[18/03 8:10 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
*3*
Jin yake kamar ya wanka mata mari tsaki ya ja yajuya cikin b'acin rai yafice daga parlourn, Zuhura ta bishi da kallon banza daga bisani tadawo da ganinta akan tarkacen da ke zube a gabanta kamar yanda ta laqawa kayan suna.
''Ta ja tsaki tasoma magana ita kadai lalle Ya Ansar ya zo min da Sabon bidi'a yanda ko a B.U.K ake buga misali da wankana shine zai kwaso hijab yakawo min kalli wad'annan zubula-zubula riguna Allah ni ba abunda zan yi da su ko aure nayi I can't Wearing this local dress haba look at me I'm big girl & fashionable a gani da wad'annan kaya ae sai class d'ina ya zube ko Nazeeya da take k'anwa ta bata saka irin wad'annan kayan ba sai ni mtcsww... Tak'ara Jan guntun tsaki tashiga tattara kayan tana cusawa cikin trolley, Ammah zan kai wa ta ajiyewa Anaal tun kafin wani ido yagani handbag's kadai Zan dauka hatta shoe's d'inan Anaal zan ba saboda size d'inta ne tarufe zip ta ja trolley d'in tanufi compound kaitsaye BQ tanufa ta turo k'ofar d'akin da aka warewa maigadi da matarshi.
"Ammah na zaune Zuhura tashigo janye da trolley Zuhura ina zuwa naganki da k'aton akwati ba dai balaguro za ki yi ba"? Cewar Ammah kenan tana kallon Zuhura sai da ta tabe baki tace ba Inda zan tafi Ammah Ya Ansar ne yakawo min kaya ni kuma ba su yi min ba shine na kawowa Anaal.
"Masha Allah Anaal ta sha godewa Ammah tafad'a tana Janyo trolley ta zuge zip tashiga fitowa da kayan da ke ciki zaro ido ta yi Kai....Kai.....kai Zuhura kayanan ba su yi yawa ba kuwa"?
Ba su yi ba Ammah ba banada buk'ata da su na kuma tabbata Anaal tana buk'atar su ki ajiye mata tadinga amfani da su kin ga wad'annan handbag's d'in tana magana ne had'e da d'ago handbags d'in da ke rik'e da hannunta bayansu bana buk'atar komai daga cikin tarkace nan hatta da akwatin na bar mata tadinga saka kayanta ciki Ammah tashiga zubawa Zuhura godiya da sauri Zuhura ta taka mata birki ta hanyar cewa haba Ammah wannan godiyan ya yi yawa Anaal fa k'anwata ce, yanda nakeson Nazeeya haka nakesonta Allah ne ya yi nufi ba za mu fito ciki d'aya da ita ba, ke kanki sheda ce da irin k'aunar da mu ke mata.
"Ammah ta gyad'a kai Shiyasa akoda yaushe mu ke godewa Allah da ya had'a mu da mutane kirki irinku mun gode mun gode Zuhura Allah yasaka da Alkhairi.
"Ameen Ammah ni zan koma cikin gida nasan da Anaal tadawo ita ma sai ta zuba mini buhu-buhu na godiya tak'arasa magana tana dariya.
"Ita ma Ammah darawa ta yi Zuhura tajuya tafice bata koma part d'in Granny ba tanufi nasu.
"Da b'acin rai Ansar ya Isa gida kwance yake akan sofa ya tsunduma tunani Sabon sauyi da yake gani tare da Zuhura yasan Zuhura tana sonshi fiye da son da yake mata, amma miyasa daga dawowarshi za ta fara kunnu da matsalolin a tsakaninsu"?
Wani irin d'aci yake ji yana yawo a ma'koshinsa babban abun takaici da yafi komai 6ata mishi rai bai wuce watsatsu kayan da take sakawa ba da yanda take k'ok'arin had'a jikinta da nashi a tsarinshi ya tsani mace mai irin wad'annan d'abi'u ina ma Zuhura za ta kasance irin yarinya nan mai niqan da ya gani, yana fad'ar haka a cikin zuciyarshi gabanshi yashiga dukan tara-tara tamkar zuciyarshi zata faso k'irjinshi ta fito babu shiri ya mik'e zaune yadafe saitin zuciyarshi ya lumshe idanunshi hoton yarinya ne ke karakani a cikin kwayar idonshi ya ware idanunshi da sauri ya mik'e tsaye yafara safa da marwa.
"Rashin mafita had'e da rashin sani ina wannan baqon al'amarin nashi yadosa yasa yanufi k'ofar fita part d'in mum yanufa ko zai same natsuwa.
*2 weeks later*
''A cikin wad'annan kwanaki da suka gabata Ansar yafara zuwa office, he's always busy Ansar mutum ne mai tsatsauran ra'ayi kamar controller Basheer Galadima abun nashi zan iya cewa gado ya yi Sam baya wasa da aiki duk abunda yasa kanshi yakanyi tsaye tsayin daka har sai yacima burinshi daga cikin halayenshi ya tsani raini shiyasa tun ranar da Zuhura ta zage shi yadauke k'afarshi daga gidansu tsakaninshi da ita sai waya shima don takira shi ne tabashi hak'uri.
_MONDAY MORNING_
"Ansar yafito daga conference hall yana sanye da dark green colour suit'' fitowarshi kenan meeting da employee's.
Abdallah na damarshi ishaq kuma na hagunshi hannunshi d'auke da tarin file's sun saka Ansar a tsakiya, elevator da zai sada shi ainihin office d'inshi suka shiga elevator na stopping ishaq ne yafara wucewa gaba da sauri yanufi office d'in Ansar yasaka keycard ya yi pressing digit k'ofar ya bud'e ya janye daga jikin k'ofar Ansar da Abdallah suka wuce sannan ya bi bayansu.
"Ansar yacire coat d'in jikinshi yajefawa ishaq yayinda ishaq ya cafe rigar, Abdallah yanufi fridge yadauko musu soft drinks a kasalance Ansar ya kar6i drink d'in had'e da zaunawa kan sofa kur6a d'aya zuwa uku ya yi ajiye.
Abdallah ya zauna kusa da shi, yace ni aganina bai kamata ka yi sauri amincewa da buk'atar employees za ka k'ara musu salary ba especially mechanic Union karka manta last month a dalilin sakarcin da sakacinsu ya janyo mana hasara d'aya daga cikin engines d'inmu shine za ka amince da buk'atarsu hakan zai basu damar cigaba da kawo maka korafe-korafe ko za ka yi k'arin albashi to ka k'arawa manyan ma'aikata su ka share su kawai "you better think about this.
"Harara Ansar ya zuba mishi cike da jin haushi yace nak'i nayi tunani kai da ka sacin k'udin company akwai uban da yace kadawo da su ko kana tsanmani bansan cewa ka zari mak'udan k'udi da sunan za ka yi ordering d'in wasu engines tsawon shekara d'aya kenan ba k'udi ba engines, a bisa bincike da nayi nagano cewa kashi d'ari bisa cas'in na mechanical union ba Yanda company ya tsare tun farko kafusawarsa ake biyansu ba alhali kuma each month company yana fitarda wad'annan kud'ad'e a matsayinka na MD na wannan company ina wad'annan kud'ad'en suke shiga"?
"Abdallah yashiga Sosa k'eya alamun rashin gaskiya suka baiyana k'arara a tare da shi Ansar ya yi murmushi yadafa kafad'arshi karka damu abokina ranar farko da na fara bincike a company nan nagano irin almudahana da ka ke yi wa Dad a company ni ba zan ce kadawo da kud'ad'e da ka d'iba ba amma inaso ka ji tsoron Allah domin _manzo Allah{S.A.W} yace abubuwa uku duk Wanda ya kasance a cikinsu to shi, munafuki ne koda ya kasance yana Azumi yana sallah koda ya yi hajji koda ya yi umarah koda yace shi musulmi ne indan yana ba da labari sai ya yi qarya indan ya yi alqawali sai yasa6a indan aka bashi amana sai ya yi ha'incin_ a cikin wad'annan abubuwa ba Wanda ba ka aikata ba Abdallah tun kafin na Zauna meeting da employees na tambaye ka adad'in salary su sai kabani labari na qarya kafin Dad ya damqa maka alhakin kula da company shi sai da ka yi alqawalin za ka yi adalcin, sai gashi ka karya wannan alqawali, Gashi kuma kanacin Amanar k'anana ma'aikata ta hanyar rage musu salary kana zubawa a naka account Shiyasa na yanke shawara abokai zaluncin naka zan yi firing nasu, wannan ya kasance shine na farko na karshe da za ka k'ara aikata irin wannan mummunan aiki.
"Kunya ya lullu6e Abdallah ya sadda kai k'asa jikinshi ya yi mugun sanyi ganin yanayin da yashiga yasa Ansar ya kece da dariya ya mik'e tsaye had'e da rik'o hannunshi tashi mu je mu yi sallah mu ci abinci k'aramin barawo da can ba ka shiryawa zuwan irin wannan ranar ba ka fara sata"?
Jiki a sa6ule Abdallah ya mik'e tsaye ka yi hak'uri Ansar nasan nayi kuskure da kuma sharrin zugar accountant domin shine yadaurani akan wannan mummunan tafarki, insha Allahu"! Daga yau nayi bankwana da zaluncin kuma zan dawo da wasu daga cikin kud'ad'e da na d'iba.
"Murmushi Ansar ya yi batare da yace komai ba yanufi k'ofar fita Abdallah ya bi bayanshi.
Zuhura da qawarta Lubnah Leebeauty suka fito daga lectures kaitsaye cafeteria suka nufa snacks da drinks suka yi ordering, suna cikin ci Zuhura tace wai kinsan har yanzu mutume ki fushi yake da ni tun faruwa wannan abu bai k'ara zuwa gidanmu ba yadaina kira na a waya sai in nice na kira shi wani abin takaici ba yabo ba fallasa yake amsa min magana.
Mctwww...... Leebeauty taja tsaki cike da takaici tafara magana wai me Ansar Galadima yadauki kanshi ne"? Ko don ya fahimcin kin kwallafa ranki akanshi ne shiyasa yake juya ki kamar waina a tada"?
Bari kawai leebeauty gaba d'aya narasa Inda zan jefa zuciyata naji sanyi, Ya Ansar yana min wulaqanci, babban abunda yake yak'ara jefa zuciyata cikin wasiwasi ko Ya Ansar yadaina sona ne"?
hum.....kenan bani kadai nake wannan tunani ba Zuhura kema kina yi"?,,,,,..a rikice Zuhura ta ajiye robar Fanta da ke hannunta ta waro idanu jikinta na rawa kamar wance ta yi wanka da ruwan sanyi lokacin hunturu na shiga uku leebeauty Ki bani shawara yanda zan gano wance alqila Ya Ansar yadosa domin wannan abin yafara rikitani ke sheda ce akan irin masifafen son da nake mishi rasa shi tamkar rasa numfashina ne.
"Yatsine fuska had'e da tabe baki leebeauty ta yi daga bisani tace, hanya d'aya ce ki ajiye girman kanki kira shi kice kinaso ganinshi da Yamma in yazo ki yi mishi titse ya fad'a miki matsayinki a wurinshi tun da ke kin riga kin sakawa ranki in babu shi bara ki iya rayuwa ba.
''Ajiyar zuciya Zuhura tasauke fuskarta fal damuwa, ba laifina bane leebeauty Ya Ansar ne yariga ya sagartani da soyayyarshi.
"Huh....to Allah yasa kar ya yi miki tawaye.
Ameen leebeauty Zuhura tafad'a cikin sauri.
_5:30pm_
Zuhura kwance a d'akinta ta Ciro wayarta daga charging ta kira Ansar dawowarshi daga office kenan yafito daga bathroom yana daure da towel a waist d'inshi wayarshi tashiga ringing da hanzari yanufi wajen da wayar take ajiye, gani Zuhura ce mai kiran nashi yasa yasaki murmushi ya yi picking had'e da karawa a kunnenshi _Hello Zuhura ya akayi ne"?_
Huh.... Ya Ansar ka manta da ni koh"?
murmushi ya yi ya zauna gefen gado _ya za'ayi na manta da abunda nakeso''?_
Ya Ansar kenan,,,,da ba manta da ni ba yaushe rabo ka da zuwa gidanmu"?
_wannan kuma laifinki ne Zuhura kinfi kowa sanin halina banaso raini naga lamari ki yanaso yawuce gona da iri shine dalilin da yasa na jaye jikina daga gareki, ba wai don hakan yana min dad'i ba Zuhura ina sonki banaso abunda zai kawo matsala a tsakaninmu_
''Farin ciki ya lullu6e Zuhura kenan zarginta ba gaskiya bane ka yi hak'uri Ya Ansar kowane d'an Adam baya wuce kuskure bana gajiyawa da ba ka hak'uri har ka ce kayafemin.
_Na yafe miki Zuhura naa_
Na gode Ya Ansar,,,,,Yau nasaka rai za ka zo wallahi nayi missing naka sosai ko abincin kirki bana iya ci sai dai na tsakara sama-sama.
Shafa gashin kanshi ya yi shikenan ki yi min tanadi mai dad'i ganinan zuwa insha Allah"!
Cike da shauk'in so suka yi hanging up agaugauce ya shirya cikin transparent material sky blue in colour har ana iya hango white vest d'inshi yashiga fashe jikinshi da kalolin designer perfumes ya zira white sandal kanshi ba hula, ya kwashi wayoyinshi da key d'in mota yafita direct part d'in Mum yawuce a main parlour yatararda Nadeeya da Basmah sai gardama sukeyi a tsakaninsu ya zauna kan sofa, yayinda basu Masan yashigo parlourn ba tsawa yadaka musu wance ta yi sanadi dawowa da natsuwarsu kai! Miye haka kun cikawa mutane kunne"?
''Basmah ta yi karaf ta fizge iPad d'in da ke hannun Nadeeya ta matsa wajenshi tashiga scrolling d'in pic's d'in da suke yi wa gardama Dan Allah Ya Ansar ka kalli pic's d'in nan karaba mana gardama, harara ya zuba mata har da d'an guntun tsaki mtcsww,,,,,,ba zan kalla ba kuma kitashi daga kaina a kunyace Basmah takoma wajen zamanta tana gunguni Nadeeya ta kyakyale da dariya k'eta ki ma daina wahalarda kanki da neman Wanda zai rama mana gardama domin ko mahaukaci ya dubi wad'annan pic's yasan wannan gashin sai Indian girl ba dai 'yar hausawa ba da yake 'yar rainin hankalince ke za ki ce wai kinsanta don tsabar kwarewa da iya k'arya har da su cewa k'awarki ce da k'awarki ce miyasa ba ki d'auki face d'inta sai ki ka d'auki iya gashin kanta"?
"Tsaki Basmah ta ja had'e da cewa so nake sai kin yarda da cewa nasanta kema da ki ke gardama kinsanta sannan zan nuna miki face d'inta.
Kafin ta bata amsa Mum tashigo parlourn da sauri Basmah tanufi wajenta Mum Dan Allah Ki kalli pic's d'inan wai Nadeeya tace wannan gashin bana Hausa girl bane"?
Mum ta kar6i iPad d'in tashiga kallon pic's tana dariya Basmah ae gaskiya Nadeeya tafad'a wannann ba bahaushiya bace Nadeeya tak'ara kyalkyalewa da dariya Ansar ya mik'e tsaye yace Mum ni zan fita"
"To,,,,,,boy sai kadawo ka gaida su Granny dariya yasa yana sosa k'eya Mum ya akayi ki ka gane can zan tafi"?
Annurin fuskarka ya tabbatar min da haka dariya kawai yak'ara yi yasa kai yafice daga parlourn Basmah da Nadeeya suka bi shi da kallo suna dariya.
Ansar yana fita ya zarce parking lot ya ja motarshi gateman ya bud'e mishi gate yafita kamar ranar farko da yafara ganinta ko yau haka yaganta sai dai yau su biyu ne fusk'ok'insu na lullu6e da niqan, yanayin tafiyarta a natse yasa yagane ta.........
Jeeddah Aliyu
[18/03 8:18 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
*6*
Good morning Mum" bata amsa gaisuwa nashi ba sai ma Jan kujera ta yi ta zauna tana facing nashi, cigaba da karanta yanayi da yake ciki ta yi yayin da shi kuma ya sadda kai k'asa me ke damunka ne boy"?
Ba komai Mum yafad'a a takaice ya za ka yi kace min ba komai bayan ga damuwa nan akan fuskarka, kuma ka kasa cin abincin sai wasa ka ke yi da fork oya,,,,tell me what's wrong"?
"I'm not in mood Mum ni kaina ba zan iya ce miki ga takamame abunda yake damuna ba.
''Boy rashin samun wadatace hutu yana d'aya daga cikin abunda yake damunka, ace mutum bashida time d'in komai sai na aiki yakamata kai wa kanka fad'a kadinga hutawa sak halin controller kadauko naso ba Kai wahala.
"Jin furucin Mum na k'arshe yasa Ansar ya yi murmushi had'e da cewa ni fa ba wani rashin hutu da ke damuna sometimes ina office nake sulalewa na bar Abdallah da ishaq da aiki natafi farmhouse na kwashi baccina. yak'arasa magana yana 'yar dariya Mum dariya ta yi tace to,,,,naji sarkin tsari yanzu abunda nakeso da kai ci abincin domin ba zan barka ba kafita batare ka ci abincin ba.
"kamar zai yi kuka yace Mum na yi loosing appetite. in bakina yadawo normal zan ci a office.
"6alla mishi harara Mum ta yi banaso gardama ka d'auki spoon ka ci abincin tun kafin mu 6ata da kai.
" yad'aga fork yasoma cin chips with sauce ya ji k'oda da anta k'amshin spices na tashi kwara d'add'aya yake tsokaluwa a fork. gani haka yasa Hajja fatee ta kar6e fork daga hannunshi tashiga feeding nashi, kamar d'a yaye sai wani 6ata fuska yake yi kamar mai cin mad'aci.
"Mum na k'oshi Ansar yafad'a kamar zai yi kuka, girgiza kai mum ta yi ta ajiye fork d'in hannunta. Ta had'a mishi tea mai kaurin gaske ya ji Ovaltine ta mik'a mishi cup, yana yatsina ya kar6i cup daga hannun Mum.
"Sai da ya shanye tea d'in tass,,,,sannan Mum tabarshi yafita office.
_Hour's later_
"Ansar yana zaune a office d'in shi da laptop a gabanshi yana operated nata. mtcsww,,,,ya ja guntun tsaki had'e da ture laptop yadafe goshi yunwa yake ji tun safe da Mum ta tilassa mishi yin breakfast bai k'ara cin komai ba.
"A halin yanzu yana buk'atar abinci mai kyau yad'aga landline yashiga ''pressing digit ya kara a kunnenshi Ishaq ka zo office d'ina inason ganinka.
Ba'a d'auki dogon lokacin ba sai ga ishaq ya zo, a kasalance Ansar yake kallonshi ishaq yunwa nakeji wane restaurants kasani da zan same abincin mai kyau da dad'i"?
"Ishaq yashiga tunani daga bisani yace Bright restaurant suna da abincin mai kyau ga dad'i sune lamba d'aya sai dai akwai tsada.
"Ansar ya tabe baki k'udi is not my problem ishaq mu je kawai ka kaini.
_Bright restaurant_
Ansar da ishaq na zauna kowane da plate a gabanshi sai aika loma yake. Especially Ansar sai cika spoon yake sosai abincin yai mishi dad'i sai kada kai yake yi.
"Table da ke opposite nasu wasu samari ne guda 2 ke zauna karaf idanun d'ayan yasauka akan wasu 'yan mata guda 2 da ke shigowa.
"Jikinshi har rawa yake yi ya zungure d'an uwanshi zayyan dubi wasu hot chicks da ke shigowa gaskiya girl's d'inan sun yi ba k'arya lalle dole na gwada sa'ata anan.
"Mtcsww,,,,zayyan ya ja tsaki kai fa Rasheed bakada hankali idonka idon mata ina gargad'inka da ka ji tsoron Allah duk abunda mutum ya yi sai anyi masa.
"Matsala ta da kai kenan zayyan duhun kai da rashin wayewa ka dubi sutura da ke jikin wad'annan chicks d'in da kyau, sun yi maka kama da natsatsu ae da ganinsu 'yan hannu ne ka ga kuwa don na taya ba laifi bane.
"Allah yashirye ka ni wannan iskanci ba da ni ba Allah ya haramta zina ba yanda za'a yi ina matsayin bawa mai neman gamawa da duniya lafiya, na aikata ta kai ma da ke yi Allah yaganar da kai.
"Ameen sarkin wa'azi Rasheed yafad'a had'e da cigaba da kallon 'yan matan yana lasar lips kamar mayye.
''Duk abunda Rasheed da zayyan suke fad'a a kunnen Ansar sai kawai ya tsince kanshi da son kallon 'yan mata ko zai gansu da illar da zayyan ya hango tattare da su.
"Rass-rass"!...gaban Ansar ya yanke ya fad'i. Cigaba da jujjuya kwayar idonshi ya yi akan Zuhura wance ta shagala da operating phone d'inta.
"Ranshi ya yi mugun 6aci jiya-jiya nan ya gama kashewa Zuhura gargad'i da kaukausar murya bayaso tana saka watsatsu kaya. Shine ta yi biriss da maganata lalle zan nunawa Zuhura kuskure ta.
''Leebeauty ta zungure 'kafar Zuhura ta yi pointing finger a side d'in da Ansar yake zaune zuu kalli can kamar Ansar Galadima"?.
"Jikin Zuhura har rawa yake yi ta mik'e tanufi wajenshi sai wani karkad'a hips take, kamar sabuwar karuwa "wow! What's presence surprise I don't expecting to see you here Ya Ansar.
Mtcsww"! Ansar ya ja dogon tsaki cike da takaici yak'are mata kallo yak'ara Jan wani tsaki wanda yafi na farko, ya mik'e a fusace kamar zai kai mata mari.
"Yajuya yanufi k'ofar fita ishaq ya tashi da sauri ya bi bayanshi, suka bar Zuhura tsaye sororo kamar bishiya kwakwa.
"Zayyan ya dube Rasheed ya kyalkyale da dariya I told you since abokina duk mutume kirki ba zai mu'amalamta wad'annan 'yan mata ba.
''Dallah ya isa zayyan ni fa zan dinga biye maka ba nakasa more kurciya na ba, remember I'm just 25yrs I'm still young so its my time.
"Zayyan ya tabe baki had'e da mak'e kafad'a. Rasheed ya mik'e yanufi wajen Zuhura yana shu'umin murmushi Hi! Beautiful naga wance tsamin ya 6ata miki rai karki samu damuwa ni zan kawar miki da 6acin ranki.
Kallon sama da k'asa Zuhura ta yi mishi mtcsww"! Ta ja tsaki ta6angaje shi ta wuce ta fincike handbag d'inta da ke kan table tafita fuuu"! Kamar zan ta tashi sama.
"Leebeauty ta tashi tana gunguni ta bi bayan Zuhura.
"Ansar yana fita yanufi wajen mota zuciyarshi na tafarfasa a lokacin guda tsanar Zuhura ta lullu6e shi.
''Cikin sauri ishaq yakaraso ya bud'e mishi mota, yashiga ishaq ya ja mota suka d'auki hanya.
"Ishaq"! Ansar ya kira sunan ishaq kamar zai yi kuka.
Na'am maigida.
"Ishaq zan tambaya ka dan Allah karka ji tsoron ganin idona ka bani, gansasshiyar amsa wance zata fitarwa zuciyata daga wasi-wasi.
''Ishaq ina tsananin son Zuhura tamkar numfashina, bani da wani buri da yawuce ta kasance mata ta uwar 'ya'yana. Ya d'an yi shiru had'e da shed'awa daga bisani yacigaba da cewa a matsayinka na wanda yake da kusanci mai k'arfi da ni, kana gani Zuhura ta dace da zama uwar 'ya'yana"?
"Ajiyar zuciya ishaq ya yi yak'ara dafe steering ka gafarce ni maigida akan abunda, zan fad'a ba tun yau ba nake gani Sam Zuhura bata dace da kai ba.
"Allah ya yi ka natsatse mutum ne kai mai tsananin kula da addini kana taka tsam-tsam da duk abunda zai shafi addininka sai na ke mamaki duk da kasancewar ka mai kamun kai me zai sa ka aure mace irin Zuhura.
"Ba wai Zuhura tana aikata masha'a ba _a,a_ sai don ta kasance mace mai baiyanar da surar jikinta, ga mazaje da ke titi ita a ganinta wannan ba illah bace a na ta k'azamin tunani sai take ganin saka matsatsu tufafi shine wayewa.
"Tun daga lokacin da na fahimcin haka a tare da ita sai nagano cewa kodai tana da karancin ilimin addini domin ba bu wata wayewa da addinin musuluncin bai zo mana da ita ba.
"Ko kuma tana da ilimin kawai bata amfani da shi, to kuma anan akwai babbar illah domin tasani ta kuma take sani Allah yashiryar da mu yasa tagano illah da ke tattare da abunda ta ke aikatawa.
"Ameen Ansar yafad'a cike da gansuwa da Amsar da Ishaq yabashi, 1 more question Ishaq
Ina sauraron ka maigida"
"A lokacin guda Ansar yasauke tagwaye ajiyar zuciya. Ishaq kana ganin wannan matsalar ta Zuhura wa ya yafi cancanta yafara tsawata mata"?
"Mahaifiyarta domin ita ce tushen tarbiyyar ta, ita ce a yanzu tafi kowa kusance da ita sai dai 'yan magana suna cewa ice tun yana d'anye ake tankwara shi, idan ya bushe sai dai ya karye.
"Indan har kwakwalwa ta ta auna dai-dai kana nufi abun da wuya ko Zuhura za ta daina saka watsatsun kaya"?
Kwarai kuwa maigida domin ga dukan alama ta yi nisa ba lalle bane a d'an k'ank'anin lokacin tadaina sakawa ba.
"Amma zan ba ka shawara a matsayinka na wanda ke sonta ka jajirce ka kawo mata illolin saka bankad'ad'un tufafi.
"Saka irin wad'annan kayan yana d'aya daga cikin dalilai da zina ta yi yawa a doron k'asa.
Maigida nasan kana matuk'a son Zuhura ka dage ka nuna mata illah da ke cikin kayan da take sakawa.
"Yak'ara sauke ajiyar zuciya Ansar ya yi ya fesar da iska mai zafi daga bakinshi, ishaq na kasance ina cikin jinse maza masu zafin kishi indan har Zuhura bata daina aikata, wannan mummuna d'abi'a lalle zan barta bari na har abada, domin ba zan ga maciji da rana tsaka nayi sakacin da zai sare ni ba.
"Ba zan aure mace da ba za ta bai wa 'ya'yana tarbiyya tagari ba, duk son nake wa Zuhura zan hak'ura da ita.
_Zuhura_
"Tun a mota leebeauty tafara zugata kai,,,,,,,Jama'a a rayuwata banta6a gani wulaqancin tsirara irin wannan da Ansar Galadima ya yi miki, a baiyanar Jama'a zai kalle ki ko kallo mai cike da k'ask'ancin ya zanga miki dogon tsaki.
"Wallahi Ansar ya gama da ke Zuu ke dai ki yi gaggawar d'aukar mataki ko kuma wankin hula yakai ki dare, yanzu dai dabara tarage ga mai shiga rijiya.
Tak'arasa magana tana kya6e baki.
"Zuhura ta share guntaye hawayen da suka zubo mata, babban abunda yake saka ni fargaba shin me Ya Ansar yake nufi da ni"?
"Me ko yake nufi da ke da yawuce yana daf da 6arar da Gwamnatinki.
"Zuu da kin ga kare yana shinshina takalmi wallahi ko na uban waye dauka zai yi.
"Ni fa ban fahimce inda wannan zaurance naki yadosa ba"? Na ji kince takalmi, kare kuma Ya Ansar bai kasance d'aya daga cikin wad'annan ababen da ki ka lissafa ba.
Dariya sosai leebeauty ta yi wance har ta k'ular da Zuhura rai a 6ace Zuhura tace look leebeauty kinsan duk duniya ba abunda yake saurin baiyanar da fushi na irin dariya, kidaina tun muna sheda juna.
''Leebeauty ta katse da dariyar da take yi I'm sorry tawan I don't mean to hurt you dariyan ne ya zo mun a bazata.
"Zuu,,,,,ni a nawa fahimta sai nake ganin kamar Ansar Galadima yana daf da canza sheqa.
Kamar ya yana daf da canza sheqa sai ka ce wani, d'an siyasa"? Ke ni fa ban fahimce inda ki ka dosa ba.
"Ina nufi Ansar yana daf da canza ki yana daf da fatali da soyayyarki.
"Wani mahaukacin birki Zuhura ta taka ta gangara gefen titi ta yi parking, duk ilahirin ga6o6in jikinta rawa yake sai kace 'yar tauri.
"Kuttt....ta hadiye wasu miyau masu d'acin gaske sai kace tasha mad'acin yanayin tashin hankalinta tamkar na wance tasami sak'on mutuwar uwa-ubanta.
"Da kyar tasamu ta yi controlling kanta ta tattara 'yan raguwar miyaunta masu d'aci ta yi amfani da su ta hanyar cewa.....
Jeeddah Aliyu
[12/04 11:50 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
*4*
Gaba d'aya hankalinshi ya raja'a da kallonta ya shagala sosai har bayaso yadaina kallon nata.
Hakan yasa yarage gudun mota ya koma tafiya sannu-sannu.
"Tafiyarta da shigar da ke jikinta suna masifar burgeshi, da yake glass d'in motarshi tinted ne shi yahana 'yan matan su gane yana kallonsu har suka 6acewa ganinshi idanunshi na kafe akan hanyar da suka bi yasauke k'arfafiyar ajiyar zuciya, ya ja mota a kasalance yanufi gidansu Zuhura.
Horn ya yi Abbah buzu ya bud'e masa gate yana ganin Ansar ne yashiga fara'a kamar gonar auduga Ansar ya yi parking yafito yanufi wajenshi.
''Barka da zuwa Muhammadu lafiya kwana biyu muka daina ganinka ko ka yi tafiya ne"?
Yauwa,,,,Abbah ina gari ba inda naje aiyuka ne suka yi min yawa da fatar yau za ka had'a mana ataye{green tea} na ranar naji dad'in shi sosai"?
Dariya Abbah buzu yashiga kyakyatawa daga bisani ya katse dariyar tashi kai,,,,,,lallai Muhammadu in natashi tafiya Agadaz da kai zan tafi saboda na fahimcin kana matuk'ar so ataye.
Dariya marar sauti Ansar ya yi yana Sosa k'eya yace ae Abbah na gayamaka in da rai lafiya wata rana kwatsan za ka ganin Agadaz, in kuma naje ba zan dawo ba har sai ka bani mata na aura yak'arasa magana cikin sigar wasa.
"Abbah buzu yak'ara yi dariya kai Muhammadu me za ka yi da buzuwa kai da ka ke da 'yar gaye irin 'yata Zuhra shima yabashi amsa cikin raha.
Ansar ya yi murmushi Abbah zan shiga ciki in ka had'a ataye kafin natafi zan sha.
Toh,,,,,,,Muhammadu a fito lafiya.
"Allah yasa Abbah Ansar yafad'a had'e da sa kai yashiga part d'in Granny da sallama yak'arasa shiga parlourn Granny da ke kishingid'e tana kallon sunnah tv tad'ago, had'e da amsa mishi yanemi waje ya zauna ya gaida Granny suka shiga fira daga bisani yafito da waya ya kira Zuhra ya Sanar da ita ya zo.
''Babu jimawa sai gata ta zo k'amshinta da yashaqa yasa ya yi saurin d'agowa ya dube ta, sanye take atamfar super exclusive d'ikin riga da skirt ya yi tight d'inta sosai kamar ta nisa rigar ya yake nonuwanta a fili d'an siriri veil tasa ta yane kanta duk haka bai hanawa Kalaba twisting d'in da ke kanta fitowa ba wance akayi mata combination da black & purple attachment, ta yi matuk'ar kyau Ansar yana kare mata kallo ya kauda fuska ya dubi Granny fuskarshi d'auke da b'acin rai kamanunshi gaba d'aya suka sauya fissibillahi! Granny Abunda Ku ke yi Sam bakwa kyautawa kalli shigar da Zuhra ta ke yi kuma haka take fita wani sa'in ba ko mayafi amma anrasa Wanda zai tsawata mata.
"Cike da takaici Granny take kallonshi daga bisani ta girgiza kai tace ni a suwa da zan tsawata mata Ansaru"?
A matsayinki na wance ta ke da iko da ita saboda kina matsayin kaka a wurinta, kin ga kenan kinada matsayin da za ki tsawatar mata.
Huh,,,,,,,Ansaru kenan da ace na isa na fad'a aji da tuni ya yi tasiri akanta tadaina wannan shasshanci a wani gefen in ka yi la'akari ba laifinta bane, irin tarbiyyar da uwarta ta tabata kenan.
''shiyasa akoda yaushe nake la'anta baqin hali irin na saude.
"Ansar yasauke numfashi ya maida ganinshi wajen Zuhra wance ta ja ta yi tsaye tana musu kallon mai cike da wulaqancin, suna had'a Ido ta ja dogon tsaki tajuya a fusace.
ke! Zuhura zo nan,,,,,Ansar yataka mata birki cikin d'aga murya cak.....tai tsaye sai dai batada niyya dawowa ki zo nace zan yi magana da ke yasake bata umurni a harzuk'e tajuyo indan na dawo me zan maka"?
Kasanni sarai bana iya jure wulaqancin musanman na d'a namiji.
kisani muddin ki ka sake ki ka fita wallahi zan barki bari na har abada.
A tsorace Zuhra tasauke idanunta akan fuskarshi, numfashinta na kai komo jiki a sa6ule tadawo cikin parlourn tai tsaye tana kallon Ansar idanunta tap da hawaye sai mutsu-mutsu take da baki.
"Nemi waje ki zauna Ansar yafad'a fuskarshi a had'e zama ta yi hawaye da take k'ok'arin dannewa suka sulalu akan kunce ta.
''Granny ta dube ta ja tsaki batun yau ba Zuhra nake kuka da irin wannan watsatsiyar shiga da Ku ke yi gara ma Nazeeya da ke domin ita tana saka mayafi sa6anin ke da ki ke fita tsirara da sunan wayewa.
''Ansar ya kar6e zance ta hanyar cewa ina wayewa Granny ga talla tsiraici"?
Bani na fad'a ba Ansaru haka suke cewa a duk lokacin da na zaunar da su ina musu nasiha.
Wannan ba wayewa bane Zuhra asalima duk mai hankali da tunani Wanda yake da wadatace ilimin islama zai danganta hakan da Jahilci domin wayewa tana samo asaline da mutume da yake ka re hakokin Allah ta'allah. Kiji tsoron mahalincinki Zuhra ki dube kanki Sam ba ki yi kama da 'ya'ya musulme ba.
su Kansu Wanda Ku ke kwaiwayo da su ba bu indan addininsu ya yarje musu su yi watsaysiyar Shiga.
Gashin attachment ne akanki Najasa ne Zuhra kin dauka ki sakawa kanki shin a haka ki ke bautawa ubangijinki"?
kalli faratanki zaqo-zaqo kin fente su da jan farce ki dubi girman Allah Zuhra ba don ni ba ki canza wad'annan mummuna d'abi'u da ki ka kwaso domin rankatakaf zuri'ar Galadima babu mai wannan d'abi'a sai ke da Nazeeya.
"Zuhra takasa furta uffan sai sharar hawaye take yi zuciyarta na tuk'uk'i tun da take duniya ba'a ta6a ci mata fuska ba irin yau burin Granny yacika yau Ansar ya wulaqanta ta a gabanta.
Granny ta kya6e baki tace Kadàina wahalarda yawun bakinka Ansaru domin wad'annan maganganu naka suna shiga kunnenta ne kamar ana busa zare a kunnen bebe tun da tana sonka kacigaba da yi mata Nasiha watakila Allah yasa adace tagano talla tsiraici ba abu mai kyau bane babban takaicin na shi ma sa'eedu ya zama shanyaye mijin tace duk lokacin da na yi mishi korafi akan shigar da yaran nan ke yi sai dai yadinga kad'a kai kamar k'adangare yana kyaci kamar zai d'auki mataki, ba kuma abunda zai iya saboda anriga an gama da shi Granny tak'arasa magana tana huci.
''Shikenan Granny zan yi iya nawa k'ok'arin na lurar da ita yajuya wajen Zuhra da ke shasshekar kuka yace yi hak'uri Zuhra nah zo mu je compound mu yi sulhu kinsan na tsani kukanki.
"Kamar jira take ta tashi da sauri ya bi bayanta Granny ta bi shi da kallon tausayi, tasan lamarin so ne kawai ba wai don Ansar yadace da Zuhra ba domin ta ko ina halayyan su yasha banban da na juna.
''Nufin Zuhra tashige part d'insu da gudu Ansar ya cinmata yasha gabanta, yana kallonta k'asa-k'asa yanzu don mun gaya miki gaskiya Zuhra shine za ki fushi"?
Ashe gyara kayanka zai zama sauke mu raba"?
"Tad'ago cikin hawaye ranta na soya tafara magana ba zai zama ba Ya Ansar amma kasani ko za ka yi min fad'a ka jani privately ba wai a gaban Ganny ba domin da kunnenka ka ji yanda take aibanta mahaifiyata.
"Ae dole ta aibanta mahaifiyarki saboda ita ce baqar uwa asarar dangin a zuciyar Ansar yafad'i haka a baiyane kuma sai ya yi k'asa da murya I'm very sorry babynaa kema kinsan Granny ta tsufa komai yafito daga bakinta fad'a kawai ta ke yi bata masa birki.
''Inasonki Zuhura sosai shiyasa nake kishinki banaso abunda zai 6ata miki rai har ki zubur min da hawayenki
tun da kinaso saka iri-iri wad'annan kayan at last ki dinga daura after dress akai, domin nasan ko nace ki saka hijab ba sakawa za ki yi ba indan mu ka yi aure sai ki dinga yi min kwalliya.
Ni da kaina zan dinga siyo miki english wear's har sai kince sun ishe ki muradina yakasance wannan kyakyawar halitta ni kadai nake kallon abata ba da 'kartti wajen ba.
Yak'arasa magana yana murmushi
"Dariya Zuhra ta yi shikenan zan dinga sakawa ko don na farantawa zuciyar da nakeso.
"Kiran sallah magarib ya katse musu zance nasu Ansar ya dube ta cike da shau'kin so yace shiga gida ki yi sallah nima zan tafi masallacin maybe nadawo maybe kuma sai gobe.
"Bara na kawo maka buta ka yi alwala noo,,,,,,ki barshi kawai zan yi a wajen Abbah
Huh,,,,,,Ya Ansar nagano ka kadai kace za ka je shan green tea kai ko d'acinsa ba ka ji
"Dariya ya yi mai sautin gaske ki je Ammah ta koya miki yanda ake had'awa inan mu ka yi aure kidinga dafa min.
ita ma dariya ta yi sai kace ba ita bace yanzu nan tagama kuka har da su shassheka.
Ansar ya juya yanufi bakin gate, cikin d'aga murya tace "Honey please in kayi sallah kadawo Allah ban gaji da ganinka ba.
Batare da yajuya ba yace naji zan dawo amma fa sai nagama shan mutume nawa{green tea}
Yana zuwa gate yatararda Abbah yana alwala ya ja kujerar roba ya zauna Abbah ya gama alwala ya mik'a masa buta tare suka jera zuwa masallacin sai da akayi sallah isha sannan suka juyo gida.
''Still a bakin gate suka k'ara yada zango Abbah yashiga room d'inshi na maigadi yafito da tarkace kayan ataye ya ajiye su kusa da k'afafuwan Ansar d'an k'aramin murhu waya yadauka ya dube Ansar yace muhammadu bari na debo mana garwashi, nasan yanzu Ammah ta isa sauke tuwo da sauri Ansar ya tashi tsaye ya kar6i murhun yi zamanka Abbah kawo na kar6o mana yanufi BQ Wanda a yanzu yazama muhallin Abbah da iyalansa shi ya kwana a bakin gate a d'akin maigadi matarshi ta kwana a BQ 'yarshi kuma ta kwana part d'in Granny.
Yana k'arasawa ya iske Ammah tana kwashe tuwo ya yi sallama had'e da gaida ta Muhammadu Kaine atafe"?
"Eh! Ammah ya gida"?
Lafiya lau Muhammadu tak'arasa magana had'e da kar6a murhun ta zuba mishi garwashi kace ko yau ka zo shan mutume naka"?
"Eh Ammah ae ni yanzu na zama buzu saura kawai Ku koya min buzanci da yanda ake nad'a rawani Allah Ammah wannan rawanin yana burgeni yak'arasa magana yana dariya.
Ammah na tayashi kamar daga sama yafara jin zazzaqar murya mai matuk'ar dad'i tana rera karatun Qur'ani mai girma cikin suratul Al- araf tsit,,,,,,,ya yi kamar anyi ruwan sama andauke ya ba za fatun kunnayenshi biyu yana sauraron wannan muryar mai zak'i da gard'in gaske baisan lokacin da ya lumshe idanunshi ba.
''Lafiya Muhammadu ko kana buk'ata wani abu ne"? Muryar Ammah ce tadawo da shi natsuwarshi cikin jin kunya yashiga girgiza kai yajuya ya koma wajen Abbah.
"Har ya kamalla shan green tea zuciyarshi na azalzalarshi akan ya tambaye Abbah wacece yaji tana karatun Qur'ani iya saninshi daga Abbah sai Ammah yasani baisan suna da 'ya ba yana kuma gudun kada Abbah ya fassara shi bai-bai dole ya mik'e ya kira Zuhra a waya tafito sai around _10:00pm_ ya baro gidan har zuwa lokacin zazzaqa muryarta tana shawagi a dodon kunnenshi.......
Jeeddah Aliyu
[13/04 8:06 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
*5*
Ansar yana zuwa gida ya kwa6e kayan jikinshi yashiga bathroom ya yi wanka yafito sanye da bathrobe, tsaye ya yi gaban mirror yana tunani Jikinshi a mace ya dauki robar lotion ya shafe skin d'inshi.
Yasanya pajamas ya fashe jikinshi da turare mai sanyi k'amshin ya kwanta had'e da kashe light ya yi switch on d'in tv Kallo yake yi sai dai gaba d'aya hankalin nashi baya ga kallon ya yi nisa a tunanin 'yan mata 3 Zuhura, mai niqan, da Mai zazzaqar murya ya lumsashe idanu yana shafar sumar kanshi a hankali _me ke damuna miyasa nake tunanin wad'annan 'yan matan guda 2"?_
Mtcsww....,,,,ya ja tsaki har k'arfe _3:00_ na sulasuli dare ya yi Ansar na kwance sai faman juyi yake yi yakasa bacci ya tashi zaune ya lankwashe k'afafunshi a tsakiyar gado yadafe k'ok'on kanshi idanunshi sun kad'a sun yi jajir alamar rashin samun baccin.
''Ya sauka daga gado yashiga bathroom yadauro alwala yafito yashiga jera nafila, har akayi kiran asuba sannan ya dakata da nafilla da yake yi yanufi masallacin ana sallame sallah bai tsaya sauraron wa'azin da liman ya ke gabatarwa ba yadawo gida. Tsananin baccin da yake ji idanunshi har wani yaji-yaji suke mishi ya haye gado yak'ara gudun Ac bai jima da kwanciya ba baccin ya kwashe shi.
_Zuhra_
"Tsaye take a gaban dressing mirror tana caba make-up kamar wance za ta tafi za6e miss world wani d'akkake lace tasaka marrow colour da touch d'in white ga lace mai kyau da tsada amma anyi mishi style d'in Allah tsine skirt d'in yankar piece ne rigar kuma dai-dai saitin nonuwa akayi mata tsaga Wanda ya baiyanar da nononta tunawa da arta6o da tasha jiya da Ansar yasa taciro after dress white in colour ta daura akan kayan. tasaka white hill shoe's ta yi rolling da veil d'in rigar sai gashi ta yi kyau na ban mamaki.
"Har tajuya tasake dawowa tak'ara Shafa powder da lipstick ta ware idanunta tasake tsuke bakinta kamar mai shirin yi kiss tajuya tak'ara juyawa a baiyane ta furta bravo,,,,, Alaiki I'm proud of myself gaskiya ni kyakyawa ce ina Alfahari da wannan kyakyawar halitta da Allah yabani tasaki murmushi ta d'auki black shade ta kwama ta zari brown handbag tanufi kan bedside drawer ta tattara handouts d'inta tafice a parlour ta iske Haj saudat Hajiya na fito Daddy yabada k'udin ki bani"?
"Eh yabani gasu tasaka hannun kusa da ita taciro 5k ta mik'a mata ta kar6a ta zarce dining area ta yi taking breakfast tana gamawa tafita ta ja motarta tafice daga gidan.
"A k'ofar gidansu leebeauty ta yi parking taciro wayarta ta kirata bayan kamar 3 minutes da kiran nata sai ga ta tafito cikin wani silk material yana shining style d'in fitted gown rigar ta matse ta sosai har ana iya gani layin pants da bra d'inta kanta yasha Kitso Ghana weaving Wanda akayi mata da brown in colour attachment hannunta rik'e da handbag d'ayan kuma tarik'o handouts ta balle k'ofa tashiga, ihu ta kurma tana zarar ido kamar wance ta ga abin tsoro.
"Zuu Galadima what's wrong with you huh"?
No thing's,,,,,,,, ko kin ga wani abu ne tare da ni"?
''Ofcourse yes,,,,,,look your dress tana magana ne had'e da nuna jikin Zuhra da yatsanta, ajiyar zuciya Zuhra ta yi tacire shade d'in fuskarta tashiga zayanewa leebeauty yanda ta yi da Ansar tacigaba da cewa leebeauty banida mafita da yawuce dole nayi yanda Ya Ansar yakeso Co's I love him so much banaso abunda zai haifar da problems a tsakaninmu,,,,,......ke! Dallah dakata wai me ke damun kanki ne huh"?
Zuhra ina tausaya miki duk ranar da ki ka Shiga tarkon taskon d'a namijin ke yadace ki dinga juya Ansar Galadima ba wai shi yadinga juya ki ba. tun kafin Ku yi aure yafara kafa miki sharad'in yau yace kisaka after dress gobe hijab zai ce ki sa daga nan zai mayarda ke, local girl indan Ku ka yi aure yadawo waje yana friendship da wayayu 'yan mata ke kuma yariga yacuce ki yahanaki morar kuciyarki daga nan sai ya auro miki 'yar bariki ke ko yabarki da zunbulele hijabi ki yi tunani k'awata.
''Zuhra ta yi shiru tana nazari kalaman leebeauty wannan ce damar da leebeauty tasamu tacigaba da zuga zuhra wannan shigar da mu ke yi zamani ne ya zo da ita ba wai mu muka k'irk'ira ba kuma shine wayewa muna high school ace mu dinga saka local dress ae sai a raina mu.
Zuu duk abunda zamani ya zo da shi ka tsunduma a dama da kai kada ayi ba da Kai ba daga baya kadawo kana kara'i kinga kenan anyi ba'ayi ba d'aukar makaho photo.
wayewa ne yasa mu ke saka wad'annan kayan amma kowa yasan mu ba 'yan iska bane wata rana ko ance mu saka bara mu saka ba Co's mun riga mun cin lokacin mu, infact ko a school mutum nawa Ki ka ga suna local dress''?
"A Wannan zamani ko matan aure basa 6oye kyakyawar halitta da Allah ba su kina kallo tsakanin mu 'yan mata da su masu aure har ba'a iya tantance waye mai aure waye marar aure.
Kina shiga school da wannan rigar za'a fara zargin ko ciki shege ne da ke saboda baki saba sakawa ba.
kuma kinfi kowa sani duk wance bata irin wannan shigar da tasaka ciki ne da ita ko kin manta da Raleeya Basheer a lokacin da ta yi ciki tadawo saka hijab da After dress tsananin gulmarta da akeyi yasa tabar school ba bu shiri ki yi wa kanki k'iyamun lailli kicire wannan katuwar rigar ki barta a mota.
"Batare da dogon tunanin ko nazari ba zuhra tacire after dress d'in jikinta ta ja mota suka nufi school.
"A lokacin d'aya suka balle k'ofar mota suka fito cikin yanga suke tafiya sai wani karkad'a hip's suke yi kamar 'yan makosa dance a haka suka nufi department d'insu.
_ANSAR_
''Ansar yana zaune a dining table sai fama juya fork yake a cikin plate.
yakasa cin abincin shi kanshi in ka tambaye shi me ke damunshi ba zai baka amsa ba, domin baisan ainihin abunda yake dawainiya da zuciyarshi ba. har Hajja fatee tak'araso kusa da shi baisaniba sai jin ya yi tadafa kafad'arshi ya zubura a tsorace yasauke ganinshi aka fuskarta, cikin sark'ewar halshe yace.......
Jeeddah Aliyu
[16/04 3:54 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*This book is dedicated to only you my adorable, my super star Aunty Sis💞 thanks so much sweetheart, I don't know how to thanks you for the love,courage, kindness you have shown to me. Thanks so much I really appreciate it. Allah yahada fusk'ok'inmu a aljanna Firdausi. Ameen*
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
*2*
Mum fa"? Nadeeya ce ta amsa mishi ta hanyar cewa tana upstairs bedroom, ya juya ya dube Yaya Baby ya lamgwa6e kai yaya Baby yakamata kutashi ku rakani Gadon k'aya naga Tsohuwa mai ran karfe domin na tabbata ba don k'afafunta sun hanata watayawa ba da tuni ta tsofa a gidanan.
"Gaba d'aya suka sa dariya yaya Baby tace ba wani tsohuwa da za ka je gani kadai za ka je ganin Zuhura.
"Sosai k'eya ya yi yana dariya k'asa-k'asa Basmah ta mik'e ni dai bara na dauko mayafina ni ma ki dauko min nawa cewar Nadeeya kenan tana kallon Basmah.
Sallama suka yi da Mum saboda Dad tuni yafita motoci 2 suka dauka saleema da Abeeda Nadeeya ce ke driving nasu yayinda Yaya Baby ke driving Ansar da Basmah. tafiya suke cikin nishad'i da haka suka iso gidan Alhaji sa'eed Galadima a lokacin d'aya suka yi parking Sannan suka nufi cikin gida part d'in Haj saudat suka nufa, gaba d'aya parlourn ya hargitsi da murna ganin Ansar bayan komai yalafa.
''Ansar yashiga rarraba idanu ko zai hango hasken zuciyarshi har idanunshi suka gaji da nemanta ya hak'ura shigowar Abdallah ne ya d'an haifar mishi da natsuwa, can dai yagaji da hak'uri ya dubi Nazeeya ya yi k'asa da murya yace Nazeeya ina Zuhura tashiga ne ko batasan na zo bane"?
Dariya Nazeeya ta yi tace tana part d'in Granny tasha kwalliya tana zaman jiran zuwanka da alama batasan cewa tanan za ka fara zuwa ba.
"Murmushi Ansar ya yi ya mik'e tsaye yanufi k'ofar fita Abdallah yace kai kuma ina zuwa ana fira za ka ta tashi"?
Part d'in Granny yafad'a kaitsaye dariya suka sa kamar had'in baki suka Mara mishi baya, yana turo k'ofar glass ta parlourn Granny ya hango Zuhura kwance ta yi pillow da cinyoyin wata mata baquwar fuska saboda sai yau yafara ganinta kamanunta kadai da ya duba yagano cewa buzuwa ce.
"Hayaniya su Abdallah ya ankarar da Zuhura ta kai dubanta bakin k'ofa idanunta suka sauka akan fuskar abin kaunarta zubur ta tashi daga jikin Ammah ta ruga da gudu tanufi wajen Ansar duk iya k'ok'arinshi ya yakaucewa rungumar da takawo mishi saida Zuhura ta yi nasara had'e jikinta da nashi yakiceta ya yi daga k'irjinshi yarik'o hannunta, yanufi wajen Granny da ke kishingid'e yasaki hannunta ya durk'usa ya daura kanshi bisa cinyoyinta mun same ku lafiya Granny"?
Lafiya qalau Ansaru ya karatu da Masu jajaye kunnuwa"?
"Ba Ansar kadai ba duk Wanda ke cikin parlourn saida yadara cikin shagwa6a Zuhura tace wai ke Granny sai yaushe bakinki za ki iya furta Ansar"?
Harara Granny ta watsa Mata had'e da cewa bansaniba Ammah tana dariya ta mik'e tace Hajiya ni zan tafi naga kin yi ba'kon bature dariya suka k'ara kwashewa da ita Ammah na fita Ansar ya sauke idanunshi akan fuskar Granny wacece wannan matar domin ni bansanta ba, kuma batayi min kama da dangin mu ba"?
Murmushi Granny ta yi tace Matar maigadin gidanan ce amma yanzu sun zame mana tamkar 'yan uwa na jini tun daga kanta har mijinta da muna jin dad'in zama da su, suna da matuk'ar kirki.
"Ansar ya yi murmushi ya juya dube Zuhura da ke tsaye idanunta kyam akanshi ko kiftawa babu yace my wife mu je garden mu zanta saboda naga wad'annan mutane sun cika nan wurin yana magana ne had'e da nuna su Abdallah da yatsa.
"Zuhura ta yi tsagal tace gaskiya da yafi nima ina buk'atar na ke6e da mijina.
Yaya Abeeda ta rik'o hannun Saleema tace zo mu tafi Saleema wad'annan yaran ba kunya ne da su ba saleema ta mik'e yayinda Baby ta Mara mata baya suka fice daga parlourn.
"Hannun Ansar Zuhura ta rik'o Honey tashi mu tafi mana, zare hannunshi ya yi daga nata Abdallah yace mu kan ba inda za mu je sai dai ku kubarmana parlour.
Harararshi Ansar ya yi had'e da cewa sai ku sha zama ya mik'e tsaye yanufi k'ofar fita Zuhura na biye da shi.
"A k'asan grass carpet suka zauna Zuhura ta zauna gabanshi tana facing nashi, ta lamkwashe k'afafunta, sai lokacin Ansar yak'are mata kallo Atamfar super exclusive ce sanye da jikinta d'inki riga da siket anyi mata style da co lace high neck raga-raga gaba d'aya ana iya hango boobs d'inta ta kusaye cut lace d'in da sauri Ansar ya d'auke fuskarshi da barin kallonta.
"Ya Ansar U.K ta kar6e ka ga yanda ka K'ara kyau skin d'inka very fresh & smoothly tak'arasa magana had'e da riqo hannunshi tana shafar skin d'in hannunshi har wani lumsasshe ido take yi.
"Tsigar jikin Ansar ya tashi yarrr...babu shiri ya firzge hannunshi ya kuma murtuk'e fuska Kidaina ta6a ni Zuhura addini bai yarje mana mu dinga ta6a junanmu anyhow ba beside shed'an zai iya qawata mana wani abu, daga baya mu dawo nuna danasani marar amfani.
"Har ya dasa aya a zancenshi Zuhura tana mishi kallon mamaki kasa hadiye mamakin nata ta yi har sai da ta furta haba! Ya Ansar don na ta6aka shine me ko ka manta ne saura kiris a Shafa fatiha a tsakaninmu"?
"D'an bazawari murmushi ya yi Wanda ke nuna Sam bai gamsu da wannan guntun bayani na ta ba, don saura kiris a Shafa fatiha a tsakaninmu Zuhura ba shi zai ba mu dama mu dinga tsallake iyaka ba.
"Tabe baki ta yi a zuciyarta tana mamaki rashin wayewa na Ansar mutume da ya je abroad karatu ace bai waye ba har sai yaushe zai waye, tad'ago ta dube shi suka had'a ido ta kauda fuska.
"Ansar ya yi murmushi kamar yasanta abunda zuciyarta take saka mata, cikin taushin halshe yakira sunanta Zuhura"!
''Na'am tafad'a kamar mai ciwo hak'ora ki yi hak'uri idan kalamai na sun b'ata miki rai kinsan ba abunda yake saurin ta6ani irin b'acin ranki.
Dad'in kalamai shi suka lullu6e Zuhura sai wani rangwad'ar da kai take yi, ganin haka yashiga tsarata da dadd'an kalamai kiran sallah magarib ya mayarda su part d'in Granny.
*WASHE GARI*
Ansar ya rabawa su Nadeeya tsaraba da ya yo musu trolley guda yacikawa Zuhura da had'ad'u Arabian gowns da hijabai different colours had'e da shoes da handbags ga kyau ga tsada misalin 'karfe _2:30pm_ yanufi gidansu Zuhura yana Shiga layin gidansu idanunshi suka hasko masa wata matashiyar budurwa wance shekaru ta ba za su haura 17yrs ba tana sanye da Hijab har k'asa sky blue colour ta yane fuskarta da niqan, tana tafiya a hankali kamar mai tsoron taka k'asa yanayin tafiyarta cikin natsuwa yak'ara tafiya da imaninshi kasa d'auke idanunshi ya yi daga kanta hakan ne yabashi damar rage gudun mota yasoma tafiya slow-slow yana kallonta har tak'araso daf da motarshi ta ra6a ta gefenshi ta wuce kanta a sunkuye tana kallon k'asa tsintar kanshi ya yi da bin ta da kallo ta cikin mirror da ke jikin motarshi idanunshi na kanta har sai da ta6acewa ganinshi sannan ya yi nasara dawowa cikin natsuwarshi.
"Cike da mamakin kanshi ya ja mota da k'arfi ya nusa cikin unguwar, horn yadanna a bakin gate d'in gidansu Zuhura maigadi ya bud'e masa gate, tsayawa ya yi ya gaisa da Abba buzu maigadi saboda tun jiya da Granny tabashi labarin kirkin mutume ya ji aranshi ya kwanta masa parking lot yanufa ya yi parking.
"Yafito daga mota ya hango Fahad yafito daga cikin gida kai Fahad zo nan"! Ya kwadawa Fahad kira bayan Fahad ya zo ya bud'e boot d'in mota yanuna mishi nasu tsaraba ga tsarabanku nan kowane ku da sunanshi akai Fahad yashiga yi masa godiya ya kinkime kayan Indan kashiga ciki ka turo min Zuhura ina part d'in Granny.
Fahad ya amsa da to..yawuce cikin gida yayin da Ansar ya ja trolley d'in da tsaraban Zuhura yake ciki yanufi part d'in Granny ''Ammah kadai ya tarar a parlour tana linkewa Granny kayanta da ta kwaso daga igiyar shanya, gaisawa suka yi Yanemi sofa ya zauna Ammah ina Granny"?
Tana d'akin ko a kirata ne"?
Noo.....ki barta kawai ae ba yanzu zan tafi ba
Shikenan.... Ammah tafad'a had'e da kwashe kayan da ta linke tanufi cikin d'akin Granny Ansar yafito da phone d'inshi ya kira wani friend d'inshi Sageer da suka yi karatu tare a U.k ya shagala da firar da yake yi da Sageer.
Ba ko sallama Zuhura tafad'o parlourn sai saukar numfashinta Ansar ya ji a kunnenshi yad'ago a rikice tana tsaye daf da shi tana zuba murmushi sallama ya yi da sageer yasauke idanunshi akan sutura da ke, sanye a Jikinta Black colour skintight da red colour d'in top a tsakiyar gaban top d'in anyi tsaga dai-dai saitin Nonuwa wannan yasa boobs d'inta a baiyane Fitinanai k'amshin na fita daga Jikinta kanta ba d'an kwali gashinta yasha gyara yana lullu6e da gashin attachment ya kwanto har gadon bayanta sai kace nata.
"Ansar yasauke ajiyar zuciya had'e da janye idanunshi daga kanta a zuciyarshi yasoma aikawa kanshi tambayoyi anyya kuwa Zuhura tana da hankali"? wannan wace irin masifa ce kalli wad'annan watsatsu kaya da tasaka"?
Yaushe Zuhura ta sauya kyawawa d'abi'aunta da nasanta da su"?
Yasaukar hannanye ta ya ji a kafad'arshi tana matsa mishi jijiyoyin wuyanshi abun ka da lafiyayye namiji wanda baya tsallaka iyakokin ubangiji cikin d'an k'ank'anin lokacin ya tsince kanshi cikin wani yanayi gaba d'aya Jikinshi ya mutu.
"Kamar Wanda aka tsakara yadawo hayyacinshi _A'uzubillahi minal shed'anin rajim_ yafad'a had'e da ture hannayenta daga wuyanshi ya mik'e tsaye Wawan tsaki ya ja cike da jin haushi yace wai meke damunki ne Zuhura"?
Yatsine fuska ta yi had'e da dusuna duwawunta akan kujera na yi maka kama da Wance take cikin damuwa ne"?
"Sororo ya yi baki bud'e yana kallonta daga bisani ya zauna nesa da ita ga tsarabanki nan na kawo miki ki bud'e ki gani ko na iya za6i"? Yak'arasa magana da murmushi akan fuskarsa.
"Tana yatsina tasauko daga kan kujera ta janyo trolley d'in ta zuge zip tasoma fitowa da handbag's wow! Gaskiya Honey ka iya za6i gaba d'ayansu favorite colour's d'ina.
Ansar yasaki murmushin jin dad'i harda su kada kai tana dauko shoes ta tabe baki, tad'ago tasauke idanunta akan fuskarshi cikin gadara tace Amma Ya Ansar wad'annan shoe's d'in ba nawa bane"?
"Na ki ne mana yafad'a with full confidence k'ara yatsine fuska ta yi lalle ma Ya Ansar kana nufi har ka manta da size d'ina"?
Sosa k'eya ya yi alamar jin kunya ni fa na dauka 37 ne size naki"?
To in Kadauka ka sauke 39-40 shine size d'ina.
Murmushi Ansar ya yi domin tun ba yau ba yasan halin Zuhura na rena arziki ba kasaifa yake mata kyauta ta ya6a ko tanuna farin cikinta ballantana har yasamu kalmar godiya daga bakinta, wannan yana d'aya daga cikin mummuna d'abi'aunta da yatsana ga kuma wasu sababbi da yadawo ya tararda ita d'auke da su.
"Watsar da takalmin ta yi a gefe tashiga zaro raguwar kaya da ke ciki zaro ido ta yi miye wannan"? Tana magana ne had'e da d'ago hijab, da mugun mamaki Ansar yake kallonta bangane miye wannan ba ke bakida idanu ne"? Yak'arasa magana cikin b'acin rai Zuhura kuwa ko a jikinta sai ma jefar da hijab d'in da ta yi Ya Ansar ba zan 6oye maka ba ni bana saka irin wad'annan kayan duk wata sutura mai nauyi bana shiri da ita, saboda banason zafi shiyasa tsakanina da Hijabi sai in zan yi sallah bana saka Arabian gown ko last year da Daddy ya je Makka yasiyo muna Arabian gown ni nawa *Anaal* na ba wa domin anan gidan ita kadai ce take saka irin wad'annan kayan.
"Tun lokacin da tafara magana Ansar yake mata kallon mamaki da takaicin wai yaushe notun kan Zuhura ya kwance"?
Gani yanayin da yake ciki yasa ta tabe baki tace ni ina mamakin anyya kuwa wad'annan tarkace a U.K kasiyo su domin kwata-kwata ba su yi min kama da kayan da suka fito daga U.K ba"?
"Ran Ansar yak'ara b'aci yashiga girgiza kai ya isheki Zuhura nace ya isa hakanan Yafad'a cikin tsawa da tafarfasa zuciya, wad'annan kayan su naga damar siya miki tunda ba za ki iya amfani da su sai ki ba wa Nazeeya ba wai kidinga gushesu a gabana ba.
Taso mishi ta yi kamar za ta cinye shi d'anye Sam babu ladabi balle d'a'a tafara magana kai wane irin mutum ne Ya Ansar"? Daga nace banaso wad'annan tarkace shine za ka rufe ni da masifa"? to ni wallahi ba uban da ya Isa ya yi min dole
A tsorace Ansar ya mik'e tsaye jikinshi har wani Mazari yake idanunshi sun canza kala zuwa jajaye.......
Jeeddah Aliyu
This is another must read and one of the best hausa Novel HUBBUL YAQEEN http://share4world.com.ng/2019/03/24/hubbul-yaqeen/ enjoy free readings
ReplyDeleteMuna godiya sosai arinka zuba mana kalaman soyayya gaskiya muna karuwa daki
ReplyDelete