[13/12 7:05 am] Jeeddah Aliyu🌹: [24/08 7:35 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```10```
```BAYAN SHEKARA BIYAR ```
Haleesa tana aji hudu a sakandire{secondary school} ta zama 'yan mata kyauta yak'ara fitowa, soyayya suke zubawa ita da Habeeb tafitar hankali, a lokacin akayi bikin aure juwairiyya da mijinta mas'ud kasance wa masa'ud yana aiki a karkashen wani shaharare _company_ a Lagos da ke sarafa shinkafa mai suna _Lamido's parboiled Rice Limited_ shiyasa ana kamalla bikinsu masa'ud yadauki matarsa suka lula Lagos.
Mal Usman da mal Audu suka tsayarda lokacin bikin Haleesa da Habeeb zarar Haleesa ta kamalla _secondary school_ za'ayi bikin aure su da yake Habeeb basida karfin siyen fili kuma har yayi gini mal Usman ya zaunarda d'an uwansa mal Audu yafad'a masa ya yanke shawarar su raba gida nasu kashi biyu kowane yad'auki nasa kaso domin Habeeb da salman su fara gini matsuguni da za su zauna da iyalinsu, mal Audu ya yi na'am da shawarar d'an uwansa wannan shine dalilin da yasa suka ra6a gida tuni Habeeb da salman suka fara gini dai-dai na talaka mai k'arami k'arfi.
```CIGABAN LABARI ```
_A washe gari_
Haleesa da zainab sun dawo daga _school_ da yake makaranta nasu bashida nisa sosai da gida da k'afa suke takowa, tafiya suke suna fira kamar yadda suka sa6a Zainab ta kalli Haleesa tace ina fatar yau ba za ki biya shagon su yaya Habeeb ba"?
A yatsine Haleesa take kallon zainab daga bisani tace mutuwa za'a fasa ko Hisabi"?
Humm....ba Wanda za'a fasa Zainab tafad'a kaitsaye.
To kidaina wahalar da kanki ta hanyar tambaya na.
Amma gaskiya ina tausaya miki saboda in yaya salman ya d'ank'eki sai kin yabawa aya zak'inta.
Haleesa ta ja tsoki mtsss wallahi ba Wanda ya isa yahanani zuwa, gani hasken zuciyata tak'arasa magana tana wani murgud'a baki murmushi zainab tayi had'e da cewa Allah ya kai lafiya amma inaso Kisani duk tsuntsu da ya kira ruwa shi, ruwa kan d'oka kafin Haleesa tabata amsa wata tsadadiya mota kirar _Range Rover elegance 2016_ wance tsawon rayuwa Haleesa bata ta6a ganin irin ta ba _driver_ motar ya fatsala musu ruwan kwatami da ke gefen hanya tun daga fuskar Haleesa har izuwa farin Hijab d'inta yalalace da ruwan kwatami, Haleesa tabi jikinta da kallo tsanani bacin rai yarufe ta musanman da tad'aga kai ta hango mai motar bashida niyar tsayawa, zuciyarta tak'ara tafarfasa, saida _driver_ motar yayi nisa kad'an da su sai kuma yayi _reverse_ yadawo daf da su ya tsaya, da yake gilasai motar _tented_ ne basu iya hango Wanda ke ciki balle k'ofar motar akayi wani mutum gajere yafito yana sanya da riga da wando bak'i da fara da _fencing cap_ bak'a kallo d'aya Haleesa tayi ma kayan jikinsa tagano _uniform_ ne da ke nuna shi driver ne bashi ne ainihi mai motar ba.
_driver_ yace Dan Allah kuyi hank'uri banganku bane.
Zuciyar Haleesa na tafarfasa idanuta sunyi jajir tace da yake kai makaho ne ae dole kace baka ganmu ba kuma don tsabar wulak'anci da reni wayo shine saida kaga dama sannan kafito ka bamu hank'uri
Haba baiwa Allah nace kuyi hank'uri wallahi ba da sanina na watsa muku ruwan nan.
Zainab ta rik'o hannu Haleesa tace _please Haleesa tun da yabamu hank'uri ki kyale shi yayi tafiyarsa mana.
A harzuk'e Haleesa ta buge hannu zainab tace hank'uri sa na banza da wofi ko kina nufi hank'uri sa zai cire min wannan wari kwatami da nakeyi ko kuma zai wanke mini kayana"?
Karar bud'e k'ofar mota ne yaja hankalinsu gaba d'aya suka mayarda ganinsu, wurin motar k'afafu sanye da _black cover shoe_ suka fara fitowa daga cikin motar sai kyalli da d'aukar ido suke yi da sauri driven yanufi k'ofar mota yarik'e had'e cewa _I'm sorry boss yarinya ce tafiye kafuwa na bata hank'uri amma taki ta hak'ura_
Sai ganin sukayi an turo driver da k'arfi gangar jikinsa tafito daga cikin mota sanye yake da _suit dark green colour_ kwayar idonsa lullube cikin _black shade_ kyakyawan matashi saurayi Wanda shekaru sa na haihuwa ba za su haura 37-38 fari tass da shi sumar kansa bak'a wulik, fuskarsa a murtuk'e yanufi wurin Haleesa tuni jikinta yad'auki rawa domin tayi masifar tsorata da gani wannan _guy_ yana isa daf da ita yad'aga kyakyawa hannusa ya sharara mata tagwaye mari, saida ta zube k'asa tsawon rayuwata ba'a ta6a mari ta ba shiyasa ta rud'e matuk'a.
cikin _husky voice_ yafara magana _you Animal who do you think you are?_
Da har za'a baki hank'uri kina cewa ba za ki hak'uri ba to sai kiyi abunda za ki iya banza kawai 'yar iska 'yar talakawa.
Tsanani tsoro had'e da firgici sukayi nasara lullu6e Haleesa tad'ago baki bud'e tana kallon wannan saurayi.
Tsawa yadaka mata ta hanyar cewa tadaina kallona dan uban ki
A tsorace Haleesa ta sada kai k'asa yayinda saurayin yaja tsoki yajuya yanufi motarsa _drivernsa_ ya bud'e masa k'ofa ya yayinda driver zagaye da gudu ya zauna a driver _sit_ yaja mota da k'arfi..
Jeeddah Aliyu
[24/08 8:37 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```11```
Suka halba kan titi Zainab tabisu da kallo daga bisani tadawo da ganita akan Haleesa, wance ke zaune da6ass a k'asa tadafe kumatu ta ita ba kuka takeyi ba, kuma batada niyar tashi tsaye da sauri Zainab ta girgiza ta had'e kiran sunanta Haleesa ki tashi mu tafi gida Allah sai saka miki wannan zalunci da akayi miki.
Har zainab tadasa aya a zanceta Haleesa na kallonta, abunda yayi matuk'ar rana Zainab kenan, da kyar ta iya mik'e wa tsaye ta kwasa da gudu tanufi shagon su yaya Habeeb, a firgici tafad'a shagon sai faman sauke take yaya Habeeb yadaka mata tsawa ke! Lafiya za ki shigo mana shago a hargitsi"?
Cikin sark'ewa halshe zainab tace yaya Habeeb Haleesa tun kafin tak'arasa Yaya Habeeb ya mik'e tsaye jikinsa na rawa yace me yasami Haleesa"?
wani mutum ne mai siffar larabawa direba sa ya watsa mana ruwan kwatami don kawai Haleesa tayi magana shine, mutume mai siffa larabawa yafito daga mota yadinga wanka mata mari saida tayi suman zaune, yanzu haka tana chan gefe hanya ko motsi bata yi.
Cikin tsanani tashin hankali, yaya Habeeb ya kwasa da gudu yafita daga shagon yayin da yaya, salman da saura yaran shagon suka Mara masa, baya yadda zainab tabarta haka yaya Habeeb yatarda dafe da kumatu, a rikice ya zube gabanta yad'ago fuskarta nan take yak'ara rud'ewa sakamako gani idanu ta sunyi kwacin jini ga kuma yatsu Mai siffa larabawa sunyi radau-radau sun kwanta a kumatu ta, Haleesa nagani yaya Habeeb sai lokacin tadawo haiyaci ta tafad'a jikinsa tafashe da mashahuri kuka, yayinda yaya Habeeb ya rungume ta tsanm a k'irjisa, yana bubuga bayanta, yaya salman yajuya wurin zainab yace Zainab ina kika ga mutume yabi"?
Zainab ta nuna titi da hannuta, yaya salman ya bi hannuta da kallo, daga bisani yaja tsoki yace watakila rashin kunya tayi masa, shiyasa wanke 'yar banza da mari.
Cikin k'una zuciya yaya Habeeb yad'ago yana huci, yace don tayi masa rashin kunya shine zai bashi damar yaraunana ta haka"?
Na ratsi duk lokacin da naci karo da wannan mutum sai na nuna masa kuskuresa na mari babylove yak'arasa magana yana huci kamar bak'i kumurci yaya salman yayi murmushi had'e da cewa malam hak'uri za kayi domin da dukan alamu wannan mutum ya tsofa a kasar _Egypt ko labanon_ saidai in kuma chan za ka bishi ka nuna masa kuskure sa ba zan hanaka ba ko ba komai _diamond girl_ yata6a yaya salman yak'arasa magana yana dariya.
Yaya Habeeb yak'ara harzuk'a jin yakeyi kamar ya shak'o wuyan salman ya yi ta dukansa, domin a yanzu shi yake basa haushi fiye da mai siffa larabawa saboda mai siffa larabawa yariga ya k'ona masa zuciya yatafi shi kuma salman yanzu yake yayafa masa tafasashe ruwan zafi a zuciya saboda kalamai salman tamkar ruwan zafi yakeji su, ya tashe ta tsaye har zuwa lokacin kuka takeyi na fitar hankali......
```DEDICATAD TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu
[13/12 7:11 am] Jeeddah Aliyu🌹: [25/08 2:55 pm] Jeeddah Aliyu```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```12```
Yaya Habeeb yarik'o hannuta suka nufi gida, sautin kuka ta ne yafito da Ammi daga d'aki tana fad'ar to fitinaniya yau kuma da wace kika zo"?
Ammi na k'arasa fitowa daga d'aki tayi turus, faskarta d'auke da zalla mamaki tace iko Allah ashe tare kuke da ita kuka me take yiwa mutane"?
Yaya salman ne sanarda Ammi abunda yafaru.
yaya Habeeb sai cika yake yana batsawa yanufi bakin famfo yacika _bucket_ da ruwa yakai mata band'aki{bathroom} yasake shiga d'akinta yadauko mata zani ya mik'a mata, ta kar6a saida yaraka ta bakin k'ofar _bathroom_ sannan yadawo yajingina jikinsa da bango jin yakeyi kamar ya rushe da kuka Ammi tace ka ga Habeebu karka nemi ka d'aurawa kanka damuwa domin ba ga ni wannan mutum za ka yi ba mafi alkhairi a tare da kai ka lallashi zuciyarka.
Yaya Habeeb yad'ago ya kalle Ammi da jajaye idanu shi yace babban takaici na bai wuce yadda Salman yake k'ara tunzira ni yak'arasa magana had'e da nuna yaya salman da yatsa.
Yaya salman ya kyalkyale da dariya daga bisani ya tsagaita da dariyar yace Allah ya huci zuciyarka _my in law_ ni kaina da zan ga wannan balarabe da na tayaka dukansa.
Ammi ta tabe baki
inna mairo ce tayi sallama tashigo a rud'e Ammi tasaki murmushi had'e da cewa zainabu takai miki rahoto koh"?
Inna mairo tace bari kawai fatee wallahi da zainabu tasanarda yadda abun yafaru baki ga yadda hankalina yatashi kai wannan mai siffa larabawa bashida imani Allah yasaka miki Haleesa.
Ammi da yaya salman sai faman dariya inna mairo sukeyi gani yanda ta tak'ark'are tana fad'a Haleesa tafito daga _bathroom_ jikinta lullube da d'an kwali _uniform d'inta_ har wani Jan k'afa takeyi ita dole sai tanuna ta maru, a hanzarce yaya Habeeb yanufi wurinta, yarik'ota sai faman sannu yake mata inna tasaki salati tana tafa hannaye sakamako gani idanu Haleesa sunyi kwanci jini tace Amma wannan mutum rashin imani sa a baiyane yake so yayi ya makkata ki, to ta Allah ba tashi ba azzulumi kawai.
Haleesa da ke tsaye tana sharar hawaye sai faman gizo fuskar mai siffa larabawa yake mata, yaya Habeeb yace ki je ki saka kayanki babylove mu je _hospital_ a duba ki Ammi ta zaro ido tace wane irin hosfutal{hospital} Habeebu"?
Kai fa baka rabuwa da d'aukar dame magaji da nishi in banda tsabar tsirfa da ba kai wahala miye na zuwa _hosfutal_ {hospital} gishiri da ruwan masu d'an d'umi-d'umi za'a nema a gasa mata idon shikenan za ta Wartsake.
Yaya salman yak'ara kyalkyale dariya yace Ammi ba hosfutal ake cewa ba _hospital za ki ce_ Ammi ta gallawa yaya salman harara tace Ko ma menene akecewa banga amfani zuwa sa ba.
Haleesa tafito cikin shirita, har yanzu da raguwa kwanci yatsu mai siffa larabawa akan fuskarta yaya Habeeb yace Ammi duba idonta ki gani yadda yayi Ammi ta kya6e baki daga bisani tace dafin hannu ne Habeebu ba wani Abu ba da an gasa mata zai daina.
Yaya Habeeb ya girgiza kai yace ni dai Ammi nafiso mu je asibiti{hospital} Ammi tace Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo yaya Habeeb yaja hannu Haleesa suka fice yayinda yaya salman ya Mara musu baya.
yaya Habeeb yashiga cikin gidansu yajawo Babur d'insa Haleesa ta d'ale yaja Babur d'in suka tafi yaya salman yabisu da kallo yana, dariya.
Duk yadda yaya Habeeb yaso su ga likita abun yaci turu saboda lokacin tashin likita aiki yayi dole yanufi wani 'karamin _clinic_ mai 'yar banza tsada bayan an duba ta aka rubuta mata magani, kusan duba takwas da d'ari biyar akayi chaji yaya Habeeb in da Allah ya taimaki Habeeb yana da 'yan kudinsa haka yafito da su ya biya had'e da kar6a magani suka fito daga _clinic_ d'in tausayi shi yayi bala'i kama Haleesa nan take ta ji wani sabon sonshi yana ratsa jinita.
ya tsaya wurin wani mai siyarda lemu da ayaba yasiya mata sannan suka nufi gida.....
[25/08 4:53 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```13```
Suna isa gida yabata magani tasha ya kuma d'iga mata wanda ake sakawa a ido, yayinda Haleesa sai shagwa6a take zuba masa, ya6are ayaba yasa mata a baki Haleesa ta sadda kai k'asa tana ci ayaba a hankali, tana d'agowa ta ga yaya Habeeb ya tsura mata ido yana kallonta tamkar zai cinye ta, tasaki murmushi tace yaya Habeeb wannan kallon fa"?
Yasauke numfashi cikin yanayi na damuwa yafara magana, babylove wannan mutum yacuce ni kalli yadda ya6ata miki fuska yak'arasa magana tamkar zai yi kuka.
Haleesa tace kasaki ranka yaya Habeeb idanu ba ciwo suke min ba.
Ta ya zan saki raina babylove alhali idanu ki suna cikin wannan yanayi"? nayi alqawali duk ranar da idanuna suka ci karo da wannan bak'in azzalimi sai na d'auki mummuna mataki akansa.
Cikin rauni murya tace Dan Allah yaya Habeeb kayi hak'uri ka manta da wannan abu.
Shikenan babylove na hak'ura yafad'a had'e da Jan karan hancita yace ni zan koma shago, cikin sigar shagwa6a turo baki tace a'a yaya Habeeb ni banaso katafi yaya Habeeb yayi murmushi had'e da cewa kin ganki yarinya nan kinaso ki had'a mini _go slow_ a shago Haleesa tayi dariya tace to shikenan tashi katafi amma anjima za ka dawo koh"?
Tun da farin cikina naso ganina me zai hanani dawowa"?
Tsanani jin dad'i had'e da nishad'i suka lullube zuciyar Haleesa Habeeb ya mik'e yafita ta bi bayansa da kallo.
A kwana a tashi gashi har Haleesa ta kamalla karatu ta, yayinda iyayyensu sai faman shirya-shirye bikin aure su sukeyi, nan da wata d'aya za'ayi bikin burin Haleesa da Habeeb ya kusa cika.
Yammaci ne mai cike da sanyaye iska mai ni'ima bishiyoyi sai faman kad'awa suke suna busa iska mai dad'i gaske yayinda hadari ya had'a kayansa gabass Wanda hakan yake nuna cewa ko kowane lokacin ruwa za su iya saukowa, a cikin wannan yanayi ne Haleesa tafito daga gida Ammi ta aike ta gidan Delu dillaliya tana sanye da _combination_ na _paperless da atamfa red&yellow colour_ da hajib d'inta _red colour_ jikinta na fitarda 'kamshi turare _pink love_ ta yi matuk'ar kyau musanmman yadda ta k'awata fuskarta da murmushi ga kuma yanayi na iska da ke kad'awa sai kawai ta tsinci kanta cikin nishad'i, tana tafiya a hankali wannan d'aya daga cikin 'dabi'a Haleesa da kyar ka ganta tana tafiyar sauri shiyasa sa'idawa ke cewa ta cika yanga kaitsaye ta nufi bakin titi ta tsallaka, shagon su yaya Habeeb ta nufa saida ta lek'a ta ga yaya salman baya cikin shagon sannan tashiga wata budurwa ta hango zaune bisa farar kujerar roba, ta kasa ta tsare sai wani girgiza k'afa take yayinda Habeeb ke zaune bisa tela yana d'ikin Haleesa tasaki murmushi domin tagano mutumi nata ya yi tsiya da sallama tashiga shagon da sauri yaya Habeeb yad'ago ya wanke ta da murmushi, yace _o'oo my baby you look so beautiful muah_
Haleesa ta washe hak'ora kamar gonar auduga, tace _thanks my love_
Daga ina kike"?
Ammi ce ta aike ni gidan Delu shine nace bara wuce ba sai na zo naga tauraro na.
Habeeb yak'ara fad'ad'a murmushinsa yace kai gaskiya kin kyauta babylove da ace kin wuce banga wannan kwalliya ba da kin gama da ni......
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU```
Jeeddah Aliyu
[13/12 7:15 am] Jeeddah Aliyu🌹: [25/08 6:46 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```14```
Haleesa ta kyalkyale da dariya tace _umh yaya Habeeb kai dai baka rabo da abin dariya_
Budurwa da ke zaune tana jiran tsanmani ta yatsine fuska da alama tafara k'osawa da surutun Habeeb da Haleesa tace haba Habeeb wannan wane irin wulak'anci ne tun d'azu nake zaune a shagonan sai yawo da hankali kake min gaskiya ni nagaji.
Cikin yanayi na mamaki Haleesa ta juya wurin budurwa, tace dallah! Dakata malama an gaya miki shi bawa ki ne da in fara d'iki ba zai tsaya ya huta ba"?
Budurwa ta zaro ido had'e da cewa ke kuma baiwar Allah daga ina"?
Ba'a saniba Haleesa tafad'a tana murgud'a baki yaya Habeeb yana dariya yace kin ga kareema ki K'ara hank'uri bani nace ki jirani ba"? Insha Allahu ba za ki fita shagonan ba sai da kayanki.
Wane irin na'kara hank'uri Habeeb"? Kalli gari ka ga yadda hadari ya yi bak'i ga kuma unguwa mu da nisa
Haleesa ta tabe baki tace kinsan unguwa Ku da nisa wayace kika kawo d'iki anan"?
Yaya Habeeb na gani Haleesa na k'ok'ari tsokano masa fitina ya mik'e tsaye yarik'o hannuta ya yi k'asa da murya yace zo mu je na rakaki babylove kada Ammi ta ga kin dad'e
Haleesa ta yi murmushi tace yi zamanka yaya Habeeb ka 'karasawa wannan mayya d'ikinta, Habeeb yace _okay baby ki kula da hanya kuma karki jima saboda kinga an fara yayyafi da alama ruwa zai sauko_
Haleesa wance tuni ta juya tasoma tafiya tace to yaya Habeeb.
Tun kafin tak'arasa gidan Delu aka fara ruwa da gudu tashiga gidan Delu bayan ta kar6i aiki da akayi mata, har ta juya Delu ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar Haleesa ki dawo ki jira har ruwa nan su tsagaita sai kitafi ba don ran Haleesa yaso ba ta zauna har akayi kiran sallah magariba ruwan basu d'auke ba tad'ura alwala tayi sallah tana sallamewa bata tsaya yin doguwa addu'a ba ta mik'a had'e da yi ma Delu sallama tafita da sauri.........
[25/08 7:44 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```15```
Tsanani sauri da takeyi yasa ko gabanta bata gani gashi an d'auke wuta gari yak'ara yin duhu ga ruwan sama da ake tsullawa kamar, da bakin kwarya da gudu taje tsallaka titi wani mahaukaci birki da taji a bayanta yasa ta rikice tarasa in da zata dosa, kawai taja tayi tsaye duk iya k'ok'ari direba{driver} motar da kwarewarsa da tuk'i{driving} sai yada ya kai ga jikinta ta zube k'asa Allah yasa bata ji ciwo ba, ta mik'e tsaye da kyar da gudu direba{driver} motar yafito sannu Hajiya baki ji ciwo bane"?
Har Haleesa ta bud'e baki tabashi amsa taji sauti murya da ko a mafalki za sheda ta hasken fitilar motar ta hasko mata kyakyawa fuskarsa mai kama da ta larabawa.
Ke! Wace irin dabbace"?
Kin wani danno kan titi kamar mahaukaciya kin yi Sa'a kinada raguwa kwana a duniya da kin mutu a banza.
Haleesa ta hadiye yawu da kyar jikinta yad'auki rawa yayinda tsanani tsoro ya lullube ta, kallon d'aya tayi masa ta kauda fuska duk da tsawon shekara d'aya har da watani rabon da tasake gani wannan fuska mai matuk'ar razanata da sauri Haleesa ta tattara siket d'inta ta kwasa da gudu bala'i gudu takeyi kamar ranta zai fita saida takai zaure gidansu sannan ta tsaya ta dai-dai numfashinta, duk haka jikinta bai daina rawa, ba ta shak'i iska ta furzar daga bisani tak'arasa shiga gida kaitsaye d'akinta tashiga Sam batayi la'akari da jik'ak'u tufafinta, tafad'a bisa katifa tasaki razananiya ajiyar zuciya tadafe saitin da zuciyarta take taji yadda zuciyarta take bugawa da sauri-sauri ta lumshe idanuta, nan take tasoma gani sa, sanye yake da _suit_ kamar yadda tafara gani sa saidai na yau _black colour_ ne idanushi manne da black _shade_ fuskarsa a murtuk'e ras ras! Sautin da ke fita daga k'irjin Haleesa kenan da sauri ta mik'e zaune ta lankwashe k'afafu ta a tsakiyar katifa tafara zance zuci waye wannan mutumi mai siffar larabawa daga ina yafito"?
Shin mutum ne ko aljani meyasa tsawon shekara d'aya da watani da na ta6a haduwa da shi yanayi zafin ransa yana nan bai sauya ba"?
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu
[13/12 7:30 am] Jeeddah Aliyu🌹: [26/08 9:40 am] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```16```
Haleesa ta dafe kanta tsanani tsoron mutume yak'ara lullu6e ta, cikin zuciyarta tace _ya Allah ina tawassali da kyawawa Sunaye ka masu girma da d'aukaka Allah karka 'kara had'ani da wannan mutume_ domin na tsorata da shi tamkar yadda nake tsoron maciji haka nake tsoronsa Allah ka shiga tsakanina da shi Haleesa tak'arasa addu'arta hawaye na zuba akan mata fuskarta.
Jin Ammi na kwalla mata kira yasa ta mik'e a hanzarce ta sauya kayan jikinta, zuwa _gown_ na atamfa nan take ta tuna da kudi da ta kar6o wa Ammi gidan Delu a lokacin da mota ta bugeta ta jefarda kud'in, tsananin tsorata da tayi da gani mai siffa larabawa yahanata d'aukar kudin na shiga uku, yau sai Ammi ta yanka ni Haleesa tafad'a tana zarar ido.
Haleesa! Wai me kike yi ne a d'aki"?
Na'am Ammi ganinan zuwa, tafice hannuta d'auke da jik'ak'un kayanta saida ta sanya su sannan tanufi d'akin Ammi, tana shiga d'akin ta ja tayi tsaye Ammi tace ina aike da nayi miki"?
Cikin sark'ewa halshe Haleesa tace Uhm...ta bada dubu biyar a kawo miki da sauri Ammi ta tari numfashinta ta hanyar cewa _madallah wannan karo Delu tayi abin kanta ta cika alqawali_
Haleesa tak'ara tsorata saboda ta fahimce Ammi buk'ace take da k'udin ke! Haleesa bani k'udin ki je ki kwashe tuwo Ammi ta katsi mata zance zuci _Haleesa ta dawo kala tausayi cikin rawar murya tace dama Ammi bayan na kar6o kudin ina cikin tafiya sai kare gidan oga tunde ya biyo ni garin gudu na jefarda kudin kuma na nema ban gansu ba Dan Allah Ammi kiyi hank'uri kaddara ce_
Tun lokacin da tafara magana Ammi take kallonta gani ta dasa aya yasa Ammi tace Naira na gugar Naira har zunzurutun Naira dubu biyar kika jefar Haleesa wannan wane irin sakarci ne"?
Ammi kaddara ce Haleesa tafad'a kamar za tayi kuka, a harzuk'e Ammi ta rarume tsintsiya ta yi kanta da gudu Haleesa tafice daga d'akin, tanufi zaure Ammi ta jefarda tsintsiya tana huci tace ```kin yiwa kanki ``` dama ke zan siyawa _dinner set_ ae shikenan tun da kin jefarda kud'in.
Haleesa na fita taci Karo da yaya Habeeb tayi tsaye tana hak'i Habeeb yak'araso daf da ita ya haskata da fitila wayarsa, da sauri ta kare fuskarta da tafin hannuta.
_babylove me kike yi anan"?_
_kudin Ammi na jefar shine za ta dakeni ni kuma na gudu_
Hamm... Babylove gaskiya yau kin debo da zafi amma bara na je na ba Ammi hak'uri Habeeb yanufi cikin gida yabarta tsaye.
A madafi{kitchen} yatararda Ammi tana kwashe tuwo ya tsugunna yayi k'asa da murya _yace Ammi nasan mu yi miki laifi musanmman a wannan lokacin da kudi suke da wuyar nema a wurin talaka amma kiyi hak'uri ki danganta hakan da k'addara_
Ammi ta yi dariya daga bisani tace in ban yi hak'uri ba me zan yi"?
A kullum Haleesa k'ara mayarda kanta k'aramar yarinya takeyi kuma wai a hakan za'a yi mata aure lallai za ka kwashi kayan takaici Habeebu.
Habeeb ya kyalkyale da dariya yace da zarar mu yi aure za ta daina Ammi.
Yatsine fuska Ammi tayi tace to tashi katafi duk abunda takeyi da sa hannuka, yaya Habeeb ya mik'e tsaye yana dariya yanufi zaure wurin Haleesa......
[26/08 6:00 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```17```
Ya lek'a fuskarta had'e haska mata fitila wayarsa murmushi tasake masa, ya lumshe idanu yace babylove bakyaji magana koh"?
Haleesa ta turo baki tace me nayi"?
Ya girgiza kai had'e da cewa ba ki masan abunda kika yi ba"?
A shagwa6e tace da nasani ba zan tambaye ka ba yaya Habeeb
Shikenan mu ajiye wannan magana a gefe ki zo mu shiga gida ki bani labari mai dad'i yak'arasa magana had'e da juya Haleesa tabiyo shi a baya tace ina sonka yaya Habeeb
Yasaki dariya mai sauti yace kin renani babylove har kwakwayo magana ta kike yi
Haleesa tace _Ni da yaya Habeeb jini mu d'aya duk abunda ya yi nima zan iya kwaikwaya_
Habeeb yajuya ya fuskanceta yana mata kallo mai d'auke da kwayar _so d'aya_ kunya ta lullu6e ta da gudu tara6a ta gefensa tashige d'akin Ammi Habeeb ya yi murmushi had'e da bin bayanta zaune yatarar da ita bisa gadon Ammi, ta mik'e k'afafu ya yi tsaye yana kallonta cikin zuciyarsa yace narasa wane irin so nake yi wa Haleesa na tabbata son Haleesa ba zai ta6a duk'ushewa a zuciyata,ba ina matuk'ar son Haleesa tamkar numfashina kafin Habeeb ya gama zance da zuciyarsa aka mayarda wuta _Nepa_ haske ya gauraye d'akin yak'ara haskaka masa kyakyawa fuskarta sai faman doka murmushi take Habeeb ji yake kamar ya hadiye ta don so, Cikin 'yar muryarta mai matuk'ar dad'i da gard'i tace yaya Habeeb ka zauna mana ni fa a kwanaki nan narasa gane kanka sai kadinga kallona kamar baka ta6a ganina ba tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
Habeeb ya zauna kusa da k'afafuta cikin rauni murya Habeeb yafara magana nima bansan dalilin da yasa nakeso kallonki babylove ba, iya abun d'aya nasani Sam bana gajiya da kallon kyakyawa fuskarki.
Haleesa ta sadda kai k'asa tana murmushi tana d'agowa ta ga Habeeb ya runtsi idanu sa ya kuma dafe cikinsa da hannu a tsorace Haleesa ta rik'o hannushi kamar za ta fashe da kuka tace yaya Habeeb meyasa ba za ka je asibiti ba"?
Ciwon ciki nan yana damu ka sosai
Habeeb ya cije lebb'e shi yace......
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu
[13/12 7:34 am] Jeeddah Aliyu🌹: [26/08 8:03 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```18```
Kema kinsan dalili da yasa banaso zuwa asibiti _babylove_ ki kyaleni kawai da zance asibiti nan.
Haleesa tak'ara marairai ce murya tace _please yaya Habeeb ka amince gobe na rakaka hospital ka ga likita wallahi hankalina yana matuk'ar tashi duk lokacin da naganka cikin wannan yanayi na ciwon_
Habeeb ya yi murmushi k'arfi hali had'e da cewa karki dame kanki akan wannan ciwo ba wani abu damuwa bane.
Haleesa ta girgiza kai hawaye suka cika mata idanu na fahimce cewa yaya Habeeb zuciyarka tafara yi wa soyayya ta tafiyar hawaiyani hakan yana nufi ka daina marmari kwanciya hankalina.
K'ank'ame hannuta Habeeb ya yi cikin yanayi na zafin ciwo had'e da zafin da Haleesa take yunk'uri haddasa masa yace Haleesa ina sonki fiye da tunani ki a kullum burina bai wuce naganki cikin farin ciki da kwanciya hankali don haka gobe insha Allah zan je asibiti don kawai, kisami natsuwa ki kuma k'ara amincewa da irin son da nake miki.
Haleesa tayi murmushi jin dad'i hawaye ta suka sauka bisa hannu Habeeb, a kid'ime Habeeb yad'ago fuskarta karki yi min haka Haleesa sani kanki ne ba abunda na tsana irin na ga hawaye akan wannan kyakyawa fuska taki yasaka yatsa shi yalak'ato hawaye ta.
Haleesa ta goge fuskarta tace Kaine farin ciki na shiyasa banida buri da ya wuce naga na zama mallaki ka.
Habeeb yasaki murmushi had'e da cewa nan da k'ank'ani lokacin burin mu zai cika _babylove_
```TSAKIYAR DARE ```
Da misali k'arfe _2:30am_ tsanani ciwon ciki na fitar hankali ya tayarda Habeeb sai faman juyi yake, had'e da nishi mai k'arfi gaske Wanda ya yi sanadi da Hasheem ya falka a firgici yanufi wurin Habeeb yana girgiza shi had'e da kiran suna shi yaya Habeeb ciwo ciki ne ya motsa"?
Da kyar Habeeb yad'aga kai da gudu Hasheem yanufi cikin gida ya fad'awa baba Audu Habeeb bashida lafiya.
lokacin da baba Audu yashiga d'akin ya tararda Habeeb yafita haiyyaci sa, baba Audu yajuya wurin Hasheem yace yi maza ka je ka fad'awa mal Usman bayan fitar Hasheem da kamar _5 minutes_ sai ya ga shi yadawo tare da baffa da salman a rikice salman yad'ago Habeeb yace sannu Habeeb Allah yabaka lafiya ya rabaka da wannan ciwon yayinda Habeeb bai ma San yanayi ba baffa yace Hasheem je ka kade6o ruwa nayi masa tofi da sauri inna mairo da ke a bakin k'ofa tajuya ta de6o ruwa a Kofi ta mik'awa Hasheem ya ba baffa cikin ikon Allah baffa na ba Habeeb ruwan ciwon ciki yalafa Habeeb ya yi bacci.
Salman yace babba matsala da anan a tsakiyar dare nan ba inda zan samo aron mota ballatana akai shi asibiti saidai mu jira wayewa garin.
Duk wannan bidiri da akeyi Haleesa batasaniba tana chan tana sharar bacci.
Har asuba tayi Habeeb yana bacci baffa da baba suka nufi masallaci suka bar Salman da Hasheem tare da Habeeb, kamar daga sama Habeeb ya bud'e idanushi da sauri salman yarik'o hannushi yace sannu Habeeb ya ciki naka yadaina ciwo"?
[26/08 9:23 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
Na Hauwa Shehu Aliyu
```19```
Habeeb yatsine fuska yace yadaina yajuya wurin Hasheem yace Hasheem de6o min ruwa nayi alwala Hasheem yajuya da sauri, yade6o masa ruwa gaba d'aya suka nufi masallaci, bayan gama sallah suka fito daga masallacin sai kawai suka ga Habeeb ya yanke jiki yafad'i k'asa a some da sauri Alhaji Garba makwaci su yadauko mota aka saka Habeeb, suna isa asibiti aka nufi d'akin gagawa{ _emergency & Accident Ward_}da shi.
Da gudu kamal yashiga gida yana kwadawa Ammi kira a rikice Ammi tafito daga d'aki tace lafiya kamal"?
Cikin rawar murya yace muna fitowa daga masallacin yaya Habeeb ya suma su baffa sun tafi su kai shi asibiti.
Dai-dai lokacin da Haleesa ta sallame sallah tafito a gigice had'e da cewa wayyo Allah na, nashiga uku tafashe da mai tsanani gaske, Ammi tarik'o ta tana lallashinta da kyar Ammi tasamu tadaina kuka.
```k'arfe 10:20am```
Da misali k'arfe _10:20am_ Haleesa, Ammi da inna mairo tare da zainab suka shiga d'akin da aka kwantarda Habeeb cikin tashin hankali marar misaltuwa Haleesa tashiga d'akin ta hango Habeeb kwance hannu shi na hagu d'aure da _drip_ da sauri ta nufi wurinsa tarik'o hannusa na dama ta matsi cikin nata, tafashe da kuka hawaye had'e majina suka soma zuba akan fuskarta da sauri salman yataka mata birki ta hanyar cewa karki tsira mana kuka anan in kuma kuka za ki yi kifita waje dole Haleesa ta hadiye kukanta sai tadawo na zuci tanayi hawaye na zuba, ta ra6a gefen Habeeb ta zauna a hankali take murza hannushi da misali k'arfe _11:30am_ Habeeb yafarfad'o yana bud'e idanusa suka sauka bisa fuskar Haleesa wance cikin d'an k'ank'ani lokacin har tayi rama cikin tsanani jin dad'i Haleesa tace _sannu yaya Habeeb_
Murmushi yasake mata daga bisani yace yauwa babylove saura mutane da ke cikin d'akin suka fara yi masa sannu ya amsa fuskarsa d'auke da murmushi, daga bisani Ammi da inna mairo suka fice daga d'akin Yaya salman ya mik'e yace bara na d'an mik'a kafata yana fita Haleesa ta matsa kusa da Habeeb ta lek'a fuska sa ta tsura masa ido gani yadda yayi masifar yi mata kyau fuskarsa sai kyalli take, tasaki ajiyar zuciya tace ciwon nan naka yaya Habeeb yana masifar tsoratani.
Murmushi yayi daga bisani yace banaso kina saka damuwa a ranki
Babylove saboda naji sauki.
Tayi murmushin nan nata mai 'karawa fuskarta kyau tace saura kuma kace
Ba za ka sha magani ba nayi fushi da kai tak'arasa magana cikin siga shagwa6a.
Habeeb yayi 'yar bazawara dariya yace ina sonki Haleesa ita ma tayi dariya tace nima ina sonka yaya Habeeb
Haleesa da Habeeb sai faman zuba soyayya suke sai kace ba'a asibiti sukeb ba _drip_ na k'arewa Haleesa ta kira _nurse_ tacire masa.
Haleesa na rike da hannu Habeeb tana wasa da yatsu sa taji ya matsi hannuta da k'arfi a firgici tad'ago taga ya runtsi idanu had'e da cije lebb'e tace yaya Habeeb ciki ne kuma"?
K'asa magana yayi faman juyi yakeyi duk da haka hannaye su na sark'e da juna, Hasheem da ke zaune a gefen bisa kujera roba yana _chat_ a waya shi ya mik'e nufi wurinsu gani yadda Habeeb ke birgima yasa yafita da gudu yakira _Nurse_ da sauri tashigo da kyar ta6an6are hannushi daga rik'o da ya yiwa Haleesa, tafara dubashi gani abun yafi k'arfinta yasa takira _doctor_
Haleesa na dur'kushe a k'asa tana kuka mai matuk'ar ban tausayi _doctor_ yadaka mata tsawa ta hanyar cewa ke! Tashi kifita k'asa tashi tayi saida Hasheem yakamata suna kaiwa bakin k'ofa tajuya, ta kalli Habeeb sai kawai ta ji yana kalma shahada.....
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu
[13/12 7:39 am] Jeeddah Aliyu🌹: [27/08 9:39 am] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```20```
Wasu yawu masu d'aci da masifar zafi suka cika bakin Haleesa saida taja dogon numfashi tayi nasara had'iye su kaitsaye suka, ratsa mak'oshinta suka dira cikin hanjinta nan take cikinta yafara k'ugi tamkar wance tayi _breakfast_ da fate wake Sam Haleesa bata lura da cewa sun fito d'akin ba saida ta ji sautin murya Ammi da kyar tad'ago kanta ta k'arewa Ammi da inna mairo da kuma zainab kallo ta ga kowane hawaye na zuba daga idanu sa, tsoro da zallumi had'e da tashin hankali Wanda tsawon rayuwa Haleesa bata ta6a gani irin sa ya ziyarce zuciya da gangar jikinta jin take wani irin mashahuri sanyi yasoma ratsa k'assa jikinta sai kawai jikinta yafara rawa kamar mazari da sauri inna mairo ta rik'e ta salman yak'araso daf da su muryasa na rawa yace Ammi meya faru naga kuna kuka"?
Kafin Ammi ta bashi amsa d'an tsamurare likita da ke cikin d'akin Habeeb yafito yana sharar gumi da _handkerchief_ da alama tak'are masa, cikin yanayi na tashin hankali Haleesa da yaya salman suka nufi sa a lokacin d'aya suka watsa masa rikitaciya tambaya _doctor ya jikinsa"?_
_doctor yaya Habeeb ya ji sauki koh"?_
Doctor ya girgiza 'kok'o kansa sai kace kadangare daga bisani yace _I'm sorry to say Habeeb is gone_
Sai Ku yi hak'uri mutuwa rigar kowa ce.
_innalillahi wa'inna illahi raji'um_ kalma da su salma ke ta mai-maitawa sabani Haleesa da ke tsaye kamar an shuka ta, ba k'arami jajircewa tayi wurin gani ta dai-daita numfashinta da ke barazana rabuwa da gangar jikinta, da kyar ta iya lala6o kalmar k'arya ce wallahi k'arya kake yi likita ya za'ayi yaya Habeeb ya mutu"? _you are bloody liar doctor_
Doctor ya yi murmushi yajuya yanufi office d'insa da alama su doctor sir an sha gani mutuwa kala-kala.
A hanzarce Ammi ta rik'o ta Haleesa tace ki sakeni Ammi girgiza mata kai Ammi tayi cikin hargowa tace kisakeni Ammii a tsorace Ammi tasaketa a hankali tafara ja da baya yanayi ta kamar na mahaukaciya sabon kamu, daga bisani tajuya da gudu ta afka d'akin yayinda Su Ammi suka Mara mata baya Habeeb ta hango tun daga tafin k'afarsa har izuwa kansa lullu6e da farin zani ta'karasa daf da gadon hannuta na rawa ta yaye zani idanu sa na lumshe tamkar mai bacci fuskarsa d'auke da murmushi kamar ka kira shi ya amsa, goshinsa na kyalli, Haleesa ta rik'o hannusa cikin sark'ewa halshe tafara magana _baka mutu ba yaya Habeeb Dan Allah katashi karka yi min irin wannan wasa I can't take it's any more please yaya Habeeb wake up don't do dis to me please yaya Habeeb I beg you proved 2 dis stupid doctor you are still alive ta'karasa magana had'e da rushewa da kuka mai k'arfin gaske_
A wannan Karo yaya salman ne ya yi yunkuri rik'ota ya mannata a 'kirjinsa, yace ki daure Haleesa ki danne zuciyarki domin ke aka yiwa wannan mutuwa saboda irin tsintsa _so da sha'kuwa_ da ke tsakani Ku amma hakan ba shi zai ba ki dama kin manta da cewa ubangiji da yaba mu Habeeb shi ya kar6i abinsa duk ma rai sai yad'and'ani mutuwa Habeeb ya riga mu gidan gaskiya Allah ya gafarta masa salman yak'arasa magana had'e da fashewa da kuka yayinda Haleesa ta 'kank'anme shi tasaki kuka mai matuk'ar ratsa zuciyar mai karatu, salman yaja ta suka fito daga d'akin.
Hasheem ya kira baffa da baba yafad'a musu Habeeb yarasu dama sun tafi gida domin su yi shiri zuwa masallacin juma'a kasancewa yau ranar juma'a ce.
Kukan Haleesa takeyi kamar ita ma za ta bi Habeeb sai faman sabbatu take yaya salman! _Haleesa ta kira shi cikin dasashiyar murya_
Na'am Haleesa shima ya amsa mata cikin murya tausayi
_Shikenan yaya Habeeb yatafi ya barni na tabbata nima nayi ban kwana da farin ciki wallahi yaya salman ba zan iya rayuwa babu yaya Habeeb mutuwa zan yi domin ban ga amfani rayuwata k....._
Da sauri yaya salman ya toshe mata baki yahanata k'arasa abunda ta je fad'a
Haleesa ta rik'o hannu salman ta aza bisa 'kirjinta tace ka saurara yaya salman ka ji yadda zuciyata take bugawa wani duhu nake gani wallahi mutuwa zan yi.
Yayinda numfashinta yadauke chak salman yad'ago fuskarta nan yagano cewa suma tayi, k'ara rungume ta yayi domin tashin hankali da yake ciki ya fi k'arfin tunani sa.
Har su baffa suka iso _hospital_ salman yana rungume da Haleesa, shi bai fad'awa jama'a a some take ballatana akawo masa agaji kuma shi bai nemo abunda zai farfad'o mai da ita shi kanshi a lokacin in aka tambaye shi, waye shi ba zai fad'a saboda tsananin tashin hankali da yatsince kanshi ciki.....
[27/08 11:35 am] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```
_the sweetest love_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu
```21```
```Da misali 'karfe 1:15pm```
Su baffa suka kar6i gawar Habeeb har zuwa lokacin Haleesa bata farfad'o ba yaya salman yasauke ta chak, yanufi k'ofar fita _reception_ da ita Zainab ta d'auko mata takalminta da suka sa6ule daga 'kafafuta sai lokacin baffa yalura da halin da Haleesa take ciki, kafin yacima salman har yasakata cikin _taxi_ ya shiga ya zauna yak'ara rungume ta baffa k'araso ya rik'e k'ofar mota yace salmanu yarinya nan suma tayi"?
Salman yad'aga kai alama eh! Baffa yak'ara cewa ya kamata kabarta asibiti domin tasami kulawa likitoci salman ya girgiza kai had'e da cewa mu tafi gida kawai baffa.
Batare da baffa yace komai ba yajuya.
Kaitsaye gida aka wuce da gawar Habeeb a d'akin inna mairo aka ajiye shi, salman yanufi gidansu da Haleesa ya debo ruwa tukunya laka masu sanyi gaske ya kwara mata a fuska, a firgici ta mik'e zaune sai faman zazzare ido takeyi tayi wuk'i-wuk'i numfashinta na fita da k'arfi tadafe 'kirjinta tace _innalillahi wa'inna illaihi raji'un Ya ubagiji mahalici sammai da kassai kasa wannan abun da nagani a mafalki kar yakasance gaskiya_
Tana d'ago idanuta suka sauka bisa fuskar yaya salman ras, ras! Gabanta yafad'i sakamako gani yana kuka da sauri ta mik'e tsaye ta dank'i hannu salman cikin rikitaciya murya tace yaya salman da gaske ne yaya Habeeb yarasu"?
Da gaske ne Haleesa ba mafalki ba Habeeb yatafi ya barmu da kewarsa, tsakaninmu da shi sai addu'a Haleesa ta fashe da kuka tsawon _6 minutes_ suka dauka suna kuka babu mai rarrashin wani daga bisani salman ya yi k'arfi halin share hawaye shi, yace Haleesa ki yi hank'uri ki yak'i zuciyarki tasoma rungumar babban rashi da mu ka yi ki share hawaye ki ki zo mu tafi ki yiwa masoyinki addu'a had'e da yi masa kallon k'arshe domin daga wannan gani da za k yi masa, ba za ki 'kara ganinsa ba sai a photo.
Haleesa ta tsagaita kukan da takeyi had'e da feto majina ta goge a hijab d'inta zuciyarta cike da 'kunci tace _ya ubangiji kai bani yaya Habeeb a yau kuma ka k'ar6i abinka ya Allah ka gafarta masa ka sada shi da haske kabari kasa kyawawan halayesa nagari su bi shi ya ubangiji talikai k'asa mini juriya da hak'uri rashin sa_
Da sauri salman yace _Ameen Haleesa_
Haleesa ta girgiza kai jin takeyi ina ma ace mutuwar Habeeb mafalki ne ba gaskiya ba tasaki mai matuk'ar ci rai har shed'ewa take numfashinta yafara k'auracewa gangar jikinta, a hanzarce salman ya rungume ta yana bubbuga bayanta tsawon dak'i'ka uku Haleesa ta d'auka kafin tasamu ta dai-daita natsuwarta salman ya cireta daga 'kirjinshi yarik'on hannunta suka nufi gidansu Habeeb ko da suka shiga gidan har anyi masa sutura yana kwance cikin makara lullube da farin likkafani, Haleesa tanufi wurinsa ta dur'kusa gaban makara so take tayi masa addu'a amma tarasa abunda za ta karanto masa, tsanani tashin hankali da firgici sun hanata kawai sai tafashe da kuka, Ammi da inna mairo da ke tsaye a bakin k'ofar d'akin suka soma tayata kukan.
```k'arfe 2:30pm```
Bayan an sauko daga masallacin juma'a jama'a suka dinga barkowa a k'ofar gidan mal Audu mai kifi domin su hallaci sallah jana'izza Habeeb, samari unguwar kowane su ka kalli fuskarsa idanu sa za ka hango sunyi jajir musanman 'yan _team's_ d'insu na _ball_ da kuma yaranshi na shago kuka sukeyi abin gwani ban tausayi domin kowasan Habeeb mutumi kirki uwa uba hank'uri Habeeb akwai hankuri sanyi hali da kyar ka ga yayi fad'a ga wasa da dariya Habeeb gwanin barkwaci ne shiyasa kowa yakeso sa mutuwa Habeeb tayi masifar girgiza d'ibin jama'a kamar yadda mutuwa ```marigayi Ahmad s Nuhu ta girgiza d'ibin al'ummah, Ya Allah ka gafartawa Habeeb da Ahmad s Nuhu Allah kasa aljana Firdausi ce makomarsu ```
_Ameen ya rabbi_
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu
No comments:
Post a Comment