```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```1```
Yarinya ce 'yar kamani _16-17yrs_ tana tafiya a hankali hannuta rik'e da _food flask_ tana sanye da atamfar _novou_ blue da touch's d'in yellow da hijab _yellow colour_ kaitsaye ta doshi wani shagon d'inki mai suna ```Ni da yaya Habeeb Teilorings center```
tana shiga shagon yanayi annuri fuskarta ya d'auke chak, kamar anyi ruwan sama an d'auke tayi tsaye tana k'arewa samari hudu da ke ciki shagon kallo yayin da idanu ta suka ciko da kwalla cikin zafin rai tanufi wurin saurayin da ke _facing_ d'in k'ofar shigowa shagon tadire masa _food flask_ cikin sark'ewa murya tace yaya salman ga abinci na kawo maka Wanda aka kira da suna salman sai lokacin yad'ago tsanani kamanu shi da yarinyar suka baiyana, fuskarsa a murtuk'e alamu babu wasa a tare da shi yace don gidanku kin saba kawo min abinci ne"?
Da sauri d'aya daga cikin samarin Wanda ke zauna daf da wata kyakyawa budurwa tana nuna masa _styles_ d'in d'iki a wayarta tun lokacin da yarinyar tashigo shagon ya sada kai k'asa alamu rashin gaskiya ya tari numfashi sa ta hanyar cewa haba salman miye haka"?
Tsoki yaya salman ya ja cike da jin haushi, yace wallahi Habeeb ina tausaya maka yarinya k'arama tana juya ka kamar waina a tanda sai an waye gari ta Kore maka _customers_ tass sannan za ka yi hankali in ka aure ta naga da uban da za ka ciyar da ita, ke kuma me kike jira ne"?
maza ki koma gida kuma duk ranar da na k'ara gani k'afar ki a shagonan sai na balla ki wannan wace irin fitina ce sai kace akanku aka fara soyayya ina lissafi a sati nan ak'alan Haleesa ta Kore mana _customers_ sun fi 10 za ki fita ko sai na taso na falla miki mari"?
Da gudu ta fice daga shagon tana kuka ta nufi gida.
A fusace yaya Habeeb yace banaso abunda kake yi min salman, ka fi kowa sani duk fad'i duniya ba abinda na tsana irin bacin rai _baby love_ amma shine don tsabar wulaqanci had'e da musgunawa zuciyata kayi mata Koran kare.
Salman ya galla masa harara cike da jin haushi yace wallahi Sa'a kayi da banyi mata dukan tsiya in yaso gaba d'aya zuciyar taka ta tarwatsi har yaya salman yadasa aya yaya Habeeb yana watsa masa mugun kallo mai cike da jin haushi, daga bisani yaja dogon tsoki yanufi k'ofar fita daga shagon da sauri kyakyawar burduwa tace Habeeb ya za'ayi katafi batare da mun gama magana ba"?
Harara ya galla mata yace ke har kina tsanmani ina da kwanciyar hankali da za ki yi magana da ni"?
Ga salman nan ki yi masa bayani d'ikinki in nadawo ya sanarda ni yana k'arasa magana yasa kai yafita, yaya salman ya ja tsoki had'e da cewa shege namamajo yayin da raguwa samari da ke shagon suka kyalkyale da dariya shak'iyanci.
Gudu takeyi tana kuka mutane da ke wuce sai kallota sukeyi, wanda suka santa kuwa sai tambayar ta sukeyi Haleesa lafiya kike kuka"?
Amma ko kallon basu eshe ta ba muradinta taga ta kai gida, tana shiga zaure gidansu taci karo da katuwar akuya Ammi ta korota saura kiris ta bangaje ta daka tsalle a gefe d'aya akuyar na ficewa ita kuma ta danna kai Ammi na tsaye da bulala rik'e da hannuta da alama da bulala tayi amfani ta kori akuyar, tana shiga tsakiyar gida ta cire takalmi ta had'e da hijab ta jefar ae kuwa sai bisa tukunya ruwa hijab d'in yafad'a tasaki kuka mai matuk'ar sautin gaske ta shige d'akin Ammi ta fad'a bisa gadonta na _silver_ tayi rub da ciki tana shasshekar kuka kamar raita zai fita.
A tsorance Ammi tashigo d'akin ta daka mata tsawa ta hanyar cewa ke lafiya kika shigo mini gida kina wannan taratsi na fitar hankali"?
Batare da ta juya ta kalli Ammi ba cikin dasashiyar murya tace Ammi yaya Habeeb nagani tare da wata a shago suna fira, Ammi bakiji irin zafin da nakeji a zuciyata duk lokacin da naga yaya Habeeb yara6i wata 'ya mace jin nakeyi kamar zan yi hauka kum.....kee! Ammi ta daka mata mahaukaciya tsawa da tayi sanadiya da ta hadiye sauran kalamai ta, cikin takaici Ammi tafara fad'a wai ke Haleesa wace irin fitaniya yarinya ce ke"?
Wane irin hauka da shirme k'urciya ne yake da mu ki"?
Domin wannan abun naki ba kishi bane shirme ne da tsabar samun wuri to ki bud'e kunne ki da kyau ki saurara, ni saboda nafara gajiya da wannan iskanci naki uwarki ce ta Haifa miki Habeebu da za ki ce ba zai kula kowace 'ya mace ba sai ke"?
ko don kina tak'ama Habeebu d'an uwanki ne shiyasa kike yi masa abunda kika ga dama shi kuma shashasha yana biye miki, don haka kiyi maza ki rufe min bakinki tun kafin raina ya baci na lakkada miki shege duka.
Nan take ta hadiye kukan ta saboda tasan halin Ammi kad'an daga cikin aiki ta ne, yanzu nan za ta had'a mata jini da majina don haka ta rufawa kaita asiri ta hadiye kuka ta Ammi ta ja tsoki ta fice daga d'akin had'e da cewa kuma kifito ga wanke-wanke yana jiranki.
Ba yadda ta iya dole ta mik'e jiki a sab'ule ta fito tana sharar hawaye had'e da majina da ke tsiyaya daga hancita, kaitsaye bakin famfo ta nufa inda tuli kwanuka wanke-wanke ke jiranta kujera 'yar tsuguno ta d'auko ta zauna ta fara wanke kwanuka lokacin-lokacin tana share hawaye da baya hannuta zuciyarta cike da jin zafin yaya Habeeb wai miyasa Ammi da yaya salman suka kasa fahimtar cewa tsabar son da nake yiwa yaya Habeeb ne yake haddasa mini matsananci kishinsa"?
_Assalamu Alaikum_
Sallamar yaya Habeeb ce ta katsi mata zance zuci da takeyi da sauri ta d'ago kaita
_wa'alaikum sallam_
Ammi da ke _kitchen_ ta amsa masa tafito hannuta rik'e da ludayi miya ta galla masa harara tace kai kuma, shashasha ta je har shago ta tayar maka da hankali shine ka biyo bayanta koh"?
Yaya Habeeb ko kallon gefen da Ammi take baiyi ba, balle tasa ran zai bata amsa sai kawai ta shafawa kanta lafiya ta hanyar Jan tsoki ta koma _kitchen_
Yaya Habeeb na tsaye ya jigina rabin jikinsa a jikin bango ya wani lamgwabe kai yana kallota, ita ma k'asa d'auke ido ta tayi akanshi kallon ```so``` mai had'e da ka bata rai take aika masa yayin da shi kuma yake aika mata kallo mai d'auke da tsan-tsan ```so``` had'e ban hak'uri gaba d'aya yadawo Kala ban tausayi harara ta galla masa had'e da murgud'a baki ta kauda fuska.
Cikin mutuwar jiki ya tunk'aro inda take........
```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```2```
~~Tsawon _5 minutes_ yad'auka a tsaye yana kallonta yayin da ita kuma ta sada kai k'asa ta cigaba da wanke-wanke ta, daga bisani ya tsunguna daf da ita cikin muryar sa mai matuk'ar dad'i da gard'i yace _I'm so sorry baby love_ wallahi ba abunda yake tsakanina da yarinyar nan _believe me baby love no thing between us_ kawai d'iki ta kawo min shine take nuna min _styles_ d'in da takeso a wayarta Dan Allah kiyi hank'uri kidaina kuka nan saboda yana masifar tayar mini da hankali kinji"?
Saida ta ja majina da tafito mata a hanci ta koma inda tafito, cikin muryar kuka tace miyasa kake min haka yaya Habeeb"?
ko don ni bana cikin Jeri kyawawa mata shiyasa kake kula kyakyawa 'yan mata"?
Na shiga uku babylove na ta6a cewa da ke ina so kyakyawar mace kuma, wane munafuki ne yace da ke bakida kyau"?
Ta turo baki had'e da cewa ni ce nagano da kaina banida shaharare kyau, kuma ga shi a kullum 'yan mata masu shaharare kyau suna zarya a shagonku kuma saboda kai kadai suke zuwa kai d'inki.
Yaya Habeeb yadafe kai ya wani zaro ido yace in har baso kike yi nima nayi miki kuka ba babylove ki ajiye wannan zance a gefe ki yarda da ni ki kuma daina kwakwato akan irin so da nake miki, da ace ana bud'e zuciya da wallahi na bud'e miki tawa zuciya ki shiga idanu ki su hasko miki irin masifafe son da nake miki wannan ce kadai hanyar da zanbi ki yarda da cewa zuciya ta mallaki, ki ce ke kadai.
Ta lumshe idanu ta tsanani dad'i kalamai yaya Habeeb suka soma ratsa jijiyoyi jikinta shauk'i sonshi yak'ara samu mafaka a zuciyarta, cikin shagwa6a tace _ina sonka yaya Habeeb_
Yaya Habeeb ya yi murmushi yace kina sona amma kuma kina wahalar da zuciyata, tayi dariya _tace ba laifi na bane_
To laifi waye na hukunta shi saboda ni kan yana mini barazana da rayuwa"?
kallon ido cikin ido mai d'auke da tsan-tsan so ta aika masa, daga bisani ta kauda fuskar ta tace laifi sonka ne yaya Habeeb da ya yi nasara kanainaye zuciyata ya ratsa jini da tsoka ya bi sassa jikina ka koya mini sonka tun kafin na mallaki wayo gane ```menene so``` har nayi wayo nagano manufa da dad'i da ke cikinsa na rayuwa da sonka yaya Habeeb ina kuma fatar na mutu da sonka ,shiyasa banaso ka ra6i kowace 'ya mace.
Wani irin dad'i ne ya lullube zuciyar yaya Habeeb ya haddasa masa sakin sanyaye murmushi ya nad'e hannu _blue shirt_ d'in da ke jikinsa yasoma tayata wanke-wanke tana wankewa yana d'aurayewa yasaka cikin _basket_
Hannushi yatara a famfo ruwa suka cika masa hannu ya watsa mata a fuska a tsorace ta d'ago ya kyalkyale da dariya, cikin yanayi na shagwa6a tace Allah ba zan yarda ba yaya Habeeb nima sai na rama
yaya Habeeb ya zaro idanu had'e da cewa yi hank'uri babylove karki jik'a ni shago zan koma.
_cup_ ta d'auka ta debi ruwan d'auraye kwanuka ta kwara masa tun daga fuskarsa har jikinsa ruwa ne ke d'iga ya 6ata fuska yace haba babylove ruwan wanke-wanke ne kika zuba min a _my favourite shirt_
Ta yi masa gwalo had'e da cewa ba kai bane kafara
Don ni ne nafara shine kika za ki watsa min ruwan wanke-wanke"?
Turo baki tayi yayin da yaya Habeeb ya yi murmushi mugunta ya sunkuce _bucket_ d'in ruwan gaba d'aya ya kwara mata tasaki mahaukaci ihu had'e da kwalawa Ammi kira wayyo! Ammi kinga yaya Habeeb ya jik'ani da ruwan wanke-wanke, da gudu yaya Habeeb yanufi k'ofar fita ita ma ta bishi da
gudu, tuni ya shige gidansu yabarta labe a zaure tana lek'e sa, daga bisani ta juya cikin gida Ammi ta kalli ta ta tabe baki tace narasa gane tsakani ke da Habeebu waye mashiririci"?
murmushi kawai tayi ta d'auki _basket_ d'in kwanuka takai _kitchen_ tadowa rik'e da tsintsiya ta share wurin da tayi wanke-wanke daga bisani ta cire jak'ak'u tufafi ta ta d'aura zani a k'irji
Ta cika _bucket_ da ruwa kaitsaye bandak'i{bathroom} ta Shiga tayi wanka, ta shirya cikin _dark blue d'in _uniform_ na islamiyya had'e da _whites hijab_ tafito rik'e da jakka mai d'auke da _Al-qu'arni mai girma da saura littafai addini_ ta nufi k'ofar _kitchen_ tace _Ammi na tafi islamiyya_ Ammi da ke ta fama fifita wuta saboda itace basu bushe sosai ba tad'ago tace adawo lafiya sannan karki manta in an tashi isalamiyya ki biya gidan Delu dallaliya ta baki ciko kudina, tajuya had'e da cewa to Ammi amma kuma in bata bani ba na k'arbo abin kudi"?
Ammi tace bansakiba uwar 'yan kaud'i ta fice tana dariya had'e da cewa kai Ammi daga zan yi miki abun kwarai
Kaitsaye gidansu yaya Habeeb tashiga had'e da sallama inna mairo na zaune a tsakiyar gida bisa kujera 'yar tsuguno cikin sakin fuska ta amsa mata, yayin da Haleesa ta durk'usa har k'asa ta gaidata _ina wuni inna"?_
_lafiya qalau Haleesa an fito"?_
_Eh! Inna zainab na ciki kuwa?_
Kafin inna tabata amsa taji muryar zainab a bayata tana cewa ba'a saniba sai yanzu kika damar fitowa"?
Harara ta galla mata tace nima bansaniba in kuma baki tashi tafiya ba, nayi tafiyata inna dai sai faman dariyar su takeyi saboda tasan da kyar ne Haleesa da zainab su had'u ba tare da suyi fad'a ba. sallama sukayi yiwa mata had'e da ficewa daga gidan.....
_DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S_
Jeeddah Aliyu
This is another must read and one of the best hausa Novel HUBBUL YAQEEN http://share4world.com.ng/2019/03/24/hubbul-yaqeen/ enjoy free readings
ReplyDelete