaya Habeeb kinada laifi''?
  Harara Haleesa ta galla mata tace miye laifi na"?
    "Laifinki babban ne Haleesa kin d'auki tsoron duniya kin daura kan yaya Habeeb sai kace wani horror wannan yana d'aya daga cikin dalilai da yasa yake miki yadda yaga dama yake zuba miki, wulaqanci son ranshi.
   ''Ki cire wannan tsoro da ki ke yi masa ki koyi tsiwa da rashin kunya sannan za ki kwance yancinki a wurinshi.
 Wani zillo Haleesa ta yi kamar za ta kife kasa ta zaro ido tace anyya  kuwa Hannah kinada hankali, ko kin manta aljannata tana k'ark'ashe k'afar yaya Habeeb wannan zama da nake yi ibada ne zan cigaba da kai kuka na a wurin Allah har ya kawo min k'arshe wannan matsala amma gaskiya bara iya yi masa rashin kunya  saboda ina jin tsoron had'uwa ta da ubangijina domin na tabbata bara ki so ki ganni a wuta jahanama  shi fa miji Hannah girma ne da shi matuk'ar kanaso ka samu rabauta dole ka bishi sau da k'afa.
    Tun lokacin da Haleesa tafara magana Hannah take mata, kallon tausayi daga bisani ta girgiza kai tace _Allahu Akbar malama Haleesa tabbas kinada k'arfi Imani_
Sai dai ba anan gizo ke sak'a Sam baki fahimce idan na dosa ba ta d'an numfasa daga bisani tacigaba da cewa
   "Ni fa ba ina nufi ki daina yi masa biyayya kawai dai ki rage wannan masifafe tsoro da ki ke masa ta haka ne, za Ku same zaman lafiya ya gyara tsarin rayuwar aurenku.
    "Haleesa ta girgiza kai had'e da cewa bara iya ba saboda tsoron Habeeb Lamido a jinina yake wannan yasamo asali tun daga farko haduwa ta da shi.
"Hannah ta ja tsoki saboda yanzu Haleesa tafara bata haushi ta mik'e batare da tak'ara furta uffan tashige bedroom ta bar Haleesa zaune talabe da kumatu tana karatun wasik'ar jaki.
******************
```WASHE GARI ```
Bayan Haleesa ta shirya Imaan cikin uniform d'inta ta rakata kamar yadda tasaba tana fitowa compound ta hango Habeeb Lamido tsaye a parking space yana magana da sa'eed kawai ta tsince kanta cikin tsanani fad'uwa gaba da sauri ta taka birki tariko hannun Imaan ta dank'a mata launch box d'inta tajuya cikin gida tana Shiga parlour taci karo da Hannah ta yi shirin fita idanu ta zaro cike da mamaki tace _Hannah ina zuwa haka naganki cikin shiri fita bayan kin ce da ni yau sai  2:00 o'clock  za ki shiga school"?_
 ''Hannah ta yi murmushi tace na manta ne tun jiya na fad'a miki mom za tayi tafiya zuwa Dubai dama mu yi magana da ita da safe zan zo kafin ta wuce sauri da nakeyi sa'eed nakeso na bi in ya yi dropping d'in Imaan sai yawuce da ni.
   ''Ki ce ina yi wa mom Allah ya kai lafiya Haleesa tafad'a.
"Hannah tace okay tak'arasa fita
Haleesa na Shiga bedroom ta cire sleeping dress d'in da ke jikinta ta daura towel tashiga bathroom.
 Daga idan Habeeb Lamido yake tsaye ya hango lokacin da Haleesa ta juya cikin gida, ya kuma tabbata saboda ta ganshi ne ta yi hakan ya yi kyaci.
   ''Imaan na kyala ido ta hango Daddynta ta falla da gudu yadauke ta had'e da cilla ta sama yana sauketa k'asa tasoma zuba masa _questions_ Daddy ina elephant da snake d'ina"?
Daddy ka siyo min biscuits da chocolate"?
Habeeb Lamido ya yi murmushi yarik'o hannunta duka na siyo miki my Angel amma sai kin dawo daga school zan baki.
"Wani irin tsalle Imaan ta daka cikin shagwa6a, take magana _Allah Daddy ba idan zan je sai ka bani abina_
 Duk yadda Habeeb yaso ya rarrashi Imaan ta tafi school tak'i har Hannah tak'araso yana rarrashinta daga k'arshe ma sai takasa mishi kuka.
   "Ya akayi ne Imaan me kike yi wa kuka"?
Hannah tafad'a had'e da rik'o d'ayan hannunta.
 Cikin murya kuka tace Daddy ne yace bara bani kayana.
 "Hannah tad'ago ta dube yaya Habeeb tace please yaya Habeeb ka bata kayan nata domin wannan ba shiru za ta yi ba ta dinga kuka kenan
  ''Habeeb ya ja iska ya fesar saboda har yanzu haushi Hannah yake ji batare da yace da ita komai ba d'auki Imaan yanufi cikin gida yadauko katuwar Leda ya bud'e yaciro elephant irin Wanda ake pumping d'inshi da iska ya bata yak'ara Ciro wani k'aramin kwali yafito da snake d'in roba za ka yi tsanmani na kware ne haka yadinga fito mata da tarkace toy's.
 Imaan tayi hugging d'inshi tace _thank you Daddy_
Murmushi ya yi had'e da pecking nata ya bud'e kwalin chocolate da biscuit ya d'iba mata yace d'auki wannan tarkace ki kaima auntynki ta ajiye miki.
   _No Daddy ni da su zan tafi school_
My Angel rigima uncle Ezekiel zai dake ki in ki ka je da toys school ki kaima auntynki ta ajiye miki in kindawo school you can play with them kinji"?
   "Imaan tad'aga kai ta sunkuce leda takasa koda d'agata Habeeb ya yi murmushi my angel bara ki iya d'aukar wannan katuwar leda ki barshi anan
 Imaan ta turo baki _Daddy bara na kaima aunty Haleesa elephant d'ina da snake ta ajiye min_
 ''Kai kuma ka ajiye min wannan ta nuna ledar da yatsanta.
  _oya je ki Kai mata_
Da gudu ta nufi part d'in Haleesa direct bedroom ta wuce tana  kwallawa Haleesa kira da yake Haleesa na bathroom bata ji kiran nata ba Imaan ta bud'e wardrobe ta jefa elephant d'inta har tajuya ta tuna da Snake d'in da ke rataye a wuyanta kawai ta jefa shi akan bed tafice da gudu.
Haleesa na fitowa daga bathroom tanufi dressing tana shace sumanta da comb cikin nishad'i tafara rera wak'ar Aashiqui mai take _Hum mar jaayenge_
Kamar daga sama ta cikin mirror ta hango k'aton maciji shinfid'e akan bed d'inta a firgici tajuyo tabbas idanuta ba k'arya suka hasko mata ba maciji ne duk duniya ba abunda Haleesa take tsoro cikin jinsi dabbobi irin maciji ko a movies taga an nuno maciji tsorata ta ke yi.
  ''Numfashinta ya tsaya chak ta zaro ido ta ta k'ark'are iya k'arfinta ta kurma ihu ta murd'a handle da k'arfi tafice da gudu ta yi tsaye a parlour tana zunduma ihu gaba d'aya amo sauti ihunta yakarad'e gida
Habeeb Lamido na zaune a parlounshi ya ji sauti ihunta cikin b'aci rai yanufi part d'inta yana Shiga parlour ya daka mata tsawa ke!...... Ihu me ki ke yi wa mutane"?
   "Cikin sark'ewa halshe tafara magana yaya Habeeb maciji a bedroom d'ina
 Habeeb Lamido ya zaro ido fuskarshi dauke da tsantsan mamaki yace maciji kuma"?
"Eh yaya Habeeb wallahi maciji bisa gadona
  "Habeeb ya yatsine fuska bara na duba in kuma na je banga komai ba kinsan sauran ya k'arasa magana had'e da juyawa da sauri Haleesa ta sha gabanshi idanuta suka ciko da hawaye _Dan Allah yaya karka je ya cije ka_
Harara ya zuba mata ya hankad'e ta yashiga d'akin wani irin haushi ya turnuk'e shi sakamako maciji roba Imaan da yagani akan bed yadauko maciji Yajuya parlour.
''Haleesa nagani Habeeb Lamido d'auke da maciji ta kurma ihu mai matuk'ar razanarwa  numfashinta yadauke tafad'i k'asa a some
Habeeb ya jefar da maciji yanufi wurinta a rikice yad'ago ta ke,ke ki tashi maciji roba ne abun wasa Imaan ne.
Duk surutu da yakeyi idanun Haleesa na  rufe ruf sai lokacin ya fahimci suma ta yi yadauke ta chak garin d'aukar ta towel d'in jikinta ya zame k'irjinta ya baiyana da sauri Habeeb Lamido ya runtsi idanu tsawon dak'ik'a uku yadauka kafin ya bud'e idanu nashi daga bisani ya shinfed'e ta akan kujera ya mik'a hannunshi........

Jeeddah Aliyu
[31/12/2016 10:02 am] aliyujeeddah: [19/11 5:37 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```73```

~~A hankali ya ja towel yarufe mata k'irji wani irin kasala mai had'e da tsintsa shawa'a suka lullu6e shi, ya zauna a gefen k'afafuta ya dafe kanshi da hannaye shi yad'ago ya sace kallonta she is still unconscious yadauke fuskarshi ya lumshe idanu image d'in abunda yafaru yafara yi masa shawagi surar jikin Haleesa yake gani da sauri ya bud'e idanu ya ware su akan fuskarta, d'an k'aramin bakinta mai d'auke da pink lips ya k'urawa ido jin yake kamar ya sumbace ta a wannan karon kasa d'auke idanunshi ya yi akanta tsawon lokacin yadauka yana kallon kyakyawar surar jikinta sai kawai ya tsince kanshi da zance zuci _ashe haka yarinya nan take"?_
Ya sauke ajiyar zuciya _she is very beautiful_
Saida shekaru ta sun yi k'ank'anta a tsarina banaso mace mai k'anana shekaru nafiso mace mai shekaru da yawa tun daga kan marigayiya salma nagano amfani auren mace take da shekaru ita ce tasan yadda ake tarairaya miji sa6ani wannan da batasan komai ba sai tsoro da kuka wannan yaya Habeeb d'in ya riga ya sagarta ta gashi yatafi ya barni da lalura ya ja tsoki da ace ina son yarinya nan da zan juri na rene ta har ta kai shekaru da nakeso matata ta kasance da su, ya shafi lallausar saje shi ya mik'e da kyar kamar Wanda yasha kayan maye yashiga kitchen ya bud'e fridge yadauko robar ruwa yadawo parlour har yanzu idanunta na rufe.
    "Ya balle murfi ruwan ya zuba a hannunshi ya tsuguna dai-dai fuskarta ya Shafa mata tasauke katuwar ajiyar zuciya saidai bata bud'e idanunta ba.
Tsabar iskanci irin na Habeeb Lamido saida ya dube saitin k'irjinta inda towel bai ida rufewa ba ya tsiyaya mata ruwa, Zubur Haleesa ta yi ta mik'e zaune a firgici ta furta _wayyo yaya Habeeb ka jefar da maciji nan kada ya cije ka_
   "Gani yadda ta yi magana Habeeb yagano har yanzu bata dawo a hayyacita ba ke"! Yadaka mata tsawa
  A tsorace ta dube shi sai fama zare ido take yi
 Ya muturk'e fuska Macijin roba ne zai cije ni yak'ara sa magana yana yatsina.
 Haleesa tak'ara zaro idanu a rikice ta furta maciji roba kuma"?
  ''Kwarai kuwa maciji roba ne tsabar rashin hankalinki ne yasa ki ka kasa gane na roba ne yak'ara sa magana yana mata kallon banza.
   "Cikin tsanani mamaki Wanda yakasa boyuwa akan fuskarta tace macijin roba to me yakawo macijin roba a room d'ina"?
''Tabe baki yayi kamar bara bata amsa ba sai da ya ja iska yace tsaraba da Imaan tace na siyo mata a Canada ne.
  Ran Haleesa ya yi mugun b'aci har takasa boyewa cikin tafarfasa zuciya tace _haba yaya Habeeb yanzu ka Lula uwar duniya har Canada karasa abunda za ka yiwa 'yarka tsaraba da shi sai macijin roba wannan wace irin d'abi'a ce"?_
   "Habeeb Lamido ya yi sororo yasaki baki da hanci yana kallonta tsanani mamaki da kuma k'arfin halinta su ka hana shi furta uffan sai faman kallonta yake.
   ''Ganin yadda ya tsareta da mayyu idanunshi yasa ta kalli jikinta ta zaro ido da sauri tasaka hannayeta takare k'irjinta.
Abunda ya yi masifar k'ular da shi ya galla mata harara Me ye kuma na wani kare k'irji"?
Abunda ki ka sake a fili sai ni ne na taimaka na rufe miki shine don tsabar iskanci za ki wani kare zai fi miki sauki ki bar shi a haka domin ba burge ni zai yi ba yak'arasa magana yana yatsina.
     "Kunya ta lullube Haleesa ko kwakwara motsi takasa wannan yaba Habeeb Lamido dama yacigaba da gasa mata maganganu masu zafi da k'ona zuciya da ki ke zance narasa abunda zan yiwa Imaan tsaraba da shi sai macijin roba da shi naga dama yi mata tsaraba, tun da nat fahimce kina tsoron maciji sai nasa an nemo mini masu rai k'ato kg zan yi a gidanan na zuba su da na kamaki kina mini kukan mutuwar saurayinki a gida sai nasaka ki a ciki sun cinye ki In yaso ki bi saurayinki da ya koya miki soyayya lahira sai Ku cigaba daga inda ku ka tsaya.
   ''Jikin Haleesa yadauki rawa ta hadiye yawu masu masifar d'aci tsoro mai cike da fargaba ya yi nasara lullu6e ta hawaye suka wanke mata fuska cikin sark'ewar harafi tace dan Allah yaya Habeeb Ka yi hank'uri karka kawo maciji a gidanan wallahi ina masifar tsoronshi ka ji tausayina yaya Habeeb.
  ''Harara Habeeb ya watsa mata dallah''! tashi ki sako kayan kirki ki zo ki gyara mini room d'ina wannan magiya da ki ke yi ba shi zai sa na fasa abunda na yi niyya.
  "Shiru Haleesa ta yi takasa tashi
 "Ina magana kin yi ignoring d'ina yana d'aya daga cikin dalili da zai sa na kawo miki maciji a gidanan.
Ba bu shiri Haleesa ta mik'e garin sauri towel d'in jikinta ya zame da sauri tadafe shi tajuya da gudu tashige bedroom d'inta.
Habeeb ya lumshe ido yana shafar sumar kanshi a hankali tsawon _3 minutes_ yadauka a haka daga bisani ya mik'e yanufi part d'inshi.
   "Haleesa na karasawa d'akinta tafad'a bisa bed ta yi ruf da ciki shikenan yaya Habeeb yagama gane mini k'irji mugu kawai da sauri ta mik'e kada yaji ta shiru yashigo yak'ara ganinta haka ta bud'e wardrobe tafito da fitted gown na atamfa tasaka ta yi light makeup ta bi lungu da sak'o na jikinta da perfumes masu sanyi k'amshi direct part d'in yaya Habeeb tanufa tun zuwanta Abuja bata ta6a shiga part d'inshi wannan shine karo na farko da k'arfarta ta taka zuwa part d'in.
Tana zuwa last stairs ta yi tsaye tana tunani  yadda za'a yi ta had'a ido da shi saboda kunya takeji yaganta half nacked
 "Tsawon _5 minutes_ ta d'auka a tsaye tana shawara da zuciyata ganin tsayuwa bara fisheta ba ta turo k'ofar glass tashiga parlour sanyi Ac da k'amshi air freshener yadak'i hancinta ta lumshe idanu, cikin muryarta mai sanyi ta yi sallama yana zaune a 3 sitter hannunshi rik'e da handle cup yana slipping d'in White wine ya amsa mata a dak'ile karaf idanunta suka sauka bisa bottle d'in white wine da ke ajiye bisa stool saura kiris numfashinta yadauke a tunani Haleesa giya ne saboda bata ta6a sani akwai juice mai irin bottle d'in giya _dama yaya Habeeb mashiyi ne"? haba biri ya yi kama da mutum wannan iskanci da yake shek'awa ashe aikin chaji ne shiyasa kullum idanunshi a lumshe yana magana yana Jan iska kamar Wanda yaci yaji"?_
Cikin abunda bai fi _30 second's Haleesa ta yi jerowa kanta wad'annan tambayoyi_
"Habeeb Lamido yad'ago ya dube Haleesa idanunshi a lumshe _yace ke me ki ke jira ne kin wani tsare ni da ido sai kace kin ci karo da marigayi saurayinki_
 Yana k'arasa magana ya yi slipping juice
  "Haleesa tak'ara tsorata musanmman da ta hango glassblower jere da white wine kala-kala tak'ara gigicewa a zuciyata tace ashe bansaniba gidan giya nake zaune ashe madam Hindu tasan d'anta mashayi ne shine ta yi ruwa tayi tsaki tayi sanadin da na aure shi ta fake da tausayina takeji
Wallahi ta cuce ni shikenan ta kassara min rayuwa.
Ke! Wai me ki ke jira ne"? ni fa na tsani kallo
  Hawaye da Haleesa take boyewa suka gangaro akan fuskarta ta kwasa da gudu tafice daga parlour tana kuka kamar ranta zai fita.
  "Tsanani haushi ya turnuk'e Habeeb muddin yarinya nan bata daina yi mini kukan mutuwa saurayinta a gida sai na yi mata wulaqanci mai Sosa zuciya yak'ara sa magana had'e da Jan tsoki ya mik'e a zafafe yanufi part d'inta cikin zafin rai ya murd'a handle ya ji k'ofar a rufe.
Da k'arfi yafara knocking Haleesa da ke kwance akan bed tana rera kuka ta mik'e zaune a firgici ta gallawa k'ofa harara kamar tana ganin Habeeb duk knocking d'in da yake yi ta yi banza da shi.
Habeeb yak'ara harzuk'a ya yi k'udiri in kama Haleesa sai ya yi mata abunda bata ta6a tsanmani ba cike da haushinta yajuya part d'inshi.

_3 hour's later_
Tsanani yunwa da Haleesa take ji yasa takasa hank'ura da cigaba da zaman bedroom dole ta bud'e k'ofa tanufi d'an k'aramin kitchen d'in da ke part d'inta idanunta sun rufe Sam bata lura da Habeeb Lamido da ke hakince a parlounta tana shiga kitchen yana danna kai da k'arfi yafinciko ta Haleesa ta tsorata matuk'a duk ta bi ta rud'e da k'arfi tsiya ya mannata da a jikin bango yad'ago fuskarta da hannunshi na dama ya tsare ta da fitinanu idanushi.
   ''Cikin b'acin rai Haleesa tace dallah! Malam ka sakeni kadaina ta6ani da hannunka da ka ke daga cup d'in barasa tsabar lalacewa a cikin gidanka na sunnah ka ke sha giya tur! Da wannan halin naka wallahi a yau ina Nadama auranka tak'ara sa magana tana Mai fashewa da kuka.
    ''Habeeb ya zaro ido kai amma wannan yarinya anyi dak'iki'ya white wine bottle da tana gani ina sha shine nata hauka yabata giya ne saura kiris dariya ta kunbuce masa sai kawai ya basar Yasaki wicked smile Chan k'asan mak'oshi yafara magana huh...my wife dama kina nufi ki ce ba ki San mashayi ki ka aura ba"?
Girgiza kai ya ja iska _very sad 'yan mata_ shiyasa bincike kafin aure yakeda amfani kin ganin kyakyawa da ni ga kuma masu gidan rana a tare da ni ba bincike ki ka amince da ni kin ga yanzu bakida za6i illah ki zauna da ni  sannu a hankali ke ma za ki fara d'aga kwalba
  Da k'arfi Haleesa ta ture shi ko motsi bai ba yi ba yak'ara matsi mata baki tsanani sha'awa lips d'inta Yakama shi dama ga Habeeb Lamido maye kiss ne{lol} kawai ya tsince kanshi da pecking lips d'inta da sauri ya tureta
  ''Haleesa wance kuka yaci k'arfinta tsanar Habeeb Lamido ta kanainaye mata zuciya tasaka bayan hannunta ta goge lips d'inta.Habeeb ya zaro ido ranshi ya yi mugun b'aci wannan shine karo na farko a tarihi rayuwarshi da ya ta6a sumbata mace ta goge bakinta tabbas Haleesa ta yi mishi wulaqanci da ba'a ta6a yi mishi kala sa ba.
   " da k'arfi ya janyo ta yace ni za ki yi wa wulaqanci huh"?
Ke ba abun alfaharinki bane ni Habeeb Lamido na had'a baki da ke lallai yau mai kwatarki a hannuna sai Allah domin sai na daura miki abunda bara ki iya ta6a gogewa banza 'yar k'auye........

Jeeddah Aliyu
[31/12/2016 10:05 am] aliyujeeddah: [20/11 7:57 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```74```

~~Haleesa ta kurma razananen Ihu Sai k'ok'ari take ta kwace daga mugun rik'on da Habeeb ya yi mata, saidai ina bara ta iya ba saboda k'arfin namiji da mace ba d'aya ba.
   "Da K'arfin tsiya ya had'e bakinshi da nata gurnani Haleesa ke yi kamar zakanya da ke jin yunwa, saida yagaji don kanshi yadauke bakinshi daga nata gaba d'aya idanunta suka firfirto kafin ta farfad'o daga azababen kiss d'in da ya yi mata yak'ara rik'on bayan wuyanta ya matse mata baki ya tattaro yawun bakinshi ya zuba mata a baki yasaka d'ayan hannunshi ya matse mata hancin kamar yadda ake yi wa yaron goye d'ure numfashin Haleesa yafara k'ok'arin fita daga gangar jikinta, babu shiri ta hadiyen yawun Habeeb.
    ''Murmushin mugunta ya yi cike da jin dad'i yad'ago fuskarta ya had'e goshinshi da nata yadaura tsinin hancinshi akan nata yana gogawa a hankali duk abunda yake yi idanun Haleesa na rufe ruf tsananin bak'in ciki ne ke kara-kainin a farfajiyar zuciyarta.
   Cikin isa da tak'ama yana wani yatsina yafara magana kamar mai ciwon hak'ora _wannan ya zama darasi a gareki Habeeb Lamido baya tolerating nonsense musanmman ga mace da yatsana_
     "Ya d'an numfasa kamar Wanda ya yi tsere gudu ya zo na d'aya yacigaba da cewa _wannan kad'an daga cikin kalar wulaqancin da za ki dinga samu daga gareni_
 yana k'arasa magana ya lalla6o hannunta na dama ya rik'on d'an yatsanta yasaka cikin bakinshi ya gantsara mata mahaukacin cizo Wanda ya yi sanadin da Haleesa tasaki ihu mai tsananin k'aran gaske.
Shhh.....yafad'a had'e da daura yatsanshi akan lips d'inta _haba! Babylove irin wannan ihun ae sai ki fasa min dodon kunne_
  Duk tsananin azaba da rad'ad'i da Haleesa take ji bai hanata aikawa Habeeb kallon mamaki sakamako sunan da yakirata da shi duk duniya mutum d'aya ne yake kiranta da wannan sunan shine marigayi yaya Habeeb.
    ''Habeeb Lamido ya katsin mata mamakinta ta hanyar furta kina mamaki ne don na kira ki da suna babylove ko ba haka bane marigayin saurayinki yake kiranki da shi ba"?
    Haleesa tafashe da kuka hank'urinta yafara k'arewa, zuciyata tafara kintsa mata ta gasa masa maganganun masu zafi saboda anzo gurin da bara ta iya hank'uri ba.
     "Tureta ya yi daga jikinshi ya rik'on hannunta _oya mu je ki gyara min d'akina_
Da k'arfin yashiga janta zuwa part d'inshi yayinda Haleesa take kuka kamar ranta zai fita tsananin kukan da take yi ya hanata maidawa Habeeb Lamido martanin abunda ya yi mata.
   "Cillata ya yi cikin bedroom yakoma gafen ya yi tsaye yana  tsotsan baki kamar mai shan sweet Haleesa ta shar6e hawaye da hannunta tasoma gyara bedsheets yatsanta sai zogi yake mata a haka ta kintsa masa d'akin ta juya za ta fice ya tare mata hanya da hannunshi ya yi mata ishara da bathroom bata ce da shi komai ba tanufi bathroom tsaye ta yi tana kallon yaddda yak'awata bathroom d'in bashida banbancin da bathroom d'inshi  na Yola ta tabe baki a zuciyata tace banza mai kwaikwayon Nasara hasarar duniya.
    Ta wanke bathroom d'in tsaf tafito yana tsaye hannayenshi zube cikin aljihhun wando, ta ra6a ta gefenshi tafice.
 ''Habeeb yadawo parlounshi ya zauna yatalabe kumatunshi da hannun ya bud'e babin zance zuci _me yasa duk abunda na yi wa yarinya nan saidai ta yi kuka bata nuna 6acin ranta"?_
 _hank'unrinta ne ya yi yawa ko kuma tsabar rashin son da ta ke mini ne yasanya take nuna halin ko in kula da cin zarafin da nake mata"?_
   ''Ya ja tsoki d'ayan bangare zuciyarshi yace rashin so ne Habeeb sanin kanka ne akwai Wanda har yanzu yake sarafa zuciyarta kai da banza da babu duk d'aya suke a wurinta.
ba zai yu ba....Habeeb yafad'a a baiyane ya mik'e tsaye yafara safa da marwa yak'ara Jan tsoki me ke faruwa da ni"?
Akan wane dalilin zan jefa kaina cikin damuwa ina ruwana da Wanda take so ae ni ba sonta nake yi ba Wanda take hauka akansa baya duniya me zai sa na nemi na damarda kaina"?
Amma kuma matata ce bai kamata tacigaba da son wani
  "To in har bataso wani ba wa ka ke da shi da za ta so"?
  Yafad'a kan kujera yadafe goshinshi yashiga nazari ko zai yi nassara lala6o amsoshin tambayoyinshi.
********************
```HALEESA```
Direct bedroom d'inta ta wuce ta yi kwance hawaye na fita a gefen idonta _me na yi wa yaya Habeeb ya tsane ni haka"?_
_me yasa a koda yaushe bashida buri da yawuce ya k'untatawa rayuwata"?_
  _na yi danasanin amincewa da aurenshi a da nayi k'udirin zama da shi amma yanzu bana tunanin zan iya cigaba da zama da mashayi wanda babu tsoron Allah a zuciyarshi lallai ya zame mini dole na nemowa kaina mafita domin ba zan yarda ba rayuwata tak'are a haka_
Haleesa ta mik'e zaune ta sharce hawaye da bayan hannunta.
tun daga ranar Haleesa bata k'ara saka Habeeb Lamido a idonta ba.

```1 WEEK LATER```
_sunday morning_
Around 10:00 o'clock peter ya kamalla breakfast ya jerawa Haleesa nata a dining table yanufi part d'in Habeeb ya Jera masa nashi a table.
     "A K'a'idar Habeeb  baya breakfast sai _11:00am_
 ''Habeeb tsaye akan gym mat machine yana motsa jikinshi ya had'a d'an uban gumi tsawon lokacin yadauka akan machine d'in daga bisani yanufi d'akinshi ya yi wanka bayan yafito yashirya cikin black three quarter da armless shirt direct dining table yawuce ya yi taking breakfast yana gamawa yadawo parlour ya zauna ya afka tunanin abunda yasha masa kai tsawon _1 week_  da ya yi tafiya zuwa Lagos sai Daren jiya yadawo yarasa dalilin da yasa yakeson ganin Haleesa bashida aiki sai na tunaninta a hankali ya lumshe idanunshi a zuciyarshi yace ba shakka sha'awar yarinya nan takamani tun daga ranarda naganta half nacked  na rasa sukuni shiyasa nakejin  wani abu a game da ita ya ja iska yafesar kamar Wanda aka mintsina ya mik'e yanufi part d'in Haleesa yana Shiga parlournta ya ga wayam bata ciki tsabar miskilincin da girman kanshi suka hana shi zuwa bedroom d'inta  shi a dole kada tagano yafara shiga wani yanayi akanta sai kawai yanemi kujera ya zauna.
```HALEESA```
 Tun wayewar gari Haleesa takejin kanta wani irin kad'aicin yadame ta ita kadai zaune a gida kamar mayya Imaan ce dama ke d'ebe mata kewa gashi tun jiya Hannah ta tafi da ita za ta yi musu weekend har k'arfe _12:00pm_ ya buga Haleesa na kwance yau ta tashi da sha'awa ta yi wa kanta girki tagaji ta cin abincin Peter musanmman yau da peter yake zuwa Church sai k'arfe 1:00pm yake dawowa sannan ya yi musu lunch abun na masifar k'onawa Haleesa rai tarasa dalilin da yasa Habeeb yake da sha'awar rayuwar nasara hatta da abinci sai wani k'aton Arne yadafa ya bashi ita dai daga yau bara ta sake cin abincin Peter da wannan tunanin tanufi parlour tana shiga parlourn ta yi turus...sakamako hango Habeeb Lamido zaune a parlournta, kallon d'aya ta yi mishi tadauke kai tashige kitchen.
Habeeb na ganin Haleesa yasaki ajiyar zuciya ganinta da ya yi yak'ara motsu mishi da abunda yakeji a game da ita ya runtsin idanu yana Mai jin haushin kanshi yarasa yadda aka yi sha'awarta ta yi masa mummunan kamu.......

Jeeddah Aliyu
[01/01 7:32 am] aliyujeeddah: [21/11 8:36 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```75```

~~Habeeb ya bud'e idanunshi yak'urawa k'ofar kitchen ido yana mamaki yadda Haleesa ta wuce shi batare da ta gaida shi ba ya ja tsoki nan take zuciyatshi tafara kintsa masa zance zuci kala dabam- dabam, watakila tafara gano kana sha'awarta shiyasa takeso ta rainaka.
Sumar kanshi yashiga hargitsawa kamar mai ciwo tabin hankali, a wani gefen bana ganin laifin kaina saboda ni lafiyaye namiji ne dole ina buk'atar mace kenan ko na yi sha'awar Haleesa ba illah bane saidai banajin zan iya had'a shinfid'a da ita koda ace sha'awarta zai illatani yakoma jikin kujera ya lafe yana mai cigaba da tunano tsari da kyawon surar Haleesa.
**********************
```KITCHEN```
Haleesa na shiga kitchen ta bud'e diff freezer tafito da katuwar kaza ta ajiye ta a gefe k'ank'arar jikinta yasake tadauko fresh tomato da tattasai da tarugu adadin da za ta yi amfani da shi ta wanke ta zuba cikin blender had'e da yin switch on d'in blender tsabar wauta irin na Haleesa ta d'age murfin tagani ko tomatoes ya yi blending ga blender yana aikin tana lek'awa tomato ya yi tsale yadira a idonta, tasaka hannun tadafe idanunta tafara zunduma ihu _Wayyo Allah idona, wayyo idona_
Gaba d'aya ta rud'e tafita haiyacinta sai faman lallube take kamar makauniya kamar daga sama Habeeb ya ji sautin ihun Haleesa ya ja d'an 'karamin Tsoki ita wannan me ta ke yi wa ihu"?
Ihun ya ji yak'aru da sauri ya mik'e yanufi kitchen d'in _ke! Lafiya ki ke yi wa mutane ihu kefa abun ihu baya miki wuya_
Idona yaya Habeeb wayyo idona bana gani
Me yasa me idon naki"?
   "Ya ji ne yashigar min ido
Tabe baki ya yi yana mata kallon sama da k'asa garin lullube Haleesa ta d'ank'o shi da k'arfi ta chukuikuye masa riga please yaya Habeeb help me
 "Habeeb ya yi sororo yana kallonta ihunta yadawo da shi cikin natsawarshi yarik'o hannunta ya bud'e fanfo ya wake mata fuska chan 'kasan mak'oshi ya furta ki bud'e idanunki iska yashiga sannan za ki daina jin zafi.
Haleesa tashiga girgiza kai bara iya ba Yaya Habeeb ka busa min
Me zan busa"?
 Habeeb yafad'a da alama mamaki akan fuskarshi''
Idona za ka busa min shiru Habeeb ya yi kamar mai nazari daga bisani yarik'o kanta yad'aga idonta ya busa saura wannan Haleesa tafad'a had'e da nuna d'ayan idonta.
Tsoki ya yi had'e da cewa ke karki mayarda ni yaronki yanzu nan ki ka wuce ni a parlour don tsabar iskanci ko ki gaida ni yak'ara sa magana had'e da busa mata idon sannun a hankali Haleesa ta ware idanunta duba d'aya ta yi masa ta kauda fuska tajuya wurin blender ta yi switch off had'e da zareta daga socket.
''A yatsine Habeeb yace a garin yaya ki ka zubawa idonki yajin"?
  Kamar bara ta amsa ba daga bisani tace murfin blender na d'age nagani ko tomatoes ya markad'u shine yashiga min idon  ''Habeeb ya ja tsoki yace bak'auya kawai da nasan wannan ne dalilin da yasa yaji yashiga idanunki da saidai ki makace bara busa miki ba.
Cigaba da aikinta ta yi kamar bataji abunda yafad'a ba.
''Wai me za ki yi da wannan tomatoes da ki ke markad'a"?
Da mugun mamaki Haleesa tajuya ta dube shi, kana nufi bakasan abunda ake yi da tomatoes ba"?
"Yad'age girar sama yana kallonta a yatsine in nasani zan tambaye ki ne"?
  Tabe baki Haleesa ta yi a dak'ile ta furta girki zan yi
''Harara ya galla mata girki za ki yi ko jagwalgwale"?
Oho... nima bansaniba Haleesa tafad'a a yatsine
  "Habeeb ya zaro ido ke ni za ki ce ma bakisaniba"?
Na fahimcin yau wani rashin kunya ki ke ji ina magana kina amsa man a tsasaye sai kace kina magana da sa'anki
 D'an bazawarin murmushi Haleesa ta yi tace karka ga laifina yaya Habeeb tun lokacin da na fahimce waye kai na kuma fahimce alkila da ka dosa nima sai nafara koyon rashin kunya tak'arasa magana had'e da murgud'a masa baki.
  ''Habeeb ya yi shiru yana kallon Haleesa ranshi ya yi mugun b'acin a zuciyarshi yace dama abunda nake gudun kenan kada yarinya nan tagano yadda nakeji akanta ya cije lips d'inshi na k'asa ya kad'a kai yafice daga kitchen.
 yayinda Haleesa bata Masan yanayi ba aikin gabanta kawai take cikin _30 minutes_ k'amshin girkinta yafara gauraye gida Habeeb da take zaune a parlour ya shak'i k'amshin girkin Haleesa ya lumshe idanu ya shafi sumar kanshi a zuciyarshi yace ko me wannan yarinya tasaka a girkinta yake k'amshin haka"?
Sanin ba Wanda zai bashi amsa yasa ya tabe baki yacigaba da kallon da yake yi.
  "Had'ad'iya jellof rice da farfesun kaza Haleesa ta had'a ganin tana da sauran lokacin sai kawai ta had'a zobo drink yasha pineapple ta yanka cucumber k'anana a ciki tasaka ice block yadda zai yi saurin yin sanyi saida ta Jere abincinta akan dining table sannan tanufi bathroom domin ta yi wanka lokacin da ta zo shigewa bedroom ta tararda Habeeb yafita.
_20 minutes later_
Habeeb na zaune a parlournshi kaitsaye Mus'ab da khaleel suka fad'o falon kowane su yanemi wuri ya zauna kallon mamaki Habeeb ya bi su da shi a yatsine yace Ku kuma daga ina"?
Khaleel ya amsa da cewa daga wurin gararin gari mu ka fito kuma wallahi mun d'ebo 'yar banzar throughout ba abunda nasaka a cikina kuma da alama mun taki babbar Sa'a tun daga compound mu ke shak'ar k'amshin girkin amarya yak'arasa had'e t kwashewa da  dariya Mus'ab na taya shi
  ''Kallon banza Habeeb ya watsa musu ya ja tsoki yace ''look karku nemi Ku raina min hankali angaya muku gidana restaurant ne''?
 ''Mus'ab ya kar6e zance ta hanyar cewa gidanka ba restaurant bane amma akwai sabuwar amarya dal a cikinsa, don haka bara mu fita gidanan sai mu d'ebi girki.
   ''Harara Habeeb ya galla masa yace idan wannan ne yakawo Ku to ba Ku zo da Sa'a ba saboda bata dafa da Ku ba sai Ku tashi Ku k'ara gaba ko yak'arasa magana yana kallon fusk'ok'in su khaleel yace ba ka isa ba Lamido ko kanaso ko bakaso sai mun cin abincin nan.
   ''Habeeb yadafe kai yasoma tunanin irin wulaqanci da ya yi wa Haleesa da kuma dokar da yakafa mata ko noodles bai amince ta dafa da sunanshi ba tsananin biyawa da ranshi ya yi da abinci da ta dafa ya kuma San miskilanci da girman kanshi bara su barshi yaci abincinta yasa ya gudu daga parlounta, sai kuma ga wad'annan rikitatun friends in nashi ba shi da za6i da ya wuce ya kwashe su zuwa part d'in Haleesa.
   "Wai tunani me ka ke yi khaleel ya katsi masa hamzari
  Tsoki ya ja yafi a kirga daga bisani ya mik'e tsaye ya dube su a d'age yace to ae sai Ku tashi mu tafi part d'inta mayu kawai sai kace wani shege yahanaku aure.
Mus'ab da khaleel suka dube juna had'e da zaro ido Mus'ab yace kaima yaushe ne ka yi auren da za ka yi mana gori dad'i abin nima na yi kusan angwancewa da k'anwarka suka kyalkyale da dariya har da tafawa sa6anin Habeeb da ya yi kici-kici da fuska can! Ya ja tsoki yashige gaba suna biye da shi suna shiga parloun Haleesa direct dining area suka wuce cike da takaice Habeeb yake kallonsu kowane su ya loda plate da jellof rice k'amshin abincin yadaki hancin Habeeb babu shiri ya zare plate ya yi serving, ba ka ji komai sai karar spoon's.
     "Haleesa taci kwalliya cikin riga da siket na atamfar super Holland ta yi matuk'ar kyau jikinta na fitarda fitinane k'amshin designer perfumes a hankali ta taka zuwa parlour idanunta suka sauka akan dining table Habeeb da zugar abokai shi suna wawosar abincinta, ranta ya yi mugun b'acin musanmman da ta tuna da dokar da yakafa masa tabbas wannan shine right time da zan yi amfani da shawara Hannah na nunawa Habeeb Lamido I'm not scare of him
_Amarya barka da fitowa kafin kifito har mun cinye miki girki_
Muryar khaleel ce ta katsiwa Haleesa tunani cikin tafiyarta mai kama da na mai tsoron taka k'asa tak'arasa wurinsu fuskarta d'auke da tsadad'e murmushi tace _sannunku da zuwa_
   "Mus'ab yace Yauwa amarya gaskiya abincin nan naki ya yi matuk'ar dad'i na dad'e ban ci abincin da ya yi dad'insa.
   "Da sauri Habeeb Lamido ya yi dropping d'in spoon ya sada kai k'asa yana juya glass cup mai d'auke da zobo tsananin kunya mai cike da danasanin biyewa friends d'inshi da ya yi yaci abincin Haleesa suka lullu6e shi.
   ''Haleesa ta gyara tsayuwarta ta dube Habeeb da yasada kai k'asa ta tabe baki tajuya wurinsu Mus'ab ta yi fari da ido karaf akan idon Habeeb wani irin mashi ya ji yadaki zuciyarshi.
Haleesa tace na gode da yabawarku duk lokacin da Ku ke da buk'atar abincin irin wannan da ma Wanda yafi wannan  k'ofa abude take saboda kunfi wasu masu cika baki da fankama tsiya sai d'an banzan girman kai rawanin tsiya ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli yaci riba ko komai Haleesa tafara fatali da dokar mutum yak'arasa magana had'e da yi wa Habeeb kallon sama da k'asa ta kama tsotsan bakinta kamar yadda yake yi da sauri Habeeb Lamido ya runtse idonshi ya mik'e azafafe hannunshi rik'e da cup yana huci kamar zaki adawa yad'aga cup d'in ya wankawa Haleesa zo6o akan fuska tun daga fuskarta zo6o ke d'iga yana sauka a k'asa........


Jeeddah Aliyu
[01/01 7:35 am] aliyujeeddah: [22/11 4:05 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```76```

~~A hankali ta bi jikinta da kallo gaba d'aya zo6o yabata mata kaya a harzuk'e tad'ago idanunta Wanda suka canza colour zuwa red, kallo d'aya za ka yi mata ka hango b'acin ranta yadda ta tsare Habeeb Lamido da ido za ka yi tsanmani za ta zanga masa mari ne.
   "Kallo mai cike da zazzafar tsana Habeeb yake watsawa Haleesa cikin tafarfasa zuciya yadaka mata tsawa cikin angry voice ya furta _How dare you ni za ki wulaqanta in front  of my friends"?_
  ''Kafin Haleesa ta ba shi amsa Mus'ab ya taso yashiga tsakaninsu ranshi a b'ace yace _what's wrong with you Lamido akan wane dalilin za ka yi mata wannan d'ayen wulaqancin matarka ce fa"?_
  ''Kallon banza Habeeb ya watsa masa so what's don tana matata shi zai bata dama tacin min zarafi a gabanku"?
   Haleesa ta yi karaf tace ancin zarafin naka yaya Habeeb ka yi duk abunda za ka iya ae ba tsoronka nakeji ba, tana k'arasa magana ta yi shigewarta bedroom tabar Habeeb Lamido sake da baki sai faman huci yake yi bai ta6a tunanin Haleesa za ta iya maida martanin abunda yake mata.
     "Mus'ab ya ja tsoki ya dube khaleel yace tashi mu tafi khaleel a zahirin gaskiya nayi danasanin zuwanmu gidanan da bamu zo ba Lamido da bara ka, same damar wulaqanta 'yar mutane ina mamaki wannan miskilancin da girman kan naka Lamido ka gyara halayyarka ko za ka jin dad'i rayuwa.
     ''Khaleel ya kar6e zance ta hanyar cewa wannan abun da kayi Lamido kasanin ba burgewa bane, wulaqanta mace ba abu bane mai kyau muna jiye maka ranar Nadama.
    ''Yana k'arasa magana yarik'o hannun Mus'ab mu tafi kawai Mus'ab kana kallon irin kallon banzar da yake mana.
    ''Habeeb ya ja tsaki yace sai me don kuntafi dama can! Ban gaiyyace Ku ba ra'ayin kanku ne yakawo gidanan don kuntafi bara jin zafi ba asalima zuwanku wulaqancin ya janyo min tunda nake da yarinya nan banta6a magana ta mayar mun da amsa ba sai zuwanku banzaye kawai.
    ''Mus'ab ya galla masa harara yace ae Kaine banza Wanda baisan darajar matarshi ba wallahi Lamido in na cigaba da tsayuwa a gabanka haushinka da nakeji zai iya haddasa min hawan jini.
    ''Habeeb ya ja tsoki had'e da ficewa daga parlourn yabar Mus'ab da khaleel tsaye suna mamaki wannan halayen nashi daga bisani suka kama gabansu.
***********************
Kuka Haleesa taci kamar ranta zai fita tabbas Habeeb Lamido yade6o da zafi daga yau bara k'ara d'aga masa k'afa saidai ya yanka ni a gidanan.

```WASHE GARI ```
_Monday morning_
Kamar yadda Haleesa tasaba tashi da wuri  ta shiryawa Imaan zuwa school tana rik'e da hannunta suka nufi compound har wurin mota ta yi mata rakiya, da kanta ta bud'e k'ofa tashiga ta yi pecking  goshinta ta mik'awa sa'eed driver lunch box d'inta yayinda driver ya ja Motan zuwa gate Imaan tana d'aga mata hannun Haleesa ta mayar mata da cewa bye, babyn aunty ki yi karatu sosai Saida suka fice gate sannan Haleesa juya tana juyawa ta hango Habeeb tsaye da sauri yad'auke kai, kamar ba shi bane yake tsaye yana kallonsu, ta raba ta gefenshi dai-dai za ta shiga cikin gida tace _ina kwana yaya Habeeb"?_
  "Saida zuciyarshi ta buga da k'arfi saboda baita6a tsanmani Haleesa za ta k'ara koda kallonshi ne ballanta magana ta fatar baki Tashiga tsakaninsu da kyar ya iya bud'e bakinshi ya amsa da _lafiya lau_
    ''Daga haka bata k'ara cewa da shi komai ba ta yi shigewarta cikin gida
    ''Habeeb ya yi ajiyar zuciya cike da mamakin Haleesa yafara zance zucin _ita wannan tana nufi har ta manta da abunda na yi mata jiya"?_
Wani 6angare na zuciyarshi yace da shi
In kuwa haka ne gaskiya tana da hank'uri da batada kyakyawar zuciya da 'yarka bara ta k'ara bata kulawa ba yanzu nan akan idonka ta wuce da Imaan da alama tana matuk'ar son Imaan kamar 'yarta ta cikinta, gaskiya Habeeb ka chanza tsari kadaina musgunawa yarinya nan tun kanada sauran daraja a wurinta kafin tadaina ganin darajarka ta rainaka.
    Ya ja iska ya fesar a sanyaye yanufi bakin gate yana kwallawa Bala kira.
_11:00am_
Habeeb na zaune a office ga tarin aiyunka sunyi mishi yawa yarasa abunda ke masa dad'i da yarufe idanunshi Haleesa yake gani a nashi tunanin sai yadanganta hakan da abunda yafaru tsakaninsu jiya yana cikin wannan halin Mus'ab ya tura k'ofa yashigo har ya zauna Habeeb yana masa kallon k'asan idon.
    "Mus'ab ya murtuk'e fuska had'e da mik'awa Habeeb hannu suyi musabaha bayan sun gama gaisawa Mus'ab ya gyara zamanshi yace ba sai gaya maka dalilin zuwa na office d'inka kwakwalwarka kadai ta isa ta zayyano maka dalilin zuwa na.
    Yad'an numfasa yacigaba da cewa abunda ka aikata jiya Sam baiyi min dad'i ba jiya na kwana da takaicinka haba! Lamido da iliminka da komai za ka mayarda matarka abun wulaqantawa Na fi kowa sanin yadda ka tsaneta amma bai kamata ka yi amfani da tsanar da ka ke yi mata ta zame maka hujja da za ka dinga wulaqantata ka ji tsoron ''Allah ka tuna duk abunda ka ke aikatawa Allah yana ganinka in har ka 6oyewa mom irin mugun zaman da ka ke yi da Haleesa ka tuna ba ka isa ka 6oyewa ubangijinka ba.
    ''Har Mus'ab yadasa aya Habeeb yana kallonshi had'e da tsotsa baki wannan tsotsar bakin ya zame masa d'abi'a ya mik'e a hankali yataka zuwa wurin water disperser yadauki glass cup ya matsa ruwa mai sanyi ya kwararawa mak'oshinsa ya lumshe idanu yana fesar da iska daga bisani ya koma mazauninshi.
   ''ya tabe baki ya dube Mus'ab a d'age yana wani cizo lips look Mus'ab karka shiga abunda ba ruwanka a ciki kafin kowa sanin halina, na tsani katsalanda a rayuwana bana shiga rayuwan kowa bai nima kanemi ka shiga rayuwana bansan menene b'acin rai ba sai da na had'u da yarinya nan ban ta6a d'aga hannun na  mari mace sai akanta, banta6a kwanciya na k'asa b'acin sai akanta a da ni mutum ne mai sanyi amma Shigowar yarinya nan a  rayuwata ya sauyani na dawo mutum mai tsananin zafin gaske na rok'e ka Mus'ab karka sake yi min maganarta saboda tun farko saida na gargad'enta akan ta bi dokoki na domin ta zauna lafiya da yake ita mai kunnen k'ashi ce sai ta yi fatali da doka ta ni kuwa me zai sa na d'aga mata k'afa"?
    ''Mus'ab ya girgiza kai yace Lamido  fahimce wani abu mana Haleesa fa k'aramar yarinya ce a hankali yakamata ka bi da ita har, ta fahimce tsarin rayuwarka ko wannan miskilancin naka kadai ya isa ya cutar da ita kuma ni ba zan fasa fad'a maka gaskiya ba saidai ka yi ta kallona a matsayin mai katsalanda a rayuwarka.
     ''Habeeb ya ja tsoki cike da takaicin Mus'ab ya koma jikin kujera ya lafe yayinda kujerar tadinga jujuya shi.
   Mus'ab ya mik'e ranshi a b'ace yace tunda kai girman kanka bara bari ka bata hankuri ni zan je gidan naka na bata hankuri yana k'arasa magana bai jira jin ta bakin  Habeeb ba ya yi ficewarsa.
 ''Habeeb ya bi shi da harara a baiyane yafara magana ba hankuri za ka bata ba in ka je ka goyata ka yawace garinan da ita ba abunda yadameni, ko angaya maka ni bawan mace ne irinka yak'ara Jan tsoki....

```HALEESA```
_Haleesa_ tana cikin kitchen sai ta ji ana sallama, da sauri ta fito ga mamakinta sai taci K'aro da Mus'ab zaune akan 1 sitter da murmushi tak'arasa shiga parlourn _sannu da zuwa Mus'ab_
   ''Yauwa Haleesa ya gida duk da naji gidan tsit yak'arasa magana yana 'yar dariya.
   Haleesa ta yi murmushi ta koma kitchen tadauko masa kwalin fruitta mai sanyi had'e da glass cup ta tsiyaya ta mik'a masa tanemi kujerar da ke facing d'inshi ta zauna ta sada kai k'asa saboda tana mai jin kunyar abunda yafaru jiya.
    ''Mus'ab ya d'an yi slipping juice d'in ya ajiye cup bisa stool ya yi gyaran murya, yace Haleesa dama zuwa na yi na baki hankuri akan abunda yafaru shi kanshi lamid'o ya yi Nadama abunda ya yi miki kawai yana jin kunyar yadda zai yi facing d'inki yabaki hankuri amma yace nace da ke ki yi hankuri Sharrin shed'an ne.
    "Haleesa ta yi murmushi domin tasan abunda Mus'ab yafad'a ba gaskiya bane  Habeeb Lamido ne zai ce a bata hankuri ae ba yau ya sa6a cin mata zarafi Wanda yafi wannan ya yi mata bai ce a bata hankuri ba sai wannan.
   ''Idanunta suka ciko da hawaye bata damu da ta goge su ba, tace ba zan 6oye maka ba Mus'ab a da ina da ra'ayi zama da yaya Habeeb koda ace zai dinga yanka naman jikina sai yagajin don kanshi ya saleme ni, amma a yanzu nayi nadamar aurenshi ba don komai sai don ya kasance mashayi ni kan bara iya rayuwa da mashayin giya tak'arasa magana cikin shasshek'a kuka.
    ''Mus'ab ya zaro idanu a rikice yace giya fa ki ka ce Haleesa"?
  ''Kwarai Mus'ab abokinka mashayi ne Sam babu tsoron Allah a tare da shi a cikin gidanan yake shan abarsa ya yi tatul.
  "Da mugun mamaki Mus'ab yake kallon Haleesa daga bisani yace to ke Haleesa menene shedarki Lamido yana shan giya"?
   Ni kuwa nakeda sheda mu je part d'inshi ka ganewa idanunka Haleesa tashige gaba Mus'ab yana biye da ita saboda iya zamanshi da Habeeb yasan ko cigarette ba yasha asalima ya tsanin duk wani abu da yake saka maye.
        ''Haleesa ta turo k'ofa suka shiga cikin parloun ta nunawa Mus'ab glassblower da ke d'auke da jerin white wine kala-kala Mus'ab ya yi ajiyar zuciya ya bud'e glassblower yaciro bottle gudu ya mik'awa Haleesa da sauri ta ja baya tana wani zare idon Mus'ab ya kyalkyale da dariya yace ki k'ar6a mana so nake ki karanta rubutu da ke jikin bottle d'in a sanyaye Haleesa ta k'ar6a ta karanta juice ne da aka sarafa da fruits sannan kuma an rubuta non alcoholic Haleesa tasauke ajiyar zuciya wani sanyi ya ziyarce zuciyata ta runtse idanu daga bisani ta ware su cikin jin kunya tace gaskiya na yarda da maganar yaya Habeeb da yake cewa ni villager ce amma kuma Mus'ab karka ga k'auyancin na saboda ban tashi a gidan da ake shan irin wad'annan abubuwan ba.
  Mus'ab ya yi murmushi yace ki kyalle Lamido shima bak'auye ne sannan kuma ba ke kadai ki ke kallon wannan juice a matsayin giya mutane da dama Wanda ba su San juice bane a haka suke kallonsa.
     ''Haleesa ta yi dariya tajuya Mus'ab ya Mara mata baya suka koma parlournta, yacigaba da bata hank'uri saida ya tabbata da ta hank'ura sannan ya yi mata sallama.
_5:00pm_
Haleesa tana zaune a parlournta Imaan ta isheta da rigima a dole sai sunyi wasan 'yar 6oya Haleesa ta yatsine fuska ta ajiye phone d'inta bisa hannun kujera ta rik'on hannun Imaan suka nufi compound daga idan suke zuwa main gate akwai tazara sosai Haleesa taciro d'an kwalin kanta gashinta yasauka a gadon bayanta, tace da Imaan zo nan babyn aunty na daure miki idanunki
   ''Imaan tadaka tsalle cikin shagwa6a tace Allah aunty ke ce first ni kuma second Haleesa ta yi dariya tace kai....ka ji min yarinya da wayyo tana magana tana daure fuskarta idanunta na rufe tace 1.....2....3.... Start tasoma lallu6en Imaan tana jin dariyar Imaan amma takasa kamata, haka tacigaba da lullube.
''Bala yaddano hancin mota cikin compound Habeeb na owners corner a zaune tun kafin su k'arasa parking space ya hango Haleesa da Imaan suna wasa yaja tsoki a zuciyarshi yace k'aramar kawai Bala yana dariya ya bud'ewa Habeeb k'ofa yafito
  "Boss yau amarya ta tuna da k'urciya wasan 'yar 6oya sukeyi yak'ara sa magana yana wani Sosa kai.
   Harara Habeeb ya watsa masa yace kadauko briefcase ka shigar min da shi ciki Yajuya yanufi cikin gida.
  "Babyn aunty where are you I'm tight zan bud'e idanuna in bara ki bari na kama ki ba Imaan ta kyalkyale da dariya tace _yeee.... Aunty if you're can catch me_
Da sauri Haleesa tanufi idan takejin sautin muryarta dai-dai Habeeb yakawo da sauri Imaan ta boye bayanshi garin lallube Haleesa ta yi tuntube za ta fad'i da sauri Habeeb yatare ta tafad'o kan  k'irjinshi..........


Jeeddah Aliyu
[01/01 7:39 am] aliyujeeddah: [24/11 7:33 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```77```

_this page dedicated to  you *Ayshat D'ansabo lemu*  thanks for the  love & support it's means a lot_

~~k'amshin perfume da ta yi amfani da shi ya ratsa k'ofufin hancin Habeeb baisan lokacin da ya lumshe idanunshi yak'ara matso da ita zuwa k'irjinshi ya matse ta gam Tsigar jikinta ta tashi Yarr! Hancinshi yadaura a gefen wuyanta yana shak'ar k'amshinta tuni Habeeb ya manta suna tsaye ne a compound yafita haiyacinsa, numfashinsa yana fita da sauri-sauri ya kasa daurewa ya ziro hannunshi cikin rigarta da sauri Haleesa ta taka masa birki ta hanyar furta _please yaya Habeeb stopped Imaan is looking at us_
A rikice yadawo hayyacinsa ya tureta daga jikinsa dama hausawa sunce tabarma kunya da hauka ake nad'eta sai kawai ya gallawa Haleesa harara _wannan wane irin sakarcin ne huh"?_
_shine illah auren k'anana yara dube ki wai wasa 'yar 6oya ki ke yi danasani na barki ki fad'i ki karya k'afa ko hannunki naga d'an iska da zai yi jinyarki dallah! Bani wurin in wuce kin yi wani tsare ni da idanu_
A zafafe yak'arasa shiga gida Haleesa ta bi shi da kallon tasauke ajiyar zuciya, tajuya ta hango Imaan zaune cikin flowers tana wasa sai faman tsinko Flowers take tana tarawa a gefenta, Haleesa tak'ara sauke ajiyar zuciya a cikin zuciyarta tace, _thank God_ ashe ba Wanda ya ganmu tanufi wurin Imaan tarik'on hannunta suka shiga cikin gida.
_9:00pm_
Haleesa na kwance a bedroom d'inta ta yi rub da ciki ta d'aga k'afafunta sama ta yi zurfi a tunanin rungumar da Habeeb Lamido ya yi mata d'azu da yamma abun yakasa fita daga zuciyarta duk lokacin da ta tuna da kyakyawar rungumar da tasamu a wurinshi sai ta yi murmushi ta kasa tantance wannan murmushin da take yi na menene ta yi wani juyi tadawo rigingine idanunta a lumshe tasoma fasalta kyakyawar Surar jikinsa ba abunda yafi burgeta a jikin Habeeb Lamido irin lallausar sumar kanshi koda yaushe idaunshi a lumshe suke kamar mai jin bacci da kyar Habeeb ya yi magana batare da ya ja iska ba kamar Wanda yacin yaji, yana yawan tsotsan bakinshi za ka yi tsanmani sweet yake sha in kuma yana magana d'aya-d'aya yake furta harafi sai kace mai bita, Haleesa ta yi murmushi  a zuciyata tace _Handsome_ kenan ga kyau saidai mugun hali da miskilancin tsiya, ta mik'e zaune ta k'urawa wall clock idanu _10:09pm_ ta d'an ja tsaki ko kad'an batajin bacci dama Imaan ce abokiyar firarta tun 8:00 o'clock ta yi bacci.

```HABEEB LAMID'O```
Zaune na zaune a parlournshi yana tura bayanai a system yunwa yakeji kamar 'yan hanjinshi za su tsinke ya rasa dalilin da yasa tun jiya da yacin abincin Haleesa d'andanon abincin yakasa fita daga bakinshi duk abunda yacin sai yaji ba tested yature laptop a gefe yanufi part d'in Haleesa cikin sand'a kamar barawo yak'arasa wurin dining table ya bud'e warmers k'amshin Egusi soup ya buge hancinshi ya cigaba da bud'e warmers yana ganin abunda ke ciki a zuciyarshi yace ba shakka wannan abincin yarinya nan ce ta girka shi yadauki Ledar tuwo semo guda d'aya ya yasaka cikin plate ya zuba soup a d'an k'aramin plate d'ayan plate kuma zuba farfesun kifi da sauri yakoma parlournshi yana ci yana wani kad'a kai _ashe haka yarinya nan ta iya girki"?_
_tafi Peter iya sarafa abinci gaskiya nayi kuskure da nace karta dafa min abinci banta6a cin abinci da ya yi min dad'i irin nata kuma har abada bara ta6a nuna mata ina jin dad'in girkinta duk ranar da tagano ina cin abincinta ajina da girmana za su zube a idonta ni kuma bara sake da abunda zai rage mini class_
Ya cinye tuwon tass! Har da su sud'e plate daga bisani yanufi bedroom ya zarce bathroom ya yi brush agajiye yafad'a kan bed cikin d'an k'ank'anin lokacin bacci yadauke shi a cikin baccin nashi yafara mafalkin leesa Zaune take a garden tana wasa da ja da farin fure tashagala da abunda take yi a hankali yake sand'a har yak'araso daf da ita ya zauna tana juyowa suka had'a ido tasake masa k'ayatace murmushi shima ya mayar mata da martanin murmushin nata kasa d'auke idanunshi ya yi akanta cikin sigar shagwa6a ta turo d'an k'aramin bakinta mai jefa Habeeb cikin tsantsar sha'awarta _yaya Habeeb wannan kallon fa"?_
  Cikin shauk'in so yarik'o hannunta ya jefa yatsanta a bakinshi yana tsotsa kamar yasami lollipop, da sauri leesa ta fisge hannunta ta wani yatsine fuska, Habeeb yadawo kalar tausayi chan k'asan mak'oshi ya furta _please leesa ki barni mana_
Shiru ta yi tana kallonshi da k'arfi yafisgota tafad'o kan k'irjinshi  ya matse ta gam ya lalla6o bakinta tsawon lokacin suka dauka a haka daga bisani ta ture shi ta mik'e da gudu tanufi cikin yayinda shima ya mik'e ya Mara mata baya a parlour ya yi nasara kama ta ya d'auke ta chak! Yanufi bedroom da ita yadireta akan bed Daga nan komai yacigaba da wakana.
 A firgici Habeeb ya falka daga mafalkin da ya zame masa, jiki gumi ya tsatsafo masa yadafe kanshi da hannayen, ya runtse idanunshi gam! Photon abunda yafaru tsakaninsa da Haleesa yadawo masa da sauri ya ware idanunshi ya ja  tsaki cike da jin haushin kanshi ya mik'e yanufi bathroom.
 Habeeb wanka ya ke yi yana zance zuci _me yasa duk lokacin da na kwanta bacci sai na yi mafalkin ina saduwa da yarinya nan"?_
 _ina da wannan mafalkin nawa zai kasance gaskiya tabbas da ba k'aramin tafiyar da ruhina za ta yi ba_
Jiki ba lakka ya gama wanka yafito har aka yi kiran asuba yana fama da tunanin leesa da yarufe idanu kyakyawar fuskarta yake gani.
********************
_7:00am_
Haleesa na tsaye cikin kitchen tana had'awa Imaan abincin da za ta tafi da shi school tuni ta takatar da peter da Girka abinci da ita da kanta take shiga kitchen ta girka duk abunda ranta yakeso agurguje ta kamalla had'awa Imaan lunch box d'inta tanufi d'akin Imaan tayi mata  wanka had'e da shirya ta cikin uniform ta zarce da ita dining area ta ja kujera ta zaunar da ita ta had'a mata tea had'e da chip's Imaan tana gama breakfast Haleesa tarik'on hannunta suka nufi compound suna, fita ta hango Habeeb da Bala a tsaye Habeeb na jefawa karnuka{ police dog's} nama suna Cin kasa k'arasawa parking  space ta yi saboda tana jin kunyar had'a ido da Habeeb.
Imaan tadaka tsalle _yeee yau Daddy ya fiddo da Rahul da Rita bara naje mu yi wasa_
Da sauri Haleesa ta taka mata birki ta hanyar ke Imaan banaso shirme ke da za ki tafi school me ye gaminki da karnunka karki sake naga kin tsaya a wurinsu ko kinmanta yau za Ku fara test ne"?
Imaan ta girgiza kai Haleesa tace to kama hanya kitafi ga sa'eed driver yana jiranki ta mik'a mata lunch box d'inta Imaan tajuya tanufi wurin Daddynta _Good morning Daddy_
Morning my angel
 Cikin shagwa6a Imaan tace Daddy shine saida kaga zan tafi school ka fiddo Rahul da Rita koh"?
Habeeb ya yi murmushi ya shafi kumatunta kin ga my angel banaso rigima kitafi school in kindawo auntynki ta fiddo miki su ku yi wasa.
    "Imaan ta zaro ido kamar taga abun tsoro _Daddy aunty Haleesa tsoronsu fa take yi ranar ma mu je garden da ta gansu da gudu takoma cikin gida tadinga fad'a tana cewa shi wannan yaya Habeeb komai so yake yi yanzu yarasa abunda zai yi kiwo sai bak'ak'en karnunka sai nace da ita aunty ba fa sunansu karnunka ba sunansu R........_Imaan ta hadiye raguwar kalamanta sakamako katsinta da Habeeb ya yi my angel wannan labarin naki basan tsawon lokacin da zai d'auka kafin naji karshensa ki bari sai kindawo daga school ki k'arasa mun kinji"?
Imaan tad'aga kai sa'eed driver yarik'o hannunta suka nufi parking space
  ''Bala ya kyalkyale da dariya Habeeb ya galla masa harara Bala ya hadiye dariyarshi yace "Boss Imaan tana mugun burgeni saboda surutun nan nata.
Habeeb ya tabe baki yace ae dole ta burge ka saboda halinku d'aya
  Bala washe hak'ora yace ni fa boss mamaki nake yi kai ga  magana wuya take maka kuma ka tsanin yawan surutu sai gashi Allah yabaka 'ya mai bala'e surutu kamar Aku{parrot}
   Habeeb ya ja tsaki yace _"Allah ya shiryeka Bala_
Bala yace ameen boss yau za'ayi ruwan sama har da k'ank'ara saboda ka yi min fata nagari da alama amarya tafara canza ka yak'arasa magana yana dariya
 ''Tsawon lokacin Habeeb yad'auka yana kallon Bala daga bisani ya girgiza kai, yace tun da kagama surutun naka daga ciki har da yi mun sharri sai ka tattara rahul da Rita ka mayarda su d'akinsu karka d'aure su kabarsu a sake kuma ka tabbata ka rufe musu k'ofa.
   "Bala yace angama boss ae tun da na fahimcin amarya tana tsoronsu bara yi sake da za su fito su tsorata maka ita.
     Habeeb ya yi murmushin takaicin  yajuya yasan muddin yacigaba da tsayuwa Bala zai iya haddasa masa bugawar zuciya direct parlourn Haleesa yadosa bata ciki tana bedroom ya yi tsaye a tsakiyar falon yana k'are masa kallo _very neat_ sai k'amashin turaren wuta ke tashi karaf idanunshi suka hasko masa dining table da sauri yanufi wurin ya yi serving d'in chip's had'e da sauce na cabbage da carrot ya ji anta da k'oda dai-dai lokacin da Haleesa taddano kai parlourn ta hango abunda Habeeb
Yake yi da sauri ta la6e tana lek'onshi tana kallonshi har yashige part d'inshi Haleesa ta yi murmushi ta kad'a eye's ball d'inta lallai Habeeb lamid'o d'an rainin hankali ne ko ya manta da kirarin da ya yi kada na kuskure na dafa ko da noodles da sunanshi sai gashi na kama shi yana satar mun abinci daga yau bara ka k'ara ganin abincin ballantana har ka sata
 "ta yi murmushin mugunta tun daga ranar Haleesa da tayi girki take zube abinta cikin warmers takai bedroom da, Habeeb yasud'ad'o yacin mai dad'i yatarar da dining table wayam!
Duk lokacin da Habeeb Lamido ya zauna bashida aiki sai tunanin Haleesa kuma baya iya cin abincin kowa sai nata yadda peter ya jera masa abincin haka zai dawo yadauke saboda ko kallon bai ishe ba cikin d'an k'ank'ani lokacin Habeeb yafara fita hayyacinsa, ganin yadda sha'awar Haleesa na neman kassara shi ya tattara kayansa ya haura Germany a tunaninshi in ya nisanta da ita zai manta da duk wani abu da yashafe ta baisan cewa hakan ba abunda zai k'ara masa sai  d'inbin damuwa, da tunani kuma yak'i ya amince da soyayya Haleesa ce ta kama shi ba sha'awa ba.
*****************
```GERMANY```
Habeeb yana zaune a wani had'ad'en wurin  hutawa kallon d'aya za ka yi masa kagano yana cikin damuwa yadda zuciyarsa ke azalzalarsa akan ya kira Haleesa ko muryarta za ta rage masa damuwar da yake ciki zuciyarsa na bugawa Ya yi dialling number ta.
Haleesa na zaune Imaan tayi pillow da cinyoyinta kiran Habeeb yashigo wayarta ta zaro idanu gabanta na fad'uwa ta yi picking................

Jeeddah Aliyu
[01/01 7:42 am] aliyujeeddah: [25/11 4:57 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```78```

~~cikin muryarta mai sanyi da zak'i ta furta _hello_ Wani irin sanyi ya ziyarce zuciyar Habeeb har ya yi nasara saukar masa da natsuwa, ya sauke ajiyar had'e da lumsashe idanu tsabar miskilancin irin na Habeeb Lamido a maimakon ya furta abunda ke neman raba shi da jin dad'insa sai kawai ya yi shiru yayinda katin wayarshi{recharge card} ke tafiya a banza jin shiru nashi ya yi yawa yasa Haleesa tak'ara cewa _hello_ ya ja iska ya fesar adak'ile yace ki ba wa Imaan waya zan yi magana da ita, jiki a sa6ule Haleesa taciro wayar daga kunnenta ta d'anko hannun Imaan ta daurawa mata  ranta a b'ace tace ki yi magana da Daddynki, ta rafka tagumi tunanin hali irin na Habeeb shin ko ya manta da matsayinta na matarshi da bara iya tambaya ko da lafiyar jikinta ne ta ja d'an siririn tsaki ta mayarda hankalinta wurin Imaan tana sauraro yadda ta ke zuba masa surutu, mai d'auke da tambayoyin _Daddy ina ka tafi ne na daina ganinka in na tambayin aunty Haleesa ina ka ke sai tace batasaniba''?_
     ''A hankali Habeeb ya bud'e idanunshi ya cize lips d'inshi na k'asa kenan yarinya nan bata ma damu da ni ba ni kadai nake fama da sha'awa da tunaninta.....cike da jin haushin Haleesa yaja tsaki yace my angel na yi tafiya shiyasa ki ka daina ganina.
  '' Daddy Ya sunan garin da ka je"?
Ya yi murmushi a kasalance ya furta Germany
"Daddy yaushe za ka dawo"?
Dafe goshi ya yi saboda yafara gajiya da tambayoyin Imaan da kyar ya furta very soon my angel
  Daddy me za ka siyo mun"?
_Anything you wants my Angel_
Imaan ta yi shiru tana tunanin abunda za ta fad'a kamar daga sama tace Daddy ka siyo min monkey da snake da lizard da......cikin zafin rai Haleesa ta kwace wayarta ta yi hanging up ta gallawa Imaan harara ke wace irin yarinya ce Imaan"?
Duk lokacin da Daddynki ya yi tafiya bara ki lissafa masa abun Kirki da zai siyo miki sai na banza da wofi ko angaya miki nan gidan zoo ne da zai kwaso wad'anan tarkace ya kawo miki.
Imaan ta kwa6e fuska kamar zai ta yi kuka cikin shagwa6a tace aunty ban gama magana da Daddyna ba kin kar6e waya
   ''Haleesa ta tabe baki ta shafi sumar kan Imaan tace ae kin gama magana Imaan fatana d'aya kada Allah yasa wannan Daddy naki 0ne & half ya biye wa shirmenki ya kwaso miki wad'annan masifun da ki ka lissafa saboda, shima irinki ne bai ji sauki ba ta k'arasa magana had'e da kya6e baki.
   ''Imaan ta zaro idanu tace aunty dama Daddy bashida lafiya"?
Haleesa ta yi murmushi a zuciya ta tace kai wannan yarinya akwai 'yar jarida da alama uwarta ta biyo da wannan d'an banzan surutu saboda ubanta kurma ne a baiyane kuma sai tace _Eh bashida lafiya amma ya ji sauki_
Aunty me ke damunshi"?
Haleesa ta girgiza kai tace Imaan tashi ki je kitchen akwai ice cream a fridge ki dauko ki sha kinji"?
Da sauri Imaan ta tashi cikin zumud'i tanufi kitchen Haleesa tana murmushi ta bi ta da kallo.
Ta 6angare Habeeb kuma yana jin kiran ya yanke sai kawai ya tabe baki yadanganta, hakan da matsalar network d'in Nigeria ya dukufa tunanin Haleesa iya saninshi ba son yarinyar yake yi ba matsananciyar sha'awarce take wahalarda shi, duk ranar da ya kusance ta zai manta da ita ya ja tsaki had'e da shafi sumar kanshi yana mamakin yadda yake ware lokacin mai matuk'ar mahimanci agareshi ya zauna yana tunaninta a da shi mutum ne Wanda bai San tunani ba sai akan Haleesa tun farkon had'uwarshi da ita har yau ita kadai ce take haddasa masa shiga yanayin na tunani.
   ***********************
```2 DAY'S LATER```
Habeeb na kwance a room d'in da ya yi booking a Alexander Hotel da ke Germany ya yi pillow da hannayenshi ya zurfafa a tunanin, Haleesa duk yarame sai wani farin da ya yi ga wata 'yar uban k'asumba da yatara akan fuskarshi kamar Wanda aka mintsina ya mik'e zaune yadauki phone d'inshi da ke ajiye akan bedside ya yi dialling number Haleesa a maimakon ya jin 'yar muryarta mai sanyaya masa zuciya sai kawai ya tsince muryar Imaan tana zuba masa surutu, ba d'ad'aukawa bai San lokacin da ya katsin kirar{hanging up} ya jefar da wayar bisa bed yarik'en kanshi da ke barazanar fita daga gangar jikinsa, ga matsananciyar yunwa yana ji tun zuwanshi Germany daga coffee sai soft drink su kadai yake daurawa cikinsa cikin d'an k'ank'ani lokacin zazza6i mai zafin gaske ya lullu6e shi.

```HALEESA```
Haleesa na zaune bisa farar kujera roba a compound Imaan na wasa akan 'yar motarta ta wasan yara wance ake sakawa a charging sai kai da kawo take yi Haleesa kuma ta duk'ufa tunanin rayuwarta Ita kanta in aka tambayeta bara ta iya cewa ga asalin abunda ke damunta lokacin sallah magarib yak'arato ta tattara Imaan da motarta suka shiga gida.
 A daddafe Habeeb Lamido ya yi 2 weeks a Germany yajuyo gida Nigeria around _10:30pm_ flight d'in da yad'auko su ya yi landing a hankali yake taka stairs d'in jirgi yana saukowa ya hango Bala.
 ''Tun akan hanya Bala yafara aika masa tambayoyi "Boss ka yi rashin lafiya ne"?
Habeeb ya yi ignoring nashi, da sauri yadafe kanshi tun a flight yake jin ciwon kai had'e da sanyi duk surutun da Bala yake zuba masa ya yi shiru bai tanka masa ba suna isa gida tun kafin Bala ya bud'e masa k'ofa ya bud'ewa kansa yana gaba Bala na biye da shi janye da luggage d'inshi direct yawuce bedroom yafad'a bisa bed ko takalmin k'afarsa bai cire ba ya lullu6e cikin blanket a rikice ya yaye blanket yashiga bathroom yadinga kwara amai Kore shar abun gwanin ban tausayi, jiri na d'ibarsa yafito daga bathroom yak'ara kwanciya, sai faman rawar sanyi yake yi hak'ora shi na had'ewa ya k'undundune cikin blanket gaba d'aya Daren rana Habeeb bai runtsa ba kwana ya yi yana kwara amai a zaune ya yi sallah asuba har 10:00am ya yi yana kwance bai San idan kanshi yake ba
''Da kyar ya lalla6o phone d'inshi ya yi dialling number Bala cikin sark'ewar halshe yace _Bala ka zo banida lafiya_ yana k'arasa magana ya jefar da waya a rud'e Bala yashigo bedroom d'in
    "Sannu Boss
Muryarshi a dusashe yace please Bala kira Dr saleem.
Bayan kamar _10 minutes_ sai ga Dr saleem ya zo bayan yagama duba shi ya debi jininsa zai yi masa blood test domin ya tantance musanbabin ciwonsa, yadaura masa drip had'e da allurai bacci ya yi awon gaba da Habeeb Dr saleem kuma Yakama gabansa, Bala ya na tare da Habeeb drip yak'are ya zare masa, sai misalin k'arfe _2:00pm_ Habeeb yafalka ya yi wanka had'e da sallah duk wannan budirin da ake yi Haleesa batasaniba, Bala kuma yana mamakin ina tashiga saboda sau biyu yana shiga part d'inta bai ganta ba, Habeeb ya ji sauki sosai yau kwanansa biyu dawowa ko compound bai lek'a ba yana kwance a d'akin Bala ke kula da shi matsalar Habeeb bayason magani ga kuma rashin cin abincin tsakiyar dare ciwonsa yadawo sabo dal, a wannan karon har da stomachache sai amai yake kwarawa kamar zai amayar da 'yan hanjinshi, a wahalce ya kira phone d'in Bala koda Bala ya zo yatarar da shi duk yajigata, yafita a hayyacinshi a tsorace Bala ya yi kanshi, yad'ago shi sai kawai Habeeb yafara wani irin nishi yana rik'en cikinshi haka bacci yadauke shi, Bala ya rafka tagumi yana kallonshi kamar daga sama Habeeb ya zabura ya mik'e yanufi bathroom, ya yi amai yana fitowa ya yanke jiki yafad'i k'asa, da gudu Bala ya yi kanshi yana girgiza shi had'e da kiran sunanshi duk girgizar da yake masa ko d'an yatsanshi bai motsa ba, Bala yarud'e iya rud'ewa babu shiri ya yi dialling number madam Hindu.
       "Madam na kwance akan katafaren bed d'inta kirar Royal bed tana sharar bacci ta ji ringing d'in wayarta, a tsorace ta falka saida ta yadda ganinta akan wall clock ta ga time _3:45am_ ta zaro ido gabanta ya yi mummuna fad'uwa hannunta na rawa ta d'auki wayar tun kafin  ta yi picking, zuciyarta ta ba ta cewa wannan kiran ba na lafiya bane sakamako ganin kiran daga Bala ne.
     ''Muryarta na rawa ta furta _hello Bala lafiya kuwa ka kira ni a wannan lokacin"?_
 _madam ki taimake ni ki zo wallahi boss yana cikin matsanancin hali gashinan kwance ko numfashi ba ya yi_
Bala yak'arasa magana kamar zai rushe da kuka
    "Numfashin madam yadinga fita da sauri gaba d'aya ta rud'e kanta ya kwance jikinta yad'auki rawa takasa furta uffan, jin shiru nata ya yi yawa yasa Bala ya katsi kiran da kyar madam Hindu tasauko bisa bed ta bud'e wardrobe taciro wrapper{zani} ta daura bisa night gown d'in jikinta, ta zira hijabinta na sallah tun kafin tak'arasa compound ta dannawa drivernta kira da sauri driven yafito da mota a rud'e madam tashiga motar suka d'auki hanyar gidan Habeeb suna isa  direban yadanna horn security's d'in gidan suka fito ta k'aramar k'ofa suna ganin motar madam Hindu da gudu d'aya daga cikinsu yajuya domin ya bud'e mata gate tun kafin ya bud'e gate madam ta balle k'ofa tafito, tafiya take yi batare da tasan inda take jefa k'afarta ba part d'in Haleesa tafara dosa taji k'ofa a rufe dole tajuya tanufi part d'in Habeeb direct ta wuce bedroom d'inshi a rikice ta yi kanshi tana kiran sunanshi............


Jeeddah Aliyu
[01/01 7:45 am] aliyujeeddah: [27/11 4:59 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```79```

~~Son, son please wake up don't leave your mother I really need you, please Habeeb wake up, gaba d'aya lissafin brain d'in madam Hindu ya kwance tarasa inda za ta jefa kanta batasan lokacin da tafashe da matsanancin kuka tana girgiza Habeeb da k'arfi ganin take yi kamar Habeeb ya mutu ita kuka Bala kuka ba mai rarrashin wani sai lokacin tunani ya zo wa Bala da hamzari yanufi d'an k'aramin fridge da ke ajiye a d'akin ya bud'e yadauko robar ruwa mai sanyi, ya shafawa Habeeb kamar _5 second's_ da Shafa mishi ruwan yasaki ajiyar zuciya mai k'arfi a hankali ya ke bud'ewa idanu har ya ware su gaba d'aya akan fuskar madam Hindu ya k'ank'ame ta cikin dashashshiyar murya, yace _sweetheart cikina kaina, ki rik'e min kaina zai cire_
Madam Hindu tak'ara rud'ewa ta juya wurin Bala cikin shouting tace _please Bala call doctor saleem immediately_
    Jikin Bala na rawa ya yi dialling number Dr saleem daf da asuba Dr saleem ya iso cikin muryar kuka madam Hindu tafara rok'onshi _please Doctor do something to save my son life I don't wants to loose him'!_
      ''Dr saleem yace calm down madam insha Allah ba abunda zai faru da d'anki  batare da 6ata lokacin ba Dr saleem yafara treatment d'inshi ta hanyar daura mishi drip da injections cikin d'an k'ank'ani lokacin bacci ya yi awon gaba da shi madam na zaune a gefenshi tana Shafa sumar kanshi ta mayarda ganinta wurin Dr saleem tace _what's wrong with my son Doctor"?_
    Dr saleem ya share zufa da handkerchief ya d'an numfasa daga bisani yace na yi matuk'ar mamaki lokacin da nagano ainihin abunda yake damunshi da farko akwai tsananin tunanin da yake yi Wanda yana daf da jininsa ya hau sai kuma rashin cin abincin Wanda ya janyo masa kamuwa  da cutar ulcer.
     "Madam Hindu ta zaro ido da alama firgicin a tare da ita ga kuma d'inbin mamakin furucin Dr saleem muryarta na rawa ta maimaita abunda Dr saleem yafad'a _tunani da ulcer_
   "With full confidence Dr saleem ya gyad'a kai yacigaba da cewa dole sai ana bashi, kyakyawar kulawa musanman cin abincinsa idan ya falka ki yi k'ok'ari a matsayinki na mahaifiyasa ki titsi shi domin ya sanar da ke abunda yake damu shi a matsayinki na uwa bara ki rasa taimakon da za ki ba shi, ba kuma ki tabbata yana taking medicine d'inshi in time domin na fahimce duka magunguna da na kawo mishi ba Wanda ya yi amfani da shi.
     ''Madam ta goge hawayen fuskarta, tace na gode Dr saleem.
    "You're welcome madam Dr saleem yafad'a yatattara tarkace shi, ya kama gabansa yabar madam Hindu cikin jimami da fargaba.
     ''Madam tasauke ajiyar zuciya ta juya wurin Bala cike da son jin k'arin haske dangane da ciwon d'anta Bala har tsawon wane lokacin Habeeb yadauka bashida lafiya sannan kuma ina matarshi da ta barka kana jinyarsa"?
    ''Domin ita ce ta dace ta kula da shi ba kai ba tun zuwa na gidanan duk, da bana cikin natsuwa ta zuciya ta take bani akwai abunda ke faruwa a tsakaninsu.
       ''Bala ya numfasa ya karkace baki yasoma kwararo wa madam Hindu zance tun kafin boss ya yi tafiya na fahimce akwai abunda ke damunshi, kwata-kwata yadaina cin abincin ranar da yadawo yafad'i cikin yanayi na rashin lafiya sau biyu ina zuwa part d'in Haleesa bana tararda ita rabona da in sakata a idanunna tun washe garin ranar da Imaan tasami hutun makaranta, lokacin da Hannah ta zo za ta tafi da ita na had'u da su a parking space Haleesa ta yi musu rakiya mu ka gaisa to fa tun daga ranar ban k'ara ganinta ba abun ya yi matuk'ar d'aure mini kai ina tashiga ne tsawon wannan lokacin da Boss yake fama da rashin lafiya yak'arasa magana cikin yanayi da ke nuna alhininsa.
     ''Madam ta mik'e tsanm..... Batare da tace da Bala komai ba tanufi part d'in Haleesa cikin Sa'a tana murd'a handle k'ofar ta bud'e ta kutsa kai tun kafin tak'arasa shiga parlourn, ta hango Haleesa zaune akan _2 seater_  k'afutata na zube akan kujerar tana yanke farce jin k'arar bud'e k'ofa yasa Haleesa ta d'ago _4 eye's_ tayi da madam Hindu rass!....gabanta yafad'i da sauri ta mik'e tsaye ta d'an sace kallon wall clock da ke manne a falon _9:07am_ jikinta yafara rawa tsoro ya baiyana k'arara akan fuskarta da kyar ta furta _sannu da zuwa mom_
Saida madam Hindu takai zaune sannan ta amsa mata ba yabo ba fallasa.
          ''Tun daga nan Jikin Haleesa ya yi sanyi nan take zuciyarta  yaba ta cewa akwai abunda yake faruwa a sanyaye ta duk'a cikin girmamawa tace _ina kwana mom''?_
    _lafiya amma ba qalau ba_
 furucin madam Hindu yak'ara tsorata Haleesa cikin sark'ewar halshe tace me ke faruwa mom''?
   ''Wannan tambaya ta Haleesa tak'ara harzuk'a madam Hindu har takasa controlling temper ta cikin zafin rai ta rufe Haleesa da fad'a _ke wance irin mutum ce Haleesa mijinki bashida lafiya tsawon kwanaki uku kuna gida d'aya ace baki saniba wannan wane irin sakarcin ne"?_
   ''Wannan ya tabbata mun da cewa baki Masan menene Kalmar miji take nufi ba, ballatana ki San yadda ake kula da shi, dalilin wannan sakacin naki gashinan d'ana ya kamu da cutar yunwa, wallahi idan wani abu yasame d'ana Haleesa har abada bara taba daina ganin sakaci da laifinki ba koda ace Habeeb ya yi miki wani laifi bai kamata ki yi masa horo da yunwa ba tak'arasa magana tana huci.
     ''Tun lokacin da madam Hindu tafara wankewa Haleesa allonta Haleesa take wuk'i-wuk'i da idanu tsananin mamakin zafafa kalaman madam Hindu suka hanata tabuk'a komai.
    Shiru Haleesa ta yi tarasa abun fad'a sai kawai tafashe da kuka madam Hindu ta girgiza kai ta mik'e a zafafe tace wannan kukan da ki ke yi bashida amfani zan iya danganta shi da kukan dad'i domin in Habeeb ya mutu bakida asara nice da asara domin ni ce narasa d'a madam Hindu na k'arasa magana tafice daga falon tabar Haleesa na kuka kamar ranta zai fita, haushi da tsanar Habeeb Lamido suka cukuikuye mata zuciya a yadda takejin zafi na kwarara a zuciyata Kamar ta had'a kayanta tabar mishi gida dama yasha fad'a mata saboda mom ya aureta a halin yanzu mom ta tsaneta, har tana danganta da laifin da batada masaniya akai tana cikin wannan halin Hannah tashigo
ta zauna a gefenta cikin sanyin murya tafara magana, Haleesa yanzu nan mom ta kira ni a waya ta zayyane mun abunda yafaru nayi matuk'ar mamaki yadda mom takasa gano laifin yaya Habeeb, jira nake yaya Habeeb yafarfad'o na fallasa shi a gabanta  in yaso ta tantance tsakani ke da shi waye mai laifi.
    ''Haleesa ta share hawaye fuskarta tace Hannah banaso, ki sanarda mom komai dangane da zaman mu da yaya Habeeb, a hali yanzu zuciyata tariga ta bushe na dau alwashi sai na azantarda ruhin d'an uwanki da soyayya ta mai tsananin zafin gaske na yi amfani da ita na rama duk wani cin kashi da ya yi min sai na nunasa masa cewa ba kowace Mace ake wulaqantawa ba sai gwanmace kid'a da karatu.
     Cikin tsananin farin ciki Hannah tarik'o hannun Haleesa tace tun farko abunda nake nuna miki kenan Haleesa ki ka k'i bani had'in kai da yanzu zance yasha banban, yanzu tashi mu tafi ki ba wa mom hak'uri nasan yadda mom takesonki bara ta iya cigaba da fushi da ke kuma duk bak'ak'en maganganu da mom ta zuba miki ki rubuta su tass....ki yi wa d'anta tanadin su Haleesa ta zaro ido tace Hannah bakida kirki yayanki ne fa
     ''So what's Hannah tafad'a had'e da kad'a eye's ball d'inta karki manta Haleesa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne don haka duk lokacin da yaya Habeeb yashiga hannunki karki raga masa ki tabbata kin sauke masa wannan miskilancin da yake tak'ama da shi.
    Haleesa ta cize lips d'inta na k'asa ta kad'a kai tace bari kawai Hannah Allah yakai damo ga harawa.
    Ameen 'yar uwa zo mu tafi kada mom tak'ara hayewa.
     "Direct bedroom d'in Habeeb suka wuce mom na zaune kusa da shi ta rafka tagumi yayinda Habeeb ke ta sharar bacci, Hannah ta zunguri kafad'ar Haleesa nan take Haleesa ta yi pity face ta zube gaban mom tarik'e hannun mom ta marairace murya _Dan Allah mom ki yi hak'uri nasan na yi kuskure amma insha Allah bara ki sake kamani da koda kwatankwacin irin wannan laifi_
  tak'arasa magana cikin muryar kuka madam Hindu tasauke ajiyar zuciya tad'ago Haleesa suka nufi parlour tasoma yi mata nasiha daga yau Haleesa karki sake sakacin sake ragama abincin mijinki a wurin ku-ku lokacin da peter yake yi min bayani tun zuwanki gidanan shi yake yi wa Habeeb girki ba ki ji yadda raina ya6acin ba amma yanzu komai yawuce ki tashi ki Shiga kitchen ki Samar mishi abunda zai cin domin Dr saleem yace da ya falka abashi abinci
    ''Da hamzari Haleesa ta mik'e tanufi part d'inta Hannah ta Mara mata baya.
  _15 minutes later_
A hankali Habeeb yake bud'e idanunshi har ya ware su gaba d'aya, k'ok'ari yake ya mik'e zauna da sauri mom ta taimaka masa, ya zauna tasaka masa pillow a baya ya jingina jikinsa, duk ya rame ya yi k'ashin wuya.
   ''Sannu son ya ka ke jin jikin naka"?
  Da sauki mom yanzu dai ina son na yi wanka na rama sallah da ke kaina.
Da sauri mom ta mik'e bara na kira Haleesa ta taimaka ma, batare da ta jira jin ta bakinshi ba tafice, Wani irin dad'i ya ratsa sassan jikin Habeeb ya kwarara a zuciyarsa, ya lumshe idanu, jin karar bud'e k'ofa yasa da sauri ya bud'e idanunshi yasauke su akan fuskar Haleesa, tasake masa k'ayatace murmushi, sannu yaya Habeeb ya jikin naka"?
   ''Saida ya ja iska yafesar sannan yace da sauki ki taimaka ki had'a min ruwa zan yi wanka
  Batare da tace komai ba tashiga bathroom ta cika masa bathtub da ruwa masu d'an d'umi-d'umi har tafito yana nan yadda ta barshi muryarta tace tadawo da shi daga tunanin da ya afka _yaya Habeeb na had'a ruwan_
   "Chan k'asan mak'oshi ya furta na gode yana bin bango yashiga bathroom  Haleesa ta bi shi da kallo ya yi matuk'ar bata tausayi ashe akwai abunda zai sa yaya Habeeb ya yi laushi, ta yi murmushin mugunta ta gyara masa bed ta feshe d'akin da freshener tana tsaye har yafito daga wanka ya zauna a gefen bed yana mata kallon k'asan ido wani irin abu yakeji yana ratsa jinin jikinsa can! Ya yi gyaran murya daga bisani yace........

Note:- _I'm sorry readers nasan za Ku ce page d'inan yayi kad'an wallahi yau nayi typing mai yawan gaske basan ya akayi ya fita gaba d'aya, ba da kyar na yi wannan a halin yanzu kaina yadau zafi ina cikin yanayi na jiyar zuciya_

Jeeddah Aliyu
[01/01 7:48 am] aliyujeeddah: [28/11 6:20 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```80```

~~ke! Bud'e wardrobe ki dauko min fari jallabiya{white colour} yak'arasa magana had'e da lumsashe idanu.
Haleesa ta tabe baki a zuciyarta tace huh...daga farfad'owarsa yafara kirana da suna nan da na tsana, a maimakon ta dauko white colour kamar yadda ya umurceta sai kawai ta dauko mishi black colour, k'i kar6a ya yi yabarta tsaye rik'e da rigar, Haleesa tasake mik'a masa rigar tace yaya Habeeb gashi  katashi ka yi sallah lokacin yana k'urewa.
   "Ya yi kici-kici da fuska very slowly yafara magana Fari nace ki dauko ba black ba.
     "Umhh....fari kace na dauko ni kuma a ganina white da black duk d'aya ne muradi kawai ka suturta jikinka ko...ya kace"?
Tak'ara sa magana tana kallon fuskarsa, saida ya tsotsi bakinshi sannan yafisge rigar daga hannunta daga zaune ya zura rigar yayinda Haleesa ta shinfid'a masa pray mat yana fara sallah tafice daga d'akin a parlour ta tararda madam Hindu da Hannah suna breakfast mom tace kin had'a masa ruwan wanka ne"?
   ''Eh mom har yafito daga wanka yanzu ma na barshi yana sallah abincinsa zan dauko masa.
  Da kyau 'yar albarka haka akeso mace tagari ta kasance, murmushi Haleesa ta yi tanufi kitchen hannunta d'auke da k'aton tray ta tura k'ofa tashiga, yana zauna inda ya yi sallah da sauri yad'ago yarame sosai idanunshi sun k'ara girma fuskarshi ta yi wani fiyau ga wata irin k'asumba da yacika masa fuska.
  Tadire tray hannunta ta zauna a gabanshi tana magana tana zuba masa kunun gyad'a kafara da wannan saboda hanjinka ya warware tak'arasa magana had'e da mik'a masa cup ya kafe ta da idanu ko kintawa ba bu Haleesa ta kad'a eye's ball d'inta ta marairaice murya ka daure kasha koda d'an kad'an ne.
     Idaunshi a lumshe ya mik'a hannu ya kar6i cup d'in daga hannunta a hankali, yake kur6a kunun har ya shanye  tass...ta kar6i cup ta bud'e food flask k'amshin faten dankalin turawa ya daki hancin Habeeb ya hadiye yawu, ta yi masa serving sai ga gogan naku ya lamshe fate tass....ya ajiye plate yana wani yatsinar fuska Haleesa tace uhmm....ciwonka yana burgeni yaya Habeeb saboda bai hanaka cin jagwalgwalen Haleesa ba tak'arasa magana tana murmushin tsokana.
   Habeeb ya daure fuska kema kinsan saboda mom tana gidanan yasa naci abunda ki ka sarafa da hannunki.
   ''Haleesa ta tabe baki tace uhmm.....yaya Habeeb kenan a wasu lokuta in kana magana kamar da gaske sau ina kama ka kana satar jagwalgwale tak'arasa magana tana dariya.
  ''Da k'arfi yafisgota tafad'a kansa ya yi mata bak'ar matsa tasaki 'yar k'ara, yadaura bakinshi dai-dai k'ofar kunnenta yace ke! Waye barawo"?
  ''Ni fa bance maka barawo ba tafad'a cikin rawar murya d'ago fuskarta ya yi yana mata kallon ido cikin ido kasa jurewa ta yi ta sunne fuskarta a k'irjinshi, jikin Habeeb Lamido na 6ari yak'ara rungume ta tsanm....ya daura kanshi bisa wuyanta yana sauke numfashi can! K'asan mak'oshi Haleesa tace ka sakeni kada su mom su shigo su ganmu a haka Allah kunya zan ji tak'arasa magana cikin sigar shagwa6a.
    'Maganar tace ta katsiwa Habeeb hamzari da sauri ya yakice ta daga k'irjinshi a kunya ce ya mik'e yanufi gefen gado ya zauna, Haleesa bata k'ara kallonshi ba ta tattrara food flask tafita da su.
   Koda ta koma d'akin ta tarar da mom da Hannah na ciki Habeeb ya daura kanshi, akan cinyoyin mom tana shafar gashin kanshi Haleesa tabe baki tanemi kujera da ke cikin d'akin ta zauna cikin sigar rarrashi mom take masa magana _please son ka sanarda ni ainihin abunda yake damunka sanin kanka ne bara ta6a samu peace of mind matuk'ar kana cikin damuwa_
   ''Idanun Habeeb suna lumshe yace c'mon sweetheart I told you hundred time's ba abunda ke damuna so stop worry yourself.
    Madam Hindu ta girgiza kai tace shikenan son, amma Dan Allah ka dinga cin abinci, kuma daga yau na hana peter ya girka abinci da kai ga matarka nan duk abunda ka ke so kafad'a mata za ta girka ma.
     "Sai lokacin ya bud'e idanunshi ya mik'ewa zaune madam Hindu ta juya wurin da Haleesa take zaune tace ni zan tafi Haleesa ki tabbata yana cin abinci sosai ya kuma dinga shan maganinsa in time.
   ''Haleesa ta gyad'a kai a zuciyarta tace kai wannan matar akwai iya yi hatta da magani tace sai na bashi sai kace k'aramin yaro ae kuwa overdose zan dinga d'irka masa.
    Madam Hindu tariga Hannah fita daga d'akin Hannah ta matsa daf da kunnen Haleesa ta rad'a, _yar uwa karki sake ki yi wasa da wannan damar da ki ka samu ba Dr saleem yace cutar ulcer da hawan jini yake damunsa ba ke Kuma ki yi k'ok'ari ki k'ara masa da cutar so_
   ''A lokacin d'aya suka kyalkyale da dariya had'e da tafawa Habeeb Lamido ya zaro ido a zuciyarsa kai   lallai yara nan sun rainani da alama gulma ta ce suke yi ya murtuk'e fuska ya gallawa Hannah harara yace ke wai uban me ki ke jira ne da ba ki tafi ba kin bar mom tana jiranki"?
Hannah ta turo baki tace mom tare take da direbanta, ni kuma da motana nazo.
    "Whatever! Habeeb yafad'a a harzuk'a.
Tsabar tsokana irin na Hannah saida tak'ara rad'awa Haleesa _yar uwa kada wannan muzurai da yake yi yabaki tsoro domin hakan zai iya rusa miki plan_
Haleesa ta yi murmushi ita ma ta rad'awa Hannah _don't worry 'yar uwa ke dai ki zuba ido ki sha kallo_
Suka k'ara kwashewa da dariya Hannah tajuya wurin Habeeb tana dariya tace bros ni zan ware sai gobe in nazo shan farfesu.
  Tsaki Habeeb ya ja yace wannan kuma matsalarki ce munafuka kawai.
   Hannah ta dube Haleesa ta yi mata signal karaf akan idon Habeeb, sai kawai ya ga Haleesa ta tintsire da dariya Hannah ta bud'e k'ofa tafice.
    ''Habeeb ya d'aure fuska yana kallon Haleesa a d'age yayinda ita kuma ta sadda kanta k'asa, tsawon dak'ik'a uku ta dauka kanta na sunkuye daga bisani tad'ago ta sace kallon Habeeb idanunshi na kafe akanta, batasan lokacin da tasake masa murmushi ba.      harara ya galla mata yace ke zo nan
   Saida anta cikinta ta kad'a ta dake kamar bata tsorata ba ta mik'e a sanyaye tanufi wurinshi Saida yak'are mata kallon wulaqancin yace jikina yabani cewa wannan rad'e-rade da Ku ke yi da ni Ku ke don haka fad'a min abunda Ku ke cewa"?
   ''Haleesa ta rusa yar da kai ya za'ayi yaya Habeeb kana zaune mu yi gulmarka"?
  Karaf yarik'en mata hannu ya shiga murza yatsunta da k'arfi, Haleesa tafasa ihu _wayyo yatsuna Yaya Habeeb karka yi min targad'e_
  Saida yagaji don kanshi yasaketa, ta koma gefe tana 'yarfe hannu a zuciyarta tace mugu kawai nan take ta tuna da bai sha maganinsa ba ta yi murmushin mugunta tace nima anan zan rama yanzu nan za ka ga kalar nawa mugunta.
    Tajuya ta dube shi ta ga har yanzu ita yake kallo ta turo baki tanufi bedside tadauko ledar magunguna sa, robar ruwa da cup tadauko ta ajiye bisa dressing mirror tasoma 6alle tablets saida ta cika hannunta duk abunda ta ke yi Habeeb ya kafenta da ido  murgud'a masa baki ta yi ta mik'a masa hannunta karaf ya d'anke hannunta tace kai bawan Allah magani za ka kar6a ba hannuna ba.
     ''Yatsine fuska ya yi Can! K'asan mak'oshi ya furta kina nufi ni zan sha wannan tulin magani"?
Kwarai kuwa ko bara ka sha bane na kira mom a waya
Tsaki ya ja yace amma dai kinsan banason magani koh"?
   Ta tabe baki tace oho...ni bansaniba cike da jin haushi ya mik'a mata hannu ta bashi maganin kamar zai fashe da kuka yace duk tulin magani nan ace ni kadai zan shanye shi, sai kace d'an kwaya.
    Saura kiris Haleesa ta tintsire dariya sai kawai ta hadiye abarta Habeeb ya runtsi idanunshi da kyar ya shanye maganin yayinda Haleesa take aikin kallonshi saboda yatuna mata da marigayi yaya Habeeb shima haka yake Sam bayason magani duk lokacin da bashida lafiya sai tasha artabo da shi kafin yasha magani.
     "A zuciyarta tace huh....kenan duk mai suna Habeeb bayaso magani batasan cewa maganar da tayi yafito fili ba.
 Tsananin kishinta ya lullu6e Habeeb cikin zafin rai ya wanka mata raguwar ruwan da yasha magani.
   A tsorace Haleesa tad'ago tana kallonshi yayinda shima ya kafenta da idanunshi da ke baiyanar da b'acin ranshi a fili.
   Nan take wani tunani yafad'owa haleesa sai kawai ta hadiye b'acin ranta, ta mik'a hannunta ta d'auki robar ruwa kamar za ta sha ta balle murfi ta kwara masa a jiki ta balla da gudu ta nufi k'ofar fita har tafita ta d'an lek'o kanta ta yi masa gwalo tasaki k'ofa ta kwasa da gudu tashige part d'inta direct ta wuce bedroom tafad'a bisa bed tad'auki pillow ta manna a k'irjinta wani irin nishad'i, takeji Wanda rabonta da ta tsince kanta cikinsa tun yaya Habeeb d'inta yana raye ta runtse idanuta fuskar Habeeb Lamido ke mata gizo.
Ta6angare Habeeb kuma Haleesa na ficewa ya tsurawa k'ofa ido daga bisani ya sulale ya kwanta rabin jikinsa na bisa bed yayinda k'afafunsa ke k'asa wani irin tafiyar tsotsa yakeji a jininsa, sai kawai ya afka tunani yafara aikawa kansa tambaya batada amsa.
   _me yasa lokacin da yarinya nan ta yi zancen marigayin sarauyinta naji mashahurin kishinta ya turnuke ni"?_
Ya mik'e zauna wani 6angare na zuciyarsa yace hakan yana da nasaba da tsananin sha'awarta da ka ke yi ya tabe baki had'e da mik'ewa yacire rigar jikinsa Yana tunanin in ya kama Haleesa irin hukuncin da zai yi mata.
*************************
_8:30pm_
Habeeb yana zaune a falonshi ya kafe akwatin talabijin da ido Haleesa ta yi sallama sai kawai ta ja ta yi tsaye cikin tsokana tace _yaya Habeeb in shigo ko in koma inda na fito"?_
     Murmushi Habeeb ya yi had'e da shafa sajen shi, ya ja iska wani irin dad'i ya ziyarcenshi jin yake yi tamkar yana yawo a sararin samaniya, amma tsabar zafin kanshi ba zai barshi ya baiyanar da jin dad'i nasa ba.
   "Ya yatsine fuska yace duk yadda ki ka za6a.
  Haleesa ta mak'e kafad'a tak'arasa shiga falon a fakace yak'are mata sanya take cikin lemon green colour gown iya guiwanta ta yane kanta da d'an k'aramin white colour veil fuskarta tasha light make-up matsananciyar sha'awarta ta lullu6enshi har ta haddasa masa kasala yasauke zazzafar ajiyar.
Kaitsaye ta zauna bisa hannun kujerar da yake zaune, k'amshin turarenta ya baibaye shi ya tsincin kanshi cikin wani hali Wanda a tarihin rayuwarsa bai ta6a riskar kansa a ciki ba.
  Kafin yadawo daga duniyar tunani muryar Haleesa ta daki dodon kunnenshi _yaya Habeeb your food is ready_
   Habeeb ya tabe baki yana mamaki me Haleesa take nufi da wannan sabon salo da ta zo mishi da shi ta na nufi za ta ja ra'ayinsa ne yafara sonta"?
Ya yi murmushi yad'ago kanshi sama yadda zai hango fuskarta yana mata duba mai cike da sha'awa, yace ki je ki juyewa Rahul da Rita ni na k'oshi.
    Haleesa batasan time d'in da ta galla masa harara ba ta murgud'a baki.
yadda ta murgud'a baki ta yi mugun bashi dariya sai kawai ya basar, yad'age gira sama yana mai cigaba da kallonta.
     "Haleesa ta narke murya tace haba! Yaya Habeeb karka yi mun haka mana karka manta mom tace na kula da cin abincinka yanzu dai ka yi hak'uri katashi mu je ka cin abinci kaji"?
   "Ignoring nata ya yi ya mayarda hankalinshi wurin TV haushi ya turnuke Haleesa a zuciyata dallah! Dube shi ina rok'onshi yana wani jan aji duk lokacin da ka shigo hannunna sai na gasa maka gyad'a a tafin hannunka.
   Saida ya gama ja mata rai ya mik'e yana gaba tana biye da shi bayan sun gama cin abinci ya mik'e ya koma falonshi.
_10:00pm_
Har Haleesa ta kwanta ta tuna Habeeb bai sha maganinsa ba da sauri tadiro daga kan bed ta zura Hijab bisa night gown d'inta, ta murd'a handle tafice kaitsaye ta murd'a k'ofar d'akin Habeeb tashiga yana kwance ya yi pillow da hannayenshi abun duniya yataru ya yi masa yawa a yadda yake ji game da Haleesa muddin bai ji d'umin jikinta ba zuciyarsa za ta iya bindiga ta tarwatsa yana cikin tunani yadda zai je mata da buk'atarshi sai gata ta zo a lokacin da yake da tsananin buk'atarta, ya lumshe idanu yasaki murmushin dad'i a zuciyarsa yace uhm....tsuntsu daga sama gashashshe.......

Jeeddah Aliyu

No comments:

Post a Comment