Saturday, 31 December 2016

NI DA YAYA HABEEB 41_60

[30/12 8:17 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```60```

Jiki a sa6ule tak'arasa fita Wannan karo ma Bala ne yafito daga cikin mota yak'araso wurinta "Barka da fitowa ranki yadad'e"
Yauwa Bala ya gida"?
Lafiya Qalau ya hidimomi biki"?
Shiru Haleesa ta yi had'e da sada kai k'asa gani yadda ta yi yasa Bala ya yi murmushi yace ba fa ni kadai bane tare nake da "Boss'
Wani fad'uwa gaba Haleesa tak'ara ji tsanani tsoro ya lullu6e ta tamkar mai ciwo hak'ora ta bud'e bakinta tace Bala kace da shi yak'araso ciki ranar ma da na tsaya da shi a k'ofar gida saida Baffa ya yi Fad'a "Bala yace okay ba matsala bara na yi masa magana Bala yanufi wurin mota ya bud'e k'ofar da Habeeb yake Zaune fuskarshi ahad'e ba bu annuri ko misk'arazairatil a tare da shi da alama zuwan sa na dole ne "Boss tace ka shigo daga ciki saboda Baffanta bayaso tsayuwa a k'ofar gida"
A harzuk'e Habeeb ya ke kallon Bala daga bisani yace banida buk'atar shiga gidansu don haka za ka iya bata dalilin zuwa na gidansu"
Ka yi hank'uri "Boss ka daure ka k'arasa daga ciki karka manta ko yanzu kafin mu zo gidanan irin Fad'a da Madam ta dinga yi ta nuna 6aci ranta k'arara a dalilin rashin waiwaye Haleesa da ka yi Yakamata ace ka danne duk wata k'iyayya da ka ke yi mata saboda saura d'a k'ank'ani lokacin ta zama mallaki ka in tashigo gidanka kana da iko yi mata duk abunda ka ga dama ba bai hanaka saboda ikonka ce.
Habeeb yadage gira sama yana duban Bala cike da gansuwa da kalaman Bala yasaki tsadade murmushinsa mai narkar da Zuciyar 'yan mata
Haleesa nagani Bala na musu-musu da baki da alama magiya ya ke yi wa Habeeb haushi ya turnuk'e ta ta juya cikin gida tana shigawo ta ci karo da Ammi sai kawai tace Ammi Key's d'in d'akin yaya Salman za ki bani batare da Ammi tace da ita komai ba tashiga d'aki tadauko mata Key's ta mik'a mata a sanyaye Haleesa tak'ara juyawa k'ofar gida tana fita taci karo da su a bakin k'ofar shigowa Zaure ba shiri ta taka birki had'e da sunkuyar da kai Kallo d'aya Habeeb Lamido ya yi mata ya d'auke kai tsawon "5-6 minutes suka dauka a tsaye daga bisani Haleesa tanufi d'akin yaya salman ta bud'e k'ofa tajuya batare da ta bari sun had'a ido tace "Bissimillah! Banza Habeeb ya yi kamar bai ji abunda tafad'a "Bala yace Boss ka k'arasa daga ciki bara na je na fito da kayan da ke cikin mota Wani tsuke baki Habeeb ya yi kamar mai tsotsa "Sweet ko mai shiri d'aukar selfie ya yi kici-kici da fuska, yajuya ya kalle d'akin yaya Salman Wanda tuni Haleesa ta tsofa a ciki tana jiranshi ya ta6e baki yanufi d'akin batare da yacire "cover shoe d'in k'afarsa kawai yadanna kai Haleesa na Zaune akan kujerar roba kanta na sunkuye tana wasa da yatsu hannunta ''Ba don sani daraja da sallama da ke ita a musulunci da ba yadda za'a yi ya yi mata sallama"
"Assalamu Alaikum" yafad'a chan k'asan mak'oshi''
"Batare da Haleesa tad'ago kanta ta amsa mai masa da cewa "Wa'alaikum sallam warahmatullahi wabarakatih...''
Habeeb ya kya6e baki a zuciyarshi yace ka ji su  Al-Sheikh za ki yabawa aya zak'i ta in kika shigo hannuna 'ya nema mai kai Kamar dunk'ule "cabbage' ya ja ya yi tsaye Haleesa bata ce da shi ga wurin zama hakan ne yasa yacigaba da zance zuci tana nufi bara tace na zauna ba amma bara naga iya gudun ruwanta kafin na wanke mata allonta saboda naga kanta na hayak'i.
A fakace Haleesa tad'ago ta sace kallonshi yana nan tsaye k'ikan hannaye shi zube cikin aljihu wandoshi da sauri ta d'auke kai a zuciyata tace tofah wata sabuwa inji 'yan caca shi wannan mai tsawo kamar fol waya yana nufi bai ga wurin zama bane ko kuma duk cikin, salon tsabar kwarewa da wulak'anci ne amma bara nace ya zauna a karo na biyu da tasake d'agowa amma bata dube shi ba tace "please have a seat''
Zaro ido ya yi daga bisani ya gyatsine fuska kamar ya ga "cockroach a zuciyarshi yace "Humm! I can't believe this Illiterate girl she known how to speak English''
Ya dube kujera da ta nuna masa da yatsanta akwai tazara tsakaninta da wance ta ke Zaune yafito da "handkerchief fari kal daga gaban aljihu "black colour coat d'in da yake sanye da ita ya shinfid'a akan kujerar sannan ya zauna ya yi crossing legs nashi yafito da "phone in shi yafara buga "game in crush candy''
Haleesa ta cika ta yi dam! Me wannan mutumin yake nufi me ye laifinshi Haleesa ke yakamata ki fara gaida shi abunda d'ayan 6angare Zuciyata yace da ita kenan......."ina Wuni yaya Habeeb"? tafad'a cikin sark'ewa harafi"
"Ignoring nata ya yi saida d'auke almost 3-4 minutes sannan yace da ban Wuni ba kya gani saida ya furzar da zazzafa iska yacigaba da cewa ke! Wai me yasa a duk lokacin da na zo gidanku sai kin yi "Wasting time in na"?
Numfashi da Haleesa ta sauke yafi a kirga da kyar ta iya controlling in "temperature' ta Co's wannan karo guy nan yakawo ta k'ul tace am sorry Yaya Habeeb wallahi.....
"Shut up please don't give me that fucking excuse yak'arasa magana had'e da cigaba da buga game in shi girgiza kai Haleesa ta yi cike da takaici tafara zance zuci na Shiga uku ni Haleesa wannan wane irin aure ne zan yi"?
"Very slowly yafara magana Kin d'auki kanki Wata tsiya sai kace ana sonki sai wani jiji da kai kike ko kin manta kina gaban Habeeb Lamido ne Wanda ba ya gajiya da furta miki kalma ```Tsana``` amma da yake ke Heartless ce har Wani Jan aji kike yi na kuma San duk wannan abu da kike yi kina yi ne don ki burgeni ni mutum ne kaifi d'aya ban ta6a sauya ra'ayi na musanmman akan abunda nace banaso don karki yi tsanmani in na aure ki wata rana za ki same gur6i a zuciyata tun daga lokacin da kika shigo rayuwata na nemi farin cikina narasa bana sonki wallahi na tsane ki tsanar da bara ta6a gushewa daga Zuciyata yak'are magana had'e da Murmushi.
Tun lokacin da yafara magana kai Haleesa yana sunk'unye a k'asa hawaye na bi kumatu ta, Habeeb ya mik'e tsaye hannunshi guda yana ciki aljihu yanufi inda Haleesa take Zaune daf da ita ya tsaye yad'an rankwafa yace ke!
A firgice ta d'ago tasauke ganinta akan fuskarshi k'asa jure kallon tsanar da yakeyi mata ta yi ta sada kanta k'asa.
Murmushi jin dad'i Habeeb yasaki sakamako hawaye da yagani akan fuskar Haleesa yace you hears all what's am saying right"?
K'asa magana ta yi kawai tad'aga masa kai cikin isa da tak'ama yacigaba da cewa "Don't you think is too early ace kin fara zubar da hawaye ki"?
"Is better ki share hawaye ki saboda bai kamata kifara zubar da su tun yanzu domin ina da buk'ata su a gida na  Haleesa tacigaba da share hawaye ta masu masifar Zafi da k'ona Zuciya.
"Habeeb ya ja tsoki had'e da cewa kina da aiki yarinya ya yi dialling number Bala yak'ara a kunnenshi "Hello! Bala wai me kike yi ne da har Yanzu ba ka k'araso ba"?
"Boss ina k'ofar gida nufina na dan ba Ku wuri za ka fi jin dad'i sakewa Ku sha fira
Kai! Banaso shirme banza da Wofi na baka _3 minutes_ ka shigo ko nayi maka abunda ba kayi tunani ba yana k'are magana ya yi hanging up"
Haleesa ta sa gefen hijab d'inta ta goge hawaye ta "Bala yashigo had'e da sallama yadire wani k'aton kwali had'e da farar Leda Habeeb ya dube Bala yace na ba ka "5 minutes kayi Mata bayani abunda ke ciki ni ina k'ofar gida kuma karka sake ka wuce time d'in na ba ka yaficewar shi batare da ya dube inda Haleesa take Zaune.
Bala yace ranki yadad'e dama "invitation card's ne mu kawo miki ga kuma waya nan akwai sim card a ciki had'e da numbers in "boss duk abunda Ku ke buk'ata Ke da k'awaye ki a lokacin biki sai ki kira "boss gobe insha Allah Zan zo na fita da Ke  'kawayeki Ku kai wa 'yan uwa da abokai arziki katin gaiyyata Har Bala yadasa aya a zance shi Haleesa bata ce komai ba gani ta yi shiru yasa yace ranki yadad'e kin yi shiru ba ki ce komai ba"?
Saida tasauke Numfashi daga bisani tace Zai fi kyau kayi min Saving digit naka domin bana tunani zan iya "calling d'in wani''
"Bala d'an murmusa yafito da Biro daga gaban aljihu shi ya rubuta digit dinshi akan kwalin da yashigo da shi ya yi mata sallama yafice.
Saida Haleesa ta share tsawon "10 minutes kafin tashiga cikin gida kaitsaye tashiga d'akin Ammi ta ajiye kwalin hannunta bata ce da Ammi komai ba ta nufi d'akinta.

```WASHE GARI ```

Tun misali k'arfe 10:30am Bala ya zo yadauki Haleesa da k'awaye ta suka tafi raba "invitation saida suka share kwana ki 3 suna raba invitation tun safe in suka fita sai da yamma lis suke dawowa.

```ON TUESDAY ```

Ita ce ranar da aka fara gudanar da shagalin biki kamu za'a yi a gidan Aunty Juwairiyya  tun daga Lagos Madam Hindu ta yo "Booking d'in Aunty funke da yaranta suka k'awata gidan Aunty Juwairiyya da "Decoration yayinda Aunty funke za ta yi wa Amarya Haleesa Makeover tun lokacin da Haleesa tashiga "bathroom da suna wanka ta rufe k'ofa tun Aunty funke tana saka ranta fitowar ta har tagaji da jira tafito daga bedroom ta nufi parlour wurin Aunty Juwairiyya ta Fad'a mata abunda ke faruwa a harzuk'e Aunty Juwairiyya tanufi bedroom d'in tadinga knocking in k'ofar had'e da kiran sunan Haleesa shiru kamar ba mai rai a ciki Haleesa da ke Zaune dirshan a tiles d'in bathroom tasaka kanta tsakiyar cinyoyinta sai faman shashekar kuka take bata tunani akwai Wanda ya isa yasaka ta ta bud'e k'ofar nan har sai sun gama shirme su, jin yadda Aunty Juwairiyya take duka k'ofa yasa Haleesa tace Aunty ki daina wahalarda kanki bara ta6a bud'e k'ofar nan har sai kun gama shagalin bikinku.
Cikin 6aci rai Aunty Juwairiyya tace a gidan uban wa Haleesa kika ta6a gani anyi kamu ba Amarya"?
"Daga yau za'a fara a kaina Haleesa tafad'a had'e da murgud'a baki...


Jeeddah Aliyu
[30/12 8:20 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```59```

_Narasa kalma da zan yi amfani da ita wurin gode miki Fatima Umar{Mrs Umar} akan irin d'ibin son da kike yi wa wannan littafi na Ni da yaya Habeeb ina miki fatar alkhairi a rayuwarki Allah yasaka miki da gidan aljanna Firdausi "I really appreciated Fatee naa_


A wulank'ance yake kallon kayan daga bisani ya ja tsoki kamar zai gutsire halshenshi, Cike da takaici ya fad'a bisa kujera yadafe goshi kallon d'aya Hannah ta yi mishi ta tabe baki ta janyo wata 'yar 'karama kitt ta shigar da "Code kitt d'in ya bud'e tafito da "Necklaces na Gold cikin Yanayi na rashin damuwa da halin da yake ciki ta mik'a masa kitt d'in had'e da cewa yaya Habeeb ga Gold's d'in da mom ta siyawa Amaryarka na tabbata kai ma za ka yaba da za6i Aunty Mami a maimakon ya kar6i kitt d'in sai kawai yasa hannu ya bugeta tafad'a kan ciyoyin Hannah idanu ta zuba masa ta girgiza Kai dama tasan za'a yi haka ta ya ya kamar yaya Habeeb Wanda idanushi suka gama bud'ewa mom ta za6a mishi mata don kawai Yaya Habeeb yana da biyayya Sam bayaso b'aci rai Mom duk abunda tace tanaso koda shi d'in bayaso a dalilin Mom zai ce yanaso abun ba don ranshi yanaso ba kenan ya amince da aure Haleesa saboda mom lallai kuwa da saura rina a kaba gani yadda Hannah ta tsare shi da ido yasa yajuya wurin Asabe da yarinye yadaka musu tsawa kai! Ku bar nan jiki na rawa suka fice saida ya share tsawon "5 minutes yana dafe da goshi daga bisani yafara magana kamar mai rad'a Hannah banaso yarinya nan shiyasa bana farin ciki da wannan aure Kinga kenan bai kamata Mom ta dinga 6anata kud'inta akan abunda bana farin ciki da shi azahari gaskiya Hannah banaso yarinya nan ina mata tsanar da fatar bakina bara ta iya misalta ta, wannan ya zama "sirri a tsakaninmu Co's banaso Mom tasani yana k'arasa magana ya koma yalafe a jikin kujera.
"Hannah ta mik'e ta zauna bisa hannu kujera da ya ke kai cikin sanyi murya tace, ni a ganina yaya Habeeb Haleesa batada matsala kyakyawa tarbiyya da take da ita yajanyo hankali Mom har ta yi maka sha'awarta, ka jira har ta shigo gidanka na tabbata za ka so ta har ta dasa aya a zanceta ya na mata kallon hadari kaji kin gama yafad'a a yatsine"?"Cike da gansuwa Hannah tad'aga masa kai saida ya ja tsoki sannan yace  ba abunda yashafe ni da tarbiyyarta, domin tsanarta ta dusashe duk Wani abu da yake tare da ita duk lokacin da na tuna cewa saura "2 weeks yarinya nan ta kasance matata sai naji na K'ara tsanarta bana tunani zan ta6a sonta.
Shiru Hannah ta yi tana kallonshi daga bisani tace Yaya Habeeb "So baya kwakwasa k'ofa kafin yashiga zuciyar d'a Adam ba kai ka keda iko da zuciyarka ballatana ka yanke hukunci shawara da zan baka ka sausauta wannan tsanar da ka ke yi mata kada rashe ya juye da mujiya "Habeeb ya yi murmushi had'e da Shafa sumar kanshi yace na fahimce cewa Hannah bakida hankali
Turo baki ta yi had'e da cewa ni ce banida hankali"?
Kwarai kuwa da kinada Hankali bara kifara tunani zan iya kamuwa da Son wannan  "Illiterate girl karki manta naga kyawawa mata kala daban-daban masu ilimi da kyakyawa sura da Kansu suke kawo talla Kansu agareni ko kallo ba su ishe ni, ni Habeeb Lamido ace zan so "Illiterate ya kyabe baki had'e da yatsine fuska "never.
Hannah ta zaro ido har da su tafa hannu kai yaya Habeeb wannan sharri har ina "last year Haleesa ta gama secondary school ta kuma haddace Al-qur'ani shine za ka kira ta da "Illiterate
Habeeb ya tabe baki yakasa Furta komai daga bisani ya mik'e tsaye hannaye shi zube cikin aljihu wando shi yace Hannah mu je ki rakani unguwa saboda na gaji da sauraro wannan surutu naki.
"Cikin Zumud'i Hannah ta mik'e ina za mu je yaya Habeeb"?
Ba ruwanki da inda za. Mu je murad'i kawai ki d'auko mayafinki ki sameni a parking space ina jiranki batare da yajira jin abunda za tace yafice.

```HALEESA```

Haleesa kwance a d'akinta photo Marigayi  yaya Habeeb manne a k'irjinta sirirai hawaye na fita ta gefe da gefen idonta ta yi nisa sosai a tunani rayuwarsu ta shagaltu iya shagaltuwa Sam bata ji motsin shigowar Aunty Juwairiyya wance ke tsaye rik'e da "curtain d'in k'ofa tana mata kallon tausayi sake la6ulle ta yi tak'arso ta zauna a gefen katifa a hankali ta d'ora hannaye ta a k'afafun Haleesa a firgici tad'ago ganin wance bata yi zato gani ba yasa ta mik'e zaune da sauri ta share hawaye da tafin hannu muryarta na rawa tace sannu da zuwa Aunty Juwairiyya saukar yaushe"?
Hannuta Aunty Juwairiyya ta rik'o a sanyaye tace yanzu nan daga "Airport kaitsaye nan driver ya ajiye ni ban ga kinfito kin yi min oyoyo na tambaye Ammi kina ina sai tace da ni kina d'aki a kwanaki nan tarasa gane kanki"
Haleesa ta sada kai k'asa tana kallon hannuta da ke sark'e da na Aunty Juwairiyya hawaye da take k'ok'ari boyewa suka zu6o akan hannun Aunty Juwairiyya a d'imauce Aunty Juwairiyya tad'ago fuskarta Haleesa! Shiru Haleesa ta yi bata amsa ba Haleesa! Aunty Juwairiyya tak'ara kiran sunan nata
"A wannan karo ta amsa da cewa Na'am"
Wannan wace irin rayuwa ce kika za6awa kanki shin me yasa har izuwa yanzu kika k'asa raba zuciyarki da soyayya yaya Habeeb"?
Bata jira amsar da Haleesa za ta bata tacigaba da cewa Haleesa Wanda ya mutu ba ya dawowa ballatana ki saka aranki cewa wata rana Yaya Habeeb zai dawo gareki hankuri za ki yi ki cigaba da yi masa addu'a ki tuna Haleesa aure za ki yi gidan wani za ki tafi, kinga kenan ko ta karfi tsiya ne dole ki manta da yaya Habeeb ki yi yak'i da zuciyarki tafitar da soyayya Yaya Habeeb Karki manta inna mairo ita ce ta yi kayan cikin Habeeb wata Tara da kwana tara tasha zafi da rad'ad'i nak'uda shi ta haife shi ta bashi kyakyawa kulawa har ya kai muzali girma ya zama abun sha'awa har kika ganshi kika bashi babban matsayi da shi a zuciyarki duk duniya babu Wanda yafi Uwa son d'ata amma ta hakura da rashinsa domin tasan cewa Ubangiji da yabata shi a lokacin da yaga dama shi yakar6i abinsa ke Haleesa me yasa bara ki hank'ura ba"?
 Ki yi gaggawa  yak'i da  zuciyarki tun kafin ta raunata miki imani ki in har ban yi kuskure a lissafi na yau wata 7 har da Sati biyu da rasuwa yaya Habeeb amma ke a kullum mutuwar shi sabuwa take zame miki wannan wane irin rayuwa ne"?
Ki sani aure ba abun wasa bane muddin kika ce irin wannan rayuwa za ki gudanar a gidan mijinki bara ki ta6a Jin dad'i.
Haleesa tafashe da kuka tafad'a jikin Aunty Juwairiyya ta k'ank'ame ta cikin shassheka kuka tace ban yi kaina bane Aunty Juwairiyya zuciyata tace takasa hank'ura da soyayya yaya Habeeb, amma insha Allah zan yi k'ok'ari na danne duk wani abu da nakeji akan yaya Habeeb Aunty Juwairiyya ta d'agota had'e da cewa oya share hawaye ki banaso na k'ara gani idanu ki da hawaye kinji koh"?
Haleesa ta yi murmushi ta bi umurni  Aunty Juwairiyya ta hanyar share hawayeta Aunty Juwairiyya na rik'e da hannuta suka fito d'akin Ammi suka shiga anan Haleesa takeji Juwairiyya da Ammi suna zance lefenta da dangin Habeeb Lamido za su kawo da Yamma Haleesa tadafe k'irji tasoma Zance zuci shikenan ba makawa na yi kusa zama mallaki Habeeb Lamido.

```5:30pm```

Tsadad'i Motoci ne ke ta fama parking a k'ofar gidan Malam Usman mai kifi kallon d'aya za ka yi wa motoci, kagano mamallaka motoci sun ci sun sha sun tada kai da Naira Kaitsaye mata suka dinga fitowa daga ciki motoci suna shiga gidan Malam Usman mai kifi daga bisani Wasu kartti majiya k'arfi suka fito da ratsatsu trolley's suna shiga cikin gidan dangin Haleesa sai faman karama b'akin nasu sukeyi ta hanyar nuna musu wurin zama, a hankad'e Hajiya khareema take kallon Mutane gidan da kyar ta dosana duwawu ta akan farar kujera roba ta zunguri Hajiya batula matar k'anin Mahaifin Habeeb ta Wani yatsine fuska had'e da cewa Hajiya batula ta ya ni figa Saida Hajiya Batula ta kya6e baki daga bisani tace Uwar miji ta Zama kaza anyya kuwa Madam Hindu tana ciki haiyyaci ta da ta amince Habeeb ya aure 'yar Matsiyata ni da naga Wannan uban lefe na yi tsanmani 'yar Governor ko 'yar Minister ce yake nema ashe 'yar gidan babu ce Wannan ae asara ce da rashin sanin zafin kud'i
"Bari kawai Hajiya Batula tun lokacin da muka tunk'aro unguwar nan bak'i ciki da takaici suke nuk'urkusa zuciyata Jin nakeyi kamar na hadiye zuciya na mutu don takaici ba rok'a da ban yi wa Madam Hindu ta tilaswa Habeeb ya aure Maryam ta Maye gurbi marigayiya Salma Amma 'yar mata nan ta yi biris da  buk'ata ta ke in tak'aita miki labari sai cewa ta yi ita bara ta yi wa  ta d'a aure dole kinga ba ta yi masa dole ba shi kuma ya kwaso mata 'yar Matsiyata duk abunda suke fad'a akan kunnen inna mairo gani abun naso ba mai k'arewa bane ta mik'e tsanm tabar musu wuri.
Bayan dangin Habeeb da na Haleesa sun gaisa a tsakaninsu daga bisani dangin Habeeb suka gabatarda da abunda ke tafe da su yayinda dangin Haleesa sukayi musu sha tara na arziki suka baro gidansu Haleesa cike da Murna irin karamawa da akayi Musu sa6ani Hajiya khareema da ta dawo da mummuna k'udiri ko ta Wane sai tashigar da 'yar ta gidan Habeeb.

```8:30pm```
Aunty Juwairiyya da Zainab zaune a d'akin Ammi sun tusa lefen Haleesa gaba suna kallon sai faman santi da yaba kayan suke yi sa6ani Haleesa da ke kwance rub da ciki akan gadon Ammi ita ba kuka take yi ba amma a yadda takeji Zuciyarta na tarfafasa gwara ta yi kuka ko za ta same sausauci k'unci da take ciki babban bak'i cikinta bai wuce yadda Mutane Unguwa har ma da na cikin gidansu suke zuzuta kayan lefe ta basu San cewa a wurinta atamfar super prints ta fiye mata tarin kayanan Zainab tace Haleesa bara ki sauko ki taya mu ganin wannan abun arziki ko kunya kike ji kada Ammi tace bakida kunya tak'arasa magana cikin tsokana
"Cikin zafin rai Haleesa ta diro k'asa ta tsalleke kayan tafice Zainab da Aunty Juwairiyya suka bi ta da kallon, girgiza kai Aunty Juwairiyya tayi tana mamaki tauri kai da kafiya irinta Haleesa.

```1 WEEK LATER ```

Tuni gidaje biyu sun fara gudanar da tsare- tsare yadda bikin aure 'ya'ya su zai gudana tsawon wannan lokacin Habeeb da Haleesa ba su k'ara gani Junansu.
Haleesa na zaune bisa kujera 'yar tsuguno a tsikiyar gida tana yanka alayahu almajiri ya yi sallama Haleesa ta amsa masa yace wani mai mota yana sallama da Haleesa a k'ofar gida, ras gaban Haleesa yafad'i nan take annuri da ke kan fuskar ta ya gushe  tace je kace batanan
Ammi ta lek'o daga cikin kitchen ta ce je ki kace gatanan zuwa tajuya wurin da Haleesa take zaune ta galla mata harara had'e da cewa me kike Jira ne da bara ki tashi ba da sauri Haleesa ta mik'e ta jefar da wuk'a hannunta Ta Shiga D'aki tasaka Hijab tafito fuskarta ahad'e tanufi k'ofar gida dafe k'irji Haleesa ta yi sakamako motar Habeeb Lamido da ta ganin nan take Numfashinta yafara kai da kawo ta runtsi idanuta...


 Jeeddah Aliyu
[30/12 8:24 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```Dedicated```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```58```

Da ina da yadda zan yi da na raba kaina da wannan aure nayi danasani amincewa da aure Habeeb Lamido domin shi kanshi uban gaiyya ashirye yake da, ya musgunawa rayuwa ta ga kuma wad'annan masifafu 'yan mata nashi na tabbata suma za su ba shi gudumuwa hanani kwanciya hankali"
Zainab ta yi ajiyar zuciya had'e da furta bai kamata ki yi sauri karaya da wuri haka dama rayuwa tagaji haka kowane d'a Adam da jaranta da Allah yake jarabba shi da ita ke kuma taki jarabba ce ta zo da haka kuma ni ganina Habeeb bashida Matsala kawai dai don kin k'ulace shi ne akan abunda yata6a wakana a tsakaninku ki yi La'akari Haleesa tun yaya Habeeb yana duniya Allah ya had'a ki da Habeeb Lamido daga wannan lokacin har izuwa yanzu tunanishi bai ta6a gushewa a tare da ke, shin wannan kadai bai isa ya haska miki cewa akwai 6oyayye sirri a tare da shi"?
Shiru Haleesa ta yi tasoma lallu6e amsar da za ta furtawa Zainab iya lallu6e ta takasa lallu6o amsar wannan tambaya hakan ne ya ba Zainab damar cigaba da magana "why are you silent Haleesa answer my question please"
" I don't have anything to say Co's am totally confused Haleesa tafad'a da alama akwai firgitarwa a tare da ita
Zainab ta yi murmushi tace a rayuwarki kin tsani zuwa wani gari amma kuma sai kika tsince kanki da son tafiya Lagos, shin ko kinsan dalilin da yasa zuciyarki ta azzalzale ki da ki tafi Lagos"?
Girgiza kai Haleesa ta yi Zainab ta rik'o hannunta saboda ki had'u da Habeeb Lamido Allah ya nufi cewa yaya Habeeb ba mijinki bane shiyasa yad'auke shi ya musaya miki da Habeeb Lamido wannan shi ake kira tun ran gini tun ran Zane ki lallashi zuciyarki ta amince da za6in Allah domin Habeeb Lamido za6in Allah ne.
Haleesa ta sauke ajiyar zuciya tace bara ki ta6a gane abunda nake nufi saboda ke kallon mutumi kirki kike yi masa alhali, banta6a gani tantiri d'a iska maras tausayi da imani irinshi shiyasa duk lokacin da na ci karo da shi sai na tsinci kaina da fargaba had'e da tsanani tsoro  shi, ke ni fa na tsane shi tak'arasa magana had'e da kya6e baki "Zainab ta yi galala da baki tana kallon Haleesa fuskarta cike da mamaki kalamanta k'asa hank'uri ta yi har saida ta furta abunda ke ranta amma wallahi Haleesa bakida kirki mijinki kika kira da d'a iska"?
Haleesa ta kalleta ranta a 6ace tace ni mijina ya rasu matuk'ar ki naso na cigaba da da kallonki a matsayin 'yar uwata mai son farin cikina karki k'ara kiran Habeeb Lamido da suna mijina.
"Zainab ta girgiza Kai had'e da cewa lallai kuwa yarinya kina da aiki domin bakin alk'alami ya bushe yafi alkhairi a tare da ke ki jajirce ki fatattaki soyayyar Habeeb daga zuciyarki ki cike gur6inta da ta Habeeb Lamido domin kuwa yaya Habeeb ya zama "past Habeeb Lamido shine "presently ki daina yaudara kanki saboda ba'a soyayya da matace.
Cike da jin haushi Haleesa ta fisge Jakkarta daga hannun zainab tace, har abada ba zan ta6a daina son yaya Habeeb karki manta tun ban mallaki hankalin kaina ya Karantar da ni me kalma "SO" take nufi ya shayar da ni zak'i had'e da d'add'ano da ke ciki ta ya ya kike tsanmani zuciyarta za ta dusashe tauraro sonshi har ta cike gur6inshi da wani' wani ma mutumin da yafi kowa tsanata zan aure Habeeb Lamido ne saboda mahaifiyarshi ba wai don yanada matsayi a zuciyata na riga na sadaukarwa yaya Habeeb da zuciyata kuma har abada ba Zan ta6a sauyawa ba tana k'arasa magana ta wuce fuuuu! Cikin fushi ta nufi gidansu tabar zainab tsaye bud'e da baki Girgiza kai Zainab ta yi cike da tausayi Haleesa tanufi gida ita kan bata ta6a gani, soyayya irin wannan ba yaya Habeeb ya mutu amma Haleesa bata fasa nuna masa zazzzafa "so ba.

```8:40pm```
Haleesa na zaune a tsakiyar gida tasaka kwano tuwonta gaba tana kallo hawaye suka zu6o mata tasanya bayan hannunta ta goge, duk lokacin da ta zo cin abinci sai ta tuna da yaya Habeeb sai taga kamar zai shigo su ci abinci tare kamar yadda suka saba haka za ta k'arasa zamanta daga karshe ta tsallake abinci ranar saidai ta kwana da yunwa musanman a wannan lokacin da ta ga iyayyeta na ta faman shirye-shirye bikin aure ta kawai mutuwa yaya Habeeb tadawo mata sabuwa tarasa sukuni bata da aiki yi da yawuce kuka, ga tsanani tsoro had'e da fargaba wannan aure Wanda ta tabbata za ta yi shine ba don zuciyar da gangar jikinta naso ba, batasan lokacin da ta rushe da matsananci kuka mai cike da zallan tausayi da karya zuciya mai sauraro, da gudu Ammi tafito daga d'aki zaninta a hannu tanufi wurin da Haleesa take zaune ta saka kanta  tsakiyar cinyoyinta tana kuka mai tsuma zuciya.
"Subhanalillahi! Haleesa me ke faruwa me kike yi ma kuka"?
Har Ammi ta gama watsa mata wad'annan tambayoyi bata d'ago ba bata kuma fasa kukanta ba "Ammi ta durk'usa gabanta ta d'ago fuskarta Haleesa karki 6oye mini abunda yake damunki domin ni mahaifiyarki ce ni na fi cancanta da nasan matsalarki 6oye mini abunda ke damunki zai iya haddasa miki gaggaruma matsala domin a wannan shekaru naki bara ki iya magance matsalarki ke kadai dole kina da buk'atar mai ba ki shawara don haka fad'a min me ke faruwa ne"?
Me ye musanbabin kukanki"?
Saida ta shar6e hawaye had'e da fayyace majina da hannunta, cikin murya mai matuk'ar ban tausayi tafara magana Ammi zuciyata takasa hank'ura da soyayya yaya Habeeb a kullum sonshi k'ara yad'uwa yake yi a zuciyata sai naji mutuwa tadawo mini sabuwa sai naji a jikina tamkar zai dawo a gareni tabbas nasan ba'a mutuwa a dawo to amma me yasa sonshi yake k'ara samu muhalli a zuciyata"? tak'arasa magana cikin shasshekar kuka
"Idanu Ammi suka ciko da hawaye cike da tausayi 'yata ta tace Haleesa tsakaninki da Habeebu "so da shak'uwa ne shiyasa har yanzu sonshi ya kasa barin zuciyarki dama ace so ne kadai a tsakaninku na tabbata, da yanzu kin fara sabawa da rashinsa amma wannan shak'uwa da take tsakaninku ita ce take neman kassara zuciya da lafiyar jikinki Ki yi hank'uri Haleesa ki rinjaye zuciyarki ta manta da Habeebu saboda aure za ki yi babu namijin da zai jure ganin matarshi tana begen wani, bara Ku ta6a samun zaman lafiya a tsakaninku ina ji a jikina Haleesa kamar matsalarki ta zo karshe shigowa wannan Habeebu a rayuwarki sai nake ganin tamkar Habeebunki ne yadawo  hankuri da tawakkali sune jigo na rayuwa duk wani d'a Adam mai imani, ubangiji da yabamu Habeebu shi ya kar6i kayansa ya kuma dube halin da kike ciki yakawo miki wannan Habeebu, ki godewa Allah kada ki zama d'aya daga cikin bayi da yake yi wa kyauta su budulce masa.
"Haleesa ta'kara fashewa da kuka tafad'a jikin Ammi tace Ammi narasa yadda zan yi da son yaya Habeeb wallahi ba laifi na bane, Ammi sonshi ne yakasa bari zuciyata ki taimake ni Ammi ki yi mini addu'a "Allah ya sausauta mini wannan masifa ni kaina ina so nayi rayuwar farin ciki tamkar yadda nake ada.
A hankali Ammi take bubbuga bayanta tace addu'a a kullum cikin yi miki ita na ke ,zan koma aike kamal wurin malam shu'iabu mai almajirai ya kar6o miki rubutu ki dinga sha kafin a fara gudanar da bikinan ina jin tsoro kada mutane su ankara da halin da kike ciki su fassara mu bai bai ace mu yi miki auren dole da d'a masu kud'i kinsan wannan zamani mutane basa gadonka amma suna gadon maganarka yi maza ki share hawayeki ki ci tuwonki kinji 'yar albarka"?
"Haleesa ta girgiza kai tace na k'oshi fura zan sha Ammi"
Ammi tad'ago ta had'e da mik'arda da ita tsaye tace mu je d'akin akwai ragowar ta baffanki ki sha.

```3:30am```
Tsakiyar dare ne ba ka ji komai sai sauti kukan tsutsaye da haushe karnuka a dai-dai wannan lokacin Habeeb Lamido yana kwance akan katafare "Royal bed" d'inshi ya yi"pillow da hannayeshi yana sharar bacci a cikin bacci nashi yafara mafalki Haleesa yana kwance a cikin ciyawa Kore shar {grass carpet} yana "game a phone d'inshi ya shak'i k'amshin turare "musk Al-ghazal" ya lumshe idanu shi daga bisani ya bud'e su yad'aga kanshi ya dube ta tana tsaye fuskarta d'auke da murmushi a hankali yasauke kwaryar idonshi akan tufafin jikinta mini skeet" iya cinyoyinta sai wata "yar yaloluwa "top ita da babu duk d'aya saboda ana hango duk wata sura ta jikinta gashin kanta yasha gyara sai kyalli da d'aukar ido yakeyi ya hadiye yawu yana lumlumshe idanu kasa hanukri yayi da sauri yafisgota tafad'a jikinshi yasa hannyeshi ya yi hugging nata tightly ya ya juyarda ita suna facing in juna yad'ago fuskarta ya had'e Goshinsu a wurin d'aya a hankali yake goga hancinshi akan nata ya lalube bakinta ya had'e da nashi yana tsotsa da k'arfi ta ture shi ta mik'e tsaye had'e da yi masa gwalo cikin zafin nama yakai mata chafka ya yi nassara damk'e hannunta tasaki d'a k'aramin ihu yadauke ta chak yanufi cikin gida da ita kaitsaye yanufi bedroom yajefa ta bisa bed yasoma "romance in ta har ya yi nassara rabata da kayan jikinta kaitsaye ya tsallaka border a firgice Habeeb ya falka daga mummuna mafalkinshi ya mik'e zaune yadafe goshinshi ya jik'e sharkaf da gumi Ya mik'a hannu ya yi "switch on d'in bedside lamp haske ya guraye d'akin yadauki remote control na Ac yak'ara gudun Ac a hankali brain in shi yafara yi mishi "backwards in nightmare d'in ya yi a baiyane yace "No I can't believe wannan wane irin mafalki ne"? narasa mafalki da zan yi sai wannan "can you imagine ni Habeeb Lamido na sadu da wannan "Illiterate nan take yafara tunawa da zafafa "Peck d'in da yadinga bata duk wani lungu da sak'o na bakinta saida ya tsotsi wani irin tashin zuciya ya turnuk'e shi take yafara jin "vomited yadaka tsalle Yadira k'asa ya afka bathroom yasoma zuba d'a uban Amai tamkar zai amayarda 'yan hanjinshi, yana gama Amai yad'auki "brush ya matsa "Toothpaste yadinga tarzar bakinshi yafesa"mouth spray yafi kala uku daga bisani ya kwabe "pajamas d'in jikinshi yadaura towel yatuna cewa yanzu fa wanka "Janaba ya hau kanshi wani dogon tsoki ya ja zuciyarshi cike da haushi mai d'auke da tsan-tsan tsanar Haleesa yafara tsalkakake jikinshi yana fitowa daga bathroom ana fara kiran farko na sallah asuba farar jallabiya sanya yanemi gefen bed ya zauna ya rafka tagumi Yana zance zuci wallahi sai na wulak'anta yarinya nan sai ta yi regretting na had'a "odour body in ta da ni ya ja tsoki wani b'angare na zucyarshi yace "c'mon Habeeb wannan fa abu 'it's just a dream" yasaki ajiyar zuciya had'e da furzarda zazzafa iska daga bakinshi yace "thank God amma duk da haka sai nayi "warning nata kada ta kuskure tak'ara zuwa mini a mafalki ta wannan sigar jin Ladam ya kwatsama kiran sallah na biyu yasa ya mik'e cikin hamzari yanufi masallaci.

```WASHE GARI ```
"Around _10:30am_ Habeeb yatashi daga bacci Ya yi mik'a had'e da doguwar hamma ya zuro santala-santalan farare k'afafushi k'asa cike da kasala yanufi bathroom yacire jallabiya jikinshi ya rage daga shi sai boxer yacika bathud da ruwa ya zuba  bubbles bath saida ya yi switch on d'in katuwar plasma TV da ke manne da bangon bathroom d'in sannan yacire boxer in jikinshi ya yi flagging da shi yashige ciki bathud yana wanka idanushi na bisa akwati talabiji tsawon "1- Half hour ya share yana wanka sai kace Wanda zai sauye "colour skin d'inshi yana gama wanka ya yi switch of d'in TV yasanya bathrope yafito daga bathroom in yanufi k'aton "dressing mirror mai d'auke da tarin designer d'in turaruka da tsadad'i body lotion yadauke d'aya daga cikin lotion d'in yashafe jikinshi ya sharce sumar kanshi da comb yasanya" black colour suit da shirt dark purple colour yadaure wuyan shi purple colour necktie ya fesa favorite perfume in shi "intense man ya kwashe phone's d'in shi da ke zube akan bedside drawer ya murd'a handle yafice yana shiga downstairs parlour ya hango Hannah zaune a k'asa 'yan gidan asabe da yarinye suna tayata arranging in kayan cikin wasu had'ad'u marrow colours trolley's yanemi d'aya daga cikin kujeri parlour ya zauna asabe da yarinye suka gaida shi ya amsa a dak'ile Hannah tada'go tace "Good morning bros"
"morning dear yafad'a had'e da d'aukar remote d'in TV ya rage "volume fuskar Hannah d'auke da murmushi tace yaya Habeeb ya ka ga kayanan"?
Tabe baki ya yi had'e da furta "Very expensive
Hannah ta washe hak'ora tace lefenka ne da Aunty Mami ta had'o a Dubai ba.....
"What's Habeeb yafad'a had'e da mik'e wa tsaye kamar Wanda kunama ta ciza yayinda babu shiri Hannah ta had'iye raguwar kalamanta Tsanani baci rai ya baiyana akan fuskarshi musanman da tuna da mafalki da ya yi da Haleesa...

 Jeeddah Aliyu
[30/12 8:29 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```Dedicated```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```59```

Ta wani kad'a kai kamar kadangarwa tace da kuwa har abada Hajiya ba zan ta6a mantawa da ke, a rayuwa ko a wance lokacin ni nafi cancanta yaya "Habeeb ya aura amma ya buge da aure aunty salma shi a dole baisan daraja da k'imar soyayya Dan Allah Hajiya ki yi duk yadda za ki yi na maye gur6in aunty salma a gidan yaya Habeeb "kin fi kowa sanin irin tsananin 'kuncin da nake ciki tun daga ranar da yaya Habeeb ya aure aunty salma har "Allah ya kar6i ranta ina fama da ciwon sonshi akan yaya Habeeb  zan iya salwatar da rayuwa ta, da sauri Hajiya khareema ta katsi mata hamzari ta hanyar cewa ki kwantar da hankalinki muddin ina numfashi sai Habeeb ya aure ki don ba zan zuba ido ina kallon ki ki k'are rayuwarki ba aure tunda kin riga kin sakawa ranki in ba Habeeb ba za ki rayuwa ba.
"Maryam tasaki ihu farin ciki had'e da k'ank'ame Hajiya khareema.

```HABEEB```

Habeeb na kwance bisa "three seater a katafare parlour madam Hindu hannunshi rik'e da "remote control madam Hindu tashigo parlour fuskarta d'auke da murmushi ta zauna akan kujera da ke "facing d'inshi "son dama inason ganinka dagane da zance gidan da Haleesa za ta zauna madam ta dakata da zanceta domin taji ta bakin Habeeb"
D'agowa ya yi ya tsurawa madam ido sai kace yau yafara ganinta daga bisani ya mayarda ganinshi wurin TV" madam ta yi murmushi saboda tasan halin d'a nata miskili ne na bugawa a jarida ba magana zai yi ba tacigaba da kallonshi can tace son wannan shine "right time da yakamata ka tare a sabon gidanka sabuwar Amarya a sabon gida tak'arasa magana tana murmushi yayinda Habeeb ya yi shiru zuciyarshi na tuk'uk'i don tsabar takaici jin yakeyi kamar ya hadiye zuciya, ko zai huta da zance da aure nan ya tsani zance Haleesa amma ita mom ba za ta gane ba ya yatashi zaune yana yatsina fuska yace "Mom gaskiya ni ban shirya zama a wannan gidan ba in fact ko "furniture's ba bu ciki kuma banida lokacin da zan yi odering nasu a yanzu Wani kallon madam ta watsa masa ta tabe baki banaso shirme banza Habeeb furniture's har wani Abu ne da za ka ce bakada "time na odering na su ka bud'e kunnenka da kyau ka saurare ni banaso dangin mahaifinka su San cewa, ni ce na nema maka aure Haleesa don haka ina gargad'inka da kada kasake kafito da alama da za ta nunawa duniya cewa Haleesa ba za6inka ba ce, ina fatar ka fahimce inda zance na yadosa"?
"Habeeb ya lumshe ido zuciyarshi cike da tsanar Haleesa ya gyad'a kai"
Cikin rashin kula da yanayi da yashiga madam tacigaba da cewa a matsayina na mahaifiyarka na umurce ka da gaugauta zuba duk wani abu da gidanka yake da bukata domin anan Haleesa za ta zauna kafin ka wuce da ita gidanka na Abuja.
'Dumm' Habeeb ya yi yana kallon madam da kyar ya iya sarafa halshe shi ya furta me kuma za ta je yi abuja"?
Harara madam ta galla masa had'e da cewa bansaniba sai kuma magana lefe kasan yanzu ne nake da tabbaci za ka yi aure saboda wance aure naka kai, kadai kayi kid'aka ka kuma taka rawarka a wurina yanzu ne za ka yi aure.
"Mamaki kalamai madam suka hana Habeeb magana sai fama musu-musu yake da baki k'iyayya Haleesa na 'Kara link'aya a zucyarshi gani mom ta mayarda hankalinta wurin TV hakan yabashi tabbaci cewa tagama maganarta ya numfasa ya lankwashe murya "sweetheart duk yadda kika tsara  banida matsala "I'm ready to obey your decision ya d'a numfasa yacigaba da cewa "next week zan tafi Japan na yi "Ordering duk wani abu da gidan yake da buk'ata yak'arasa magana kamar zai fashe da kuka.
"Madam ta yi murmushin jin dad'i kalaman Habeeb tace Allah ya yi maka albarka dama nasan bara ka ta6a bani kunya.
"Humm! Habeeb yafad'a had'e da murmushi yak'e a zuciyarshi ya k'udiri aniya sai ya k'auntatawa Haleesa sai ta gwanmace tak'are rayuwarta a "kirikiri prison" da ta rayuwa a gidanshi ya ajiye "remote d'in hannunshi ya mik'e yanufi k'ofar fita daga parlourn.


```HALEESA```

A dai-dai wannan lokacin Haleesa da zainab suka fito daga islamiyya suna tafiya suna fira, har sun yi kusa shiga unguwarsu wata mota "dark blue kirar Prado tasha gabansu had'e da taka wawa "brake ba k'aramin tsorata Haleesa da zainab su ka yi a lokacin d'aya k'ofofi motar suka bud'e Maryam da k'awarta zeely suka fito kowanesu yasha "black shade Haleesa da zainab suka dube juna fusk'ok'insu shinfid'e da mamaki zeely ce ta kawo karshen mamaki nasu ta hanyar furta wacece Haleesa a cikin Ku"?
Haleesa ta ji "rass-rass"! Gabanta ya yanke yafad'i ta zare ido tarasa kalma da za ta furta
 Zainab ta yi karaf tace lafiya Ku ke neman Haleesa"?
Sai kace had'in baki a lokacin d'aya suka zare "black shade d'in da ke lullu6e da kwayar idanusu Maryam ta aika musu wulak'antace kallo tace Ku! 'Ya'ya matsiyata za Ku amsa tambayar da aka yi mu Ku ne ko za Ku tsaye nuna halinku na 'ya'ya maula.
A fusace Haleesa tace ni ce Haleesa kuma ina shawartaki da ki saita kalamai ki domin duk wani rashin kunya da kike tak'ama da shi ni nan zan yi magani ki Haleesa tak'arasa magana had'e da yi musu kallon sama da k'asa.
Maryam da zeely suka kwashe da dariya har suna tafawa Zeely tace da kyau 'yar talakawa nasan cewa ba ki San ko mu su waye bane shiyasa har kike da baki fad'a mana magana ta juya wurin Maryam tace k'awata kora mata bayani kina dasa aya na d'ora daga inda kika tsaya domin na fahimce cewa wad'annan dak'ik'ai sai mun wanke musu allonsu ciki da waje.
Maryam ta yi murmushin tace Haleesa ba wani abu bane ya kawo mu a wurinki illah mu yi miki gargad'i akan Habeeb Lamido"
Da sauri Haleesa tad'ago ta dube ta sakamako sunan da ta ji ta Kira yayinda Maryam tacigaba da cewa sani kanki ne bakin rijiya ba wurin wasa makaho bane in ban da ke da rigima ina ke ina yaya Habeeb ae yafi k'arfin ajinki, to wallahi ina gargad'inki da kaukausar murya ki koma waje bokanki ya warware k'uli da ya yi miki har yaya Habeeb ya furta kalma mafi tsada da daraja akanki domin ba yadda za'a yi yaya Habeeb yana cikin haiyyaci sa yafurta kalma so akan 'yar matsiyata irinki"
Cikin tsawa da bacin rai Zainab tace ko a cikin dabbobi narasa jinsi da zan daganta Ku da shi jahilci da rashin tarbiyya ne da ya yi muku katutu yasa Ku ka tsayar da mu akan hanya, Ku na fad'a mana magaganu marasa tushe balle kan gado, shawara da zan ba Ku Ku je Ku nemi tumakai irinku Ku kwada masu halinku na dabbobi mu nan ba mu da lokacin saurare wannan shirme naku.
Maryam ta fusata ta cakmi hijab d'in zainab tace ke! 'Yar matsiyata har ni za ki fad'awa maganar banza lallai yau sai na ci ubanki a wurinan.
"Sakar mata hijab kafin ni na fara cin ubanki Haleesa tafad'a tana huci Maryam ta zaro ido kafin ta furta abunda ta yi niyar fad'a Haleesa ta yi kukan kura cikin fushi ta fusge hannuta daga wuyan Zainab ta ware hannayeta tashiga tsakaninsu, tace Zainab rik'e min jakka ta domin wannan fad'a nawa ne ke bara ki iya ba Maryam tasaki murmushi dama haka takeso ta jingi  Haleesa ta kuma daki banza, domin tasha alwashi lallai yau sai ta kassara Haleesa"
"Maryam tad'aga hannu da sunan ta wanke Haleesa da bahago mari Haleesa ta rik'e hannuta yayinda ita ta kai mata mari har saida maryam taga wasu farare taurari suna shawagi akan fuskarta Maryam ta durk'ushe k'asa dafe da kumatu cikin hargowa Zeely ta yi kan Haleesa wani k'aton dutsi Haleesa ta k'ink'ima tace na ratsi kina k'arasowa zan rusa miki kai babu Shiri Zeely ta taka birki Haleesa tana huci tace na fahimce cewa ba Ku da tarbiyya ba Ku san daraja iyayyenku hakan ne ya jawo muku fad'a a titi akan d'a namiji to kun yi kuskure domin Habeeb Lamido nawa ne ni kadai in har kin cika mace ki je wurin boka da naje, ya dasawa Habeeb sona kema ya nema miki gur6i a zuciyarsa Haleesa na k'arasa magana ta rik'o hannun zainab tace zo mu tafi Zainab wad'annan k'anana kwari ne rashin kunya nasu na k'arya ne.
Wannan kalamai na Haleesa sun yi matuk'ar k'onawa maryam rai nan take ta ji wani mashahuriya tsanar Haleesa ta darsu a zuciyata ta ji a ranta sai ta dauki mummuna mataki akan Haleesa.
Haleesa ta shar6e hawaye tace kin gani ko zainab tun tafiya bata yi nisa ba, har na fara cin karo da k'alubali auren Habeeb Lamido.....


Jeeddah Aliyu
[30/12 8:37 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```Dedicated```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


                ```57```

"Da kyar Habeeb ya mik'e tsaye shima ba don ranshi yaso ba, saidai bashida yadda zai yi, "kamal ya wuce gaba suna biye da shi suka Shiga cikin gida Bala ne ya yi sallama Ammi da ke cikin d'akinta ta amsa masa kamal yak'arasa cikin d'akin ya sanarda "Ammi Wanda suke sallama Hijab d'inta, tasaka tace da kamal kace da su su shigo, a fakace Habeeb yake satar kallon tsakiyar gidan ba laifi suna da tsaftar cikin gida k'ofar gidance kadai a wargaje, Haleesa da ke kwance a d'akinta iska yakad'a "curtain  d'in "Window d'akinta tashak'i k'amshin turare da ko a mafalki za ta sheda mamallaki shi, zubur ta mik'e zaune tadafe k'irjinta Habeeb Lamido tafad'a a baiyane kamar wata zararra, "Habeeb da Bala suka k'arasa d'akin Ammi a bakin k'ofa suka duk'a, cikin husky voice d'inshi yace da Ammi ina wuni mun sameku lafiya"?
Karaf sautin maganarshi ya sauka a kunne Haleesa, zaro idanu tayi saboda tayi "recognized voice nashi shi kadai ne mutumi da ta6a had'uwa da shi mai irin wannan voice"
Ammi ta amsa da lafiya qalau Ya su Hajiya"?
Lafiya qalau suke a cewar Bala"
Masha Allah Ammi tafad'a karo na biyu da Bala yak'ara fitowa da bundle d'in kud'i ajiye a gaban Ammi, had'e da cewa ga wannan Ammi ki siye goro da sauri Ammi tace wane irin goro d'anan"?
"Bala yasada kai k'asa yakasa magana, Habeeb ya yi magana tamkar mai rad'a ta hanyar cewa in kika ce ba za ki k'ar6a ba Ammi ba zan ji dad'i ba sai naga kamar ban sami kar6uwa a wurinku.
Ammi ta numfasa tace an gode Allah yasaka da alkhairi
"Ameen a lokacin d'aya Habeeb da Bala suka fad'a.
Haleesa ta mik'e tsaye tanufi window ta yaye "curtain ta lek'a saura kiris numfashinta yadauke sakamako hango Habeeb Lamido da tayi yana duk'e a k'ofar d'akin Ammi da sauri-sauri numfashinta yadinga fita, Habeeb da Bala suka yi ma Ammi sallama suka fice da baya-baya Haleesa tayi tafad'a bisa katifarta da6as wani irin gumi ya lullu6e ta jin tayi an yaye curtain d'in d'akinta tad'ago da sauri Ammi tagani tsaye tana mata kallon "mamaki tabe baki Ammi tayi tace kitashi ki shirya ga bak'i chan a k'ofar gida suna jiranki karki 6ata musu lokacin Haleesa kamar za ta fashe da kuka tace Ammi me zanyi musu"?
"Ammi ta galla mata harara had'e da cewa bansaniba tajuya tafice Haleesa tayi ajiyar zuciya tsawon "5 minutes tadauko a zaune tana tunani irin had'uwa da za ta yi da "Habeeb Lamido jin tayi Ammi na kwad'a mata kira ta mik'e a firgice ta nufi d'an k'aramin "table da take Jere da tarkace kayan "make up d'inta tashafa 'yar powder akan face d'inta ta chanza kayan jikinta zuwa atamfar Deviva wax "blue colour da touch d'in pink" tasanya hijab pink tad'an Shafa body splash" cikin sanyi jiki tafi ce daga d'akin.
Habeeb yaja tsoki had'e da kallon wrist watch kirar Rolex da ke daure a hannunshi ya yatsine fuska yace Bala me wannan kuchaka yarinya take nufi ne zan 6ata almost "20 minutes a banza inajiranta"?
Ka K'ara hank'uri "Boss kasan halin mata da kyalkyali watakila ta tsaya yi ma kwalliya ne.
Tsanani haushi da takaici Bala suka lullu6e Habeeb yakasa furta komai, sai faman huci yakeyi.
"A hankali Haleesa take tafiya kamar mai jin tsoron taka k'asa gabanta na ta fama dukan tara-tara taja tayi tsaye a zaure ta d'an lek'a ta hango Bala tsaye yayinda Habeeb yana cikin mota da sauri tadawo da kanta cikin Zaure tasoma tunani yadda za'ayi ta fita k'ofar gida ta tsaya da wani d'a namiji da suna zance ba yaya Habeeb d'inta ba, hawaye suka cika "mata idanu ga wani tsanani tsoro Habeeb Lamido da ke ratsa jini da gangar jikinta tasauke numfashi yafi a kirga daga bisani ta yi k'undubala had'e da k'unar bak'in wake tak'arasa fita, Bala yasaki ajiyar zuciya domin shima ya kagara Haleesa tafito ya huta da "complains d'in "Boss d'inshi barka da fitowa ranki yadad'e Bala yafad'a yana washe hak'ora Haleesa tayi murmushi yak'e had'e da cewa yauwa Bala ya gida"?
"Gida lafiya da fatar mu sameki lafiya"?
"Lafiya qalau Daga haka kowane su ya yi shiru Habeeb yak'ara harzuk'a a zuciyar shi yace me wannan 'yar iska yarinya ta taka ne da bara ta iya gaida ni tana nufi ni ne zan fara yi mata magana"?
Tsoki yaja yacigaba da zance zucinshi lallai kuwa za mu kwana anan "I think she don't know who I'm that why take d'aukar kanta wata Tsiya batasan cewa Habeeb Lamido baya taking nonsense from local girl's like her" musanman ita da na tsana yak'ara ja tsoki.
Tsawon "10 minutes suka share ba Wanda yace da d'a uwanshi k'ala Bala ne yakawo kashe shiru nasu ta hanyar cewa ranki yadad'e ki k'arasa "Boss yana ciki Ku gaisa Haleesa tad'ago ta du6e Bala tace ka fad'awa "Boss d'in naka ya fito mana ko yana nufi cikin motar zan shiga ta'karasa magana tana yatsine fuska.
Babu shiri Bala ya hadiye wasu miyau saura kiris su sark'e shi, ya yi k'asa da murya ta yadda Habeeb ba zai ji abunda yake fad'a cikin Sigar lallashi yace "please Haleesa ki yi hank'uri ki daure ki k'arasa in kika ce za ki fara da haka basan ya zamanku zai kasance anan gaba ko ba komai ke ce k'arama Dan Allah za ki je ba don ni ba ko kuma "Boss.
Haleesa ta yi shiru kamar mai nazari daga bisani ta nufi 6angare da Habeeb yake zaune tadafa k'ofar mota cikin sanyi murya tace ina wuni yaya Habeeb"?
"Ignoring nata ya yi for some minutes" yayinda Haleesa tafara gajiya da tsayuwa kawai ta yi "decided tayi tafiyarta bara ta iya jure irin wannan wulak'anci "Habeeb ya ja tsoki sanadi da yasa Haleesa ta dube shi 'kas'kantace kallo ya watsa mata mai cike da tsana da sauri tadauke fuskarta da bari kallonshi, chan  k'asan ma'koshi ya kira ta da sunan da tafi tsana ke! Akan wane dalili za ki bata mini lokacin"?
Cikin tsanani mamaki Haleesa ta dube shi daina kallona da wannan "ugly face naki yafad'a yana yatsine fuska kamar ya ga kashi ran Haleesa in ya yi dubu ya6aci a rayuwarta Sam ta tsani wulak'anci sai ga shi yau har k'ofar gidansu ake ci mata fuska kuma takasa d'aukar mataki gani yadda tasada kai k'asa batada niyar bashi amsa tambayarshi, sai kawai yacigaba da gasa mata maganganu masu matuk'ar zafi da sosa rai, na zo gidanku ne a dalilin mahaifiya ta ba wai don kinada wani matsayi a wurina na kuma amince zan aurenki ne domin na koya miki tarbiya saboda na fahimce cewa ke d'in bakida wadataciya tarbiya Wanda hakan ne yabaki damar shanya ni a k'ofar gidanku to kisani mace bata min wulak'anci, na kyaleta batare da na d'auki mummuna hukunci akanta yad'an numfasa me kika d'auki kanki"?
"I say who do you think you're"?
A tsorace Haleesa ta ja baya tana zarar ido domin ita kanta lamari Habeeb Lamido yafara bata tsoro ko a garin mahaukata bata ta6a gani neman aure irin nashi ba, wani shege murmushi yasaki Wanda Haleesa ta yi ma lak'abi da murumshin mugunta ya d'aga mata gira yad'an cije lips d'inshi na k'asa kamar mai rad'a ya furta "you're nothing but useless sai kinyi danasani shigowa rayuwa na banza 'yar k'auye "remember I told you for the first time my saw on you naji na tsaneki tsana mai tsanani gaske "I hate you I absolutely hate you I'll do anything just to make your life miserable yak'ara sa magana yana murmushi.
Haleesa tasauke ajiyar zuciya idanuta taf da kwalla muryar ta na rawa tace Allah yafika yaya Habeeb duk wani sharri da kake nufi akaina Allah zai kareni saboda banta6a nufar wani mahaluki da sharri, yadda baka sona nima haka abu yake a wurina, duk irin zaman da ka tanada min nayi a gidanka bazan ji ciwo ba saboda kai d'in ba komai bane a wurina tana k'arasa magana tashige cikin gida tabar Habeeb da rad'ad'i kalamai ta cikin k'unar zuciya yace wai Bala uban me ka ke jira ne"?
Da sauri Bala yashiga mota yaja suka fice daga unguwar, Bala ya yi k'asa da murya yace "Why you do this to her boss"?
Habeeb yasaki ajiyar zuciya a kasalance ya furta "b'cos I hate her bana sonta in fact yarinya nan bata dace da ni ba.
"I Known boss amma kuma in har madam ta ji irin wulak'anci da ka tsulawa yarinya nan me kake tunani zai faruwa"?
Harara Habeeb ya galla masa yace sai in Kaine munafuki da zai je ya sanar mata da abunda yafaru.
Bala ya yi murmushi had'e da cewa Allah ya huci zuciyar "Boss.
 Haleesa na shiga gida ta zarce d'akinta tafad'a bisa katifarta tasaki kuka mai tsuma zuciya, nan take tafara tunani irin rayuwar da tayi da marigayi Yaya Habeeb tsawon rayuwa ta bata ta6a sani bak'in ciki d'a namiji sai akan Habeeb Lamido, lallai ina da aiki domin da ido na hango tsan-tsan tsana ta a kwayar idonshi to me nayi masa ne da yatsane ni haka"?
Rashin sani amsar wannan tambaya yasa ta mik'e tafice domin ta yi alwala sallah magariba.

```3 Day's later ```

"Iyayye Habeeb maza suka zo nema masa aure Haleesa Batare da kace nace iyayye Haleesa suka amince aka tsayarda lokacin nan da wata d'aya ranar Haleesa ta yi kuka kamar ranta zai fita gani ba Wanda ya kulata yasa ta dangana ta share hawaye ta.

```Gidan Alhaji Yusuf Lamido ```

Da gudu Maryam tafad'o parlour Hajiya khareema d'a kwalin da mayafinta a hannuta, tafad'a jikin Hajiya khareema tafashe da matsananci kuka a tsorace Hajiya khareema tad'ago Maryam cikin rawar murya tace lafiya Maryam kukan me kike yi"?
Maryam tak'ara rushewa da kuka hawaye kaca-kaca akan fuskarta shikenan Hajiya a karo na biyu narasa yaya Habeeb wallahi Hajiya mutuwa zan yi in har ban aure yaya Habeeb saboda, shine bugun zuciyata ba zan iya rayuwa ba shi yanzu nasami labari a babban gida wurin Dada wai Habeeb zai yi aure.
Hajiya khareema tasauke ajiyar zuciya tace kutuma ubanan yanzu dama d'an banza yaro nan yana da niyar K'ara aure a rayuwarshi, ba hanyar da ba mu bi ba ni da mahaifinki ya amince ya aure ki amma yak'i to wallahi bai isa ba ko yana so ko ba yaso sai ya aure ki wai 'yar gidan uban waye zai aura waye ubanta duk fad'in "Nigeria"?
"Maryam ta shar6e hawaye tace Hajiya 'yar talakawa ce ba su mallaki komai ba sai tari tsiya da fatara.
Hajiya khareema taja tsoki cike da takaici tace yanzu akan 'yar matsiyata Habeeb ya yi fatali da soyayyar da kike yi masa tabbas zan bi kowace hanya don gani Habeeb ya zama mallaki ki.
Maryam tasaki murmushi jin dad'i..

Jeeddah Aliyu
[30/12 8:44 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

              ```55```

Tsawon lokacin Ammi da Zainab suka share suna kallonta daga, bisani Ammi ta nunata da yatsa cikin murya mai cike da gargad'i tafara magana ke! Haleesa karki mayarda mu tsofafi banza mana a gaban matar nan kika ce kin amince da aure d'ata, a bayanta idota za ki dawo ki ce bakya sonshi ke tsoro shi kike ji to in ma bacci kike yi kiyi gaggawa ki falka domin wannan shirme naki mu bara mu dauke shi ba ai bakin alk'alami yariga yabushe ke kika amsa da bakinki kina sonshi ba wani ne ya yi miki dole ba kowa yana miki murna Habeebu yatafi ga kuma wani Habeebu yadawo, shine za ki tsiro da wani sabon tsirfa to ahir d'inki babban farin cikin mu Haleesa kindawo da walwala da farin cikin da kika rasa birjirewa wannan aure tamkar kinyi butulci da musaya da Allah ya yi miki kuma karke sake na 'kara jin wannan zance yafito daga bakinki, saboda ina tausaya miki in Baffa ki ya ji wannan tatsuniya ba zai yi miki da kyau ba.
Haleesa ta rushewa da kuka tace ni fa na amsawa mommy ne kawai don ina ji kunyar na dube tsabar idonta nace banaso gudan jininta, amma azahirin gaskiya bana sonshi kuma bana fatar ya maye min gurbin yaya Habeeb nariga nasakawa raina narasa  yaya Habeeb rashin na har abada tak'arasa magana had'e da rushewa da wani sabon kuka.
Ammi ta girgiza kai tace kin yi wauta Haleesa da kika amsawa Hajiya Hindu kinaso d'ata, a gaban baffanki domin shi mutum ne da bayaso magana biyu don haka ki rungume 'kaddara sai ki yi 'ko'kari ki danne zuciyarki tafara sonshi Ammi na'karasa zance ta tafice daga d'akin tabar Haleesa da Zainab kowane su da abunda yake sa'kawa a ranshi, Zainab tarik'o hannun Haleesa ta yi k'asa da murya Haleesa karki yi haka ya alkhairi yana binki ke kuma kina neman ki guje masa a tunanina za ki fi kowa Murna da farin cikin, shigowa wannan Habeeb d'in a rayuwarki, da k'arfi Haleesa tafincike hannuta daga rik'o da zainab ta yi mata cikin k'unar zuciyar tace da kesan waye Habeeb Lamido da baki furta min wad'anan kalamai Zainab ta tabe baki daga bisani tace ta za'ayi nasan waye shi batare da kin sanarda ni ba"?
Haleesa taja gwaro numfashi, Habeeb Lamido mugu ne bashida tausayi shine mutumin da driver shi ya watsa mana ruwan kwatame shekaru biyu da suka wuce ya kuma zabga min mari har gudu biyu.
A firgici Zainab ta zaburo idanu bud'e cikin sark'ewar halshe tace I can't believe  kina nufi mai siffar labarawa shine Habeeb Lamido"?
Kwarai kuwa shine kuma ba wannan ne kadai had'uwa ta da shi nan take ta kwararu wa zainab had'uwarta da Habeeb da kuma irin furucin da ya yi akanta, tacigaba da cewa ya kike tsanmani zamanmu zai kasance"?
Zainab ta yi ajiyar zuciyar tace dama haka tasha faruwa k'iyayya ta rikid'e ta koma soyayya ni dai gaskiya ina supported d'in wannan al'amari Allah yasanya alkhairi wata k'atuwar harara Haleesa ta gallawa zainab yayinda zainab ta kwashe da dariya ta mik'e tsaye cikin sigar tsokana tace sai da safe Mrs Habeeb Lamido Haleesa ta kai mata duka tafice da gudu cikin yanayi na jimami Haleesa ta koma ta zauna ta rafka tagumi hawaye masu cike da k'unar zuci suka wanke mata fuska.

```BAYAN KWANA BIYU ```

Yammaci ne sakaliya yanayi gari kamar akwai hadari sai iska akeyi mai matuk'ar dad'i gaske, madam Hindu na kishigid'e a "parlour ta hannuta rik'e da newspaper Habeeb ya yi sallama yashigo yanemi kusa da ita ya zauna kallo guda za ka yi masa ka hango tsantsa damuwa da take shinfid'e a fuskarshi, cikin kulawa madam tajuya wurinshi hannunshi ta rik'o me ke faruwa ne son naga kamar kana cikin damuwa"?
Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya numfasa kamar mai ciwo hak'ora yace "nothing mom"
Sam madam bata gansu da amsa da yabata domin tadana yak'ini musanbabin damuwar tasa, duk bai wuce zance aure ita ko "this time around ba za ta d'aga masa k'afa kawai sai tayi murmushi tacigaba da cewa ina fatar wannan shiri da ka yi na tafiya gidansu Haleesa ne in baka mata ba yau ne muka yi alqawali da kai za ka je"?
"Habeeb ya lumshe ido game da 'kan'kame yatsun hannu mom ya yi k'asa da murya yace "please mom ki d'auke min tafiya nan bara iya ba tun da na amince da aure banga wani amfani zuwa na ba yak'arasa magana tamkar zai fashe da kuka.
"Madam ta yi murmushi had'e da cewa haba Habeeb bansanka da magana biyu ba naga cewa tuni mun gama wannan zance me yasa za ka dawo da hannu agogo baya, katashi katafi Allah ya yi maka albarka.
"Ba yadda Habeeb ya iya dole ya mik'e tsaye cikin sanyi murya yace sai nadawo mom"
Adawo lafiya ka gaida ta batare da yak'ara furta uffan yafice daga parlour yayinda madam ta bishi da kallo.
Yana fita Bala P'A ya shek'o da gudu yanufo wurinshi yace "Boss fita za mu yi ne"?
A kasalance Habeeb yafurta kalma "eh Bala yanufi "parking space yajanyo mota kirar "mercedez  benz c class" ash colour kafin Bala ya bud'e masa k'ofa ya bud'e da kanshi yashiga Bala yaja mota maigadi yabud'e gate suka fice daga gidan.......

 ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

*Dedicated to Shehu Aliyu family's*


Note:- _Alhmdullilahi naji sauki sosai ina mik'a godiya agareku masoya na na gode da addu'arku Wanda suka kirani da Wanda ma basuyi min yajiki ba na gode sosai Allah yasaka da alkhairi na gode_


             ```56```

Bala yajuya a "sit d'in baya yace "Boss ina muka nufa"?
K'atuwa harara Habeeb ya wulga masa cikin tsawa yace dallah! Malam ka kalli gabanka bara ka iya yi min magana bane sai ka juyo"?
"Sorry Boss Bala yafad'a kaitsaye
Habeeb yaja tsoki saida yagama shan k'anshimsa sannan yafad'awa Bala sunan unguwar su Haleesa Bala yadafe kai yace "Boss tuni na wuce titi da zai sada mu da unguwar yanzu kuma dole sai mu yi round mu koma ainihi hannun mu.
Cike da jin haushin kalamai Bala yace bana son surutu Bala karka dame ni, Bala yagyd'a kai, har suka isa unguwar Habeeb yana zance zuci gani sun iso yakasa koda kwakwara motsi yasa Bala ya yi karanbani kiran sunanshi, "Boss mu iso gidan"
Firgigit Habeeb ya d'ago kamar Wanda yatashi daga bacci yasaki tagwaye numfashin daga bisani yace ina ne gidan"?
"Bala yanuna gidansu Haleesa da yatsashi yace nan ne gidan Habeeb ya zaro golden "eye's nashi tamkar Wanda yaga abin tsoro cikin sark'ewa halshe yace wannan gidan buski shine gidan in-laws d'ina"?
"Kwarai kuwa "Boss shine gidan su aljanarka kasan ranar ni na kawo "Madam sai yanzu nagano fa'idar kawo ta da nayi saboda in katashi zuwa zance ba sai mu sha wahala neman gida, Bala yak'arasa magana had'e da washe hak'ora.
"Habeeb yadafe goshi yana kallon Bala ta k'asan ido jin yakeyi kamar ya shak'e wuyan Bala sai yadaina motsi sannan yasake shi, cike da takaici yace Bala "you are such a fool a rayuwarka ba abunda kasani sai surutu maras amfani, kai yanzu a ganinka na dace da wannan yarinya"?
Bala ya sunkuyarda kai ya Sosa k'eya yace "Boss ina da amsar wannan tambaya amma ina tsoro fad'a saboda banaso ranka yab'aci.
Bala!
"Yes Boss
"ll'l  You answer my questions or not"?
"Yes Boss
To kabani amsa na dace da wannan yarinya kuwa"?
Kun dace "Boss tun da ka ga madam ta za6e ta a matsayin matarka to tabbas kun dace saboda ba yadda za'ayi "Madam tayi maka za6en tumu dare amma ka gafarce ni in har na fad'i abunda ya6ata maka rai.
"Numfashin mai matuk'ar zafin gaske Habeeb ya furza yak'ara yadafe goshinshi "oh! My goodness mom she try to kill me" yad'ago ya kalli wata k'atuwar gota wance ke d'auke da ruwan kwatame masu masifar wari yak'ara yadda ganinshi akan Katanga gidan jar k'asa ce duk ruwa sun zaizzaye ta, ya yatsine fuska had'e da toshe hanci, yajuya wurin Bala yace yanzu Bala kana nufi akwai, mutane a gidanan kuma suna rayuwa a ciki"?
"Bala yayi murmushi mai sautin gaske daga bisani yace kwarai kuwa boss suna rayuwa cikin jin dad'i tamkar yanda kake rayuwa.
Habeeb ya galla masa harara yace "ur very stupid Bala taya zakace mutanen da ke rayuwa cikin wannan kango suna jin dad'i tamkar yani"?
Ya furzar da numfashi mai zafin gaske cikin 'kunar  zuciya yacigaba da cewa na tabbata daga mai gidan, har iyalinsa idan aka yi masu "Blood test dole a taradda su d'auke da kwayoyin cutar"maleria kalli wannan bala'in da ke kusa dani yanuna 'katuwar gota da ke kusa da su da yatsanshi wallahi ina matuk'ar tausayawa mazauna wannan unguwa.
"Bala ya girgiza kai yace "Boss amfani masu kud'i in har suka ci karo da irin wannan abin tausayi su taimaka"
Habeeb ya yi masa kallon k'asan ido daga bisani ya tabe, baki yace mu yi abunda ya kawo mu "Co's na fara gajiya da zaman wannan wuri mai cike da barazana ga lafiya ta yak'arasa magana yana wani yayatsine fuska"
Kafin Bala yabashi amsa kamal yafito daga cikin gida janye da keke sa, da sauri "Bala ya balle k'ofar mota yafito, ya tsayarda shi, yaro ko maigidanan yana ciki kuwa"?
"Eh yana nan"
Dan "Allah ka yi mana sallama da shi"
"Toh kamal yafad'a yajingine keke sa ya juyawa cikin gida, Bala ya koma wurin mota ya bud'ewa Habeeb k'ofa ya yi k'asa da murya yace "Boss yakamata kafito kafin maigidan yafito Habeeb ya tsuke fuskar ya zuro k'afafu shi k'asa daga bisani gangar jikinshi tafito daga cikin mota, yajigina jikinshi a jikin mota ya yi "crossing hand's d'inshi akan k'irjinshi kamal yafito yace gashinan fitowa'
"Toh madallah na gode aboki na Bala yafad'a had'e da rik'o hannun "kamal, ya sunan ka"?
Sunana kamal"
Kamal amma kai k'ani Haleesa ne saboda naga kun yi kama saidai tafi ka kyau.
Kamal ya yi murmushi yace "Eh yayinda Bala yacigaba da cewa Haleesa tana ciki kuwa"?
"Eh tana ciki'
Har Bala ya bud'a baki da niyar yak'ara watsawa kamal wata tambaya Habeeb yadaka masa tsawa "shut up Bala wai kai me ke damunka ne"?
"Bala ya waro idanu had'e da furta "sorry Boss' a zafafe Habeeb yace "sorry for ur self next in ka k'ara yi min irin wannan shisshigi you ll'l be fired Yak'arasa magana had'e da Jan tsoki yayinda Bala yak'ara shiga firgici, kamal da ke tsaye yana kallon iko Allah har yajuya sai yaji tak'o tafiya Baffa sai kuma, yaja ya yi domin yanaso yasan wannan balarabe daga wance duniya yafito.
Malam Usman yak'araso da sauri Bala yace barka da fitowa yayinda Habeeb yad'an rusuna yace ina wuni"?
Lafiya qalau sannuku da zuwa saidai kuma ban sheda Ku ba"?
Bala yajuya ya sace kallon "Boss d'in shi "Habeeb yad'aga masa gira sannan yajuya wurin Malam Usman yace sunana Bala wannan kuma yalla6ai Habeeb shine Wanda yake neman 'yar wurinka, dama mu zo ne mu gaidaku mu kuma nemi izzini gani Haleesa.
"Har Bala yadasa aya malam Usman yana gyad'a kai daga bisani yace masha Allah yajuya wurin kamal yace kamal shiga gida ka kira babanka Audu, yazo mu yi bak'i bayan shigar kamal gida da kamar "5 minutes" sai gashi yafito tare da malam Audu bayan sun gaisa da Habeeb duk wani tambayoyi da yake zubawa Habeeb Lamido Bala ne yake bashi amsa, saboda gogan naku ko dogon motsi bayaso yi, daga bisani malam Usman ya yi masa iso cikin zaure gidan kamal yadauko tabarma ya shinfid'a mishi, cike da kyakyami Habeeb ya dosana duwawo shi akan tabarma yayinda, malam Audu yacigaba da tambayoyi nashi Bala na bashi amsa, malam Audu ya gansu da amsoshi da Bala yabashi saboda haka suka mik'e tsaye a lokacin d'aya shi da Malam Usman Bala yafito da "bundle na 'yan N1000 na dubu d'ari ya mik'awa Malam Audu yace malam ga wannan asiye goro, cike da mamaki mal Audu da mal Usman suke kallon kud'in da ke hannun Bala mal Audu ne ya yi yun'kuri katsiwa Bala hamzari ta hanyar furta Mun gode kwarai Allah yasaka da alkhairi amma ba za mu kar6i kud'inku ba yana k'arasa magana yafice yayinda Mal Usman ya kira kamal yace zo ka shiga da su ciki su, gaisa da Amminku daga haka bai k'ara furta uffan ba yafice daga zaure....

Jeeddah Aliyu
[30/12 8:49 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

              ```53```

Ki daina ya6o d'an uwanki a wurina saboda hakan bashida amfani a tare da ni, zainab tarik'o hannu Hannah tace tashi mu je kiyi alwala Hannah ki kyale Haleesa saboda a halin yanzu bata cikin haiyyacinta batare da Hannah ta furta uffan ta bi bayan zainab bayan madam ta  gama sallah tanufi gadon Ammi inda Haleesa take kwance tadinga rarrashinta har tayi nassara shawo kanta tadaina kuka, sai misali k'arfe _8:20pm_ madam Hindu tabaro gidansu Haleesa.

```9:30pm```

Madam Hindu na kishigid'e a had'ad'e parlour yayinda Hannah take zaune a gefe tana chat a "phone d'inta, Habeeb ya yi sallama had'e da shigowa parlour kaitsaye yanufi kujera da madam Hindu take zaune ya zauna kusa da ita had'e da daura kanshi a kafad'arta, ya wani narke sai kace 'karamin yaro madam tashafi sumar kanshi cikin kulawa tace da alama _son_ ka kwaso gajiya ga shi inaso zan yi magana mai matuk'ar mahimmanci da kai"?
"Don't worry about me mom ba wani gajiya a tare da ni da bara nayi fresher up nadawo mu yi magana ya mik'e tsaye cikin tsokana yace Allah yasa kud'i ne za ki bani domin nasanki da kyauta tun da na shigo parlour nan naga fuskarki shinfid'e da farin ciki naji a jikina babba kyauta za ki yi min ni kadai batare da Hannah ba
Hannah ta kyalkyale da dariya tace kai yaya Habeeb Sam baka rabo da abin dariya to abunda yafi kud'i ne mommy za ta baka
Murmushi yayi yana shafar sumar kanshi da gaske ne sweetheart za ki bani abunda yafi kud'i"?
Haka ne son ka je ka yi wanka kadawo ka ji babbar kyautar da zan baka.
"Your wish is my command sweetheart yafad'a had'e da juyawa ya haura upstairs Hannah tace wannan kyautar "special ce mu biyu za mu raba batare da yajuyo ba yace karya ki ke yi yarinya ni kadai mom za ta ba.
Mom kina gani yaya Habeeb zai amince da za6inki kuwa"?
Ajiyar zuciya madam ta yi daga bisani tace bana tunani zan same matsala daga wurin Habeeb saboda tun yana yaro ba mu ta6a samu sa6ani ra'ayi duk abunda nakeso shima yana sonshi, so bana tunani akan wannan za'a same matsala, kuma da bakinshi ya sha fad'a min cewa na nemo mishi mata kin ga kenan fad'uwa ce ta zo dai-dai da zama.
Habeeb na shiga bedroom ya cire kayan jikinshi yasaka rigar wanka {bathrobe} yashiga bathroom bayan yafito daga wanka, farar jallabiya yasanya yafice daga bedroom d'in madam da Hannah na zaune inda yabarsu a zaune, tun kafin ya zauna yace Hannah ki je kitchen ki dauko min "soya milk mai sanyi Hannah ta mik'e tanufi kitchen yayinda ya mayarda ganinshi wurin mom yace "sweetheart ga ni nadawo madam ta yi murmushi tace son lokacin ya yi da za ka aje iyali domin zamanka haka bai dace ba
"Hannah tadawo hannuta rike da kwalin soya milk had'e da "handle glass cup ta mik'a masa harara ya galla mata yace bara ki iya zuba min bane"?
Hannah ta yi murmushi ta bud'e murfi kwalin soya milk d'in ta zuba masa a cup ta ajiye kwalin bisa stool ta koma wurin zamanta ta zauna yayinda madam tacigaba da cewa a dalilin haka yasa na nemo maka yarinya mai hankali da natsuwa babban abunda yak'ara Jan hankalina agareta kyakyawar tarbiyya da ta ke da ita.
Tun lokacin da madam tafara magana Habeeb yake kallonta had'e da snipping d'in soya milk d'insa, gani ta dasa aya a zanceta ya yi d'an bazawari murmushi kamar mai rad'a yace mom kina nufi aure za ki yi min"?
Kwarai kuwa _son_ nagaji da gani ka haka domin basan har wane tsawon lokacin za ka dauka kafin ka nemo wance ka ke so shiysa, na nemo maka wance ta dace da kai kuma na tabbata za ka so ta.
Numfashi yasauke yace mom wacece wannan yarinya da kike ta faman zuzutawa"?
Haleesa k'anwar Juwairiyya matar masa'ud manager ita ce yarinya da na za6a maka kuma nasan za ka yaba da za6i na.
Habeeb ya zaro ido soya milk d'in da ya kur6a baisan lokacin da yahadiye ta da k'arfi ta sark'e shi yafara tari kamar ranshi zai fita madam da Hannah sai faman sannu suke masa da kyar tari ya tsaya yad'ago jajaye idanushi yasauke su bisa fuskar mom d'in tashi cikin yanayi na tashin hankali yafara magana mom duk wad'anan ababbe da kika lissafa akan wannan yarinya ni ba ko d'aya da nagani a tare da ita asalima banta6a gani, mahaukaciya irinta ba wai ina kushe za6inki bane mom ki yi bincike akanta kafin ki yanke hukuncin aura min ita yak'arasa magana tamkar zai fashe da kuka.
"madam Hindu  ta gyara zamanta had'e da rik'o hannunshi "Son Haleesa batada matsala duk wani bincike da addini ya yarje ayi kafin anemi aure nasa ayi min akanta da iyayyeta kuma, gaba d'aya su sun same kyakyawar sheda a wurin jama'ar gari....

```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

              ```54```

A matsayina na mahaifiyarka ba yadda za'ayi na za6a maka abunda zai cutar da kai Haleesa na matuk'ar bani tausayi kai kanka in ka ji labari rayuwarta za ka tausaya mata, nan take madam ta zayano masa labari rayuwa Haleesa tacigaba da cewa _son_ nasan kana da kyakyawar zuciya da tausayi dalilin da yasa ka aure salma kenan Haleesa ta cancanta  ka tausaya mata ka aure ta domin tana buk'atar kulawa ka yi tunani halin da 'yarka kwara d'aya tal take ciki ka gano cewa kana buk'atar Haleesa a tare da kai amma tun da bakada ra'ayi akanta ba zan tilassa ka ba saidai basan ta wace hanya zan bi domin ba iyayyeta hank'uri"
Cikin sark'ewa halshe yace akoda yaushe banida za6i da ya wuce naki sweetheart duk abunda kike so nima ina sonshi akan wannan bara mu ta6a samu sa6ani ra'ayi, farin ciki na shine na kasance d'a mai biyayya a gareki don haka na amince da za6inki ni kuma haka tawa k'addara ta take bara ta6a samu za6ina.
Tsanani tausayi farucinshi Yakama madam amma kuma ba taji za ta, iya chanza ra'ayinta akan Qudirinta"
parlour ya yi tsit kamar ba masu numfashin a ciki baka ji komai sai 'karar sautin tv madam ce ta yi yunk'uri kawo karshen shiru nasu ta hanyar fad'ar Allah ya yi maka albarka Habeeb biyayya da kake min kai ma Allah yabaka 'ya'ya da za suyi maka fiye da wance ka yi min.
_Ameen sweetheart_ yafad'a had'e da kwantawa akan cinyoyinta ya lumshe idanu.
A hankali madam ta ke shafar sumar kanshi cikin lafazi mai sanyi ta kira sunanshi Habeeb!
"Humm! Yafad'a a kasalance.
Banaso wannan al-amari yadauki dogon lokacin, saboda haka ka Ware _time_ ka je gidansu Haleesa ku fahimce juna ka kuma gaida iyayyeta, daga bisani na sanarda da Alhaji bello su Kai kud'in gaisuwa.
Har madam ta dasa aya idanushi na lumshe, yace kina nufi zance zan je"?
Kwarai kuwa ko ba za ka iya zuwa bane"?
Ni na isa nace bara iya zuwa saidai kunya nakeji tun da na zo duniya banta6a tsayuwa da wata 'ya mace da sunan zance Allah kuwa sweetheart kunya nakeji yak'arasa magana yana yatsine fuska.
Madam ta yi "dumm! Tana shafar gashi kanshi daga bisani tace ka daure my son ka je ta hakan ce za Ku fahimce juna kuma iyayyeta za su fi gansuwa su gano cewa da amincewarka za ka aure 'yarsu.
Habeeb yak'ara ya mota fuska da alamu yashiga sark'ak'iya da kyar iya bud'a baki yace shikenan mom in nasame lokacin zan je'
Wane irin in kasame lokacin son kawai gobe ka je
A kid'ime Habeeb ya mik'e zaune yace mom gobe fa kika ce"? Gaskiya gobe "I don't have time but I promise you next week zan je
"Next  week ya yi nisa son" ranar Saturday kana free saboda weekend ne ba aiki ka yi k'ok'ari ka je
Tamkar zai fashe da kuka yace na ji
Madam ta yi murmushi had'e da shafar gefen fuskarshi da bayan hannunta tace Haleesa yarinya ce tagari za ka ji dad'i zama da ita.
"For God sake mom kidaina wannan magana haka nan nace na amince zan aure ta cigaba da maimaita zance yarinya nan za iya haddasa min "headache yana k'arasa magana ya mik'e tsaye Hannah ta kyalkyale da dariya tace yaya Habeeb zan yi maka "escort na kware da iya tsara zance kaitsaye zan tsara maka ita nan take ta zurma a kogin sonka.
Wawan tsoki Habeeb ya ja cike da haushi had'e da takaici ya haura upstairs a zafafe ya murd'a handles yashiga bedroom yafad'a bisa bed yasaki huci bakinshi na fitarda iska mai masifar zafi hannaye shi ya daura ya yi pillow ya 'kurawa ceiling ido tamkar yana karanta wani abu a wurin daga bisani yasauke numfashi mai karfin gaske, yafara zance zuci lallai yarinya nan sai ta yi "regretting na shigowa rayuwa ta saboda tarasa masoyinta don kawai ina da sunanshi shine take bibiya na har ta yaudare mom da ladabi ta na karya tayi sanadi da mom ta had'ani aure da ita wallahi sai ta yi danasani sani na a rayuwa domin ba zan ta6a Maye mata gurbi tsoho masoyinta sai na had'a ta da hawan jini sai na wulaqantata irin wulaqanci da bata ta6a gani a rayuwarta.
A 6angaren Haleesa kuwa tana gani  madam Hindu ta tafi tasake bud'e sabon babi na kuka Ammi ta watsa mata kallon mamaki tace Haleesa kukan me kike yi"?
Haleesa ta mik'e zaune tana shar6e hawaye tace wallahi Ammi banaso Habeeb Lamido ba zan iya zaman aure da shi har abada ba zai ta6a maye min gurbi yaya Habeeb asalima ni tsoro shi nake ji.
Ammi da zainab suka yi sororo suna duban Haleesa duba na rashin fahimtar inda kalamai ta suka dosa....



Jeeddah Aliyu
[30/12 8:53 am] aliyujeeddah: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu

              ```51```

~~Meke faruwa ne Haleesa na ga kina zarar ido''?
Muryar Zainab ce tadawo da ita daga natsuwarta taja gwaron numfashi daga bisani, tace ba komai zainab ta yi murmushi rashin yarda da amsar da Haleesa tabata Haleesa kenan nasan abunda kike yi wa zarar ido duk bai wuce sunan Habeeb da kika gani a jikin number motar nan ta'karasa magana had'e da nuna number motar da yatsanta tadafa kafad'ar  Haleesa tacigaba da cewa yakamata ace zuwa yanzu kin manta da rayuwarki da Yaya Habeeb Co's He will never comeback to us yaya Habeeb ya mutu Haleesa ba zai ta6a dawowa so ki manta da shi ko Ke ma za ki ji dad'i rayuwarki, hawaye suka cikawa Haleesa idanu saboda a yanzu batada wata matsala da ta wuce Habeeb Lamido tarasa dalilin da yasa take yawan tunani shi, cikin sanyi murya tace zainab bara na shiga gida batare da ta jira amsa da zainab za ta bata tashige zaure gidansu, tana jefa k'afarta tsakiyar gida ta yi turus Ammi da madam Hindu sai wata kyakyawar budurwa mai kama da Habeeb Lamido ta hango zaune, suna fira nan take tagano cewa wannan budurwa ita ce Hannah, ajiyar zuciyar Haleesa ta yi cikin tsanani jin dad'i gani bak'i{visitor's} nasu tayi sallama a lokacin d'aya suka amsa mata madam Hindu tace idonki kenan Haleesa kin manta da mommy koh"?
Cikin yanayi naji kunya ta durk'usa tace ina wuni mommy"?
"Lafiya qalau Haleesa zo ki zauna anan ta nuna mata kusa da ita Haleesa ta zauna tajuya wurin Hannah da ke ta faman zabga murmushi, tace Mommy ko ban tambaya ba wannan ita ce Hannah madam ta yi murmushi tace kin chanka dai-dai Hannah da Haleesa sukayi dariya fira sukeyi Haleesa sai kyalkyale dariya takeyi madam tace ashe Haleesa kina dariya"?
Haleesa ta sada kai k'asa tana dariya k'asa-k'asa Ammi ta yi 'yar gajeriya dariya daga bisani tace tun daga lokacin da Haleesa tadawo daga Lagos take wannan fara'a narasa me Ku ka bata da yasauya ta a d'an k'ank'ani lokacin Ammi ta'karasa magana had'e da dariya madam da Hannah suka kwashe da dariya sallama baffa da baba Audu ce ta katsi musu dariyar da suke yi bayan sun gaisa a tsakaninsu madam tajuya wurin su Haleesa tace Haleesa da Hannah Ku ba mu guri za mu yi magana Haleesa ta mik'e had'e da rik'o hannu Hannah tace zo mu je gidan su zainab Ku gaisa.
"Madam ta gyara zama tafara magana malam Usman wata alfamar nazo nema a wurinka shine dalilin da yasa nace inaso magana da kai, bansaniba ko za ka amince da buk'atana"?
"Malam Usman yajuyo ya dube d'an uwanshi daga bisani yace fad'i Alfarma taki Hajiya kuma Allah yasa zan iya.
Malam usman dama alfarma da na zo nema alkhairi ne bansaniba, ko ta ya za Ku d'auki wannan al-amari azahiri gaskiya tun daga ranar da naga Haleesa na yaba da hankali da tarbiyyarta musanman da naji tarihi rayuwarta da marigayi Habeeb Wanda hakan ne yajanyo na yi wa d'ana Habeeb sha'arwata a tunani na Haleesa tarasa Habeeb ga kuma wani Habeeb yadawo ina matuk'ar tausayi rayuwa Haleesa 'yarku na buk'atar abokin rayuwa Wanda zai sota yabata kulawa wance za ta sa ta manta da rayuwa da tayi da marigayi Habeeb yanayi da Haleesa ta tsince kanta a ciki yadda ta mayarda kuka da tunani abokai rayuwarta, hakan zai iya shafar lafiyarta kun ga kenan za'ayi biyu babu an6ata d'aya biyu bata gyaru ba amma kuma a matsayinku na iyayyeta menene ra'ayinku"?
A lokacin d'aya baffa, baba da kuma Ammi suka sauke ajiyar zuciya domin abu ya zo musu a bazata basu ta6a tunani jin wannan, furucin daga bakin madam Hindu baba Audu ya numfasa, yace tabbas Hajiya kin zo mana da abu mafi girma, da farko inaso kisani mu talakawa ne ba mu da komai akullum fafutukar Neman nasawa a bikin salati mu ke ni aganina, sai naga kamar d'anki baidace da 'yarmu wutsiyar ragumi tayi nesa ga k'asa.
Ka ga malam Audu kada Ku fassara ni baibai, ni mutumce kamarku don kawai Allah ya yi min arziki sai Ku banbanta kanku da ni to kusani duk d'aya mu ke a wurin Allah sai Wanda yafi wani tsoronshi, ban zo nan don na cutarda 'yarku kafi nazo nan saida nasa akayi min bincike akanku nima na baku damar Ku yi bincike akaina da kuma d'ana Habeeb.
A wannan karo malam Usman ne yabata amsa ta hanyar cewa shikenan Hajiya, mu amince da buk'atarki domin bamusan abunda Allah yake nufi a cikin wannan al-amari Haleesa tarasa Habeebu a lokacin da tafitarda rai da tak'ara samu farin ciki sai kuma ga wani Habeebu yashigo rayuwarta Allahu Akbar Allah mai iko, mu amince Hajiya amma a bisa sharad'i d'aya sharad'i kuwa shine har sai Haleesa ta furta da bakinta ta amince da d'anki domin mu ba za mu yi mata dole ba.
Murmushi madam Hindu tayi da ke baiyanar da farin cikinta tace nima bana goyo bayan ayi mata dole, Ku barni da ita agabnku zan yi magana da ita insha Allahu za ta amince ae Haleesa yarinya ce mai biyayya......
  ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

              ```52```

~~Tun lokacin da su Haleesa suka shiga gidan su zainab fira ta barke a tsakaninsu, _ringing_ d'in wayar Hannah ce ta katsi musu firar tasu gani "mommy ce ta kira yasa Hannah bata yi picking ba ta mik'e tsaye had'e da cewa Haleesa tashi mu tafi mommy ce ta kirani watakila wuce wa za mu yi Haleesa ta mik'e zainab ta Mara musu baya da sallama suka shiga gidan madam tace zo zauna Haleesa za mu yi wata magana da fatar za ki bani had'in kai"?
Haleesa tad'aga kai madam ta rik'o hannuta cikin k'ask'antar da kai tafara magana Haleesa burin kowace uwa tagari d'anta ko 'yarta su sami abokin rayuwa nagari shiyasa na za6e ki a matsayin matar da nakeso Habeeb ya aura"
A firgice Haleesa tad'ago dara-dara idanuta tasauke su bisa fuskar madam kallo d'aya za ka yi mata gano tsintsa tashin hankali da take cikin, yayinda madam tacigaba da fad'ar amincewarki kadai nake nema Haleesa saboda iyayye ki sun amince, shin Haleesa kin amince da Habeeb ya maye gurbi marigayi Habeeb a wurinki"?
Wannan tambayar ta "madam Hindu ta yi matuk'ar gigita Haleesa had'e da haddasa mata shiga tashin hankali maras misaltuwa, ta zazzare ido tamkar ta ga wani abin tsoro yayinda zuciyarta ke bugawa kamar ana buga ganga nan take tafara shid'ewa numfashinta yafara k'ok'ari k'auracewa gangar jikinta tsanani tashin hankali da rashin mafita suka lullu6e ta sai faman zazzare ido take mayuwaci abu ne ta kalli tsabar idon madam Hindu tace batason d'anta babban tashin hankalinta bai wuce yadda za ta rayuwa da Habeeb Lamido mutumin da yakira ta da suna 'yar iska mai bibbiya d'an namiji kenan furucin sa zai tabbata na cewa ina sonshi.
Da k'arfi madam ta girgiza Haleesa tadawo haiyyacinta kin yi shiru ba ki ce komai ba Haleesa ko bakyaso Habeeb ne"?
Karki dame kanki Haleesa ba za mu yi miki dole ba har. madam ta dasa aya Haleesa tana kallonta ta sauke numfashi yafi a kirga daga bisani ta tattaro k'uzari had'e da jarumtaka ta cikin sar'kewa halshe tace, mommy ko za'a daura min bakin bindiga banida bakin furta kalma banaso jininki akwai 'yan mata da yawa a gari Wanda suka fi ni baki yi la'akari da kasancewa ta 'yar talaka kika tsalleke su kika za6e ni a matsayin wance ta dace da d'anki ta ya ya zan bad'a miki k'asa a ido nace banaso jininki"?
 "Tun lokacin da narasa yaya Habeeb nasan cewa nayi bankwana da farin ciki na har abada, don haka "mommy na amince da yaya Habeeb ko ba komai yana d'auke da suna mutumin da yake mahad'in rayuwa ta na gode da wannan karamawa ta ki tana k'arasa magana ta mik'e da gudu tashige d'akin Ammi tafad'a sama gado tafashe da kuka mai k'arfin gaske.
"Malam Usman yace Hajiya ko za'a hank'ura da wannan al-amari saboda naga har yanzu Haleesa bata fitarda marigayi Habeebu a ranta kada aje gyara gira arasa ido ta je takasa zaman lafiya da d'anki kin ga anyi ba'ayi ba d'aukar makaho photo.
Karka damu malam Usman kayi 'ko'kari ka yak'i wannan tunani daga zuciyarka karka manta har yanzu Haleesa tana fagge na jinyar mik'i da ke zuciyarta na rashin marigayi Habeeb a cikin wannan yanayi Habeeb za'ayi amfani da wannan damar yakafa sanssani yak'i neman za6e zuciyar Haleesa Wanda a sannu za ya maye gurbi Marigayi Habeeb har ta manta ta ta6a rayuwa da wani Habeeb addu'arku kawai nake nema a cikin wannan tafiyar.
"Shikenan Hajiya Allah yasanya alkhairi yasa abunda za'a ci amfaninsa ne Allah yahad'a Kansu ya kad'e fitina a tsakaninsu.
_Ameen malam Audu_
Yayin da madam Hindu tacigaba da cewa sai magana tagaba Habeeb zai zo yagana da Haleesa su fahimce juna daga bisani zan yi magana da d'angin mahaifinsa su kawo kud'in gaisuwa a kuma sanya, lokacin banaso auren yadauki dogon lokacin.
A wannan karo baffa ne yayi magana yace ba damuwa Hajiya duk yadda kika tsara haka za'ayi Allah yasanya alheri _Ameen_ daga haka su baffa suka mik'e had'e da ficewa daga gidan Hannah da zainab suka shiga d'akin Ammi cikin tattausa lafazi suka soma rarrashi Haleesa da kyar suka samu tadaina kuka da take yi Hannah tace Haleesa kidaina kuka domin yaya Habeeb mutumin kirki ne bashida matsala za ki ji dad'i zama da shi wani d'agowa Haleesa ta yi ta watsawa Hannah mugun kallo mai cike da tambayar kinada hankali kuwa daga bisani tace.....

 ```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[30/12 9:50 am] aliyujeeddah: [15/09 12:28 pm] Jeeddah Aliyu: [07/09 8:03 am] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu

            ```45```

Note:- _Masoyan Ni da yaya Habeeb Ku yi hank'uri 2 day's kudaina gani post hakan yafaru ne a dalilin matsananci ciwon baya da nake fama da shi_


Tsawon lokacin madam Hindu tadauka tana sak'e-sak'e daga bisani tad'ago ta dube Haleesa, wance ta sada kai k'asa kamar mai d'aukar karatu tausayi ta ya kamata har taji a zuciyarta lallai ita ce za ta kawo karshen matsalar Haleesa muryar Bala driver ce tadawo da hankalin madam Hindu tajuya waje Bala da ke dur'kushe a gabanta madam ki taimake ni kada narasa aiki na domin yadda naga Boss ya harzuk'a kwano tuwo na zai iya yak'arewa a gidanan, madam Hindu tayi dariya tace Bala kai da Habeeb ba'a shiga tsakaninku matsayin biyu kake takawa a wurin shi kaine driven shi kuma kaine P.A{personal assistance} gaskiya Bala kai d'an gata Habeeb ne.
"Bala driver tamkar zai rusa ihu yace wallahi madam a wasu lukuta Boss Sam baya la'akari da matsayin mutum kaitsaye yake tsula maka tsiya, cikin salon tafiyarshi ta k'asaita yake taka stairs hannushi d'aya na cikin aljihu wando shi batare da ya kalli Wanda suke parlour ba yanufi k'ofar fita tak'o tafiyarshi kadai Haleesa ta ji amma saida gabanta yafad'i da sauri Mommy ta dakatar da shi Habeeb fita za ka yi ne"?
Ya wani 6ata fuska kamar zai yi kuka yace "Eh!
Amma kuma za ka fita ne batare da Bala driver ko kana nufi kai za ka yi driving da kanka"?
Whatever! yafada kaitsaye
Look son I known you can't drive musanmman yadda ababe hawa suke cikoso a gari Lagos kayi han'kuri kutafi da Bala.
Dafe goshi ya yi da alama yafara gajiya da surutu mommy nashi mom bana bukatar Bala I can managed with myself amma ke za ki iya d'aukar shi aiki "Co's I don't need him anymore madam Hindu tayi murmushi tace banaso fitarka kai kadai Habeeb ka yi hankuri kutafi tare da sauri Bala ya zube gabanshi yace am sorry Boss nasan nayi laifi amma ba zan 'kara ba Haleesa ta ja tsoki a zuciyarta tace dube yadda ake rarrahinshi sai kace Wanda aka yi wa wani laifi, d'an reni wayo kawai wallahi na tsini mutum mai girman kai muryarshi ta katsiwa Haleesa zance zuci ta baza kunnenta domin taji abunda zai fada mom na tsani mutum mai surutu a rayuwata sai kuma gashi shine halaya Bala duk abunda idanushi suka gane mishi, sai yafallasa yak'arasa magana had'e da gallawa Bala harara madam Hindu tace duk abunda bakaso daga yau zai kiyaye Habeeb ya mik'e kafad'a had'e da cewa mom I have to go!
Yajuya yafice daga parlour madam Hindu tajuya wurin Bala tace tashi kutafi Bala da sauri Bala ya mik'e yabi bayanshi, Haleesa ta tabe baki tacigaba da zance zuci ta kai amma wannan guy ya kware da wulaqaci sunanshi Sam bai dace da shi ba saboda yaya Habeeb d'ina is very simple man da kyar ka ga yaya Habeeb d'ina yayi fushi amma wannan He is always angry fuska a muturk'e so arrogant.
Haleesa! Da sauri Haleesa tad'ago tace Na'am mommy!
Da alama kema zaman gidanan yafara isarki koh"?
Murmushi Haleesa tayi batare da tace komai ba madam Hindu ta mik'e tsaye had'e da cewa ina zuwa tanufi upstairs yayinda Haleesa tasaki ajiyar zuciya tace Allah yasa mayarda ni gidan aunty juwairiyya za tayi saboda jin kai na nakeyi tamkar prisoner ga zuciyata ta hanani sukuni na zama _heart restless_ musanmman duk lokacin da idanuna sukayi tozali da Habeeb, nakan tsince kaina cikin matsananci fad'uwar gaba.
Har madam Hindu tafito Haleesa bata sani ba saida tadafa ta a tsorace Haleesa tajuya, cikin tausayawa  madam Hindu tace Haleesa kidaina yawan tunani Kada ya shafi lafiyarki murmushi Haleesa tayi madam Hindu tacigaba da fad'ar mu je ki rakani unguwa saboda na fahimce cewa kin gaji da zama guri d'aya tana gaba Haleesa na biye da ita har suka isa parking space da gudu "Driven madam Hindu yak'araso ya bud'e masu mota kirar _BMW 6 series_   Haleesa da madam Hindu suka parke a owner's corner yawo sukayi sosai Haleesa ta ga gari Lagos sai d'an banza go slow tsiya madam Hindu ta yi wa Haleesa shopping nagani nafad'a "ready made da jallabiya's masu matuk'ar kyau da tsada sai around 10:30pm suka dawo gida Aderwale ya yi parking ya bud'ewa madam k'ofa yayinda Haleesa ta bud'ewa kanta Aderwale yataya ta kwashe bag's had'e da ledoji da suka yo shopping a parlour suka zube kayan madam Hindu tace Haleesa ki k'arasa da kayanan ciki duka naki ne, Haleesa ta duk'a k'asa tayi wa madam godiya da sauri madam ta d'agata haba! Haleesa miye haka"?
Duk abunda nayi miki bana buk'atar godiya saboda na dauke ki tamkar Hannah Haleesa tayi murmushi tace duk da haka na gode mommy Allah yasaka miki da alkhairi.
Ameen Haleesa ki je ki kwanta madam nak'arasa magana ta nufi bedroom d'inta Haleesa ta kwashe kayan tanufi bedroom d'in Hannah, tsanani gajiya da ta de6o ga kuma bacci fal idonta yasa ta haura wrong stairs a maimako ta haura left wanda zai sadata da room d'in Hannah sai ta haura right na part d'in Habeeb kaitsaye ta murd'a handle tashiga...
[10/09 9:37 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
           
          ```46```

Bedroom d'in Hàbeeb tana shiga ta jefarda kayan hannuta da yake d'akin akwai duhu Sam bata lura da, Habeeb da ke kwance wani juyi tayi tacire mayafinta had'e d'an kwalinta ta jefa bisa bed suka fad'a akan fuskarshi daga bisani tanufi switch ta kunna wuta haske yagauraye d'akin karaf idanuta suka sauka akan bed Habeeb na kwance ya yi matashi{pillow} da hannaye shi fuskarshi na lullube da mayafinta da jefa akan bed Haleesa ta zaro ido jikinta yadauki rawa tasoma ja da baya a hankali yacire mayafinta da ke kan fuskarshi ya jefa mata batare da bud'e idanushi yafara magana, d'aya bayan d'aya sai kace mai koyon magana _hey what's are you doing in my room at dis time"?_
Cikin sark'ewa halshe Haleesa tace I'm so..rry I made a mistake am  looking Hannah's room but I'm so sorry.
_hey shut up I don't wants any apologies from you just pack your things  & leave my room right now_
A tsorace Haleesa ta tattara kayanta jikinta na rawa ta bud'e k'ofa tafice tsanani rud'ewa yasa Haleesa takasa gane inda za ta dosa dole ta koma downstairs parlour anan tayi tsaye daga bisani ta haura stairs d'in zai sadata da room d'in Hannah tana shiga d'akin ta jefarda kayan hannuta, tafad'a kan gado tasoma zanci zuci wai gari yaya naje room d'in yaya Habeeb"?
Gaskiya nagaji da gidanan gaba d'aya naji garin Lagos yafita min a rai, tun zuwa na banyi waya da Ammi ba gashi na baro phone d'ina gidan aunty juwairiyya ballatana na kira yaya salman ya had'a ni da Ammi, mtss gidanan ban had'a komai da su ba yakamata zuwa yanzu ace nasan lokacin da zan dauka a gidanan, domin ba zan iya cigaba da zamansa, banaji ko 1week zan iya k'arawa a garinan.
Ta b'angare Habeeb kuma Haleesa nafita ya ja tsoki ko uban me yarinya nan ta zo yi a d'akina oho"?
Na tsani yarinya nan Sam banaso ganita duk lokacin da idanu sukayi arba da ita sai naji tsanarta na 'kara yad'uwa a zuciyata.

```washe gari ```

Tun misali 'karfe 10:44am Haleesa ta falka tayi wanka ta shirya cikin d'aya daga cikin jallabiya's d'in da madam Hindu ta siya mata rigar _black colour ce anyi mata ado da blue colour stone's_ tayi rolling da mayafin rigar duk da batayi make up ba she look very beautifully ta nemi gefen bed tayi zaune ta zabga d'an uban tagumi, zuciyarta cike da tunani yadda za'ayi tafita saboda tana masifar tsoron had'uwa da Habeeb idanuta suka cika da kwalla jin karar bud'e k'ofa yasa tayi maza ta goge hawaye fuskarta madam Hindu ce tashigo jikinta sanye da atamfar Sheraton tayi matuk'ar k'ar6a fatarta Haleesa me kikeyi a d'aki da har yanzu baki fito kiyi breakfast"?
Haleesa tayi murmushin yak'e tace mommy yanzu nakeso fitowa sai kuma ga ki'
To tashi mu tafi Haleesa na kamalla breakfast ta nufi 'karamin parlour ta zauna k'asa kamar yadda tasa6a, hankali madam Hindu tajuya wurinta, Cikin murmushi tace Haleesa har yanzu kin k'i kisaki jikinki sai wani d'ari-d'ari kikeyi Haleesa tayi murmushi had'e da sada kai k'asa 'kamshin turare intense man yacika parlour da sauri Haleesa d'ago idanuta suka sauka akan fuskarshi yana sanye da coat red colour da black colour trouser hannushi na cikin aljihu yayinda d'ayan hannun rik'e da file's fuskarshi a had'e Sam ba alama fara'a a tare da shi kaitsaye yanufi kusa da madam Hindu ya zauna kamar mai rad'a yace _Good morning mom_
Morning son da fatar katashi lafiya"?
_lafiya qalau mom_
Batare da Haleesa tad'ago tace ina kwana yaya Habeeb"?
Yayi ignoring nata tamkar wani kurma, yacigaba da maganarshi mom ga wad'anan documents za ki yi sign nasu zan wuce da su Abuja.
Madam Hindu ta bata fuska tace Habeeb bakaji Haleesa tana gaidaka"?
Ya yatsine fuska a wulaqance yace lafiya  sani halinshi da mom tayi yasa batayi masa complain akan yadda ya amsa gaisuwan da Haleesa tayi masa sai kawai tayi ignoring nashi had'e da k'ar6a documents d'in tayi signing phone d'inshi yayi ringing ya mik'e cikin yanayi tafiyarshi ta k'asaita yafice, yayinda a fakace Haleesa tabishi da kallo, cikin zuciyarta tace banza d'an girman kai shi wannan da Allah yayi shi gidan sarauta da bansan iya adadi iskanci da zai dinga tsulawa mutane, madam Hindu ta katsita ta hanyar kiran sunanta Haleesa kar6i file's d'inan ki kai ma Habeeb nasan halinshi da mantuwa zai iya tafiya ya manta da su daga baya yadinga yi min k'orafi cikin sanyi sanyi jikin Haleesa ta kar6i file's d'in tafice tana fita ta hango shi a parking space Bala driver ya bud'e mishi mota zai shiga tazara da ke tsakaninsu zai iya tafiya kafin tak'arasa sai kawai tayi decided ta kwala masa kira yaya Habeeb tafad'a da k'arfi batare da yajuya ba ya tsaya chak gani haka yasa Haleesa ta kwasa da gudu Habeeb da ke tsaye zuciyarshi tamkar za ta kama da wuta jin sautin gudunta, yak'ara harzu'ka ya tsani ya ga mace na gudu da sauri yashige mota Haleesa ta'karaso tana sauke numfashin gudu da tayi, tadafa k'ofar mota tace yaya Habeeb gashi mommy tace nakawo maka,
Da k'arfi yafisge file's d'in har yana had'awa da yatsun Haleesa garin fisgar file's  zobenta na azurfa yasa6ulle sakamako ramar da tayi zobe yadaina tsayuwa a yatsanta Haleesa ta matsa daga jikin motar tana yarfe hannu cikin k'unar zuciya yace da Bala kai! tsayuwar me kake yi ne"?
Jiki na rawa Bala ya bud'e k'ofa ya zauna a sit d'in gaba yayinda Aderwale driven madam Hindu yaja mota yanufi gate Haleesa tabisu da kallo daga bisani tanufi cikin gida zuciyarta cike, da d'ibin tsanar halaya Habeeb airport  Aderwale ya ajiye su fitowar da Habeeb zai yi daga cikin mota zobe yafad'o daga jikinsa ya duk'a yadauki zoben yana jujuya shi ras-ras gabanshi yafad'i sakamako ganin sunan da ke rubuce a jikin zoben ```NI DA YAYA HABEEB ``` Yafad'a a baiyane me wannan sunan yake nufi"?
Meyasa gabana yafadi anyya kuwa yarinya nan ba bibiyana takeyi ba"? nan take, yatuna da haduwarsu da kuma ganin da yayi mata a gidansu......


```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[15/09 12:29 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [14/09 10:56 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

                ```47```

Haleesa na Shiga cikin gida ta koma mazaunita ta zauna, madam Hindu ta dubeta cikin kulawa tace kin bashi file's d'in Haleesa"?
Haleesa tad'aga kai madam Hindu tacigaba da kallon tv yayinda Haleesa ta sada kai k'asa tasoma aikin nata{tunani} madam tajuya ta tsurawa Haleesa ido gani yadda ta zurfafa a tunani tausayinta yakamata nan take ta k'udiri anniya sai takawo karshen matsalar Haleesa saboda yarinya ta shiga ranta matuk'a.

```ABUJA```

Misali 'karfe _12:15pm_ flight d'in yadauko passengers daga Lagos yasauka a airport na Abuja, a hankali Habeeb Lamido yake saukowa daga stair's na jirgi Bala driver yana biye da shi a baya driven madam Hindu na Abuja ne ya yi picking nasu kaitsaye gidan Habeeb Lamido da ke Garki driven yadosa yayinda Habeeb Lamido ke ta fama da zance zuci na hadu da 'yan mata kala daban-daban ban ta6a haduwa da very smart girl irin Haleesa, zuciyata tana bani cewa Haleesa ta zo d'aukar famsa abunda na ta6a yi mata ko kuma ta fad'a a tarko sona shiyasa take bibiyana in kuwa d'aya daga ciki ya kasance gaskiya lallai sai na wulaqanta ta Co's ban ta6a haduwa da yarinya da naji farat d'aya na tsaneta irinta, kamar daga sama ya ji sautin muryar Bala driver yana fad'ar Boss mu iso gida Habeeb yasauke ajiyar zuciya had'e da yafito daga cikin mota.

```BAYAN KWANA BIYU ```

Haleesa na kitchen tana wanke plate's da cups d'in da sukayi amfani da su kasancewa yau Sunday Janet tana church, madam Hindu kuma tafita ba yadda batayi da Haleesa su fita tare Haleesa ta k'i a cewarta bataji dad'i cikin sanyi jiki take wanke plate's d'in K'amshin turare intense man da tashak'a ya haddasa mata fad'uwa gaba, Habeeb Lamido ne tsaye a k'ofar kitchen yana aika mata kallo mai cike da tsana Cikin tsanani tsoro Haleesa tajuya karaf suka had'a ido, da sauri ta sada kai k'asa Habeeb ya ja tsoki yak'arasa shiga kitchen d'in cikin muryarshi mai matuk'ar dad'i yafara magana kamar mai rad'a ke! Uban me kike jira a gidanan da har yanzu baki tattara komaitsa ki kibar mana gida"?
Wani irin shock yaja Haleesa jikinta yafara sharking, takasa furta uffan yadaka mata tsawa ke! Ba magana nakeyi da ke ba"?
Yak'arasa magana cikin k'unar zuciya muryarta na rawa tace Dan Allah kayi han'kuri ba laifina bane mommy ce har yanzu bata bani izzini tafiya gida.
_You're very stupid kina nufi mom ce mai laifi ashe bakida mutunci"?_
A lokacin d'aya mamaki had'e da tsoro sukayi nassara lullu6e Haleesa ko kwakwara motsi takasa yayinda haushinta yak'ara turnuk'e Habeeb a harzuk'e yafisgo hannuta yace wai ke me kike tak'ama da shi waye ubanki duk fad'in African da har zanyi miki magana kiyi ignoring nawa"?
Hawaye suka wanke fuskar Haleesa tsanar Habeeb ta kanainaye zuciyarta, da k'arfi ta fincike hannuta saidai kash takasa kwace hannu nata ranta a 6aci tace dallah malam kasake min hannu, kallon uku saura kwa6o ya watsa mata ya yatsine fuska cikin sigar wulaqanci yace ki kwace hannunki mana Haleesa ta girgiza kai tace kai kanka kasan da zan iya kwace hannun nawa ba bazan tsaya ina rok'a mutume da baisan daraja da k'imar d'an Adam irinka.......
[14/09 11:02 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu

                ```48```

Da k'arfi Habeeb ya murde mata hannu yace kin tafka babban kuskure na shigowa rayuwata tuni nagano cewa kina bibiyana, kuma sai na tabbata miki da cewa bansan daraja da k'ima mace banza 'yar iska irinki mai bin d'an namiji har gidansu da wannan Neman gindi zama da kike yi a wurin mom da fitowa kika yi kika fad'a mata gaskiyar dalili zuwanki gidanan.
Haleesa ta zaro manya idanuta masu cike da tsoro ta hadiye miyau masu masifar d'aci ta rushe da matsananci kuka tace karka jefeni da mummuna kalma yaya Habeeb don ina zaune a gidanku bashi zai baka damar ka fad'a mini magana son ranka, ka tambaye mahaifiyarka za ta fad'a maka dalilin zama na a gidanku. Habeeb ya galla mata harara had'e da cewa ke! Munafuka ni fa nagano cewa abu biyu ne yakawo ki a gidanan  kodai kin zo daukar famsa wulaqanci da nayi miki a baya ko kuma kin zo neman soyayyata jin wannan furuci na Habeeb yak'ara rud'a Haleesa ta runtse idanuta tana kuka kamar ranta zai fita saboda zafi biyu Habeeb Lamido yahad'a mata ga zafin murd'e mata hannu da yayi ga kuma na magaganu da yake ta faman gasa mata, yayinda Habeeb yacigaba da cewa bara na fad'a miki ko a k'afa aka daura min ke zan kwance na yar Co's nafi k'arfinki  infact ban ta6a jin na tsani wata 'ya mace sai akanki don haka kidaina yaudara mom ta hanyar ihun da kike yi kina cewa yaya Habeeb ya mutu ba zai ta6a dawowa gareki wai ke ga ki 'yar duniya Haleesa ta bud'e idanuta tasoma watsawa Habeeb kallon mamaki daga bisani tace tir da wannan duk'usashiya kwakwalwa taka da har ta tasanya maka tunani cewa ni Haleesa ina sonka me zanyi da kai bana d'aya daga cikin shashashu 'yan mata da kudinka da kyakyawa surarka za su rud'a kuma yau d'inan zan bar maka gidanku bara ka k'ara ganina ba har abada Habeeb Lamido ya ja tsoki wulgar da hannunta da k'arfi ya juya cikin tafiyarshi ta k'asaita yafita daga kitchen d'in Haleesa ta dur'kushe 'kasan tile's tafashe da kuka tasoma danasani zuwa garin Lagos da kyar ta mik'e tsaye ta nufi room d'in Hannah tafad'a kan bed tafara zance zuci ashe Habeeb Lamido mahaukaci ne in banda hauka don kawai ya ganni a gidansu zai ce ina sonshi mtss shashasha kawai mai k'aramar kwakwalwa nan take tafara tunina rayuwarta da yaya Habeeb da yaya Habeeb yana raye me zanzo yi a garin Lagos da har wannan arrogant zai same damar wulaqantani, Haleesa tacigaba da shashekar kuka madam Hindu ta murd'a handle tashigo d'aki ta hango Haleesa kwance tana kuka da sauri tanufe ta Haleesa lafiya me kike yi ma kuka"?
Cikin muryar kuka Haleesa tace mommy gida zan tafi, inaso gani Ammi naa nagaji da garinan tak'arasa magana had'e da rushewa da kuka madam Hindu ta rungume ta tace haba Haleesa don kinaso zuwa gida shine za ki dinga kuka"?
Yi maza ki share hawayenki ki tashi mu tafi na ajiye ki gidan Juwairiyya gobe masa'ud yasaka ki a flight ki koma Yobe da sauri Haleesa ta k'ank'ame mommy tace na gode mommy Allah yasaka miki da alkhairi, madam Hindu tad'ago ta tana murmushi tace Ameen Haleesa 'yar gidan mommy jiki na rawa Haleesa ta had'a kayanta madam Hindu sai faman dariya take yi mata had'e da tsokanarta a haka suka fice daga gidan zuciyar Haleesa cike da farin ciki tabar ma Habeeb gidansu, suna isa gidan Juwairiyya tun kafin Aderwale yabude mata k'ofa ta bud'e da kanta tafito Aderwale yabud'ewa madam Hindu k'ofa tafito tana dariya tace Haleesa sai murna kike yi za ki tafi kibar mommy koh"?
Haleesa ta rufe fuskarta da tafin hannuta Juwairiyya nagani su tafara washe hak'ora saboda kullum sai yaya salman ya kira waya ya tambayi Haleesa, madam Hindu ta zauna a parlour yayinda Haleesa tanufi d'akinta juice da ruwa masu sanyi Juwairiyya takawowa madam Hindu ta tsiyaya mata, a glass cup ta mik'a mata kur6a d'aya zuwa biyu madam tayi ta ajiye cup d'in bisa stool tajuyo tana facing Juwairiyya, tace Juwairiyya akwai magana mai matuk'ar mahimmanci da nakeso zanyi da ke akan Haleesa.....

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```



 ```NI DA YAYA HABEEB ```

_the sweetest love_
```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu

                ```49```

Tun daga lokacin da nadaura  idanuna akanta naji tashiga raina matuk'a, nayi matuk'ar tausayawa Haleesa a dalilin labari rayuwarta da yaya Habeeb da tabani gani halin da take ciki da Kuma yabawa da ingantaciya tarbiya da takeda ita yasa na yi wa d'ana Habeeb sha'arwata ko ba komai tarasa Habeeb ga kuma wani Habeeb yadawo watakila ko don sunan Habeeb kadai zai iya saka tarage tunani marigayi Habeeb bansaniba ko iyayyenku za su amince su ba wa Habeeb aureta har madam Hindu ta dasa aya Juwairiyya tana mata kallon mamaki daga bisani tace mommy karki ce na katsi miki hanzari sai naga kamar Haleesa bata dace da Habeeb ba saboda mu talakawa ne duk zuri'armu ba mai kud'i Juwairiyya tak'arasa magana had'e da sada kai k'asa, madam Hindu tayi murmushi tace Juwairiyya Yakamata ki bada kyakyawa sheda akaina da zuri'arta bana d'aya daga cikin masu kud'in da ke kyamar talaka a wurina mai kud'i da talaka duk d'aya ne shawara na zo neman a wurinki ya kamata ki k'arfafa min guiwa domin na cima aikin alkhairi da nayi niyya karki manta shekaru biyar a baya da suka wuce Habeeb yarasa matarshi a waje haihuwa, dalilin haka yakasa k'ara aure Juwairiyya ina buk'atar Habeeb ya yi aure saidai duk lokacin da na tuntube shi da zance aure sai yace na nemo mishi matar aure, ni kuma narasa yarinya da zan nemo masa wance za ta soshi tsakani da Allah ba don kud'inshi ko kyakyawa sura da Allah yabashi sai gashi kwatsan Allah yakawo min Haleesa har gida, kuma ta cika duk wasu sharudd'a da nakeso matar Habeeb ta kasance da su Juwairiyya tasauke ajiyar zuciya tace shikenan mommy sai kifara sanarda Habeeb in ya amince da Haleesa a za6inki daga bisani sai a sanarda iyayyenmu domin su ne kadai a halin da Haleesa take ciki za su iya tankwarata ta amince da zance aure.
Habeeb bashida matsala Juwairiyya duk abunda nakeso shima yanasonshi bamu ta6a samu sa6ani ra'ayi, Haleesa ta d'aga hankalinta tana buk'atar ganin Ammi karki hanata tafiya ni kuma zanyi amfani da wannan damar naje Yobe na nemawa Habeeb aureta.
Ba matsala mommy duk yadda kika ce haka za'ayi'
"Madam tayi murmushin farin ciki tace kira min Haleesa mu yi sallama, Juwairiyya ta mik'e tsaye tana washe hak'ora kamar mai talla toothpaste Haleesa na kwance Abba na bisa cikinta yana wasa doki, Juwairiyya tana dariya tace wannan k'aton yaro za ki aza bisa ciki yana doki sai yafasa miki ciki, Haleesa ta mik'e zaune tace Abba naa ba k'ato bane, Juwairiyya ta tabe baki had'e da cewa ki taso Ku yi sallama da "mommy za ta wuce Haleesa ta mik'e tsaye suka fice tare Madam nagani Haleesa ta'kara fad'ad'a murmushinta tace Haleesa ni zan wuce ki gaida Ammi kafin nazo mu gaisa.
"To mommy zai taji na gode sosai da d'ibin alkhairi ki agareni madam ta zuge zip handbag d'inta tafito da bundle na dubu d'ari ta mik'awa Haleesa gashi Haleesa ki yi wa su Ammi tsaraba Haleesa ta girgiza kai had'e da cewa hidima da kike yi da ni mommy tayi yawa ba zan kar6i kud'inki ba.
Madam ta mik'e tsaye ta mik'awa Juwairiyya kud'in Juwairiyya takasa k'ar6a kad'a kai "madam tayi batare da tace komai ba ta ajiye kud'in bisa hannu kujera, tajuya tafice cikin sanyi jiki Haleesa da Juwairiyya suka Mara mata baya da sauri Aderwale yafito ya bud'ewa madam mota, tashiga Haleesa ta dafa k'ofa tace mommy narasa da wance kalma zaiyi amfani da ita wurin gode miki, banida abunda zan saka miki da shi mommy saidai, zan cigaba da yi miki addu'ar fatan alkhairi ke da zuri'arki.
Madam tayi murmushi da ke nuna taji dad'i kalamai Haleesa daga bisani tace ba komai Haleesa ni na d'auke ki tamkar Hannah, Haleesa da Juwairiyya suna tsaye har motar madam tafice daga gate d'in gidan sannan suka juya zuwa cikin gida, Haleesa tafad'a bisa kujera ta ja wata doguwar ajiyar zuciya Juwairiyya ta zauna kusa da ita cikin sanyi murya tace Haleesa meyasa kike so komawa Yobe alhali da bakinki kika ce sai kinyi _3 week's_ za ki koma gashi _1 week_ kawai kika yi kince za ki koma ko anyi miki wani laifi ne"?
"Ba abunda akayi min kawai dai nagaji da garinan
Shikenan bara na shirya na rakaki kasuwa gobe sai ki bi morning flight"
Murmushi Haleesa ta yi, cikin zuciyarta tace hakan shi zai saka Habeeb Lamido yagano kwakwalwa da zuciyarshi sun cuce shi da suka haska masa cewa na zo Lagos ne saboda shi, ta yatsine fuska a baiyane tace _disgusting_ Juwairiyya ta zaro idanu tace lafiya kike Kuwa Haleesa"?
"Yes am absolutely fine
Murmushi Juwairiyya tayi ta mik'e tsaye had'e da cewa ki je ki d'auko mayafinki mu tafi batare da ta jira amsar da Haleesa za ta bata tashige bedroom d'inta.
Yinin ranar sun k'arace shi ne a yawon siye banza siye wofi ba su ne suka dawo gida ba sai ana kiran sallah magariba, don haka a gajiye suka shiga cikin gida kaitsaye kowane su yanufi bedroom d'inshi Haleesa ta jefarda mayafinta bisa bed tanufi bathroom tayi alwala bayan ta gama sallah ta zabga tagumi tasoma tunani Habeeb Lamido zuciyarta cike da mamaki shi wai ina bibbiya shi to me zan tsinta a wurinshi mtss mahaukaci kawai marar tunani, da kyar ta samu ta rinjaye zuciyarta tabarta ta gabatarda sallah isha dawowar masa'ud yasa tafito parlour ba rarrashin da banyi mata akan tayi zamanta koda  _1 week_ ne ta'kara musu amma Haleesa ta k'ek'ashe k'asa tace ita dai tafiya za tayi dole masa'ud ya kyaleta......
  ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu

               ```50```

```WASHE GARI ```


~~Da wuri Haleesa ta tashi ta yi wanka tana jiran fitowar Masa'ud yakaita airport, saida yagama ja mata rai sannan yace tafito su tafi koda tafito _10:30am_ ta buga gashi flight d'in da zata bi zai tashi k'arfe _11:30am_ sai faman complaints take mishi ya6ata mata lokacin Juwairiyya sai faman dariya take yi gani yadda Halee take zumud'i tafiya saida suka ga tashin jirgin su Haleesa sannan Masa'ud da Juwairiyya suka nufi gida.

```YOLA```

Jirgi na sauka bayan Haleesa tafito batare da 6ata lokacin ba, taja trolley d'inta taxi tashiga tana gani driven taxi d'in yashiga unguwarsu tasaki sanyaya ajiyar zuciya tasaki iska ta furzar tace _Home, sweet Home_  har k'ofar gidansu taxi d'in tayi parking cikin zumud'i ta balle k'ofa tafito, dai-dai lokacin da Hasheem 'kanin marigayi yaya Habeeb yafito daga cikin gida Haleesa ta tsura masa ido da sauri-sauri numfashinta yake fita saboda sai yau ta'kara tabbatar da tsanani kama da Hasheem yakeyi da Yaya Habeeb banbanci su kawai yaya Habeeb yafi shi, tsayi gani yadda take kallonshi yasa yasake mata murmushi yak'araso daf da ita cikin tsokana yace babylove ya akayi ne naga kin wani tsare ni da ido sai kace yau kika fara ganina ke da kika je Lagos a maimako ki waye sai kika k'ara kwaso k'auyanci.
"Ko kwakwara motsi Haleesa ta kasa yi da k'arfi Hasheem ya kira sunanta Haleesa!
Haleesa ta dube shi tayi ajiyar zuciya, kafin ta yi magana mai taxi yace malama sallame ni na tafi Hasheem yace nawa ne kud'inka"?
D'ari uku ne yallabai Hasheem yafito da _N 500_ ya mik'a masa shi kuma ya bashi chaji yadauki trolley d'inta ya wuce gaba tana biye da shi sai tambayoyi yake zuba mata yayinda Haleesa takasa bashi amsar ko d'aya daga ciki da sallama yashiga cikin gidan had'e cewa Ammi fito ga bak'in Lagos da rana tsaka da sauri Ammi tafito daga d'aki tana gyara d'auri d'an kwalinta tana had'a ido da Haleesa mamaki ya baiyana akan fuskarta da gudu Haleesa ta'karasa wurinta ta rungume ta tasa kuka Ammi ta bubbuga bayanta, haba! Haleesa meye kuma abun kuka"?
Cikin muryar kuka mai cike da shagwaba tace Ammi nayi kewarki'
Hasheem da ke gefe ya kyalkyale da dariya yace lallai yarinya nan dad'i ya yi miki yawa ki ce kukan dad'i kikeyi to ni zan tafi anjima zan dawo na kar6i tsaraba na yak'arasa magana had'e da yaficewa.

```3 hour's later```

Haleesa na zaune a d'akin Ammi sai labari madam Hindu take ba wa Ammi, kwarai Ammi ta yaba da kirkin "madam Hindu
Tace duk lokacin da tashigo Yobe zata zo Ku gaisa.
Murmushi Ammi tayi tace Allah yakawo ta lafiya
"Ameen Ammi bara na je na gaida inna mairo ta zari hijab d'inta had'e da ficewa, tana Shiga gidan zainab ta shek'o suka rungume juna sai da aka fara kiran sallah magariba Haleesa ta koma gida  bayan ta gama sallah tafito tsakiyar gida tasha iska yaya salman ya yi sallama yashigo, Haleesa ta amsa mishi, ya zauna kusa da ita tana bashi labari Lagos Salman ya kyalkyale da dariya yace Haleesa manya ke da kika yi _1 week_ kacal a Lagos har wani labari za ki bayar
Haleesa ta turo baki tace Allah yaya salman nayi yawo saidai ba sosai ba kuma baka ga gidan da na zauna Allah gidan yahad'u kamar a abroad ae kuwa Salman da kamal suka dinga yi mata dariya Haleesa ta gallawa kamal harara tace gwara ni na je lagos nayi kauyanci kai kuma kamal baka ta6a zuwa ba tak'arasa magana had'e da yi masa gwalo har baffa yashigo gida suna zaune tsakiyar gida suna fira shima ya zauna akayi firar da shi kowane su zuciyarshi cike da tsan-tsan farin ciki sakamako gani yadda Haleesa take annashuwa da nishad'i sai misali k'arfe _11:44pm_ kowane su yanufi d'akinshi Haleesa tasuya kaya zuwa wata 'yar k'aramar vest ta daura zani bisa ta kwanta tana daura kanta bisa pillow ta lumshe idanu  nan take  face d'in Habeeb Lamido yafara yi mata shawagi a eye's nata da sauri ta bud'e idanuta _"why Habeeb why don't leaves my heart to be in peace"?_
Ba gidanku kadai ba har garin Lagos na baro maka _but you still following me_
Hawaye suka ziraro mata a gefen idanu suka sauka bisa wuyanta, kuka Haleesa tayi sosai daga bisani bacci ya yi awo gaba da ita anan ma bata tsira ba saboda mafalki shi tadinga yi Habeeb ya zamewa rayuwarta karan tsaye.

```BAYAN SATI D'AYA ```

Haleesa da zainab sun dawo daga islamiyya yamma suna tafiya suna fira, tun daga nesa Haleesa ta hango mota kirar _KIA cerato_ a Parke a k'ofar gidansu wani matsananci fad'uwar gaba taji saboda ta ta6a gani Habeeb Lamido cikin irin wannan motar, zainab tace Haleesa bak'i masu kud'i mu ka yi ne na hango had'ad'iyar mota a k'ofar gidanmu"?
Haleesa tad'ago ta dube ta tasauke ajiyar zuciya tace oho! Tafad'a kaitsaye suna k'arasawa k'ofar gida idanu Haleesa suka sauka bisa number motar _Habeeb Lamido 5_  abunda idanuta suka hasko mata kenan tsanani tsoro had'e da tashin hankali suka chukuikuye mata zuciya Wanda hakan ya haddasa mata zaro idanu tanemi yawu bakinta tarasa, a zuciyarta tace na shiga uku me wannan shu'umi ya zo yi a gidanmu..."?



```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```


Jeeddah Aliyu
[30/12 9:53 am] aliyujeeddah: [05/09 4:07 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

```®NWA```

 Na Hauwa Shehu Aliyu

               ```43```

Zaune take ta rakka d'a uban tagumi sallamar Madam Hindu ce tadawo da ita natsuwarta, da sauri tanufi wurinta, sannu Haleesa kintashi ya jikin naki"?
Murmushi Haleesa tayi tace I'm okay mom ba abunda yake min ciwo
"Alhamdulillah hankalina ya yi matuk'ar tashi Haleesa da naganki cikin wannan hali har naji a raina lallai ya Zame mini dole na tambaye ki waye yaya Habeeb"?
Tuni idanu Haleesa sun ciko da kwala ta sada kai k'asa cike da tausayi madam Hindu tarik'o hannuta karki kiyi kuka Haleesa in har wannan tambaya nawa zai haifar miki da tashi hankali to kiyi han'kuri karki fad'a kinji"?
Haleesa ta share hawaye had'e da majina tad'ago jajaye idanuta cikin sark'ewar halshe, tafara bawa madam Hindu labarin rayuwarta da yaya Habeeb tana dasa aya ta rushe da kuka mai matuk'ar sautin gaske, madam Hindu ta rungume ta tana sharar hawaye domin ita kanta labari Haleesa ya matukar bata tausayi, cikin tausasa halshe tafara rarrashin Haleesa ta hanyar furta mata kalamai masu dad'i Haleesa ta share hawayeta tace mommy narasa yaya Habeeb yatafi yabarni da soyayyarshi a zuciya a kullum tunani nakeyi anyya zan samu Wanda zai so ni  kamar yaya Habeeb"?
Za ki samu Haleesa in har kika saka hank'uri da tawakalli Allah zai kawo miki wanda yafi yaya Habeeb Murmushi kawai Haleesa tayi domin tasan abunda madam Hindu take fad'a ba zai ta6a kasancewa gaskiya ta lafe a jikin mommy tana sauke ajiyar zuciya.

```3:00pm```

Madam Hindu da Haleesa na zaune a _dining table_ Janet na gefen su tsaye yayinda Haleesa ke ta fama jujuya spoon d'in hannuta zuciyarta cike da zullumi yadda za ta ci abinci da ke gabanta.
A hankali yake taka stairs hannaye shi na cikin aljihu "black Jean's d'in da yake sanye da shi jikinsa na fitarda k'amshin turare intense man fuskarshi a had'e tamkar tsohon soja kallon d'aya Haleesa ta yi masa ta kauda fuska, yayinda shi kuma ko kallo bata isheshi ba da sauri Janet taja masa kujera ya zauna wani wulaqantace kallo ya watsawa Janet ya doshe hancinshi yana yatsinar fuska tuni Janet ta nisanta da shi saboda ta fahimce da ita yake madam Hindu ta dube shi tana murmushi tace son me ke faruwa naga ka doshe hancinka"?
"Very slowly yafara magana mom bakyaji yadda parlour nan ya gume da odour"?
Humm! Habeeb rigima sarki 'yan kyayami ni ba abunda naji tajuya wurin Haleesa tace Haleesa ko ke kinji wari a parlour"?
Girgiza kai Haleesa tayi cikin rawar murya tace nima  mommy ba abunda naji.
Cike da jin haushin Haleesa Yaja tsoki sanin halinshi da mommy tayi yasa da kanta tayi mishi  "serving yatsine yake cin abinci sai wani ya6ata fuska yakeyi, sai lokacin madam Hindu ta lura da Haleesa bata cin abincinta Haleesa ki ci abinci ki mana
Haleesa tad'ago ta dube mommy tace toh! Ta tsurawa abincin idanu fried rice with pepper chicken da had'e com slow a sama sai d'an uban Bama cream da Janet ta yaya6a mata duk duniya ba abunda Haleesa ta tsana irin Bama cream masifar wari shi takeji, tun ranar farko zuwanta Lagos yaya masa'ud ya yi musu take away na jallof rice aka saka shi tanaci saida tayi Amai kunya takeji tace da mommy bataci Bama cream kada wannan Mr arrogant yadauke ta a matsayi _villager_ Haleesa ta sauke numfashi ta ciko spoon ta kai bakinta runtsi idanuta tayi ta hadiye abinci yasoma ratsa throat nata duk iya k'ok'ari Haleesa nagani abincin yashiga hanjinta abun yagagara sakamako wani amai da yataso mata da sauri ta furzar da na bakinta tasoma kakari a firgici madam Hindu tarik'o ta "what's worry Haleesa"?
Haleesa takasa magana sai faman yun'kuri amai takeyi madam Hindu tajuya wurin Habeeb da ke cika yana batsawa jin yakeyi tamkar ya shak'o Wuyan Haleesa ya gagaura mata dirty Slave's tace "please son halp me with glass of water
Cikin zafin rai Habeeb ya mik'e yature kujera yafice daga dining area a zuciyarshi yace in har sai na bata ruwa ta mutu madam Hindu ta mik'e da kanta tadauko robar ruwan faro ta mi'kawa Haleesa da sauri ta k'ar6a tasha tad'ago idanunta da sukayi jajir madam Hindu tace sannu Haleesa murmushi mai cike da jin kunya Haleesa tayi tace yauwa mommy"
Yakamata na kira doctor Elizabeth ta duba ki.
 Haleesa ta girgiza kai had'e da cewa no need mom dama banaci wannan abin duk lokacin da naci shi sai nayi amai ta'karsa magana had'e da nuna Bama cream da yatsanta dariya mommy tayi sosai Haleesa na tayata daga bisani ta tsagaita dariyar nata ta dungurewa Haleesa kai tace next time in har zuciyarki bayaso abun karki kara ci kinji"?
Haleesa tad'aga kai madam Hindu tasake yi mata serving d'in wani abinci, hankali kwance Haleesa take ci abincinta
Kinga kin kore mana wannan sarkin kyakyami abun kad'an ya haddasawa Habeeb tashin zuciya shi mutum ne matuk'ar tsafta gaske tsaftarshi har ta zarce ta masu hankali har madam Hindu ta dasa aya a zanceta Haleesa tana kallonta......
[05/09 9:48 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu

             ```44```

~~Murmushi Haleesa tayi tace mommy yana da gaskiya tsafta cikon addini, madam Hindu ta tabe baki tace Tsaftar Habeeb ta fitar hankali ce'
A wannan karo Haleesa rasa abun fad'a tayi sai kawai tasaki murmushi madam Hindu ce tafara kamalla cin abinci ta mik'e tsaye tace Haleesa in kin gama ina downstairs parlour Haleesa tad'aga kai tana gani madam Hindu tafice ta ajiye spoon tadafe goshinta tafara zance zuci "how long zan dauka a gidanan"?
Miyasa duk lokacin da naga Handsome nake rasa peace of mind"?
hawaye suka cika mata ido a baiyane tace I miss you yaya Habeeb da kana tare da ni da duk banshiga wannan halin ba I really miss you yaya Habeeb no matter where I'm I'll never ever forget your memories"
Bayan hannuta tasaka ta goge hawaye fuskarta, ta mik'e tanufi downstairs parlour madam Hindu na zaune a two star yayinda Habeeb yake zaune a k'asa ya jingina kansa jikin kujera yayi "crossing leg's nashi ya lumshe, idanu kamar mai bacci Haleesa tayi chak tana tunani ta yadda za'ayi ta'karasa parlourn madam Hindu na d'agowa ta hango ta tsaye tace Haleesa ki 'karaso mana Haleesa tamkar za ta fasa kuka tasoma tafiya zuciyarta cike da tsoron Habeeb jikinta na shacking tashiga parlour Sam bata lura da 'kafafu Habeeb ba jin tayi kamar ta taki wani abu tana sauke idanu ta k'asa taci Karo da k'afarta akan k'afafu Habeeb saura kiris tasaki fitsari a tsorace ta dube shi still idanushi a rufe da sauri ta sauke 'kafarta tajuya wurin madam Hindu taga hankalinta na waje TV tasaki ajiyar zuciya ta zagaye k'afafushi tanufi kusa da k'afafu madam Hindu ta zauna a k'asa madam Hindu tace tashi ki zauna akan kujera girgiza kai Haleesa tayi cikin sar'kewa halshe tace "No mommy nan ya isa  nima nafi jin dad'i zama a k'asa madam Hindu tayi murmushi tacigaba da kallonta cikin zuciyar Haleesa tace thank god da guy nan ya ji lokacin da na take shi "He' gonna kill me a karo na biyu ta'kara kallonshi idanu shi a rufe ta tsurawa lips d'inshi ido ta tabe baki had'e da fara zance zuci kalli lips nashi very pink da su maybe yana using lipstick yana matsayin namiji yana Shafa lipstick wannan ae abin kunya ne mtss d'an daudu kawai da sauri ta kauda fuskarta da bari kallonshi.
Duk abunda takeyi Habeeb yana kallonta ta 'kasan ido a zuciyarshi yace _what's hell dis crazy girl looking at my face"?_ ta taka min 'kafa but she staring me just like plasma tv mtss I hate dis girl for d first time my eye's saw on her.
Mtss Haleesa ta'kara
Jan tsoki a zuciyata tacigaba da zance zuci ta _I don't known why anytime my eye's Shaw dis arrogant man  I feel like crazy_ wata zuciya tace da ita ke Haleesa ina ruwanki da shi ki yi abunda yake gabanki shi d'in He doe's Care about you lokacin da ya ganki Sam bai nuna yata6a saninki "so forget about him tak'ara satar kallonshi ta yatsine fuska watakila bacci yakeyi naga tun lokacin da nashigo parlour nan idanu shi a rufe kin ji ki da wani zance banza Haleesa da ba bacci yakeyi ba da you're d first person da za ki sani Co's da yanzu ya falla miki mari ko kin manta kin taka 'kafarshi Haleesa tasaki ajiyar zuciya mtss nagaji da wannan zance zuci zuciyata ki barni na huta ta sada kai k'asa.
A zuciya Habeeb yace oh! God mommy akwai kwashe-kwashe ko zama me wannan crazy girl takeyi a gidanan oho"?
Gaskiya nagaji da gani ugly face nata I'll pack my luggage to leaves dis House be for I loose my temper nayi mata rashin mutunci har wani sunan ta rad'a min wai aljani mai idon magge ni ban kirata da suna aljana ba sai ita ce za ta kirani da aljani k'aramar yarinya kawai.
Madam Hindu ce tayi nassara katsi masa zance zuci da yakeyi ta hanyar kiran sunanshi Habeeb bai dai bacci  kake yi a zaune ba"?
Ya bud'e idanushi yace idanu na biyu mommy ba bacci nakeyi ba
Cikin tsanani tsoro Haleesa tad'ago dama guy nan idanu rufe su kawai ya yi ba bacci yakeyi ba na shiga uku ni Haleesa tuni jikinta ya jik'e da gumi Bala driver ne yayi sallama yashigo falon yana kyalla ido ya ga Haleesa yadaka wani uban tsalle yana murza idanu shi yace boss yakasa furta abunda yakeso fada sai faman maimaita sunan Boss yakeyi madam Hindu tadaka mishi tsawa kai! Bala wannan wane irin sakarci ne"?
Ina matuk'ar yabawa k'o'kari Habeeb da yake iya zama da kai wani abin mamaki duk inda ya jefa k'afa yana tare da kai.
Bala driver yacire fencing cap yasoma fifita da ita yace madam wallahi aljana nagani a parlour nan, mtsss Habeeb yaja dogon tsoki ya mik'e cikin zafin rai da sauri Bala yanufi wurinshi yace Boss dubi chan ka gani aljanarka ce a zaune dama ni nasan za ta biyo ka kasan aljannu sun fi so kyawawa irinku ka shiga uku boss aure ka za tayi cikin tafarfasa zuciya Habeeb ya wanka masa mari shut up Bala I think you are insane yature Bala ya haura sama da gudu a tsorace madam Hindu tajuya wurin Bala tace aljana kuma Bala ina aljanar take"?
Bala yanuna Haleesa da yatsa yace gatanan zaune kusa da ke madam sau uku muna haduwa da ita a Yobe kuma kowane haduwa da mu kayi da ita sai yadauki dogon lokacin kafin mu sake ganita
Madam ta kyalkyale da dariya tace Bala wannan Haleesa ce ba aljana ba amma zo ka bani labari yadda haduwarku ta kasance nan take Bala ya kwararo wa madam Hindu labari haduwarsu da Haleesa madam Hindu tace Haleesa abunda Bala yafad'a gaskiya ne"?
 Haleesa tad'aga kai miyasa baki sanarda ni kinta6a haduwa da Habeeb ba"?
Mommy gani nayi haduwar batada mahimanci, tafad'a cikin rawar murya madam Hindu tayi shiru alamar tunani nan take zuciyarta tafara sak'a mata wani abu......

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S```

Jeeddah Aliyu

1 comment:

  1. This is another must read and one of the best hausa Novel HUBBUL YAQEEN http://share4world.com.ng/2019/03/24/hubbul-yaqeen/ enjoy free readings

    ReplyDelete