Sunday, 9 April 2017

SONKI NE SANADI ~1

*SONKI NE SANADI*


_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*AuntySis AuntySis AuntySis everywhere.*
*Kowa AuntySis nima nace wacece AuntySis din nan.* *Lokacin da na san AuntySis I can say she is d simplest,* *best and sweetest person I eva come across in my entire life. She is so loving and caring,unique in her own ways.*
_*Sadaukarwar taki ce gaba dayanta AuntySis💞. Allah yasa kifi haka.*_

*Jidderh luvs u much.*❤


    *°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

             
*Da sunan Allah mai Rahma mai jink'ai Allah ya yi dad'in tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad{S.A.W} da iyalansa da sahabbansa.*

_Gargad'i:-Ban rubuta wannan labarin don cin zarafin wani ko wata ba wannan littafin k'irk'irarran labari ne idan ya yi dai-dai da halinki ko halinka ayi min Afuwa Akasi ne_


       
           *Kano 2011*
                   _12:22pm_

   *1*

Jerin motoci ne kirar land cruisers guda 3 bak'ak'e wulik da su sai shek'i suke yi suka fito daga Malam Aminu Kano Airport kamar yanda suka fito a Jeri haka suka hau kan titi a Jeri, sai faman sharara gudu suke daga karshe suka doshe Nassarawa GRA wani tanfatsetse gidan suka nufa kamar had'in baki a lokacin d'aya suka yi horn, Gateman ya wangale musu gate a tsakiyar compound suka yi parking a lokacin d'aya motoci 2 k'ofofinsu suka bud'e mutane 6 suka fito sanye da uniform na custom da gudu suka nufi d'ayan mota mutum 2 daga cikin mutane 6 suka bud'e k'ofofin na seat, d'in baya.
   "Controller General Alhaji Basheer Galadima ya zura k'afafunshi k'asa yafito daga cikin mota yana sanye da d'akakiyar farar shadda "everything's da ke jikinshi white colour ne. wasu kyakyawawa 'yan mata 5 suka fito daga cikin gida fusk'ok'insu d'auke da fara'a Direct wajen Daddyn nasu suka nufa cike da k'asaita da taqama ya zuro k'afafunshi suka sauka k'asa sannan gangar Jikinsa ta baiyana kyakyawan matashin saurayi Wanda shekarunshi na haihuwa, ba za su haura 28yrs ba wankan tarwad'a ne yana da tsawo sosai yana da manyan idanu da  yalwa gashin gira yana da dogon  hancin ga laulausan sajen kwance akan fuskarshi had'e da d'an gajeri gemu gashin kanshi a kananad'e kamar abunda yake sanyawa relexer goshinsa d'auke da abin sallah bak'i wulik da shi.

''Jikinshi na sanye da black Jean's da red long shirt yadaura black jacket akai jikin jacket d'in kamar gashin damisa, k'afarshi rufe cikin red boot Fuska na fitarda annurin murmushi Wanda yak'ara, baiyanar mishi da kyakyawar fuskarshi.''
"Da gudu 2 daga cikin 'yan mata suka nufe shi ya ware musu hannayenshi ya Ansar oyoyo abunda 'yan mata suke fad'a a lokacin da ya yi musu masauki a fad'add'e k'irjinshi _oh my little Siblings I really miss you_
Peck ya yi musu a kumatu sannan yasake su d'aya daga cikinsu take magana cikin shagwa6a ya Ansar ba ka d'agani ba zaro ido ya yi huh.... Nadee troublemaker can't you see you're big girl now"?
  "I'm not ya Ansar please pick me up''
Murmushi ya yi ya sunkuce ta had'e da d'agata sama, kamar teddy bear Yayinda Daddy da raguwar 'yan mata suke musu dariya, yana dira ta k'asa d'ayar ta ware hannanyeta nima ya Ansar waro idanu ya yi fiye da farko "you again Basmah 'yar lukuta kinsan fa ke nauyi ne da ke"?
  ''Juyawa ta yi wajen Daddynsu cikin shagwa6a tace Daddy kanajin ya Ansar koh"?
Daddy yana dariya yace c'mom my Boy ita ma kadauke ta ka huta da rigimarta ,kamar zai yi kuka yadauketa yana nishi daga bisani ya ajiyeta yajuya wajen 'yan matan 3 ya rungume mai red colour lace _I miss you yaya Saleema mun same ku lafiya"_
  ''Miss you too Boy lafiya qalau ya gajiyar zaman flight"?
Ganinku ya watsak'ar mun da gajiya yak'arasa magana yana dariya, yak'ara rungume guda d'aya da ke sanye da Arabian gown yaya Abeeda naa ya kid's d'ina"?
Lafiya qalau suke sunyi miss naka me too yafad'a yasaketa yanufi wajen wance da ke sanye da gown na shadda, ita ma rungumeta ya yi welcome Home Boy"
"Thanks Yaya Baby ina Mommy naa"?
Mommynka tana cikin tana jiran zuwanka, a shagwa6e yace shine ba fito tarbana ba"?
  ''Dariya Baby ta yi had'e da rik'o hannunshi suka nufi cikin gida yayinda Daddy da raguwar girls d'in suka Mara musu baya, Hajja Fatee na zaune Jikinta sanye da tsadad'en cotton swiss voile Idanunta manne da Medical eyeglasses, farace Sol kamar balarabiya fara'a take kamar gonar auduga ta tashi da sauri had'e da ware hannayenta "you're highly welcoming Home my boy da sassarfa yak'arasa wajenta yashige Jikinta ya yi hugging nata tightly _I miss you mom I really miss you mom_ sai fad'a yake yi yana nanatawa d'ago fuskarshi ta yi tana shafar fuskar nashi miss you too Boy sai kawai yasa mata kuka, had'e da k'ara qamqameta _Mom tsawon shekaru da nayi bana tare da ku nayi su ne cikin tsananin k'uncin wasu lukata idan na tuna da ku Allah kuka nakeyi kamar mace, sai naji na tsane karatun da naje yi please mom karku k'ara separated nawa daga gareku saboda ku ne farin cikina_  "In tears yak'arasa magana.
  "A karo na biyu da Hajja Fatee tad'ago shi ta share mishi hawaye Kadàina kuka boy this time kadawo gida kenan mu ma ba'ason ranmu ka tafi wata uwar duniya ka share share tsawon 4yrs batare da mu ba don kawai cigabanka ne da cikar burin Mahaifinka.
  "Daddy yak'araso wajensu yana dariya  Boy ba ka girma har yanzu kananan da shagwa6arka, lallai kuwa akwai rikice babba tsakaninka da Basmah domin na tabbata ba za ta barmaka rank d'inta na Auta ba.
  ''Da sauri Basmah tak'araso cikin shagwa6a tace zancenka gaskiya ne Daddy indan ka ga na barmishi Mom aure nayi.
  "Gaba d'aya suka sa dariya Ansar ya ja hancinta ni kuma kingani nan komai wuya komai tsanani duk runtse duk wahala no thing separate me from them yak'arasa magana had'e da rik'o hannun Dad d'in nashi.
  "Dariya iyayyen nashi suka yi wance ke nuna sun ji dad'in zance nashi, har part d'inshi suka rakashi yayi taking bath saida suka ga shigarshi bathroom sannan suka dawo main parlour, yayinda Housemaids suke ta faman arranging dining table.

"Ansar yafito daga wanka daure da towel a waist nashi, Direct dressing mirror ya wuce ya yi tsaye yana kallon kanshi ya shak'i iska cike da nishad'i ya furta Home, sweet Home ba abunda yakai gida dad'i yad'auki  comb Shiga shace gashin kanshi mayunka kala-kala yadinga shafawa gashin nashi, tsawon lokacin ya6ata a gaban mirror sai kace mace Farar Jallabiya yasaka yafeshe Jikinshi da turaren Malik al-dud kaitsaye yanufi part d'in mom suna Zaune a parlour da alama suna zaman jiranshi ne, yana murmushi ya yi sallama, a tare suka amsa masa sallama yana dariya ya dubi Daddy yace Dad mutafi masallaci naga time d'in sallah azhar ya yi Girl's d'in suka sa Dariya Nadeeya tace Ya Ansar kananan  yanda ka ke zaman abroad ba sauya ka ba har yanzu kananan da halinka na rashin wasa da lokacin sallah.
 Ya yi murmushi Wanda yak'arawa fuskarshi annuri yace Nadee zama abroad ba zai sa mutum ya watsarda kyawawan d'abi'unshi sai in dama yanada burin canza sheqa daga yanda aka sanshi zuwa dabi'un Nasara ko kuma Allah yayi nufi sauyawarka to anan kuma bakada mafita domin Ubangiji shi yake tsarawa 'yan Adam rayuwa amma ni Alhamdulillah! Yanda na tafi haka nadawo ba abunda yasauya a tare da ni.
  "Gaba d'ayan su hamdallah suka yi da jin furucinshi Daddy ya mik'e tsaye ya dube Mum da ke sharar hawayen farin ciki yasaki mata murmushi Ba kuka za ki yi ba Fatee ki godewa Allah da yanufe ki da wannan ni'ima domin samun 'ya'ya nagari  irin Ansar a wannan zamani sai an tona
 "Alhamdulillah! Dukan godiya sun tabbata agareka Allah da ka nufe ni da samun d'a mai nazari da riqo da addini islama, ya Allah ka Albarka ce rayuwarshi kasa wa karatu da ya yi albarka.
  _Ameen Mum_
Girl's d'in suka fad'a a lokacin d'aya yayinda hawaye suka cikawa Ansar ido yakasa cewa komai farin ciki fal akan fuskarshi.
  "Dad yarik'o hannunshi suka fice mum ta dubi girls d'inta tace kutashi mu je mu yi sallah.

_10 minutes later_

Gaba d'ayansu suna zaune akan dining table ba ka ji komai sai karar spoons sai faman kad'a kai Ansar yakeyi alama yana jin dad'in abincin da yake ci Bayan sun kamalla cin abincin suka yada zango a parlour.
  "Ansar ya yi doguwar hamma had'e da mik'a Dad ya dube shi cikin kulawa yace Boy ka je ka kwanta domin akwai gajiya mai d'ibin yawa a tare da kai.
  "Ansar yasaki murmushi to Dad yafad'a had'e da mik'ewa tsaye Mum zan je na kwanta in lokacin sallah La'asar ya yi a tashe ni.
   "Basmah ta riga Mum magana Ya Ansar ni da kaina zan je na tashe ka ya laqace mata hanci yana murmushi yajuya yanufi part d'inshi.
"Yacire Jallabiya jikinshi ya ajiye a gefen bed ya kunna Ac ya haye k'aton Royal bed d'inshi bai jima da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da shi.

*TUSHEN LABARI*

"Alhaji Basheer Galadima su biyu kacal iyayyensu suka haifa a duniya shi da qaninshi Alhaji sa'eed Alhaji Basheer custom ne, Wanda a halin yanzu yana taka matsayin controller General mahaifinsu yarasu tun suna cikin ganiyar kurciya mahaifiyarsu Haj Hajjo tana nan a  raye tana zaune a gidan Alhaji sa'eed a tangamemmen part d'inta.
  Alhaji Basheer Galadima matarshi d'aya hajja Fatee sunyi aure saurayi da budurwa asalinta bafulatana Yola ce kuma, tafito daga gidan sarauta Allah yabarkace su da 'ya'ya har guda 6 Abeeda ita ce babban ta yi aure har da 'ya'ya 3 saboda tana d'aukar long time kafin ta haihu, sai saleema ita ma kamar Abeeda ce ta yi aure 'ya'yanta 3 khadeeja wance taci sunan Hajjo shiyasa ake kiranta da Baby ita ma ta yi aure da 'ya'yanta 2 sai shalele d'an gaban goshi kwali d'aya Muhammad Ansar sai Nadeeya wance yanzu take level 1 a B.U.K sai Basmah auta tana final year a secondary school.
  "Hajja Fatee cikkakiyar 'yar kasuwa ce tana da manya-manya boutiques cikin garin Kano tana dauko kaya a kasashe duniya kamar, irinsu Indian, Dubai, Indonesia mace ce mai dogaro da kanta.
  "Alhaji Basheer Galadima burinshi ya gina company saboda da ya yi retired yanada babba kadara da za ta dinga kawo mishi k'udi, shiyasa yaware duk wani tanadi da yajima yanayi ya gina babban company Wanda yakeda burin mik'a alhakin kula da shi a hannun tilo d'ansa yayinda shi kuma in ya yi retired ya fantsama harkoki siyasa.
  "Alhaji sa'eed Galadima d'an kasuwa ne sana'arshi siyarda gwalagwalai matarshi ta aure guda 1 me suna Haj saudat ya'yanshi 5 Nafeesa ita ce babba ta yi aure da jimawa saboda tana kamalla secondary school akayi mata aure 'ya'yanta 4 sai Abdallah sa'an Ansar kuma amininshi a halin yanzu shine ke kula da ragama company Alhaji Basheer sai Fahad sai zuhura sai kuma auta Nazeeya zuhura sa'ar Nadeeya ce sannan kuma ita ce Ansar zai aura tun kafin ya tafi U.K akayi musu baiko jira kawai ake yadawo asha bikinsu.
"Ansar yana matuk'ar son zuhura tamkar numfashinsa kamar yanda ita ma take sonshi kamar ranta zan iya cewa son da  Zuhura take mishi yazarce Wanda yake mata.

*Back to story*

Karfe _4:03pm_ dai-dai Basmah tashigo d'akin Ansar ta tashe shi bayan ya yi wanka ya yi sallah yashirya cikin english wear's sai faman zabga k'amshin yake, yafito daga part d'inshi kaitsaye na iyayye shi yadosa a parlour ya iske 'yan uwanshi zaune shima yanemi sofa ya zauna ya dube su cike da jin dad'i yace.........

Jeeddah Aliyu

2 comments:

  1. This is another must read and one of the best hausa Novel HUBBUL YAQEEN http://share4world.com.ng/2019/03/24/hubbul-yaqeen/ enjoy free readings

    ReplyDelete