Tuesday, 9 May 2017

SONKI NE SANADI 7~19

[18/04 12:06 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*7*

Candijam ashe kuwa Ya Ansar yadauko ruwan dafa kansa, domin na tabbata fasa aure na tamkar yake da yada6awa kansa yunka.
  "Tabe baki leebeauty ta yi ke yanzu za ki iya auren wanda baya sonki"?
Ke ubanwa ya gayamiki Ya Ansar baya sona"?
"Ubana leebeauty tafad'a tana kallon fuskar Zuhura mtcsww"! Zuhura ta ja tsaki had'e da Jan mota da k'arfi ta haura kan titi.

*5:44pm*

Ansar yafito daga cikin gida yana tafiyar sauri yanufi parking lot ya ja motarshI kirar kia cerato dark blue in colour, da k'arfi yafizgi motar gateman ya bud'e masa gate yafice.
  "Kaitsaye unguwar su Zuhura ya dosa dai-dai wajen da yasaba ganinta anan ya yi parking, zullumin yake had'e da addu'a Allah yasa mai niqan ba ta wuce ba har aka yi kiran sallah magarib yana zaune yana jiran tsanmani daga bisani da ya tabbata tariga ta wuce, dole ya ja motarshi ya tsaya bakin masallacin ya yi sallah magarib ya jira isha.
   ''Bayan ya yi sallah isha ya yanke shawarar shiga gidan su Zuhura, yasha black tea wajen Abbah maigadi.
 "Horn ya yi Abbah ya bud'e masa gate Ansar ya yi parking yafito yanufi bakin gate ya tarar da Abbah har miyar da gate yarufe yana zaune, yasha rawani da baqin yanki  irin nasu na buzaye.
  "Sallama Ansar ya yi mishi had'e da mik'a mishi hannu, suka yi musabaha daga bisani ya zauna Abbah akwai shi ko sai andafa"?
Murmushi Abbah ya yi yace sai anfada muhammadu ban yi tsanmani za ka zo yau ba da tuni na dafa mana.
  "Shima Ansar murmushi ya yi ba damuwa Abbah ko yanzu za mu iya dafawa da zafinsa yana k'unar baki yafi dad'i sha.
  "Abbah ya yi dariya kai muhammdu lallai ka zama cikakke buzu saura kawai nafara yi maka nad'i.
 Dariya Ansar ya yi Abbah har nad'in ina so ni fa duk abunda zai fito daga gareku Abbah ina sonshi.
  Dad'i ya lullu6e Abbah yasan k'aunarsu da Ansar daga Allah ne domin yanda yake musu hidima, kamar su suka haife shi daga Abbah har Ammah suna matuk'ar k'aunar Ansar suna jinshi tamkar d'ansu Auwal da ya6ata shekaru masu dama da suka shud'e.
"Kamar yanda Ansar yasaba d'aukar murhu yad'ebo garwashi ko yanzu hakan ce tafaru ya sunkuce murhu yanufi BQ wajen Ammah.
  "Da sallama yashiga Ammah da ke d'aki ta amsa masa muhammadu ne"?
"Eh"! Ni ne Ammah ya gida"?
Lafiya qalau muhammadu.
Ammah tafad'a had'e da hankad'e curtain{La6ule} tafito k'ara gaisawa suka yi Ammah ta kar6i murhun ta zuba masa garwashi, yayinda Ansar ya baza kunnen ko zai ji qira'a da ya ji ranar.
  "Gashi Muhammadu Ammah ta katse masa tunani ya kar6i murhun a sanyaye har ya juya ya yi tak'o d'aya zuwa biyu sai ya ja ya tsaya, cike da jin kunya yajuyo yana kallon Ammah. Ya zame masa dole ya tambaye Ammah abunda yake azabtar da ruhinsa, ko zai same sauki ya kuma fita daga halin qila wa qala.
  "Muryar nan tashi  asanyaye yace Ammah Dan Allah aron Cassette d'inan na qira'a da naji kina sauraro ranar za ki bani. Qira'a ya yi min dad'i inason na nemo irinshi.

"Ga mamakinsa sai yaga Ammah tana dariya sai da ta yi mai isarta sannan, tace Muhammadu ba cassette bane Anaal ce.
  "Rass-rass.....gaban Ansar ya yanke ya fad'i zuciyarshi tashiga bugawa da sauri-sauri sai kawai ya yi murmushin yak'e yace ikon Allah ni na dauka a DVD plate ne.
''A'a bashi bane k'anwarka ce Anaal k'ara shiga rud'ani ya yi shi dai yana jin sunan nan a bakunan mutane gidanan, dai-dai da sau d'aya bai ta6a cin karon da mai wannan sunan _shin wacece Anaal"?_ lallai yakamata na nemo sanin akan wannan Anaal mai zazzaqar murya. A karo na biyu yak'ara juyawa jiki a mace yafita yana zuwa ya mik'awa Abbah murhun garwashin, ya ja kujera ya zauna yashiga tunanin wacece Anaal"? Ko ma wacece ita Allah yabarkace ta da dad'in murya gashi ta iya karatun Qur'ani kowane harafi tana bashi hakk'insa zuciyata tana mararin had'uwa da ke Anaal n.........muhammadu"!
Abbah ya katse masa zancen zucin da yake yi.
    "Na'am,,,,,,Abbah.
Muhammadu ka tayani murna k'anwarka Anaal saura surah d'aya ta hadace Al-qur'ani mai girma.
Ba ka ji farin cikin da nakeji ba muhammadu nikan zuwa Najeriya ya yi min rana 'yata ta albarkatun da ilimin addini da na zamani.
Allah yasakawa Alhaji sa'eed da gidan aljanna ya yi min alheri da har na ko ma ga ubangijina ba zan manta da shi ba.
"Shi dai Ansar mutuwar zaune ya yi sai yanzu ya fahimcin Anaal 'yar Abbah da Ammah ce.
To ya akayi duk zuwan da nake yi gidanan ko a bisa kuskure banta6a had'uwa da ita ba.
Ansar ya had'iye yawu yace Ameen Abbah ai yi wa Kaine ita kuma Anaal Allah yasa mata albarka a karatunta yasa abunda za ka ci amfani sa ne.
Ameen muhammadu
           ''Yayinda Abbah yacigaba da cewa waton Muhammadu ba yabon kai ba wallahi ina alfahari da 'yarta sai dai kashhh.....akwai abunda yake cin min tuwo a kwarya.....Abbah yad'an shed'a damuwa ta baiyana k'arara akan kyakyawar fuskarshi. Daga bisani yacigaba da cewa sanin kanka ne Muhammadu mu baqi ne kowane lokacin za mu iya komawa k'asarmu, Agadaz a can Agadaz muna zaune ne a wani k'auye dajin Allah Jama'a mazauna wannan k'auye ba abinda mu kasani sai kiwon awakai da rak'uma muna rayuwa tamkar wad'annan awakai da rak'uma kasan dalilin da yasa nace da kai haka"?
    "Ansar ya girgiza kai.
Abbah yace saboda ba mu da wadatace ilimin addini islama balle aje ga ilimin boko shi ka ajiye shi a gefe domin ba mu basan menene shi ba.
  ''Zuwanmu Najeriya mu ka fahimcin menene addinin musuluncin har mu ke gudanar da ibadunmu adai-dai shiyasa nake da burin Anaal tana, gama sakandire na aurar da ita saboda ina fargaba komawa Agadaz da ita mahaifina zai iya aurar da ita ga jahilan k'auye.
Abbah yak'arasa magana kamar zai fashe da kuka.
  "Sauke numfashi Ansar ya yi yace wannan ba abin damuwa bane Abbah insha Allah, kafin tak'arasa karatun nata Allah zai kawo mata mijin aure. Sai dai Abbah wani hanzari ba gudu ba a yanda naji kana yaba hazaqarta me zai hana kabarta ta je makarantar gaba da sakandire kafin Allah yakawo mijin sai ka aurar da ita.
   "Jikin Abbah yadauki rawa yana girgiza kai kul,,,,,muhammadu karka sake yi min maganar makarantar gaba da sakandire nan, banda tambad'ewa da lalacewa da rusawa 'ya'ya mutane tarbiyya ba abunda suke koyarwa. Ai ni na d'auki darasi daga kan yaran gidanan ada kafin su je makaranta nan duk fad'in unguwar nan ba 'ya'ya da suka fi su natsuwa da ingantattaciya tarbiyya sa6ani yanzu da ake buga misali da tarbarbarewa tarbiyya akansu.
''Ansar ya gyara zamanshi yak'ara fuskanta Abbah ya yi k'asa da murya ni a nawa gani Abbah duk mutume da ka ga ya je highschool ya sauya kyakyawan halinsa zuwa mummuna to dama can yana da burin yin hakan. A yanda naji kana yaba hazaqar Anaal bai dace ace karatunta iya secondary ya tsaya ba.
  ''Abbah kai kanka kana da yak'ini akan irin tarbiyyar 'yarka take da ita bai kamata kasa shakku akanta ba. Kabarta tacigaba da karatu irin basirar da take da irin wance al'ummar musulme za su amfana da ita ne.
"Har Ansar yadasa aya Abbah yana kallonshi yana kad'a kai alamar yafara gansuwa da jawabin nashi. Abbah ya gyara zama Muhammadu ban k'i ta taka ba nima na gabarta maka da nawa uziri, ba wai ina shakka ko kwankwanto akan Anaal bane ina tausayawa irin rayuwar da za ta yi indan lokacinmu komawar mu Nijar ya yi batare da ta yi aure ba.
 "addu'a kawai za ka yi mata Abbah domin Allah yana saurin kar6a addu'ar iyayye akan 'ya'yansu.
Shikenan Muhammadu Allah ya za6a mata abinda yafi zama alheri a rayuwarta.
   ''Ameen Abbah tana aji nawa ne"?
Tana shekarar karshe Abbah yafad'a had'e da mik'ewa yasauke green tea ya zuba a cups sai tiriri yake ya zuba sugar kad'an ya mik'awa Ansar cup d'aya.
Ahankali Ansar yake kur6a green tea saboda zafi da yake da yana sha Abbah na bashi labarin Anaal Ansar yana shanye green tea yadire cup cikin girmamawa ya dube Abbah bara na shiga ciki Abbah na gaida su Granny.
Toh Muhammad a fito lafiya.
Ansar ya amsa da cewa Allah yasa ya juya a natse yashiga part d'in Granny a parlour ya tarar da ita da littafin izziya ta kwama medical eyeglasses tana karatu.
"Tsaye ya yi yana kallonta ya kwashewa da dariya a firgice Granny tad'ago sannu a hankali ta ajiye littafin hannunta ta zare eyeglasses d'in idonta ta dubi Ansar ta galla masa harara kai shak'iyi ni ka ke yi wa dariya"?
    "Dole nayi miki dariya Granny kinga yanda ki ka tak'ark'are kina karatu sai kace zamani da ki ke cikin ganiyar kurciyarki lallai tsohuwa nan kin mana wayo, nima ya zama dole na koma islamiyya.
  Yak'arasa magana had'e da zaunawa kusa da ita dariya Granny ta yi ba dole na tak'ark'are ba na fi wannan dak'iki'ya matar taka wance ko Hizzib 10 ba bu akanta sai d'an banzan fad'in ran tsiya.
  "Uhm,,,,,Uhm,,,,Granny karki yi wa matata sharri.
Ba sharri nake mata ba gaskiya ce nake fad'a ga malama a gida a maimakon su dinga zama tana, daura musu karatu tunda sun karkare zuwa islamiyya shiririta ta hanasu.
"Ansar ya girgiza kai takaicin ya baiyana k'arara akan fuskarsa Granny lamarin yaran ne sai addu'a especially Zuhura domin gara Nazeeya sau dubu da ita.
   "Granny ta yi ajiyar zuciya mai k'arfi bari kawai Ansaru hannunka ne baya ru6ewa ka yanke ka 'yar da tuni nace ka hak'ura da auren Zuhura babban takaicina da al'amarin Zuhura rashin kula da addini lokacin sallah ya yi ta yi zamanta tana latsar waya, har sai wata sallah ta riske wata sannan ta had'e su tagama ta kai tsakiyar dare tana latsar waya batare ta yi sallah isha ba, sai da safe ta yi ta wannan bala'in da me yai kama"? Mahaifiyarsu taana kallon wannan tabargaza da suke tafkawa bata iya kwa6arsu sai kace 'ya'yan ido, shi kuma sa'eedu baya iya aiyana komai tariga ta shanye shi. Hatta da girki yaran nan basu iya ba saidai Anaal tashiga kitchen su kuma, su hakince parlour suna latsar waya basu San cewa Kansu suke kwara ba Anaal ba domin duk namiji da aure Anaal wallahi ya yi dace da mace tagari mai nagartaciyya tarbiyya Anaal ga hankali da natsuwa ga ladabi da biyayya uwa-uba ilimin addini da na zamani a rayuwata banta6a gani yarinya mai natsuwa da kamalla irin Anaal ba.
Kalle ni da tsofan nawa nake zaunawa Anaal ta daura min karatu sa6anin su da kurciyarsu sun k'asa yi a kullum cikin yi musu nasiha take akan su daure su koma islamiyya sai dai su yi mata dariya ko tsaki. Sai anan gaba za su gano amfani nasiha da Anaal take musu.
"Gumi ya tsiyayowa Ansar saboda shi baisan bankad'a na Zuhura har ya yi k'amari haka ba. Haushi da tsanarta suka lullu6e shi ya ma tsani cigaba da zancenta domin zai iya hadasa masa bugawar zuciya hakan ne yasa yakawo karshen zancenta nata ta hanyar cewa........



 Jeeddah Aliyu
[18/04 12:06 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com


*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*9*

Kanta na sunkuye tana wasa da fingers nata ta furta ina littafai ka"?
A maimakon yabata amsa sai kawai ya tsareta da idanu jikinta yabata yana kallonta a tsanake tad'ago eyes nata ta zube su a nashi, kallon-kallon suka shiga yi kasa jure kallonshi nashi ta yi sakamako d'an banzan kwarjini da yai mata ta sadda kai k'asa.
   "Nace ina littafai ka"? tak'ara watsa masa tambaya karo na biyu.
''Ya Shafa gashin kanshi har zuwa ga d'an siririn gemunshi yana kallonta, ta k'asan ido yana murmushi.

''Anaal ta kwa6e fuska tafara magana da zuciyarta wannan karatu ya zo ko kallon mutane"? Ni fa na tsani kallo ya wani kafe ni da idanu ba ko k'intawa. "Ya Ansar please ina littafanka dare yanayi fa"?
Ya d'age giran ido yana kallonta banida su yafad'a kamar mai rad'a.
  ''What's doe's mean"?
Babu ko ke bakisan kalma babu bane"?
  ''Amma kuma ka ce karatu ka zo dauka"?
             ''Yeah!
Kuma bakada littafai"?
       ''Ya gyad'a kai
Kana nufin ba ka shirwaya karatun ba zuwa kawai ka yi"?
                ''Nop
"Tabe baki Anaal ta yi saboda Ansar yafara kaita bango, iya tsawon rayuwarka kata6a ganin wanda yaje gona ba fatanya kuma yace noma ya je yi"?
  "Murmushi ya yi ba sai ya ara a wajen makwacinsa ba, ko ke bakisan mutum zai iya aron abunda bashida shi ba"?
Au.....kana nufi ni ce ma Zan ba ka aron littafi"?
Eh man ko bara ki bani bane"?
  Batare da tabashi amsa ba ta tashi tashiga bedroom d'in Granny ta iske ta kwance tana jan casbaha, tad'auki Jakarta na islamiyya.
   ''Tafice ta zauna mazauninta na tun asali Qur'ani za mu fara ko wane littafi"?
  Ansar yasaki murmushi shi dama qira'arta yakeso yak'ara ji ba wani karatu da ya zo yi, mu fara da Qur'ani.
    ''Daga sama za mu fara ko daga k'asa sai mu yi sama"?
       ''Mu fara daga sama yafad'a cikin zumud'i.
  Taciro Qur'ani daga Jakarta ta mik'a masa  za mu fara daga fatiha.
  Ya gyad'a kai cikin zazzaqar muryarta tafara karanto basmallah kanta na sunkuye tacigaba da karatu har ta kai karshe suratul fatiha.
   ''Tafad'a suratul Baqara a wannan karon Ansar kasa jurewa ya yi saida yad'ago ga mamakinsa sai ga ba Qur'ani a hannunta da kai take rero masa karatun.
 
''Yakoma jikin kujera ya lafe ya zuba mata na mujiya{idanu} tana karatu yana aikin kallonta duk da jikinta yabata ita yake kallo ba Qur'ani ba hakan bai sa tad'ago ta dube shi saida takai dai-dai ayan da yadace ta tsaya sadakallahul azim"! Tafad'a had'e da tad'ago kanta.
   "Mik'o min Qur'ani na.
Kamar daga sama muryarta yadak'i dodon kunnenshi a kasalance ya mik'a mata ta miyar a jakka.
   "Taciro Ahalari me su'al wa jahab ta mik'a masa. Ya kar6a yana jujjuya shi ka bud'e shafi na farko ta umarceshi.
''Ya naga wannan kina nufi da shi zan yi karatu"?
"Kwarai kuwa saboda yafi sauki ganewa.
Toh ai ni nayi wannan.
Humm.....za ka maimaita ne sai naga kamon ludayinka koda zan canza maka wani ka bud'a shafi na farko za mu fara karatu nafara jin baccin.
   "Saida yai murmushi sannan ya bud'e shafin na farko, kamar yanda ta karanta mishi Qur'ani batare da ta duba ba haka tafara karanto mishi wannan.
  Shafi d'aya ta karanta mishi ta dasa aya.
Iya nan za mu tsaya gobe za ka yi mun bitarshi sauran littafai sai gobe zan zo maka da su.
   ''Na gode malama amma kuma sai naga kamar wannan da ki ka fad'a min ya yi kad'an ki k'ara mun mana yak'arasa magana yana wani langwa6e kai.
   ''Girgiza kai ta yi bazan k'ara ba kuma sunana Anaal ba malama sai ka kiyaye.
  "Huh....malama kenan ni fa d'alibinki ne fa ta ya zan dinga fad'ar sunanki kaitsaye ba ko dan sakayawa"? Ai sai ki dinga kallona a matsayin d'alibi marar d'a'a.
  ''Amma kuma ni nace Ka fad'in sunan nawa Dan Allah Ya Ansar karka ce za ka dinga kirana da malama Allah ba zan ji dad'i ba tak'arasa magana kamar za tai kuka, batasan hakan da ta yi ba ta yi masifar burge Ansar ya lumsashe idanunshi yadauki tsawon d'ak'ik'a 2-3 idanunshi a lumshe daga bisani ya bud'e su fasss"! akanta.
    "Kamar me koyon magana yafurta zan yi tunani akai malama tah.
   ''Cuno baki ta yi tana jujjuya kafad'arta alama shagwa6a ba sai gogan naku yasaki baki da hanci ya shagala iya shagaltuwa da kallonta.
  ''Da sauri ta mik'e tsaye ta sunkuce Jakarta sai da safe ka gaida su Nadeeya ko juyawa bata k'ara yi ba tashige d'akin tabarshi zaune.
   "Sai da yadauki tsawon lokacin a zaune kafin ya mik'e yafita yau ma bai nemi Zuhura ba yai tafiyarsa a gate ya tsaya ya yi wa Abbah sai da safe yafice.
   "Cike da nishad'i yake driving yana murmushi har ya iso gida murmushi bai gushe daga kan fuskarshi ba.
   "Yayi parking motarshi a parking lot gani securities birjik da kak'in custom ga kuma blacks cars d'in Daddy a Parke ya tabbatar mishi Daddy ya zo.
   "Ya kai duba ga wrist watch d'in hannunshi 10:15pm yanufi part d'inshi yasan irin wannan lokacin Daddy ya kwanta sai dai da safe koda zai same ganinsa.
   ''Yana rage kayan jikinshi ya fad'a bathroom yasakewa kanshi shower yana fitowa ya tsane jikinshi da towel ya Shafa lotion yasaka pyjamas d'inshi yak'ara gudun Ac ya haye gado ya karaton addu'a kwanciya bacci ba wai don yana jin baccin ba. Kasancewar baccin zai iya d'auke shi "at any time.

       "Ya lumshe idanu muryar Anaal ke yawo a kunnenshi in juya hagu yak'ara juyawa side d'in dama daga karshe yadauki pillow ya jefa a k'irjinshi ya matse shi gam he had a sleepless night duk lokacin da ya yi yunkuri rufe idanu Anaal yake gani yayinda kunnenshi ke jin sautin amon muryarta Yajuya side d'in damansa, Yak'ara zurmawa a tunani ba shi ne yai bacci ba sai around 2:30am.

_"Washe Gari_
_11:00am_

Ansar yafito cikin shirinsa na tafiya office black trouser ne a jikinsa da red colour long sleeve ya tsuke wuyansa da black necktie k'afarsa sanye da cover shoe black in colour jikinsa na fitar da k'amshin turaren "mesmerized Cologne kafad'arshi na rataye da briefcase hannunshi d'aya yana sakad'e cikin aljihun wandonshi, fuskarshi  d'auke da murmushin abin sallarsa sai walk'iya Yake.
    "Shigar ta yi masifar yi masa kyau Ansar irin mazanan ne masu murd'ad'e jiki he's very giants man kallo d'aya za ka yi masa kagano ba duk namiji zai iya karawa da shi ba.
    "Direct parlourn Mum Fatee yanufa tsit parlour yake ba kowa  k'amshin turaren wuta ya gauraye parlourn.
   ''Ya ajiye briefcase da hannun kujera ya nufi staircase ya hango Mum Fatee da Housemaids a kitchen suna had'a breakfast. yafasa haura stairs yanufi kitchen d'in ta baya ya rungume Mum Fatee "Good morning Mum"!
    ''Morning Boy katashi lafiya"?
Am Fine Mum"
That's Good My Boy Daddy yadawo har yai bacci yana tambayarka.

Jiya da nadawo daga gidan Granny naga Prado's d'inshi a parking lot lokacin naga dare ya yi shiyasa ban shigo ba bara naje mu gaisa yajuya yafice da d'an gudunsa ya haura staircase.
  "Controller General Basheer Galadima yana kishingid'e jikinsa sanye da farar Jallabiya da sallama Ansar yashiga parlourn, Daddy oyoyo Ansar yafad'a kamar k'aramin yaro.
    "Controller ya tashi zaune yana murmushi Ya kuma ware hannayenshi Ansar na zuwa yashige k'irjinshi hugging d'in Juna suka yi tightly Boy ya aiki da hak'uri da jama'a hope komai yana tafiya yanda yadace"?
   "Alhamdulillah Daddy ni kaina banta6a tsanmani abubuwan za su daidaita kamar haka ba.
  "That's Great I'm proud of you my Boy dama nasan za ka iya handle d'in company nan ka kuma tafiyar da shi yanda yadace, Allah yai maka albarka.
      "Ameen Daddy.
Ansar yasaki Daddy ya zauna kusa da shi sai doka murmushi yake shi dai duk duniya in kacire Allah da manzonshi ba abunda yakeso sama da iyayyenshi, bashida burin da yawuce ya kyautata musu kasancewar shi kadai suka Haifa d'a namiji gaba d'aya hope d'insu yana kanshi.
  "Gyaran murya controller ya yi alamar zai yi magana mai mahimmancin, kwanaki baya sa'eed ya kirani akan zance aurenka da Zuhura so yake ayi kafin azumi nace yabani lokacin zan yi magana da kai naji naka ra'ayi.
Ansar ya tsince kanshi da fad'uwar gaba ya rikice yashiga in da in da Dad...ddy...azumi fa"? Gaskiya ya yi sauri ni anawa tsari sai Zuhura ta gama karatu zuwa lokacin na kamalla gini na.
   "Murmushi controller ya yi shikenan Boy tunda haka ka za6a inda rai da lafiya kamar gobe ne.
         ''Mum Fatee ta yi sallama tashigo ta dube suna murmushi firar me akeyi shine ba'a jirani ba"?
Controller ne yabata amsa cikin sigar wasa fuskarshi d'auke da murmushi ina ruwanki da ko firar me mu ke yi keda ki ke shigewa d'akin da 'ya'yanki kuna shawara abinku na ta6a tambayarki abunda ku ke tautaunawa akai"?
   "Au.....Daddy tanan ka 6ullo to ae shikenan sai kutashi mu je ku yi breakfast in tayi tsami ma ji.
Ba abunda za ku ji domin wannany firar ta tsakanin d'a da uba ne ko Boy"? Controller yak'arasa magana had'e da kallon Ansar Dariya sosai Ansar ya yi yace haka ne Daddy.
"Zaro ido mum fatee ta yi lallai Boy haka ma za ka fad'a in dai Daddy ne tafiya zai yi yabarni da kai gidanan mu had'e maka kai ni da Girl's d'ina.
  "Ansar yana dariya ya mik'e tsaye ya rik'on hannun Mum Fatee zo mu je Mum zan sanarda ke amma in ku ka had'e min kai ai na Shiga tara.
Controller da Mum suka sa dariya cike da farin ciki suka nufi dining area, Ansar ya ja ma Controller kujera ya zauna sannan shima ya zauna mum Fatee ta yi musu serving.
    "Suna gama taking breakfast Ansar yai sallama da su yanufi office.

_8:00pm_

Kamar yanda jiya Ansar yadira gidan Granny yau ma hakan ce tafaru, saida ya tsaya a main gate wajen Abbah yasha green tea sannan yanufi part d'in Granny a parlour ya iske Granny tana kallon sunnah tv.
   "Bayan sun gaisa suka shiga firar duniya Ansar yana yi yana kallon k'ofar d'akin Granny ko zai ga Anaal tafito.
   Kamar daga sama ya ji muryar Zuhura Granny Ya Ansar ne ya zo naga motarshi a parking lot"?
   "Ta bankad'o curtain tashigo tana gani Ansar tasaki murmushi idonka kenan my love yanzu abunda ka yi min fissibillah"! Kana gani yadace"?ko ba komai na ba ka hak'uri.
Kallon hadarin kaji Ansar yai mata yadaure fuska tamau ya had'e rai.
   "please Ya Ansar I said am sorry ta zube gabanshi tashiga zuba masa magiya.
Ko kallo bata isheshi ba sai ma kauda fuskarsa da ya yi.
Bud'e curtain aka yi had'e da sallama cikin sauri Ansar yajuya ya kalli bakin k'ofa, sanye take da hijab sky blue in colour iya gwiwarta duk da fuskarta ba make-up ta yi masifar yi ma Ansar kyau.
   "Ina wuni Ya Ansar"?
Anaal ta gaida shi
Muryarshi har wani shacking take yi ya amsa da la...fi..ya....malama Anaal ya gida ya karatu"?
Ta rausayar da kanta tace Lafiya qalau Alhamdulillah.
Ta juya cikin tafiyarta a natse tashiga bedroom d'in Granny yayinda Ansar ya rakata da ido saida tabacewa ganinshi sannan yadawo da dubanshi ga Zuhura wance takafe shi da nata idanu...

Jeeddah Aliyu
[18/04 12:06 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
 
    *11*


Anaaal yakira sunanta cikin tautasan lafazi Na'am tafad'a had'e da kallonshi nasan za ki yi mamakin faruwar wasu abubuwa tsakanina da ke, toh ba abin mamaki bane in ki ka yi la'akari da kyakyawar alaqa da ke tsakanina da Abbah.
   ''Ya d'an yi _shiru na kamar _5 seconds_ daga bisani ya nisa yacigaba da cewa banaso ki matsantawa kanki da tunani, ni na d'auke ki kamar K'anwata ta jini duk abunda ki ke da buk'ata kada ki boye min ki d'auke ni matsayin Friend wanda ba za ki iya boye masa duk wata damuwa da ki ke ciki, kamar yanda nima ba zan boye miki halin da nake ciki ba.
   "Anaal ta yishiru tana wasa da gefen hijabinta gaba d'aya kalaman Ya Ansar sun daure mata kai ta ya za'ayi tayi k'awance da namiji ko namiji Ansar Galadima gaskiya abun da wuya wai gurguwa da aure nesa.

     ''Anaal kin yi shiru ba ki bani amsa ba ko bakyaso na zama abokin shawararki"?
Girgiza kai ta yi cikin sanyi murya tafara magana ba haka bane Ya Ansar na yarda da kai 100% saidai ba ka tunani wannan sabuwar alaqa tamu ba zai kawo matsala ba"? Domin ni ina gudu duk wani abu da zai kawo fitina daga gareni.
   "Murmushi ya yi bana tunani faruwa hakan in ma kina jin tsoro me zai hana mu dinga huld'a mu a 6oye"?
Jikin Anaal yadauki rawa da kyar ta iya furta a 6oye kuma"? To wai me yasa za mu dinga 6oye alaqar mu al'hali mu ba wani mugun abu mu ke aikatawa ba''?
Ansar yak'ara dafe steering cikin dabara da wayo yace saboda kina jin tsoro amma ni bayanshi banada wani dalilin kwakwara, amma kuma in kin amince kowa yasan cewa akwai k'awance a tsakaninmu ni a wurina ba matsala bane.

''Da Sauri Anaal tace No! Banaso kowa sani saboda gudun zargi Ansar ya yi murmushi jin dad'i yace shikenan daga yau mu zama friends koh"?
  ''Dariya marar sauti Anaal ta yi tace haka ne.
  Dai-dai Gate d'in Aminu Kano commercial ya aje ta yadube ta a tsanake k'arfe nawa za ku tashi"?
Shiru tayi tak'i fad'a masa da kyar ya shawo kanta ta amince ta fad'a masa.
  ''Kina da waya"? Tambayar da yak'ara watsa mata kenan.
Kamar tace A,a sai kuma ta tuna k'arya ba halinta bane.
  "Ta gyad'a kai phone d'inshi yadauko ya mik'a mata saka mun digit d'inki, hannunta har rawa yakeyi tasa mishi numberta ta mik'a mishi phone d'inshi har tayi yunkuri bud'e k'ofa yakira sunanta can k'asan mak'oshi _Anaaal..._
   "Yanayin yanda yaja sunan nata ya haddasa mata kasala tajuya tana facing nashi _Na'am_ ta amsa had'e da kafe shi da idanu, shima tsareta ya yi da shu'umin kallo da sauri taje kauda fuskarta shima cikin sauri yadakatar da ita No...Anaal karki juya please akwai abunda nake kallo a fuskarki.
   "Narke fuska ta yi kamar za ta yi kuka Ya Ansar zan yi latti fa
Shima kamar zai yi kuka ba za ki yi ba Anaal kallon 10 seconds zan yi miki.
  ''Ten seconds fa Ya Ansar"? Gaskiya ya yi yawa.
    ''Okay five seconds ya yi"?
Eh! Tafad'a had'e da gyad'a kai
Toh ki juyo mana kamar za ta fashe da kuka tajuya tana kallonshi kasa jure shu'umin kallon da yake mata tayi ta runtse idanuta gam yayinda Ansar yasami damar k'are mata kallo wani irin abu yakeji yana masa yawo tun daga d'an yatsar k'afarsa har zuwa tsakiyar kansa.
    "Ya lumshe idanu Jin shiru shi ya yi yawa yasa Anaal ta bud'e nata idanu gani nashi idanu a rufe-ruff, yasa tashiga kallonshi electric shock taji yana janta kamar zai karar da jini jikinta. Jikinta na mazari ta 6alle k'ofa tafita jin karar bud'e k'ofa yasa Ansar ya bud'e idanunshi.
Ta bud'e seat d'in baya tad'auki schoolbag d'inta a kunyace tadafa k'ofar da ke saiti da shi _Na gode Ya Ansar_
A maimakon ya amsa mata sai kawai ya wanketa da murmushi yaciro k'udi ya mik'a mata _ga wannan ki yi breakfast_
  ''Mak'e kafad'arta ta yi Uhm..... Uhm...kabarshi kawai Granny tabani two hundred kuma Abbah yabani na transport sun wadace ni.
   ''Ya galla mata harara k'udin Granny da Abbah daban wannan nawa ne ko kina nufi banida matsayin da zan miki kyauta ki kar6a''?
Batare da tace komai ba tasa hannu biyu ta kar6a had'e da cewa na gode Allah yasaka da alkhairi amma gaskiya sunyi min yawa bara iya kashe su ni kadai ba.
   "Tabe baki ya yi cikin gatse yace ki kashe rabi ki jefar da rabi.
  "Anaal ta zaro ido har da su dafe k'irji k'udi ne zan jefar"?
''Eh! Man yafad'a cikin rashin damuwa.
   Humm....tasauke numfashi ni kan bara iya jefar da k'udi ba.
Ansar ya yi murmushi yace toh ki je ki kashe su duka tunda ba za ki iya jefarwa ba.
 tajuya jiki a mace tanufi Cikin makaranta Ansar ya bita da kallo yana Shafa gejere gemunsa sai da ta6acewa ganisa sannan yaja mota yanufi gida.

_10:33am_

Ansar yafito cikin shirin shi na tafiya "office jikinsa sanye da ash colour suit da blue colour long sleeve, kaitsaye part d'in Mum Fatee yanufa ya yi taking breakfast sannan yanufi office.
_11:30am_ yashiga conference hall tsawon lokacin suka dauka a meeting d'in agajiye yafito daga hall yanufi office d'inshi Ishaq na biye da shi dauke da files.
   "Yana shiga office yacire coat yanemi sofa ya zauna ya dube ishaq yace ishaq yunwa nakeji ka je ka yi min order abincin me kyau.
   ''Okay Boss Ishaq yafad'a had'e da ficewa wannan ya ba Ansar damar afkawa tunanin Anaal baisan dalilin da yasa yarinyar take burgeshi ba yake jin kamar in yana tare da ita kada su rabo
   ''Komai na Anaal ya yi mishi musanman kyawawan d'abi'unta ina ma ace Zuhura ita ce Anaal ba shakka da na kasance me Sa'a a rayuwa.
   "Yanda ishaq yafita yabar Ansar cikin tunani haka yadawo ya tarar da shi yana cikin cin abincin idanunshi suka kai duba ga wall clock da ke manne a bango Office d'in nashi.
 ''Ba shiri ya yi dropping spoon ya mik'e tsaye ya kwashe phone's d'inshi had'e da car key yanufi k'ofar fita jikinsa ko ina rawa yafita a bakin k'ofa yaci karo da ishaq maigida Ansar ina zuwa haka''?
    "Fitan gaggawa ne yakamani ishaq ba zan jima ba zan dawo ka je office d'ina akwai Documents a locker ka dauka ka kai office d'in Abdallah, kace naje ya had'e su da wanda na bashi jiya yana magana ne had'e da tafiya Ishaq yana biye da shi har parking lot. Saida ya ja mota sannan Ishaq yakoma ciki domin aiwatar da abinda maigida Ansar yasaka shi.

"Kaitsaye Aminu Kano commercial Ansar yadosa dai-dai wajen da ya ajiye ta anan ya yi parking yashiga rarraba idanu yana kallon students d'in ke wucewa, ko zai yi nasara ganinta saida yashare 10 minutes har students sun fara raguwa sosai har yafitar da ran ganinta sai gata tafito ita da 'yan d'alibai uwanta su biyu itace cikon ta 3 sun jero ita ce a tsakiya sai faman fira suke murmushi kwance akan fuskarta.
     "Ansar yasauke ajiyar zuciya yayinda numfashinsa yadinga hal6awa da sauri bai ankara ba har suka wuce shi a rikice yasauke glass d'in mota _ke Anaal_ ta tsaya cak kamar me amfani da remote control ko a mafalki za ta sheda wannan muryar, ta dubi k'awayenta Ramlah da zeenat cikin sanyi murya tace yaya na ya zo daukana sai anjimanku.
   ''Zeenat ta yi karaf ta shar6e zance dama kina da yaya shine ba ki ta6a gayamana ba"?
Kafin Anaal tabata amsa Ramlah tarigata ta hanyar cewa zeenat kenan kamar bakisan halin Anaal na zurfin ciki ba ae ba za ta gayamana ba kada mu yi mata snatched d'in yayan nata.
Oops......Anaal tadafe goshi abin ya zame mata biyu ga Ya Ansar yana dankara mata horn ga wad'annan fitinanu k'awaye nata biyu sun saka ta a gaba.
    "Tarausayar da kai kunga Ya yana min horn ku jira gobe in muka had'u ku tuhume ni yanzu dai ku barni na tafi kada ya yi min fad'a.
Zeenat ta tabe baki kyaji da shi domin ni ban yarda wannan guy kuna da blood relationship da shi ba.
 ke da ki ka ce yayanki ya6ata tun kina jinjira shine don kin raina mana hankali za ki ce wannan yayanki ne. Ramlah ta kar6e zance ta hanyar cewa watakil boyfriend d'inki ne bakyason mu sani.
Zaro ido Anaal tayi Ya Ansar ne boyfriend d'ina kanki d'aya kuwa Ramlah"?
   ''Rass nake Ramlah tafad'a tana wani rangwadar da kai cike da takaici Anaal ta galla mata harara daga bisani ta ja tsaki mtcsww"! Batare da tayi sallama da k'awaye nata ba tanufi motar Ansar ta bud'e seat d'in baya tasaka schoolbag d'inta kamar yanda tayi da safe.
   ''Ranta a 6ace ta balle k'ofa tashiga Ansar yana waya yajuyo ya dube ta yasake mata shu'umin murmushinsa mai tafiya da imani da zuciyar 'ya mace. Tsigar jikinta yatashi Yarr...ta kauda fuska Ansar ya ja mota suka tafi hannunshi guda yana dafe da steering d'ayan kuma dafe da waya yana kamalla waya yak'ara juyowa yana kallonta. daure fuska tayi dan Allah Ya Ansar ka kalli gabanka kada garin wannan kallon naka ka 6arar da mu.
   ''Dariya ya yi cike da nishad'i yace Anaal sarkin tsoro wai meke damunki ne naga kin wani daure fuska kina kunbure-kunbure''?
Cuno baki tayi kamar za ta yi kuka tace ba su Ramlah bane suka ce wai....wai...kai...uhm... Uhm... Manta kawai.
6ata fuska ya yi miye haka za ki fara gayamun magana kuma ki ce na manta''?
Ya Ansar maganar batada ma'ana balle tushe miye amfani jinta"?
   ''A gareki zai yu batada amfani amma ni a wurina tafi komai amfani gayamin me su Ramlah suka ce''?
  "Ni fa ba zan fad'a ba gara ka hak'ura kawai tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
Shikenan Anaal tunda ba za ki fad'a ba amma kisani hak'ik'a kin jefa zuciyata cikin kwankwato, har nake tunani ko ba ki yarda da ni bane kina mini wani kallo na daban wanda Allah kadai yasan abinda ya ke nufi.
   "Cikin rauni murya Anaal tace kada ka fassara ni bai-bai ya Ansar, har ga Allah na yarda da kai na tabbata ba za ka iya cutar da ni ba.
  ''In har kinsan da haka meyasa ki kasa gayamin abunda k'awayenki suka fad'a
Anaal ko kina tsoro abunda suka fad'a ya zama gaskiya"?
Wani irin mashi yadak'i zuciyar Anaal ya haddasa mata matsanancin fad'uwar gaba a rikice ta yada ganinta akan kyakyawar fuskarsa, muryarta na rawa tace Ya Ansar kana nufi kaji abunda Ramlah tafad'a"?

     "K'ayatatcen murmushi ya yi Anaal kenan Sanin kanki ne ni ba kurma bane ta ya ki ke kwankwanto akan naji abunda Ramlah tafad'a"? Ba kwakwanto nake ba Ya Ansar ina mamaki ne ta yanda kunnenka ya ji alhali kana nesa da mu
      ''Kidaina mamaki domin wannan ba abin mamaki bane.
  Humm....Anaal tafad'a had'e da rafka tagumi
  Ansar ya kalle ta ganin yanda yanayinta ya nuna yasa yafara lullu6e ta, da dadd'ad'a kalamansa  ta hanyar cewa Anaal karki sakawa kanki damuwa domin kowane dan-adam da kaddarar da Allah, ya yi nufi akansa kuma bai isa ya kauce mata ba kinganni nan nayi imani da kaddara me kyau da marar kyau domin shine cikar imanina, karkace za ki tsawaitawa zuciyarki domin ita zuciya ba kowane abu take juriyar dauka ba saidai ina gargad'inki kada ki kasance me tauyewa zuciyarki hakkin ta.
  "Gaba d'aya Anaal tashiga sark'ak'iya tarasa gane ina wad'annan kalaman na Ya Ansar suka dosa ba, rashin sani ma'anarsu yasa ta kauda fuskarta da barin kallonshi.
   ''Shima bai k'ara cewa da ita uffan ba sai ma k'ara volume d'in tape da ya tun kafin yak'arasa gida Anaal tace ka tsaya zan sauka anan.
   ''Batare da yace komai ba ya taka birki har ta rik'e k'ofa za ta bud'e ya kira sunanta{in a romantic voice} _Anaaal_ a kasalance ta amsa da _na'am_
kin wani bani baya Ki juyo ki kalle ni mana.
Shiru tayi kamar ba za ta juyo ba daga bisani tajuyo suna had'a ido yasake mata shegen murmushi nan nashi.
   "Yace ubangiji shi yake tsarawa 'yan Adam rayuwa komai yasame ki ki kasance me tawakali da godiya ga Allah{S.W.T} wannan shawara ce nake ba ki a matsayina na amininki kuma yayanki.
   _"na gode_ tafad'a asanyaye ta bud'e k'ofa tafita tadauko schoolbag d'inta daga seat d'in baya, batare da tak'ara tanka masa ba tajuya tanufi gida.
    ''Yayinda Ansar ya bita da kallo rass"! rass"! Gabanshi ya yanke yafad'i ba ko tantanma Anaal ita ce yarinyar nan Mae niqan  yanayin tafiyarsu d'aya yasauke ajiyar zuciya had'e da shafar sajenshi saida ya tabbata Anaal ta isa gida sannan yaja mota yanufi gidan....

Jeeddah Aliyu
[18/04 12:06 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
 
  *12*

Horn ya yi Abbah ya bud'e masa gate Bayan ya yi parking yanufi bakin gate wurin Abbah. Yana k'arasawa Abbah ya bashi hannu suka yi musabaha Ansar yadauki buta Abbah ta ruwa yanufi bathroom d'in Abbah da ke gateman room Yakama ruwa, ya yi alwala tare da Abbah suka nufi masallacin.
    ''Bayan sun dawo daga masallacin Ansar ya yi sallama da Abbah ya ja motarsa yakoma office _5 dot_ yabaro office yanufi gida direct part d'inshi yafara yada zango ya yi wanka ya shirya cikin blue Jean's da yellow t-shirt Mae gajeran hannu ya feshe jikinsa da Elite gentleman Parfume ya had'a da favorite Parfume d'inshi mesmerized Cologne wani irin k'amshi na musanman yake fita daga jikinsa. Car key had'e da phones d'inshi yadauka yanufi part d'in Mum Fatee.
 
       "A parlour iske Basmah tasha kwalliya cikin Arabian gown ya ji adon Stone's sai fama kashe selfie take, tsaye ya yi yana kallonta ya girgiza kai yanemi kujera ya zauna har ya kai zaune Basmah batasan ya shigo ba sha'anin gabanta kawai take.
    "Tsawa Ansar yadaka mata ke"! Mahaukaciya.
"A tsorace Basmah tajuya tana kallonshi OMG"! You scared me Ya Ansar tafad'a a shagwa6e. Harara ya galla mata Wai yaushe za ki yi hankali Basmah"?
   "Ni fa da hankalina Ya Ansar.
  Ina ki ga hankali Basmah ba hali ki yi wanka sai kin wahalarda camera wayanki, ke ba wani kyau ba sai dan banza d'aukar pic's dama ku munana kun fi kowa son pic's.
   "Basmah ta langwa6e kai tafara bubbuga kafa a rugs carpet "Allah Ya Ansar ina da kyau friends d'ina har cewa suke ina kama da kai.
   ''Zaro ido ya yi kamar ya ga abin tsoro wa ki ke kama da shi"?
  "Kai tafad'a had'e da nuna shi da yatsa.
   "You're completely mad Basmah kalle kanki lukuta da ke za ki wani had'a kanki da ni God forbid.
   "Basmah kamar za ta yi kuka tace ni wallahi slimming zan yi nadawo kamar wannan ta rik'e baki tana tunani wa ma za ta ce kamar daga sama tace _Anaal_ saboda ina son body structures nata.
Ansar ya tsincin kanshi da fad'uwar gaba sakamako sunan Anaal da Basmah ta kira.
   ''Basmah tana dariya tak'araso kusa da shi Ya Ansar bari na kashe mana selfie guda da kai, na daura akan dp na kafin yabata amsa har ta kashe musu guda biyu tureta ya yi ke dallah banaso shirme ki je ki had'a min abincin yunwa nakeji.
  "Basmah ta mik'a masa phone d'inta fuskarta d'auke da dariya tace Ya Ansar duba ka gani yanda mu ka yi kyau kace wai ba ma kama hancin kawai za ka gwada min sai girman jiki da na fi ka Allah ba don wannan ba da kamanu mu sak d'aya.
   ''Fizge phone d'in ya yi naji sarkin sharhi ki je ki yi abunda nasaka ki.
  ''Tajuya tana mai cigaba da cewa yau Mum da kanta tahad'a maka favorite d'inka.
  "Da sauri Ansar yace com slow"?
 ''Eh Basmah tafad'a had'e da shigewa corridor da zai sadata da kitchen. Cikin d'aga murya Ansar yace shi kadai za ki zuba mun karki saka shinkafa.
  "Toh ita ma ta amsa cikin d'aga murya.

     "Da sauri Ansar yake scrolling pic's d'in mtcsww"! Ya ja tsaki had'e da ajiye wayan a hannun kujera, yadauki nashi ya yi dialling digit d'in Anaal wayarta a rufe mtcsww"! Yak'ara zuba tsaki.
   "Basmah tashigo d'auke da plate tajanyo k'aramin center table ta daura plate d'in akai tak'ara komawa kitchen ta dauko mishi drinks da ruwa.
   ''Yana cin had'in salad d'in yana lumshe ido saida ya cinye tass ya ture plate ruwa kawai ya sha yaciro chewing gum mai k'amshin strawberry daga pocket d'inshi ya 6are ya jefa baki.
   "Basmah ta mik'a mishi hannu nima zan cin Ya Ansar.
Me za ki ci mayya"?
Tana dariya ta furta chewing gum.
Ciro d'aya ya yi ya jefa mata ta cafke.

    Yakoma jikin kujera yalafe idanunshi a lumshe ya furta Basmah me ki ka sani game da Anaal"?
Da mugun mamaki baki bud'e Basmah take kallonshi takasa furta komai sai kallonshi take yi. Shi kuma sai tauna chewing gum d'inshi yake yi hankali kwance.
      "Ajiye zuciya Basmah ta yi ta mik'e daga mazauninta ta koma kusa da shi ta zauna bisa hannun kujerar da ya ke zaune.
   "Ya Ansar wannan tambayar naka ya sakani cikin rud'ani akwai wata alaqa ne tsakaninka da Anaal"? Banaso zuciyata tafara kintsa mini abinda ba shi bane ma'ana zargi.
    "Yad'ago ya dube ta a d'age ki fara amsa mini tambaya na firstly in yaso daga baya kya iya naki tambaya.
 "Langwa6e kai Basmah ta yi _Anaal yarinya ce Mae hankali da natsuwa tana da tsananin hak'uri, sai dai miskila ce tabugawa a jarida ba abinda yafi burgeni da Anaal irin iliminta ba irin bin Anaal da banyi ba akan mu qula k'awance amma tak'i sai dinga fuskewa kamar dae banyi mata ba duk da wannan har yanzu ina k'aunarta_ tak'arasa magana kamar za ta yi kuka.
  Tun lokacin da Basmah tafara magana Ansar yake zabga murmushi, hannun Basmah yarik'o don't worry 'yar lukuta zan had'a ki k'awance da Anaal kinsan duk gidanan tamu tafi zu wa d'aya duk abinda nakeso kema kinasonshi koh"?
   "Basmah ta yi dariya tak'ara dank'e hannunshi can kasan makoshi ta furta Ya Ansar do you love her''?
Zaro ido ya yi who"?
Anaal mana tafad'a tana kallon kwayar idonshi.
  Tabe baki ya yi had'e da girgiza kai capital No we are just a friends.
"Sauke ajiyar zuciya Basmah ta yi thank God da har zuciyana yafara saqa mini, irin k'alubali da za ka fuskanta daga wajen Dad da Mum.

"Ansar ya mik'e tsaye karki damu k'anwata insha'Allah ba abinda zai Shiga tsakanina da Anaal ko kin manta da irin d'inbin son da nake wa Zuhura''?
Ban manta ba Ya Ansar amma kuma zuciya tana canza sheqa daga nan ta koma nan.
  "Ban da tawa zuciya domin Zuhura takeso ita kadai na d'auki Anaal ne tamkar ke.
Murmushi Basmah ta yi tace ni dae yanzu yaushe za ka had'a mu k'awance''?
   ''Tabe baki ya yi ke fa kin fiye gaggawa.
Har Basmah tabude baki za ta yi magana ya katse ta sai na dawo Basmah karki 6ata min lokacin da wannan surutun naki yasa kai yafita Basmah tabishi da kallonshi.
   "Yana fita bai zarce a ko ina ba sai inda yasa6a jiran wucewar Mae niqan, so yake ya gasganta zarginsa shin Anaal ce ko ba ita ce ba.
   ''Cikin Sa'a bai fi _5 minutes_ da zama ba sai gata ta ta tsallako titi yau ita kadai ce,  da sauri ya 6alle k'ofa yafito Anaal naganinshi tadauke kai kamar bata ganeshi ba ta ra6a shi za ta wuce cikin sark'ewar lafazi Ansar ya Kira sunanta Anaal''!
  "Ta tsaya cak da saurinsa ya k'arasa kusa da Ita Anaal shine za ki wuce ni ba ko gaisuwa ko kina tsanmani don kin rufe fuskarki da niqan ba zan gane ki ba''?

   "Dariya ta yi Mae  sautin ka yi hak'uri Ya Ansar ban yi zaton za ka ganeni ba. Naga cewa nasha wuce ka amma ba ka ta6a nuna kasan ni ba.
  Shima dariya ya yi ba gashi yau na nuna nasanki ba.
  ''Tafiya tacigaba da yi zan wuce gida naji anfara kiran sallah magarib.
  "Okay....Ni ma da nayi sallah zan shigo ki ce da Granny ta aje min Mae dad'i.
Ba wani Mae dad'i da za ta aje ma kadai sai kashigo.

_8:30pm_

''Ansar yana zaune a parlourn Granny suna fira Anaal ta yi sallama tashigo sanye da hijab har k'asa pink in colour.
   Tanemi kusa da Granny ta zauna ta k'asan idon ta kalli Ansar batasan cewa shima tun shigowarta yake aikin kallonta ba.
  "D'ago idanunta tayi gaba d'aya ta dube shi yau za mu yi karatu ne''?
 A maimakon ya6ata amsa sai ya kafeta da idanu d'auke fuskarta ta yi ta mayarda ganinta wajen Granny tace Granny na dauko maganinki na Shafa miki tun yanzu?
    "Girgiza kai Granny ta yi kije ku yi karatunku anjima ki Shafa min Anaal ta mik'e tashiga bedroom tadauka jakkar littafai.
Tana cikin karatu sai ga Zuhura tafad'o parlourn kamar wance aka jefo. Da mugun mamaki take kallonsu Ya Ansar shine za ko gidanan ko kanemi ni"? Narasa me ke damunka a 'yan kwanaki nan ka ke share ni.
Shhh......Ansar ya aza yatsanshi a lips alamar tayi shiru amma ita gimbiyar ko a jikinta sai ma k'ara kaimi ta yi wane irin shhh..."? Toh wallahi ba zan yi shiru ba har sai naji, dalilinka na shirya mini wannan wulaqancin.

_"Sadakallahu-azeem_ Anaal ta dasa aya kada ta kwasawa kanta zunubi, saboda in ana karatun Qur'anic ba'a surutu. Ta mik'e tsanm tanufi bedroom Zuhura ta bi ta da kallon tuhuma.
K'atuwar harara Ansar ya gallawa Zuhura wannan wane irin dabancin ne? Ya ana karanta Qur'ani za ki zo ki cika mutane da surutunki na banza da wofi?
''Idanu Zuhura ta zaro Ya Ansar ni ka ke kira da suna dabba? don kawai na nuna damuwata akanka?
          ''Eh! Na fad'a ke dabbace domin abunda ki ka aikata dabba ne kadai zai aikata shi.
Shikenan Ya Ansar naji ni dabbace amma inason kasani komai wuya komai runtse kana nan tare da dabba, ba uban da isa yaraba ka da ita mutum zai gaji da tsohun munafuncinsa da zugaka yabari domin ni da kai mutu karaba ne takalmin kaza.
  "Rai 6ace Ansar ya mik'e har yaware hannu zai wanka mata mari, Granny ta taka masa birki kai Ansar kul karka daketa duk wad'annan zafafan maganganu da take fad'a ba da kowa take ba illah ni. Kabarta kawai abinda ta girma tayi wayo tarrarda da uwarta saude tana min kenan.
Amma Granny haka zan cigaba da zuba mata ido tana gasa min magana iya son ranta haka za mu yi aure bata gani girma na?
Hak'uri za ka yi Ansaru domin kace ka ji ka gani kana sonta, rashin mutumcin da bankad'a ba ka ma ga komai ba sai ranarda igiyar aure ta gita a tsakaninku.

Mtcsww"! Zuhura ta ja dogon tsaki kamar za ta gutsere halshenta, tajuya fuuu.....tana wani jujjuya mazauna ita a dole ga shak'iyiya.
Ansar yana huci yakoma ya zauna yayinda Granny tacigaba da rarrashinsa da kalamai masu kwantarda hankali sai around _10:30pm_ ya yi sallama da Granny yawuce gida har yatafi bai k'ara gani Anaal ba.

_washe Gari_

Ba zato ba tsanmani Anaal taci kora da Ansar yana zaman jiranta zai kaita school.
Jiki ba lakka ta bud'e k'ofar mota tashiga kallon d'aya ta yi mishi taga damuwa shinfid'e akan fuskarsa.
   Cikin sanyayiyar muryarta tace _ina kwana Ya Ansar_
Lafiya Anaal yau kin kusa ki yi latti.
Wallahi kuwa yau bacci nayi sosai da kyar Granny ta tashe ni.
Ansar ya kad'a kai kin more 'yan mata ni jiya ko runtsewa ban yi ba yanda naga rana haka naga dare.....

Jeeddah Aliyu
[18/04 12:06 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

13

Cikin yanayin na tausayi Anaal tajuyo tana kallonshi Ya Ansar bai kamata kadauki abunda yaya Zuhura tayi da zafi ba. Har ya yi sanadin hanaka bacci nata halaya ne haka dole sai kana hak'uri had'e da lurarda ita.
  ''Haba Anaal zuhura k'aramar yarinya ce da zan dinga tsara mata yanda za ta gudanarda rayuwarta?
Ba k'aramar yarinya bace amma kafita hankali da tunani matuk'ar tana sonka toh dole ta bi abinda ka ke so.
  Anaal kenan lallai har yanzu ba ki San wacece Zuhura ba. In kina neman mace 'yar raini wayo marar tarbiyya, fitsarariya ki ka kawo ga Zuhura sai ki Shafa fatiha. Kina ji fa Granny ta kira da munafuka yak'arasa magana cike da takaici.

   ''Naji Ya Ansar anan Zuhura ta yi kuskure amma kamar yanda ka ji Granny tace, daga wajen mahaifiyarta ta koya domin ita ma ba ragawa Granny ta ke yi ba.
   ''Mtcsww! Ansar ya ja tsaki Allah ya kyauta dukansu ba laifinsu bane Baba sa'eed ne mai laifi shi da ya zuba musu ido suna wulaqanta mishi mahaifiya.
  Nima abinda nake fad'a kenan a zuciyata. A shekaru Granny bai kamata ace tana fuskantar irin wannan cin zarafi ba.
Bari kawai Anaal Granny na zaman hak'uri dad'inta bata bari ta kwana balle ta tashi da yanzu, sun mayarda ita juji.

   ''Dariya Anaal ta yi ae Granny batada sauki muddin tsautsayi yasa kata6o ta za ka ji ba dad'i. Ni dai shawarar da zan ba ka kacigaba da hak'uri da Zuhura dama haka auren zumuncin ya gada. Ni shiyasa bai ta6a bani sha'awa ba, Saboda in zama bai yi dad'i ba nan take yake 6ata zumuncin.
6ata fuska Ansar ya yi ba wani hak'uri da zan yi zan nemawa kaina mafita ae ba aurenta nakeyi ba ballatana nai hak'uri infact ba ita kadai bace 'ya mace da zan dinga shanye wulaqancinta.
Zaro ido Anaal ta yi kai Ya Ansar banaso cika baki duk son da ka ke yi ma Zuhura za ka iya barita akan d'an k'ank'ani abu?
Harara ya galla mata zan tabbatar miki ba cika baki nakeyi ba, muddin Zuhura bata sauya munana d'abi'unta ba ni kuma ba abinda zai hanani sauyawa. Yana k'arasa magana dai-dai yakawo gate d'in makaratansu ya yi parking.

Tajuya fuskarta d'auke da k'ayatatcen murmushi _thanks_ tafad'a had'e da langwabe kai.
   ''Ya mayar mata da Martani murmushinta _you're welcome Dear_
Tadauki Schoolbag d'inta yaciro k'udi ya mik'a mata mak'e hannu ta yi, ya murtuk'e fuska ki kar6a mana.
 Ko na jiya ya Ansar da kabani suna cikin schoolbag ban kashe ko kwadala a ciki ba.
Wannan kuma ke ya Shafa ki kar6a tun kafin raina ya 6aci. Girgiza kai tashiga yi kamar mai shirin yi kuka Ya Ansar Allah ba abinda zan y.....katse ta ya yi ta hanyar d'aga mata hannu ya balle k'ofa yafito ya ja schoolbag d'inta da k'arfi dole tasakarsa masa ya zuge zip yasaka k'udin a cikin ya mik'a mata tak'i kar6a ya ajiye a k'asa yashiga mota yaja yabarta tsaye tana mamakin wannan k'arfin halin nashi.
Lokacin tashinsu school ya yi tana fitowa gate taci karo da shi bata yi mamaki ganin nashi ba. Saboda taji a jikinta zai zo.
  ''Tun daga lokacin Ansar ya mayarda kanshi driven Anaal shi yake dropping nata school ya kuma yi picking nata shaquwa mai ban mamaki tashiga tsakaninsu.

   "Ansar bai zai iya yini d'aya cur batare da yaga Anaal ba. kamar yanda ita ma in bataganshi ba batada kwanciyar hankali har sai ta kira shi a waya taji muryarshi sannan take samun natsuwa. dukansu a tunaninsu shaquwa da amintaka ce take hadasa musu hakan.
 
_8:05pm_

Ansar yadano hancin motarshi a farfajiyar gidan Baba sa'eed yanufi parking lot ya yi parking. Yanayi na wanda ya kwaso gajiya yafito daga mota yana rataye da briefcase da tarin file's a hannunshi saida yanufi main gate ya gaida Abbah sannan yanufi part d'in Granny.
Da sallama yashiga parlourn Anaal kadai ya tarar zaune tana Assignment Granny na bedroom tad'ago can k'asan mak'oshi ta amsa masa sallama, suna had'a Ido ta balla masa harara had'e da murgud'a baki ta maida dubanta ga Assignment d'in da takeyi.
    "Sanyaye Murmushi Ansar ya yi yanufi wajenta hannayenshi na zube cikin aljihu wandonshi. Ya yi tsaye a gabanta yana kallonta k'asa-k'asa yana shu'umin murmushi nan nashi.
   ''K'amshin turare shi ya baibaye k'ofufin hancinta kasala had'e da wani irin sanyi Mae ratsa k'asusuwan jiki yasauka mata.
  _Anaaal_
Yakira sunanta kamar Mae ciwon hak'ora.
_Na'am_
Ta amsa had'e da d'agowa suka sake had'a idanu ta cuno baki tana gunguni.
Wai laifin me nayi da Anaal take ta murgud'a min baki?
Cike da zallan mamaki take kallonshi au baka masan laifin da kayi ba?
  "Saida ya zauna a kujera da ke facing nata yace of course yes! Kema kinsan da nasan laifin da nayi da tuni na fara ba da hak'uri.
   ''Humm! Jiya me hanaka  zuwa gidanan?
Ko kasan na kira all digit naka switch off?

  Murmushi ya subuce masa yashiga shafar laulausan sumar kanshi yana lumsashe idanu.
   ''Lallai Anaal kinfara damuwa da ni ada na dauka ni kadai ne nasan mahimmancin ki.
  Tabe baki tayi cikin rashin damuwa da furucin nashi tace karka damu wannan, yana d'aya daga cikin halayena duk dalibin da nake koyarwa in banganshi ba nakan nuna kulawa ta akai.
   ''Ta6e baki ya yi baisan lokacin da ya ja siririn tsaki ba. Daga haka ba wanda yak'ara tankawa d'an uwansa ita tacigaba da Assignment d'inta yayinda shi kuma yacigaba da aikin kallonta.
  Phone d'inshi ya yi ringing a wulaqance yake kallon wayan mtcsww"! Ya ja tsaki har kiran ya tsinke bai yi picking ba. Batare da mai kiran nashi yagaji ba yak'ara calling nashi back still ignoring call d'in ya yi.
  ''Anaal tad'ago ta dubeshi wulaqancin ba kyau Ya Ansar ka daure ka amsa kiran maybe, alkhairi ne yake binka kana gudunsa tak'arasa magana tana dariya. Ya tabe baki wannan kiran banajin akwai alkhairi a cikinsa tunda kin ce nayi picking, zan yi saboda ke. Kinsan ni d'alibi ne nagari bana tsallake umarnin malama tah.

O'o....ka ji da shi. Tafad'a had'e da cigaba da rubutunta.
Me zan ji da shi 'yan mata"?
D'agowa tayi ta jefa Biro a baki tana kallonshi fuskarta d'auke da murmushi, lallai nayi k'oshin d'alibi ina matsayin malamarka ka kirani 'yan mata.
  To miye a ciki don na kira ki da 'yan mata ae ke ba 'yan maza bace? Ashe kuwa in haka ne magana na yana kan hanya.
  Please ka d'auki wayanka kada Mae kira yaji zafi ignoring nashi da kayi.
Kafin ya yi magana kiran ya sake shigowa afusace ya yi picking _Zuhura_ yafad'a da kaukausar murya ya yi shiru yana sauraron abinda take fad'a mtcsww"! Ya zuba tsaki don kinga mota na a picking lot saime kina bi na bashi ne"?
Oh" nayi tsanmani kina bina bashi ne da za ki dameni da kira.

Mtcsww! Look Zuhura karki nemi ki takurawa rayuwata ki barni na huta mana. Ya yi shiru yana sauraronta hmmm! wannan kuka da ki ke yi ko a jikina domin nasan na munafuncin ne. Sai kin kwance min zariyan wando a kasuwa kidawo gida ki daura mun am tired I'm completely tired of your stupidity so let's me be....
Anaal da takasa kunne tana sauraron Ansar batasan lokacin da kyalkyace da dariya ba.
Kasa cigaba da magana ya yi yana kallonta da mugun mamaki, dariya take yi har da su dafe ciki. Gani haka yasa yace da Zuhura shikenan naji.
Na hak'ura mana yafad'a yana mushirikin murmushi.
No....ki yi zamanki karatu Anaal za ta fad'a min karki damu in nagama zan nemi ki.
I love you more.
Ya yi hanging up ya maida ganinshi wajen Anaal wance ke kwasan dariya abinta ya talafe kumatu yana kallonta ganin yanda ya shagala da kallonta, yasa ta katse dariya da takeyi ta rufe bakinta da tafin hannu.

''Gyaran murya ya yi me ki ke yi wa dariya Anaal?
Shiru tayi kamar bataji tambaya da ya yi mata ba.
Yakira sunanta cikin laushin murya kamar Mae rad'a.
_Anaal_
Ta amsa da
_Na'am_
Nace me ki ke yi ma dariya?
A maimakon ta bashi amsa sai tasa dariya cikin muryar dariya, tace maganarka ce tabani dariya iya jina banta6a jin ance a kwance zariyan wando saidai ace zani.
Humm......toh ae ni bana daura zani wando nake sakawa kinga kenan ba zanyi zaurance da zani ba.

 mik'ewa tsaye ta yi ta dube shi kallon ido cikin ido tace duk da haka zani ake cewa.
Murmushi yasake mata naji malama tah next time zance zanin Anaal cos na gayamiki bana daura zani.
Turo baki tayi tajuya har tayi tako d'aya zuwa biyu ya dakatarda ita ta hanyar cewa wai ke ina za ki je naga sai wani rawan k'afa ki ke yi?
Jakka zan dauko mu yi karatu tafad'a had'e da kallonshi.
Ki dawo ki zauna yau ba zan yi karatu ba.
Saboda me?
Saboda yau alhamis a tsarin kowane makaranta islamiyya ana hutu, nima yau hutawa zan.
     ''Zaro ido ta yi yanzu a waya naji kana gayawa yaya Zuhura karatu za ka yi, shine za ka sauya ra'ayi da wuri haka?

  "A waya nace zan yi karatu a zahiri kuma nace ba zan yi ba, gara kidawo ki zauna ki cigaba da assignment d'inki zai fi miki sauki da wannan tsayuwar da ki ke yi.
  ''Tana gunguni tadawo ta zauna a mazauninta Yayinda Ansar yafito da laptop d'inshi yasoma shigar da bayanai da ke cikin  file's.
Annal tad'ago tana kallon yanda yake operating laptop d'in a yangance ta, ta6e baki had'e da yatsine fuska. Kamar ance Ansar yad'ago yaga tana kallonshi tana yatsina ya akayi ne 'yan mata naga kina mun kallon burgewa? yak'arasa magana yana kashe ido d'aya.
Murmushi tayi wanda yak'ara k'awata ainihin kyaun fuskarta, kallon tausayawa nake maka ba na burgewa ba kalli yanda ka ke operating laptop kamar wanda bashida lakka kai komai sai ka sa yanga ko ni sa nake Mace nafika kama jiki idan, haka ka ke yi a office duk ranarda  Dad yakamaka zai yi suspended naka ko ya yi firing naka gaba d'aya.
  "Tun lokacin tafara magana Ansar yake kallonta yana zuba murmushi. Shi dai komai Anaal take yi burgeshi yake yi musanman in tana magana jin yake kamar yana yawo a gajimare saboda tsananin dad'i da gard'i da muryarta take masa.
  ''Mik'ewa ya yi yanufi wajenta yadaura mata laptop a cinya ya tattaro tarin file's d'in ya aza a hannun kujerar da take kai.


Jeeddah Aliyu
[18/04 12:06 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

15

Da yake gilasai motar tinted ne ita bata ganinshi amma shi yana ganinta. Kamar yanda take murmushi shima murmushi yake har yafi nata, tana Isa ta bud'e k'ofa tashiga had'e da sallama sautin wakar Indian ne ya amsa mata ta kai duba wajen Ansar sai faman kad'a kai yake yana bin wakar sai kace tare da shi akayi ta.
Tayi dariya o'o su Indian boy ko sallama Ba'a amsawa?

Yayi dariya yarage volume ya dube ta yi hak'uri my Lucky duk lokacin da nake sauraron wak'ar nan ni kadai nasan halin da nake shiga.
Hmm,,,ta tabe baki kana jin abinda suke fad'a ne?
Bai bata amsa ba sai kawai ya ja mota.
Cike da nishad'i ya dube ta yace
_inasonki  tamkar bugun numfashina a duk lokacin da na rufe idanuna kyakyawar fuskarki nake gani. Banida buri da yawuce naji ki kwance akan k'irjina, nafara sonki tun daga ranar da idanuna suka fara tozali da ke ina sonki sosai fiye da son nake yi wa kaina_
Tun lokacin yafara magana har ya yadasa aya jikin Anaal rawa yake kamar mazari tsoro da rud'ani suka lullu6e ta.
Ansar yacigaba da cewa _juyo ki dube ni ki yi min murmushi nan naki mai sanyaya zuciya, ba....._ ya Ansarrr da k'arfi cikin kururuwa Anaal ta kira sunanshi a tsorace ya hadiye sauran kalamansa yana mata kallon tsoro.
A zafafe tafara magana kanka d'aya kuwa? Ka kuwa San abunda bakinka yake furtawa? toh wallahi indan ma mafalki ka ke yi ka falka wannan hauka da shirme har ina? Au dama shine dalilin da yasa kace mu zama friends ashe akwai wata, mummuna manufa a k'asan zuciyarka?
Toh ni wannan cin amana ba da ni ba wannan ae abin kunya ne.

Ansar ya dube Anaal baki bud'e daga bisani ya kece da mahaukaciyar dariya har yana had'awa da dukan steering, da kyar yai controlling dariyan cikin pity face yace nifa ina fassara miki abinda  wak'ar take nufi ne Allah sarki poor girl ke kin dauka da ke nake?
Ae ko giyar wake nasha Anaal babu kalma son a tsakaninmu. Ni fa banta6a yi miki wani kallo fa ce na k'anwata ta jini Anaal ina ba ki kulawa ne a matsayinki na wance batada 'yan uwa domin ba lallai bane wasu matsalolinki ki iya tunk'arar iyayyenki da su ba, shiyasa nake tunani ni ne zan maye miki gur6in yaya Auwal na rok'eki kada ki sake wannan mummuna tunani a tsakaninmu.
''Tsananin kunya ya lullu6eta, takasa koda motsa d'an yatsa gaba d'aya ta susuce gani haka yasa Ansar ya kira sunanta cikin laushin murya _Anaal_
Kasa amsawa tayi sai ma rufe fuskarta da hijabi da tayi abin ya bashi dariya sai kawai yadinga kwasan dariya shi kadai har ya iso gate d'in makarantarsu batasaniba saboda fuskarta na rufe.
_Anaal mun iso ko yau ba za ki je school d'in bane mu koma gida?_
Da sauri ta bud'e fuska amma bata bari suka had'a ido ba ta bud'e k'ofa tafita yadinga kwalla mata kira tayi biris da shi sai da yaga shigarta cikin school sannan yaja mota yatafi yana dariyar shirmenta.

"Direct Anaal tawuce class ta ajiye schoolbag d'inta tana fitowa taci karo da zeenat, 'yar buzuwa ashe kin shigo?
Mtcsww''! Anaal ta ja tsaki rai 6ace tace banaso iskancin zeenat sau nawa ina kashe miki gargad'i kidaina kirana 'yar buzuwa?
Oho"! Nasani miki da alama yau akwai wanda yata6a ki bara na ajiye schoolbag d'ina nadawo tashige class tabar Anaal tsaye.
Har zeenat tadawo Anaal batasaniba tayi zurfi a tunanin, shirme da ta tafka.
Dafa kafad'arta zeenat tayi meke damunki ne Anaal?
Tayi ajiyar zuciya had'e da kallon zeenat mekika gani ne?
Damuwa, damuwa nagani fal akan fuskarki.

Hmm! Haka dai ki ka fad'a amma ni ba abunda ke damuna.
Wai Anaal yaushe za ki rage zurfin ciki? Ni fa k'awarki ce, ki tuna daga ni har Ramlat ba ma 6oye miki duk wani abu da yashafe mu saboda mun yarda da ke sa6anin ke da har yanzu ba ki aminta da mu ba, gaskiya k'awance da ke Anaal akwai wahala ina amfani irin wannan zama ki sauya halinki ace ko abu zai kashe ki ba za ki iya bud'e baki ki fad'awa wani ba.
Kisani Anaal barin kashi ciki baya maganin yunwa ki ta boye sirrinki mu kuma zamu cin gaba da gayamiki na mu domin mu yarda da ke d'ari bisa d'ari ke da ba ki yarda da mu ba chan ta matse miki.
Tana k'arasa magana tajuya tanufi hanyar assembly tabar Anaal tsaye sororo taja jiki asanyaye ta bi bayanta.
A wajen suka iske Ramlat domin yau tazo a makare
Ana gama assembly Zeenat taja hannun Ramlat suka nufi class batare da sun kulata ba wannan ya tabbatarwa da Anaal zeenat ta warwarewa Ramlat zare da abawa.

Tana shiga class tanufi seat d'insu cikin sanyinta tafara magana haba! K'awaye na bai kamata ku yi saurin d'aukar zafi akaina ba dama ba wani abu bane yau na tafka shirme da abin kunya shine ku ganni a haka, wallahi har yanzu kunya nakeji tamkar ina gabansa har inaji da wane ido zan sake tozali da shi tak'arasa magana tana yarfe hannaye.
Zeenat da Ramlat suka kalli juna Ramlat ta mik'e ta zauna akan desk ta dafa Anaal wanene shi wane irin abin kunya ki ka tafka har da zai dame ki haka?
Har ta bud'e baki za ta bata amsa uncle d'insu mai d'aukarsu darasin mathematics Yashigo dole Anaal ta hadiye sauran kalamanta.
Uncle d'in yana cinye period d'inshi mai darasin physics yana jiranshi a bakin k'ofa yafita shi, kuma Yashigo a takaice Anaal batasami damar sanarda su damuwarta ba sai during breakfast.
Direct shop d'in siyarda snacks da soft drink suka nufa.

 Ramlat da zeenat Suka nemi dogon bench suka zauna yayinda Anaal tashiga shop taciro 1k tasiyo recharge card na N200 tadawo ta zauna taciro 'yar Nokia ta daga pocket tasaka recharge card d'in Zeenat tace Anaal ki k'arasa mana labarin da ki ka fara ba mu nakagara naji waye wannan mutume da ki ke magana akanshi.
Ajiyar zuciya Anaal tayi tashiga kwararo musu abinda yawakana da sanyin safiya tsakaninta da Ansar tana dasa aya suka sa mata dariya kamar zautacin.
 Anaal batasan lokacin da tashiga tayasu dariya ita kanta sai yanzu shirme nata yabata dariya sai da sukaci dariya iya son ransu sannan, Anaal ta lallube wayarta tashiga rubutawa Ansar text massage.
_Sallam da fatar ka isa gida lafiya? Dan Allah Ya Ansar kayi hak'uri da abinda yafaru d'azu sharrin zuciya ne, domin ko makaho yashafa ka yashafa ni yasan kafi k'arfina me za kayi da 'yar masu gadi irina?  A halin yanzu tunani nake tayaya zan had'a ido da kai, wallahi kunyarka nakeji fiye da tunaninka kahuta lafiya_

Tana gamawa tayi sending ta mik'awa Ramlat waya ku duba send items ku ga text d'in da na tura masa, na ban hak'uri ya yi kuwa?
A baiyane Ramlat ta karanta zeenat tace anyya Anaal alaqarki da Ansar bata sauya daga yaya da k'anwa ba?
Nima abin zan fad'a ki ka rigani Cewar Ramlat
    "Amma wallahi kun bani mamaki da har idanunku suka rufe ku ka manta da matsayina wanda haka yasa ku ke, dangatani da mutume da yafi karfina toh tunda kun manta bara na tuna muku ni Anaal ba kowa bace ba kuma, 'yar kowa ba face 'yar masu gadi banida dangin iya balle na baba a Nigeria cin rani mu ka zo ni da iyayyena kamar yanda nasha jin dubanan mutane suna kiranmu da 'yan ci rani.

Tun farko ganinku da Ya Ansar ku ka fara wannan tunanin a tsakanimu, shin ban taka musu birki ba ta hanyar sanarda ku matsayi irin na Ya Ansar ba?
[18/04 12:06 am] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

14

Da mugun mamaki Tad'ago tana kallonshi ya d'aga mata gira kince ina operating laptop a yangace, shine na kawo miki ke da bakya yanga ki yi min aikin nasan za ki iya.
 Muryarta na rawa tace ni....ni...
Ke...ke...me? Ya katseta da hanzari ba abunda za ki fad'a sai kinyi shi ko na murd'e miki kunne.
   "Turo miki ta yi ni fa malamarka ce kuma ba kyau yi wa malami rashin d'a'a.
Ina ruwana da zamanki malamata in ke malamata ce ni kuma yayanki ne. Ina da matsayin da zan saka ki aiki ki yi koda ranki bayaso.

Ni fa ban iya ba zan maka jagwalgwale ki yi d'in ae ni nace inaso ba yanda ta iya dole ta ture takardan assignment nata a gefe, ta d'auki files tasoma karanta abinda ke ciki wani shegen murmushi ta yi tasoma shigar da bayanai duk abinda take yi Ansar yana tsaye gabanta, hannayenshi zube cikin aljihun yana kallonta cikin abinda bai wuce 1-2 hour's ba ta kammala aikin.
Ta zungura masa laptop kar6i kayanka sarkin kallo na gama.
Bai kar6a ba sai ma k'aimi yak'ara wajen kallonta ta ajiye laptop da files akan kujera za ta juya tashiga bedroom yasha gabanta ina za ki je?
Baccin nakeji tafad'a tana kallonshi, yasauke gwaron numfashi ya langwa6e kai can k'asan mak'oshi ya furta Anaal banaso ki tafi.
Murmushi ya subuce mata ta d'an zaro ido wai saboda me?
Ni ma bansaniba kawai banaso ki tafi.
Ya za ka yi da ni saboda bacci nakeji har wani yaji-yaji nakeji a idona?
Ya zan yi Anaal dole na barki ki kwanta sai da safe.
Toh sai da safe ka gaida su Basmah.
Za su ji.
Daga haka ta ra6a gefenshi ta wuce har ta tura k'ofar d'akin Granny, tajuya yana tsaye inda tabarshi idanunshi na kafe akanta.
Tasake mishi sanyayen murmushi shi ma ya mayar mata da Martani tashige d'akin ya jima tsaye yana nazari daga bisani yadauki laptop da files d'inshi yafice.

Tun kafin yak'arasa parking lot ya hangon Zuhura zaune akan farar kujerar roba, tana gyagyad'i da alama ta kashe lokacin tana zaman jiranshi tausayinta ya kamashi duk lokacin da suka sami sa6ani da Zuhura sai ta rasa kwaciyar hankali har  sai sun daidaita.
Files d'in hannunshi ya buga mata ta mik'e tsaye a firgice sai muzurai ta ke yi Ansar ya kyalkyale da dariya.
A shagwa6e tafara bubbuga k'afa a k'asa Ya Ansar kai koh?
Ya katse dariya da yakeyi Zuhura zaman me ki ke yi anan?
Cikin rashin damuwa tace ina gadin motarka ne.
Ya yi murmushi kamar bai fahimcin inda ta dosa ba.
Ya Ansar Kadàina sona koh?

Girgiza kai ya yi har abada ba zan daina sonki ba, halayenki ne kawai nafara gajiya da su da za ki canza kidawo Zuhurarki ta asali ni kuma da zan nuna miki nafi kowa sonki da k'aunarki.
Lumshe idanu Zuhura ta yi Sabon sonshi na k'ara ratsa jinin jikinta. Nayi maka alqawali Ya Ansar duk abinda ba ka so zan daina   burina banaso ka daina sona.
Ya tabe baki in har bakyaso nadaina sonki ki gyara halinki.
Zan gyara Ya Ansar Allah zan gyara.
It's your own good domin duk son da nake miki zan iya barin k.....please Ya Ansar kar ka k'arasa In har kai za ka iya barina ni ba zan iya barinka ba. kariga ka zama jinin jikina farin cikina idan ka barni rayuwana za ta tagaryara zan shiga k'uncin mafi muni a rayuwa, ka tausaya min Ya Ansar karka barni tak'arasa magana had'e da zubewa gabanshi ta yi kneel tana kuka kamar ranta zai fita.
Sosai tausayinta ya kama shi baisan lokacin da yad'ago ta ba, saida ta mik'e tsaye yashiga yarfe hannaye kamar wanda yata6a electric shock.
Zuhura ta dube shi da kod'ad'in idanunta za ta yi magana yad'aga mata hannu Zuhura ki shiga gida gobe za mu yi magana kinga yanzu har _11:00pm_ ta yi.
Kamar ba za tafi ba sai kuma tajuya jiki a sa6ule kamar kazar da kwai yafashewa a ciki.
Yashiga mota yanufi gida agajiye yafad'a bathroom yasakewa kanshi shower, bayan Yafito daga wanka yasaka pajamas ya haye gado duk yanda yaso yai bacci yakasa sai faman juyi yake  hannu ya mik'a akan bedside yadauki phone d'inshi yashiga dialling number Anaal cikin Sa'a wayan yana bud'e bata rufe ba.

Anaal wance ta yi d'ai-d'ai akan gadon Granny tana sharar baccinta hankali kwance vibration d'in wayarta da ke k'asan pillow  yashiga zayar a dodon kunnenta. A firgice ta falka ta tura hannun ta dauko wayan da kyar ta iya ware idanunta saboda masifafen baccin da takeji, ta kai duba akan screen d'in 'yar Nokian ta _Ya Ansar_ ta furta a baiyane cikin yanayi na kid'ima lafiya Ya Ansar zai kirani a tsakiyar dare?
Tasauke ajiyar zuciya mae cike da tsoro ta lek'e kasan floor inda Granny take kwance akan k'atuwar mattress d'inta baccinta take haik'an har da su minshari, hannunta na rawa ta danna koren madanni takara a kunne in shock ta furta _Hello Ya Ansarrr_
Hello da ta furta had'e da yanda ta ja sunanshi ya haifar masa da kasala ya lumsashe idanu.
_Ya Ansar kana jina kuwa?_
Takatse masa shauk'in da ya afka.
_inajinki Anaal na katse miki bacci koh?_
Wannan ba damuwa bane damuwa na Allah yasa lafiya ka kirani a wannan lokacin?

_lafiya Anaal amma ba lau ba_
Subhanalilah''! Me ke faruwa?
_Na yi iya k'ok'arina Anaal domin nasami bacci nakasa sai wani k'uncin da zafi da nakeji zuciyata, tana mun shine na kira ki ko zami relief_
Mamaki ne yarufe Anaal takasa koda kwakwaran motsi ta zama speechless ko za ta iya magana a wannan yanayi me za tace da shi she's totally confused with shock.
_Anaal ki yi magana mana_
Ajiyar zuciya ta yi me zance Ya Ansar?
Kina nufi bakida abin cewa?
Banida ya Ansar amma kai in kanada abin cewa ina sauraronka.
_Anaal_
Na'am
Kinsame?
A'a sai kafad'a
Kar nafad'a ki yi min dariya.
Murmushi tayi had'e da cewa ba zan ba.
Ya gyara kwanciya kamar Mae rad'a yafurta muryarki yana mun dad'i.
Dariya tayi marar sauti tak'ara Jan blanket ta k'ududune yanda za ta ji ta very comfortable, Ya Ansar kenan. miye abin dad'i a wannan muryar nawa Mae kama da antashi engine markad'e.
   ''Ki godewa Allah Anaal domin ke mae Sa'a ce a rayuwa ubangiji ya albarkace ki da abubuwa da dama, wanda ba kowace 'ya mace ce take da su ba you're one of the talented, brilliant and intelligent girls komai naki yana burgeni fatana Abbah yabarki kicigaba da karatu banaso ya yi saurin aurarda ke.
Ajiyar zuciya tayi Bana tunanin Abbah zai barni na je makaranta gaba da sakandire burinshi ina gama secondary nayi aure. Amma wallahi har ga Allah inason na cigaba da karatu ko domin na tallafawa iyayyena banaso, rayuwar Abbana tak'are a gadi.

''Indan kuwa haka ne zan ba ki shawarar da za ki cima burinki, kidaina kula samari ki nisanta kanki daga gare su idan Abbah yaga bakida takamame saurayi zai hak'ura yabarki ki cigaba da karatunki domin na tabbata irin son da Abbah yake miki ba zai miki auren dole ba.
Murmushi Anaal tayi ae kuwa Ya Ansar ka zo da shawara Mae kyau da ingancin na gode fa.
Kidaina gode min Anaal domin alqawalin ne na daukawa kaina duk wani buri da farin cikinki ni nan zan Samar miki da su. Ni dai burina kiyi fatali da samarinan na zamani, yawancinsu mayaudara ne.
Shikenan Ya Ansar zan yi amfani da shawararka.
Fira yashiga yi mata Mae dad'i sai murmushi take tana dariya marar sauti ta yanda Granny ba za ta jiyo ta ba around 2:56am baccin ya sace Ansar yana maqale da waya a kunne, sai saukar numfashinsa Anaal taji ta yi murmushi ''Allah sarki Ya Ansar kayi bacci a dai-dai lokacin ni kuma baccin yakauracewa idona.
Kasa kashe wayan tayi tacigaba da sauraron saukar numfashinsa tsawon lokacin tadauka a haka, sai daga baya ta tuna tana karar mishi da credit ne a banza. Jiki a sa6ule ta katse kiran yayinda ta afka zance zuci.
Gaskiya yaya Zuhura tayi Sa'a samun Ya Ansar a matsayin mijin aurenta ga kyau ga iya furta lafazi mai dad'i, ba abinda yafi burgeni da shi irin yanda yake d'aukar wanka uwa-uba ilimin Addini da na zamani da yake da shi. Tasauke ajiyar zuciya gaskiya Ya Ansar kahad'u 100% Allah yabani miji Mae irin d'abi'unka.
Har akayi kiran sallah asuba a kunnenta jin anfara iqama yasa ta tashi, ta tada Granny tashiga bathroom tayi alwala saida tayi raka'atul fijir sannan ta sallacin sallah asuba.
Tana gama sallah tashiga azkar d'in da take yi da safe tana ganin Granny tafita zuwa parlour ta zubura tadauko, wayarta saida tafara checking balance d'inta mtcsww"! Ta ja tsaki cike da jin haushi Naira biyu da kobo 56 suka rage mata, duk da haka sai tayi dialling numbernshi.

A lokacin yadawo daga masjid kenan yana cire jallabiya yaji ringing wayarshi, share kiran ya yi saida yagama cire Jallabiya sannan yanufi bed ya kwanta yana d'aukar wayan kiran na tsinkewa.
Har ya yi niyyar ya ajiyen wayan sai kuma wani tunani yafado masa ya duba miss call d'in sam bai yi  tsanmani Anaal ce takira shi ba.
Da sauri ya yi calling nata back.
Anaal najin wayarta tad'auki vibrate dama tasaka wayan a meeting ne jikinta har rawa yakeyi tayi received.
_Hello''! Ya Ansar_
Hi Lucky ya akayi ne?
Dariya tasa yau kuma nice Lucky?
Kwarai kuwa domin ke Mae Sa'a ce ko kinsan cewa ke ce mace ta farko da na ta6a raba dare ina waya da ita, dawowa na daga masallacin kenan gashi kuma ina waya da ke.
Anaal ta kad'a kai kuma ni ce Mace ta farko da kafara hanawa bacci ba.
Gaba d'aya suka sa dariya.
Ae dole kayi dariya Ya Ansar kayi bacci abinka kabarni da sauraron minsharinka yanzu haka da headache na tashi tak'arasa magana cikin shagwa6a.
 Wani irin nishad'i ya kai masa ziyarar bazata ya lumshe idanu oh! Sorry my Lucky zan zo miki da extra ki d'an kora kinji?
''O'o ni banason magani.
Shikenan sai nazo zan nemo abinda zai warkarda ciwon kan. Yanzu ki je shirya kada kiyi latti kice ni ne sanadi.
Tana dariya ta katse kiran wani irin dad'i takeji yana ziyarta ta.
Cike da nishad'i tashiga bathroom tayi wanka tana fitowa, ta goge jikinta tashafa lotion iya powder ta goga tasaka uniform, ta d'auki schoolbag d'inta tanufi parlour ta iske Granny tana sauraron Labarun BBC a 'yar k'aramar radio ta cikin girmamawa ta gaidata, Granny ta amsa had'e da cewa har kinfito?
''Eh Granny
Toh Allah yabada Sa'a ki je cikin drawer purse d'ina na nan ciki kidauki N200.
Na gode Granny akwai raguwar canji jiya ya isheni nayi k'udin adaidata har nayi breakfast.
Shikenan adawo lafiya saboda ke ba Karin kumallo ki ke yi ba ballantana nace kisha koda 'yan ruwa shayi ne.
Dariya Anaal tayi karki damu Granny nariga na saba in ba 10:00am tayi ba bana iya cin komai.
Ke ki kasani da tsirfarki ta tsiya, sai kitafi kada kiyi latti a narke a banza ke ba wani abincin kirki ki ka cin ba.
Tafice tana dariyar Granny kaitsaye BQ tanufa ta wajen Ammi ta jima wajen Ammi kafin tayi sallama da ita tanufi bakin gate wajen zaman Abbah bayan ta gaidashi yabata k'udin breakfast da na adaidata shi kan batace bazata kar6a ba domin tasan sai ya tuhumeta ina tasami k'udi shiyasa tarufawa kanta asiri ta kar6i k'udin.
7:06pm tafito daga gida tun daga nesa ta hango motar Ansar inda suka saba had'uwa, tun kafin tak'arasa tafara murmushi.

Jeeddah Aliyu
[19/04 9:13 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
 
 *10*

Zuhura ta yatsine fuska Ya Ansar ka yi shiru ba ka ce komai ba ko kana nufi har yanzu ba ka yafemin ba"?
  ''Ansar ya yi murmushi yana kallonta ta k'asan ido yayinda Zuhura tak'ara zurmawa a sonshi domin kallon ya yi mugun ratsa 6argo jikinta. Tak'ara langwa6e kai cikin shagwa6a tace ''Please my luv answer me.
K'ara haska ta ya yi da k'ayatatcen murmushi sanin kanki ne Zuhura bana iya dogon fushi da ke matsala na d'aya da ke bakyajin magana.
   ''Ka K'ara hak'uri da ni my luv da mu yi aure zan dinga jin maganarka.
Tabe baki ya yi yayinda Granny ta ja tsaki da sauri Zuhura tajuya ta dube Granny saida ta yatsine fuska kafin ta furta ke kuma ke da wa"?
Banza Granny ta yi da ita tacigaba da kallonta Zuhura tak'ara yatsine fuska tadawo da ganinta wajen Ansar my luv I miss you so much especially your hot & romantic voice mu je daga waje na fayyace maka yanda nayi missed naka. Wannan tsohuwa ba za tabarmu mu sake ba tak'arasa magana had'e da nuna Granny da baki.
   ''Ansar yak'ara fad'add'a murmushinsa ki je kawai in na kamalla abunda na zo yi zan nemi ki.
  Zuhura ta mik'e tana dariya k'asa-k'asa shikenan my luv sai kafito tajuya tafita, Ansar ya bi ta da kallo daga bisani ya dube Granny me Anaal take yi a d'akin ne Granny ko yau ba za'a fad'a min karatun bane"?

     "Granny ta kya6e baki tasoma kwallawa Anaal kira sai ga ta tafito sanye da hajibi iya gwiwa Army colour ya yi matuk'ar k'awata fuskarta.
   "Gani Granny
Ga me nemanki nan Granny tafad'a had'e da nuna Ansar da yatsa, kallo d'aya Anaal tayi masa ta kauda fuska saboda duk lokacin da tayi arba da kyakyawar fuskarsa sai ta tsince kanta da fad'uwar gaba ga wani masifar kwarjini da yake mata.
   "Yayinda Ansar ya kafeta da ido baya ko k'intawa ga wani shu'umin murmushi kwace a fuskarsa, yana wani shafar laulausan sajenshi.
Batare da ta furta uffan ba tajuya ta koma d'akin tadauko jakkar littafanta kamar yanda ta zauna jiya nesa da shi ta langwashe k'afafunta, tana facing nashi ta bud'e jakka tafito da Al-qur'ani mai girma ta mik'a masa had'e da cewa ka sauko k'asa shine ladabin d'aukar karatu.
   ''Angama malamata ya furta can k'asan mak'oshi ya zauna k'asa ya langwashe k'afafu kamar yanda ya ga ta yi yasoma koro karatun da ta gayamishi jiya har izuwa inda ta tsaya, ta kar6i Qur'ani tak'ara mik'a masa ahallari yafara karatu da saninsa yake karanta fassara ba dai-dai ba dakatar da shi tayi ta hanyar cewa bawan Allah wa gayamaka wannan fassarar da ka ke yi"?
"D'agowa ya yi yana kallonta da shegen murmushinsa mai tayar da hankali me kallonsa da sauri ta kauda fuskarta.
   "Kamar mai rad'a ya furta Ke!
Da sauri tadawo da ganinta wajenshi cikin sark'ewar lafazi tace ni kuma"?
  "D'aga mata gira ya yi a maimakon yabata amsa tsigar jikinta yatashi yarr.... Ya Ansar ta kira sunanshi had'e da langwa6e kai kamar me shirin yin kuka.
   ''Anaaaal......shima yakira sunanta har da su qalqala wani bak'on yanayi Anaal tashiga wanda a tsawon rayuwarta bata ta6a riskar kanta a ciki ba.
 
Sannu ahankali yarufe littafin hannunshi yajigina jikinsa a kujera ya lumshe sexy eye's d'inshi yana shafar gashin kansa.
Jikin Anaal ya mutu mutuss...ta kasa koda kwakwaran motsi tad'ago ta sace kallonshi karaf suka had'a ido ya wanketa da murmushi batasan lokacin da ta mayar masa da Martani murmushin nashi ba.
   "Tsawon lokacin suka d'auka in ya dube ta ya yi murmushi ita ma ta kalleshi ta yi murmushi, muryar Granny ce ta ratsa dodon kunnensu ni zan shiga ciki na kwanta in kungama  karatu Anaal ki kashe kayan kallo ki rufe k'ofa.
   "Toh Granny Anaal tafad'a cikin rawar murya.
   "Ansaru sai da safe ka gaida gida.
Gida zai ji Granny sai da safe Allah yatashe mu lafiya.
_Ameen Granny tafad'a had'e da shigewa d'akinta_
  "Ya Ansar kacigaba da karatunka mana.
Ba zan iya ba malama Anaal
Saboda me ba ka iya karatun bane ko me"?
"Na iya saidai ba zan iya karantawa ba.
Toh bani littafina ta mik'a masa hannu kurawa hannunta ido ya yi fari tass da shi kamar kata6a jini yafito 'yan yatsunta zaro-zaro k'umbarta yasha adon Jan lalle sai zobe kwara d'aya tal na azurfa da ke sakade a yatsanta, Ansar ya yi nisa a kallon yatsan nata sai ji ya yi tafizge littafin hannunshi cikin zafin nama yajanye littafin.
   "Yashiga kallonta k'asa-k'asa cikin muryar shagwa6a tace Please Ya Ansar Kadàina kallona banaso.
   Ya yi murmushi had'e da zaro masifanfu idanunshi in a romantic voice yafurta wai meyasa Anaaaal"?
   "k'ara rikita ta ya yi saboda duk lokacin da yaja sunanta sai tsigar jikinta ya tashi ga wani sanyi da ke ratsa k'asusuwan jikinta.
   "Kawai ni banason kallo tafad'a har da murgud'a d'an k'aramin bakinta mai kama da gidan tsuntsu.
   "Ansar ya ja iska daga bakinshi yafesar idanunshi ya mayar akan pink lips d'inta cikin zuciyarshi yafara fassalta kyakyawar surarta.
   ''Anaal fara ce tass irin farin nan me surkin ja-ja-ja ita ba doguwa bace kuma ba za'a sakata a Layin gajeru ba tanada round face me d'auki da dogon hancin mai kama da pencil idanuta manya ne sosai shiyasa in tana magana take lumshe su kamar me jin bacci Anaal tana da jiki saidai ba sosai ba 'yar lukuta da ita, gashin girarta da na idanuta bak'i wulik da shi kamar tana saka na kanti duk lokacin da Anaal ta yi murmushi ko magana sai kumatunta ya lotsa{dimples}.
   "Ansar yasaki naunauyar ajiyar zuciya baisan lokacin da ya yi subul da baka ba ta hanyar furta _Anaal mai kyau_
A tsorace tad'ago na'am me kace"?
_Anaal me kyau nace ko ke ba me kyau bace?_
Humm....Ya Ansar kai koh tafad'a cikin sirriyar murya.
  ''Me nayi"?
"A wannan jar fata nawa kamar Jan k'osai za ka kirani me kyau kawai malam kana zagina.
   "Dariya ya yi Anaal kenan ai ni ba abunda yafi tafiya da imanina a halitttarki irin farar fatarki.
   ''Eyeee.....tafad'a har da zaro ido nan take gogan naku yagano yasaki layi sai kawai yawaice ta hanyar cewa in tambaye ki mana Anaaal
Gyad'a kai ta yi saboda a halin yanzu ta kagara ta tsince kanta alone ko za ta samu damar aikawa da Kanta tambayoyi.
 
Shekarunki nawa"?
  Batasan lokacin da tasa dariya ba tashiga 'kya'kyatawa kamar wance taga comedy na emanuella. What's funny Baby"? Ansar ya watsa mata tambaya yana leqon fuskarta, tarufe bakinta da tafin hannunta tana cigaba da dariya abinta.
   "Shikenan tunda ba za ki gayamin ba zan tambayi Ammah nasan ita ba za ta yi min dariya ba kamar ke.
  ''Humm! Kasan da Ammah meyasa ka tambaye ni"?
Saboda ke yafi dacewa na tambaya ko bakiji hausawa suna cewa waqa a bakin mai ita yafi dad'in sauraro ba"?
  ''Ta za'ayi nasani al'ahali ni ba bahaushiya bace.
   "Humm....! Anaal kenan komai naki yana burgeni har nakeji ina ma ace muna rayuwa a gida d'aya da kullum sai nasaka ki a gaba ina kallo.
   "Zaro ido Anaal ta yi tana dariya kai Ya Ansar wallahi kana da abin dariya meye abin burgewa a tare da ni da har za ka dinga kallona"?
  Ansar ya lumshe kyawawan idanunshi yana murmushi ba za ki gane bane Anaal amma a sannu zan ganar da ke.
   ''Ka ji da shi ni bani littafina na tafi baccin nakeji.
   "Ke da Granny kuna saurin kwanciya bacci jikinku baya tsami ne Kalli wall clock kigani yanzu _10:15pm_ ta yi"?
  Tabe baki Anaal ta yi kace bara ka iya karatu ba to zaman me zanyi anan"?
   ''Ki tayani fira.
Fira, fira fa kace a maimakon karatu sai mu buge da fira"?
  Eh man"! Yafad'a yana kallon cikin idanunta.
  Humm...ni kan badani ba ka je part d'in Hajiya yaya Zuu na jiranka kusha fira abinku tak'arasa magana tana mai mik'ewa tsaye.
   ''Shima mik'ewa ya yi yana kallonta ad'age ai ba ke za ki nuna mun Zuhura ba nasan da ita nasan kuma tana jira na amma nace ki tayani fira "anyway tunda ba za ki iya ba za ki iya tafiya sai da safe yajuya yanufi k'ofar fita yabarta tsaye sororo tana mamakin miye abin fushi anan"?
 "Har ya yi tako biyu yadawo ya mik'a mata littafinta yak'ara juyawa yafita.
_sai da safe Ya Ansar_ Anaal tafad'a cikin sanyi murya. Qala bai ce da ita ba ya bud'e k'ofa yafita tabe baki Anaal ta yi tajuya  asanyaye tashiga d'akin.
   ''Ansar yana fita yanufi parking lot yaja motarshi Abbah ya bud'e masa gate yanufi gida yana isa gida Direct part d'in shi yawuce yacire kayan jikinshi yashiga bathroom ya yi wanka yana fitowa phone d'inshi na fara ringing kamar ba zai yi picking ba saida yagama Jan ajinsa sannan ya yi picking _Hello my luv_ Ya Ansar sarkin alqawali kace najira ka za ka zo shine ka yi tafiyar ka koh"?
  _"Oops! I'm very sorry my luv nima ba'a son raina na tafi batare da nemi ki ba amma kiyi hak'uri gobe inshaAllah zan zo har sai kinga ji da ganina_
  Humm.....my luv har abada idanuna ba za su ta6a gajiya da ganinka ba karka manta Kaine farin cikin rayuwata jin dad'ina you're my everything Ya Ansar I love you so much.
   ''Yatsine fuska ya yi had'e da cewa I love too Baby ki kwanta kiyi bacci mai dad'i had'e da mafalkina.
   "Your wish is my command my luv kaima kayi mafalkina mai dad'i.
   ''Batare da yabata amsa ba ya katse kiran yasaka pajamas d'inshi ya haye bed, ya tsunduma a tunani _Anaal_ da kyar yasamu bacci yadauke shi.

        _7:10am_

Ansar yafito daga part d'inshi yana sanye da bak'ar jallabiya sai uban sauri yake kamar zai tashi sama, kaitsaye parking lot yanufa yashiga motarshi saida ya yi warming nata daga bisani yafizge ta da k'arfi maigadi ya bud'e masa gate.
    "Kaitsaye gadon K'aya yanufa layin gidansu Zuhura yashiga yanemi nesa da gidan ya yi parking lokacin-lokacin yana duba agogon da ke da jikin motarshi

 _7:15am_


Anaal tafito daga gida jikinta sanye da school uniform a hankali take tafiya ga k'atuwar schoolbag d'inta rataye a bayanta, bakin titi tanufa tasami adaidata da zai kaita school.
   ''Tun kafin tak'araso Ansar ya hangota yasaki ajiyar zuciya had'e da hamdallah. Yana kallonta har ta ra6a shi ta wuce yana ganin takai titi yaja mota ya bi bayanta, Horn yadinga dana mata juyowa d'aya ta yi ta kalli motar tadauke kanta batare da tagano wanda ke cikin motar ba saboda gilashi motar tinted ne.

    "Ansar yana gani tayi nassara tsayar da wani mai adaidata ya yi saurin saukar da gillasai _ke Anaal bakyaji ne tun d'azu ina miki horn"?_
   "Muryar sa Anaal tagano saida gabanta yafad'i a d'an rikice tajuya ta dube shi Ya Ansar tafad'a abaiyane tadawo da ganinta ga mai adaidata malam dan Allah minti 1.
   "Okay hajiya amma ki yi sauri.
Tajuya tanufi motar tadafa k'ofar da ke saiti da shi ta d'an tura kanta cikin motar _ina kwana Ya Ansar_
Lafiya kishigo nayi dropping naki.
  ''Shiru ta yi tana kallonshi tarasa kalma da za ta furta masa gani shiru nata ya yi yawa yasa yace kishigo mana kina 6atawa kanki lokacin.
   "Ba yanda ta iya dole tajuya sukuku kamar kazar da kwai yafashewa a ciki takoma wajen mai adaidata tabashi hak'uri.
   "Ta bud'e k'ofar seat d'in baya ta ajiye schoolbag d'inta ta zauna a seat d'in gaba ya ja mota suka halba kan titi.
Shiru ya biyo baya Anaal tana nazari me Ansar yake yanufi da ita yayinda Ansar yake tunani shin me ke shirin faru da shi"?


Jeeddah Aliyu
[01/05 1:18 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*16*

Zeenat, Ramlat kudaina had'ani da abinda yafi 'karfina Ya Ansar yafi k'arfina nesa ba kusa ba tuni ya girmewa ajina mutuncin da tausayina da yakeji sune sanadin alaqarmu kuma, har abada alaqarmu ba za ta sauya daga haka ba. Har Ramlat ta bud'e baki za tayi magana Anaal tad'aga mata hannu ya isa Ramlat mu rufe wannan zancen domin, duk abinda zan fad'a ba za Ku fahimce ni ba.
Tana k'arasa magana ta mik'e kutashi mu tafi class.

''Ke ba za ki yi breakfast bane?
Ta girgiza kai banajin yunwa in kum gama kusameni a class tajuya tai tafiyarta ta barsu da aikin kallonta.


_Ansar_

Lokacin da Anaal ta tura masa text yana meeting phone nashi a rufe sai around _12:30pm_ yafito daga conference Hall, yana zaune a office d'inshi zamanshi kenan Abdallah yashigo yana waya da girlfriend d'inshi, har yagama wayan Ansar yana kallonshi.

Mtcsww! Ansar yaja tsaki Wallahi ka ji tsoron Allah! Abdallah shin wace ri6a za ka ci in ka 6ata 'ya'ya wasu?
Kai bakajin tsoron wata rana a 6ata naka domin zina bashi ce. 6ata fuska Abdallah ya yi kafara koh?
Wai kai Ansar ba halin ka ji mutum yana waya sai kafara yi masa wa'azi?
Wannan yarinya da ka ji ina waya da ita tana matuk'ar sona tamkar ranta. Ba tilassata nayi ba shaukin so ne ya d'ibeta tayi min alqawalin komai nakeso za ta mallaka min daga ciki harda kanta, shine don ina gaula irinka za'a bani kyauta abun irin wannan nace ba zan kar6a ba.

Ni fa lafiyayyen namiji ne ina buk'atar jin dad'i a wannan zamani ba abinda ya kai mata musanman in kanada k'udi shiyasa na za6e su, don na dinga barje gumina akansu. Duk 'yar da k'addara ta fad'a kanta ta afka tarkona wallahi sai na moreta idan kuma na gama tsotse albarkatun jikinta nai mata wulaqancin da ko kare ba zai ci ba.

      "Girgiza kai Ansar ya yi haushin abokinshi ya kamashi ba tun yau ba yasan halin abokin nashi da neman matan tsiya amma bai ta6a tsanmani iskancin nashi ya yi tsamari haka ba.
Abdallah lamarinka ba tsoron Allah a ciki kai ko tsoron cuta bakayi indan so ka ke ka more rayuwa kayi aure mana.
Ubangiji ya yarje mana mu aure mata d'add'aya har guda 4 amma in za mu iya adalcin tsakaninsu, in ba za ka iya adalcin ba ka aure guda 1 ta isheka barje gumi domin zina bala'i ce kada sanadinka ya janyo mana masifa a zuri'a.
Abdallah ya mik'e tsaye yana murmushi ya dube Ansar yace karka damu d'an uwa zanyi aure very soon duk wannan abin da nakeyi akwai wance zuciyata takeso, banida burin da yawuce na mallake ta a matsayin matata ta sunnah.

Na yarda da ita za ta kai min budurcinta har gidana. Wad'annan tarkace da ka ga ina moresu a farmhouse d'in Dad ba ta aure a ciki kawai abokan jin dad'i ne. Inanan da matata kamila, malama mai nagartaciyyar tarbiyya tana jirana a gefe da zaran nagama more rayuwa za mu yi aure zan watsarda duk wani shashshancin na rungume halak d'ina.

Mtcsww! Ansar yaja tsaki 'yar iska dai irinka dama mazinacin sai mazinaciya kuma inaji maka tsoro ranarda Dad zai kamaka da karuwa a farmhouse d'insa, wallahi za ka sha mamakin irin hukuncin da zai dauka akanka.
A yatsine Abdallah ya dubeshi sai in Kaine munafukin da zai fad'a masa.
Murmushi Ansar ya yi kaima kasan ni ba munafuki bane da na iya munafuncin da tuni kashinka ya bushe banza kawai bunsuru.
Abdallah ya yi murmushi yana Sosa k'eya kanka akeji ni ka ga tafiya ya murda handle yafice tun fitar Abdallah Ansar baisan dalilin da yasa yakejin matsanancin fad'uwar gaba ba.
Ya kifa kanshi a desk yashiga nazarin kalaman Abdallah lokacin yashare Mae tsawo yana fama da tunani, ganin zai wahalarda kanshi a banza yasa ya mik'e yashiga bathroom d'in da ke cikin office d'inshi ya wanke fuskarshi yafito yana goge fuskar tashi da k'aramin towel sai lokacin yatuna wayoyinshi da ke rufe yana budewa text message suka fara shigowa rututu na Zuhura yafara karantawa _Honey na kira duka layuka ka a rufe just to tell you how much I missed you in kayi switch on please ka kirani ina matuk'ar son naji sanyayiyar muryarka Mae sanyaya min zuciya. ILYSVM_
Ansar ya tabe baki yacigaba da karanta text d'in yana cin karo da na Anaal yafara doka, murmushi kamar Wanda akayi albishir da kujerar makka tun yana murmushi sai ga bawan Allah yana kwasan dariya shi kadai, ya duba wrist watch d'in hannunshi remains 15 minutes a tashi su Anaal daga school ya mik'e ahanzarce yadauki key yajefa sama ya chafe ya bud'e fridge yaciro gwagwanin coke Mae sanyi gaske yafice.

Yaja mota cikin nishad'i yana driving da hannu d'aya, d'ayan kuma yana rik'e da coke lokacin zuwa lokacin yana kur6awa a haka ya iso gate na school d'insu yanemi wajen da yasaba tsayuwa ya yi parking.
Ya zauna zaman jiran a tashe su.

_2:15pm_
Anaal tana fitowa ta hango shi saida gabanta ya yanke yafad'i duk wannan uban sauri da take yi tunaninta ta sulale ba sai tajira shi ba koda zai zo ya tarar ta yi tafiyanta, sai gashi haqarta bai cima ruwa ba.

 'kamar wance za ta fashe da kuka ta nufi wajenshi kunyarshi takeji matuk'a jin take kamar za ta nitse k'asa cikin tatata tak'arasa hannunta na rawa ta bud'e k'ofa bata bari suka had'a ido ba cikin laulausar muryarta tace _ina wuni Ya Ansar?_
Batare da ya amsa ba ya kur6a coke d'inshi kallonta yake yi ba ko kiftawa, yayinda ita kuma ta sadda kai k'asa tana wasa da yatsunta. Tsawon lokacin suka dauka ahaka shi bai tanka ta ba ita kuma bata k'ara cewa komai ba.
Anaal so take ya tayarda mota tun kafin su zeenat su fito tasan halinsu da fassara yanzu nan za su fassara ta da cewa saboda Ansar ta sulalo bata jira su ba.
Kamar za ta kurma ihu ta kalle shi, ta sauke idanunta a fuskarshi eye's ball d'inshi suka had'e da nata yasauke gwangwani coke ya cije lips yana kallonta turo baki tayi _Ya Ansar Dan Allah kayi hak'uri ka ja motar nan banaso su zeenat su gani_
   ''Ya tabe baki daga bisani ya yi murmushi ya yiwa mota key suka halba kan titi, ya kur6i Coke ya dube ta ta k'asan ido ya mik'a mata raguwar Coke d'in _Anaal, Anaal, Anaal sarkin kunya kar6i Coke ki jik'a mak'oshi ki ko zai rage miki wannan kunyar_

Uhm! Tai ajiyar zuciya kallo d'aya tayiwa gwangwanin ta kauda fuska, tasake takurewa cikin hijabi.
Ke kan yarinyar nan bakida mantuwa abunda yafaru tun safe ace har zuwa yanzu ba ki manta da shi ba. Lokacin da naga text naki dariya naci sosai
"Ta galla masa harara harda su murgud'a baki, tai masifar burgeshi musanman yadda d'an k'aramin bakinta yajuya.
Yasake mik'a mata Coke _na k'oshi_ tafad'a a gajarce, kina nufi ba za ki sha raguwa na ba? kina kyankyamin aza bakinki a inda na aza nawa?
''Ta kalle shi da mamaki tana nodding head nata, Uhm.... Uhm..ni ba haka nake nufi ba.
Mekike nufi da kin k'oshi?
Cikina a cike yake abinda nake nufi kenan.
Uhm... Anaal kenan abinda ki ka fad'a azahiri bashi bane a bad'ilinki jikina yabani cewa kyankyami na ki Ke, da Auwal ne yasha abu yarage miki da bara ki ce ba za ki sha ba.

Wai ni Lucky har sai yaushe zan maye miki gur6in Yaya Auwal ne? Duk wani hanya da zabi na zame miki d'an uwa na bi amma ke sai kora da hali ki ke mun, ayanda nakeji ko abincin da yafito daga bakinki zan iya ci saboda inajinki ajinina tamkar Basmah.
 Ba shiri ta katse hamma da takeyi tashiga kallonshi tai yi murmushin ta mik'a hannu yabata Coke saida ya yada idanunshi akan fuskarta kafin yabata.
Tayi Bismillah ta kur6a sau d'aya sai kawai tashiga jujjuya gwangwani saida ta d'auki ''long time kafin tak'ara kur6awa a karo na uku tana kur6awa sai tayi kamar takware, ta mayarda na bakinta cikin gwangwani tafara tarin karya, duk abunda take yi Ansar yana kule da ita yashiga yi mata sannu.
_sannu Lucky ko na tsaya ne na nemo miki ruwa?_
Girgiza kai tayi ya kar6e coke d'in daga hannunta yi hak'uri my Lucky na matsa miki kinsha abunda ranki bayaso gashi garin haka har kin kware.
"Tayi murmushi batare da tace komai ba daga haka ba Wanda yak'ara magana.
Ga mamakinta sai taga Ansar yana shan Coke d'in ba abinda yasha mishi kai, a rikice takira sunanshi ya Ansarrr! Wannan coke da ka ke sha yalalace na mayarda na bakina ciki.
"Ya zaro ido na baki fa?
Eh! Tafad'a tana kallonshi.
Shine ba ki fad'a mun ba?
"A tunanina ka ga lokacin da na mayarda shi.
Wannan tunaninki ne ni ba abunda nagani yasake kur6a abinshi, da sauri tace ''please Ya Ansar Kadàina sha Àllah nasaka na baki a ciki.
"Ya tabe baki aikin gama yariga ya gama duk abunda yakai ciki, ya zama nama k'azantar da bakagani ba tsafta ni ba ruwana Coke nasha ba yawun bakinki ba.

"Anaal ta rausayar da kai tana kallonshi sauk'in kanshi ya burgeta matuk'a suna isa inda yasaba ajeta ya yi parking, alokacin yak'arasa shanye Coke d'inshi yasauke glass yajefarta gwangwani.
Yadawo da ganinshi kanta, ita ma shi take kallo yasake mata shu'umin murmushi ya akayi ne an Lucky nah? Naga sai wani kallona ki ke yi ko nayi miki kyau ne?
''Tayi murmushi had'e da cewa ina yaba kirkinka ne a zuciyata. Na jima banci karo da mutum Mae kirki irinka ba.
 Ga ka da sauk'in kai komai naka Mae sauk'i ne ba ka d'auki rayuwa da zafi ba, na gode da irin kulawarka akaina ina Mae maka albishir tuni ka maye gur6i yaya Auwal a zuciyata yaya Auwal yariga ya6ata ko su Abbah sun fitarda da rai sake ganinshi shekaru 16 da 6atanshi tun ina 'yar shekara 1 ya6ata har yau ba Wanda yaji labarinshi, tana k'arasa magana idanunta suka ciko da hawaye.

"Girgiza kanshi yashiga yi karki yi kuka Lucky shaquwarmu daga Allah ne, nai miki alqawalin daga yau zan tayaki da addu'a indan yaya Auwal yana raye Allah da yabainarshi.
   _''Ameen_ tafad'a tana kallonshi lokaci d'aya suka sakewa junansu murmushi ta bud'e k'ofa tafita yabita da kallo har ta6acewa ganinshi sannan yaja mota.

_zuhra_
*4:00pm*
Zuhra na kwance a parlour akan kujera tana chat wayarta tayi ringing, tayi picking had'e da karawa akunne _Hello Leebeauty!_ kinsan banida wadatace k'udi amma zan kira Ya Ansar yakaimu ta d'an yi shiru tana saurare abinda leebeauty take fad'a tayi dariya haba! Leebeauty kema kinsan k'udi ba matsala bane, a wurin Ya Ansar kedai ki shiriya da wuri za mu biyo gidanku mu d'auke ki.

_okay ya yi kyau sai nazo_ ta kashe kiran tashiga dialling number Ansar ringing d'aya zuwa biyu Ansar yadauka _Hello!_ yafad'a akasalance
Hi! My luv yakake ya office?
_Lafiya Alhmdllh_
Ya akayi ne?
Dama my luv shopping nakeso ka kaini kayan kwalliya na sun k'ara  banida k'udi a hannuna kuma Alhaji ya yi tafiya.
Ansar ya girgiza kai yana mamakin zuhra ita dai bata buri da yawuce yadinga kashe mata kudi, gashi bata jin maganarshi kuma ba gode mishi takeyi ba.
 shikenan naji zan zo na kai ki da k'arfe nawa za ki je shopping d'in?
Ka zo around 5:30pm ya yi.
Okay ba matsala sai nazo
Ya yi hang up.

_5:30pm_
A gidansu zuhra ya yi masa ya tsaya bakin gate ya gaisa da Abbah, sannan ya zarce parking lot ya yi parking yaciro wayanshi ya kirata yafad'a mata yazo saida ta6ata 8-10 minutes kafin tafito sanye cikin wata arniyar fitted gown na material golden colour shara-shara da shi yalafe a fatar jikinta wuyan rigar shown me your back ne anjara duwatsu a Ingiya kamar sark'ar wuya {necklace} a wurin shown me d'in.
 D'inki ya yi kyau saidai babbar matsalarshi yanda ya baiyanar da ilahirin surorin jikinta k'afarta sanye da hills blue in colour,hannunta d'auke da wata 'yar k'aramar purse ita ma blue ta yane kanta da d'an siriri mayafi har ana iya hango dogon kiston attachment d'in kanta, ba laifi tayi kyau matuk'a a fuska saidai sutura jikinta ce za ta dusashe kyaun da tayi.
Domin duk Wanda yasan ciwo kansa sai ya yi tir da ita, yayinda samari 'yan bana bakwai za ta tafi da ruhi da gangar jikinsu musanman yanda Allah ya yi mata kira ta jiki zuhra akwai diri hips d'inta kadai abin kallo ne ga gaba ga baya.

''Tana rausaya kamar ganye bishiya yana kad'awa alokacin iskan damina, tun kafin tak'araso Ansar yafara cika yanayi batsewa ranshi ya yi mugun 6aci wai matar da zai aura ce wance za ta zame masa uwar 'ya'yanshi anan gaba ita ce cikin wannan bak'ar shiga.


Jeeddah Aliyu
[03/05 9:17 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*17*

Hankalinta kwance ta bud'e mota tashiga k'amshin turare ta yadak'i hancinsa ya lumshe idanu Wanda suka kad'a sukayi jajir saboda 6acin rai.
_sorry my luv na barka kanata jira_
Harara ya zuba mata cikin hargowa yafara magana wai ke zuhra wace irin yarinya ce me taurin kai da naci?
Sau ina gayamiki banaso irin banzaye tufafin nan da ki ke sakawa?
Na fahimcin kinfiso sai na nuna miki 6acin raina k'arara akan wannan mummunar d'ab'ia taki....Dallah dakata Ya Ansar akan wane dalilin za ka dinga yi mun ihu aka?
Aure na ka ke yi da za ka kafamin doka na bi, duk tsiya da azarbabinka ka jira har a zarga min igiyoyin aurenka alokacin ka ke da iko akaina ba yanzu da nake gidanmu ba don haka ka saurara mun.
  ''Ke ashe bakida tarbiyya har ni za ki kalla ki gayawa magana?
An gayamaka magana kai da karufe ido kafad'amin son ranka fa? Ko angayamaka tsoro nakeji? Idan ma haka kadauka kayi gaggawa ka sauke domin ni ba uban da nake tsoro.

Zuhra! Yadaka mata tsawa had'e da nunata da yatsa kallon wulaqancin take aika masa tana yatsina da tabe baki.
''Ki natsu ki saita tunaninki dosashiyar kwakwalwarki ta hasko miki, da Wanda ki ke magana kada garin rashin tarbiyyarki ki furta abinda zai zame miki danasani marar amfani.

"Idan akan irin wannan cin zarafi da ka ke min ne Ya Ansar ba zan jin d'ar ko shakka furta maka, kowace irin kalma ce tafito daga bakina balle har nayi danasani. Ka bi ka takurawa rayuwata ka hanani shakat ni ba iskanci nakeyi ba balle kace ina wannan shagar ne don nasami customers ko akwai uban da yata6a gayamaka yaga k'ato akaina?

Wani irin k'ololo ya tokarewa Ansar a mak'oshi yasaki baki da hancin yana, kallon zuhra bai ta6a tsanmani rashin mutuncin zuhra har ya kai haka ba.
Zafin zuciya yadebe shi ya wanka mata bahagon mari sai da taga wuta jahanama{lol ta bakin yara} ya bud'e k'ofa azafafe yadank'o hannunta yaciro ta daga mota ya yar6e ta waje da6ass.....tayi fad'uwa 'yan bori.
''Tir! da wannan rashin tarbiyya naki tir! Da wannan halin naki wallahi ayau zuciyata cike take da nadama furta miki so tabbas na yarda da 'yan magana da suke cewa so makaho ne{love is blind} cikin hukuncin ubangiji yaji tausayina ya haska mini ganina. Idanu na sun waye daga makata da na shiga, ba ki dace da rayuwata ba wallahi zuhra ba ki dace da zama uwar 'ya'yana ba.

Zuhra ta mik'e da kyar idanunta sun canza launi hawaye na zuba kamar anbud'e famfo bak'ar zuciyar nan ta ta, ta motsa idanuta suka rufe ruf yanda ka ke tunani ban dace da kai ba, Ya Ansar nima abin haka yake yanda ka ke nadama akaina nima haka nake nadama saninka arayuwa na tsaneka, Ya Ansar wallahi na tsaneka bana sonka I hate you kafita daga rayuwata, mari da kayimin Allah yasa isa banyafe ba mugu bak'in azzulumi Wanda uwarshi ta haifa ba jini Mae zuciyar fir'una d'an tasha asarare...... kukan kura Ansar ya yi yadank'e wuyanta yadinga zuba mata mari baki da hancinta na jini.
_subhanalillah!_ Muhammadu me nake shirin gani?
Muryar Abbah ce ta d'aki kunne Ansar yasaki zuhra ba shiri kunya ta lullu6e shi da sauri har yana tuntu6e yashige motarshi, yafizge ta da k'arfi yanufi gate wani abin takaici gate d'in arufe yake yafito a harzuk'e ya bud'e yak'ara fizgar mota da k'arfi.

Abbah yaduk'a gaban zuhra tashi, tashi zuhra me yahad'aki da shi?
Domin wannan ba halin Muhammadu bane yi hak'uri ki tashi.
Haushin Abbah yaturnuk'e zuhra ba don da tana ganin girmanshi ba da ba abinda zai hanata fad'a mishi maganar da har ya mutu ba zai manta da ita ba. duk da haka bata barshi kara zube ba saida ta zabga Mae tsaki ta mik'e tana kuka mai sautin gaske tanufi cikin gida.
 Tana Shiga main parlour ta zube tashiga kururuwa _wayyo ni Allah na shiga uku na lalace wayyo bakina hancina_
Da gudu Hajiya saudat da Nazeeya suka fito daga rooms d'insu tsananin tashi hankali ya baiyana a tare da su har suna had'a baki ta hanyar watsawa zuhra tambaya meke faruwa ne zuhra?
Accident ku ka yi ne?
Hajiya saudat ce tak'ara watsa mata wannan tambaya.
  ''Zuhra takasa amsa tambaya ko d'aya sai birgima da gunjin kuka ta ke yi.
Da kyar da sud'in goshi Hajiya saudat ta ciyo kanta tadaina kuka.
Tana shassheka tashiga kwararowa Hajiya abinda yafaru tana dasa aya Hajiya saudat da Nazeeya suka lailayo ashar kamar masu fad'in karatu suka aikawa Ansar.

Dama ya lafiyar kura Hajiya saudat masifafiyar mace ce 'yar tijara tun tana yarinya yara suka laqa mata suna Sauda 'yar bala'i in tana fad'a har da bakinta ke kunfa kamar tasha omo.
   ''Akan 'ya'yanta da uban kowa za ta iya karawa ko ubansu bata yarda yakai hannun akansu ba ballantana wani banza Ansar lallai Ansar ya tsokano tsuliyar dodo.

Jakkar uban nan duka tun kafin aure lallai Ansar yanuna min shi d'an tunkiya ne, don tsabar kazar uba zai ware dantse yadake ki a cikin gidanku ni tun da nake duniya banta6a jin wannan abin uban ba duk kwarewa iskanci irin na d'a namiji sai akai mishi mace a gidanshi yake dukanta. Sai ga wannan d'an k'ashi bishi abin kazar uba yakafa tarihi ga 'yata ke Nazeeya bani wayata na kira uwarshi naji ita ce tabashi k'arfin guiwa dukan 'yata tun kafin aure.

    Jikin Nazeeya na rawa tadauko mata waya tana Mae cigaba da masifa da kumfar baki tasa kiran Mum Fatee, tana jin mum Fatee tad'aga kiran nata bata ko tsaya amsa sallama da gaisuwa da take mata ba, tashiga 'yayyafa ruwan rashin mutunci wato Hajja fatee da saninki Ansar ya zo har gida ya yiwa zuhra dukan akawo wuk'a?
   ''Haba Hajiya saudat wannan wane irin magana ne? In rai ya6aci hankali akesawa yanemo shi ta ya Boy zai daki zuhra da Sanina?
Kuma ita zuhra da tace da ke Boy yadake ta shin kin tambaya ta dalilin dukan nata?
''Kan ubanan lallai Hajja fatee kin cika cikakkiyar 'yar reni wayo d'anki ya sauke k'arfin da Allah yabarkace da shi akan  'yata don tsabar wulaqancin kice na tambayeta dalilin. Toh ba za'a tambayeta d'in ba wannan ae son kai ne in har ke ba za ki tsawata masa ba zan tabbatar miki ni uwace da ba za ta lamunce aci zarafi 'ya'yata ba, wallahi sai na d'auki mummuna mataki akansa sai ya gane ba irin 'ya'yana ake duka a zauna lafiya.

''Mum fatee ta ja tsaki mtcsww! Ke ni saurara min banda k'addarar so me Boy zai yi da tsatsonki 'ya'ya Sam ba tarbiyya sun lalace sun bandare, ae ke sa'a ki kayi da har Boy yafurta kalma so akan fitsarariyar 'yarki.

Au! Haka ma za ki ce Hajja fatee? A maimakon kibani hak'uri sai ki buge da fad'amin maganganu banza?
Eh! An fad'amiki d'in ko kindauka ke kadai ce ki ka iya yankar k'auna da tijara?
Shikenan Hajja fatee ki zuba ido ki ga irin hukuncin da zan dauka domin 'yata ba jaka bace balle wani k'aton banza majiyi k'arfi yadinga dukanta.
Kafin mum fatee tabata amsa har ta datse kiran tana huci kamar kubunbuwa.


Jeeddah Aliyu
[05/05 8:45 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*18*

Ansar yana tuk'i{driving} yana had'a gumi duk da Ac mota da ke bud'e bai hanawa zufa tsatsafowa daga, sasssa jikinsa ba.
Gudu yake shararawa kamar zai tashi sama bai ta6a shiga 6acin rai kwatankwacin wannan ba, tsanar zuhra ta baibaye shi a k'asan zuciyarsa da raguwar sonta.
   "Yana isowa gida a fusace yashiga  danna horn kamar zai tashi unguwa, da gudu maigadi yabud'e masa gate yanufi parking lot ya yi parking batare da ya kashe wutar mota ba yakifa kansa a steering yasoma tunanin, ranar da yafurtawa zuhra Kalmar son Kalmar da a yanzu tazame masa tamkar dafin maciji ya yi nadama marar iyaka jin yake ina ma zai iya komawa baya da ba abinda zai hanashi goge wannan kalma saidai kash! Abinda yake gudu yariga yafaru.

Kiran sallar magarib yadawo da shi natsuwarshi jiki ba kwari ya kashe mota yafito yanufi masallacin, bayan sallar isha yadawo gida kaitsaye part d'inshi yanufa ya zube parlour ya yi matashi{pillow} da hannayeshi yak'urawa pop ido yana nazari ta ya zai bar zuhra batare da hakan yata6a Zumuncin iyayyesu ba.
Domin ahalin yanzu bayajin zai iya aurenta gaba d'aya tafice mishi arai.
Basmah tayi sallama bai iya amsa mata ba saima zuba mata rinanun idanunshi da ya yi, jiki na rawa Basmah tak'arasa wajenshi ta zube guiwowita gabanshi ta rik'e hannunshi meke faruwa da kai ne Ya Ansar banta6a ganinka cikin wannan yanayin ba?
Shiru ya yi yakasa bata amsa domin wani Sabon tafarfasan zuciya yakeji. Kayi min magana Ya Ansar a ciki na baro Mum tana fad'a ita ce ma ta aikoni na kira ka sai gashi na tararda kai cikin wannan yanayin, ka sanarda ni abinda yake faruwa ''please.

Ansar yasauke gwaron numfashi mai d'auke da wata zazzafar iska
Basmah nayi danasani marar adadi na furtawa zuhra kalmar so. Ashe yarinya nan batada mutuncin? Rashin tarbiyya ya yi mata katutu wai har ni zata zaga a cikin gidansu.
Zaro ido Basmah tayi ranta a6ace tafara magana, zagi fa kace Ya Ansar?
Kwarai kuwa zagi Basmah infact ba kalan zagin da batayi min ba. Har ce min tayi an haifeni ba jini.
Ran Basmah yak'ara sosuwa ba shakka zuhra batada mutuncin ita yanzu ko mai zaginka tagani ba sai inda k'arfinta yak'are ba, shine don tsabar rashin tarbiyya za ta ware k'aton bakinta ta zage ka. Wallahi sai na nuna mata kafi k'arfi a zage ka sai na nuna mata k'aryan rashin kunya takeyi sai nacicin mata mutuncin wallahi.
Sai lokacin Ansar yaji ranshi ya yi sanyi  yasaki murmushi yacigaba da kallon Basmah da takarkare tana ta faman zabga fad'a.

Matse hannunta da ke cikin hannunshi ya yi ya ja dogon hancinta c'mon 'yar lukuta ni basanki da fad'a ba ki kyaleta kawai ni nasan matakin da zan dauka akanta.
Girgiza kai tayi ka dubi girman ''Allah Ya Ansar ka fitarda yaya zuhra daga zuciyarka ka manta da ita tun fil'azal batadace da kai ba. ka d'aukar min alqawalin za ka barta bari na har abada wallahi banaso ka aureta tak'arasa magana hawaye na zuba daga idanunta.

''Rud'ewa Ansar ya yi yad'ago fuskarta yana kallon cikin idanunta, haba! Basmah meyasa za ki zubarda hawayenki akan wata banza?
Ni nace inason zuhra ba wani ya tilassani ba nayi miki alqawalin Basmah komai wuya komai runtsi ba zan auri ta ba koda kuwa sonta ne sanadin bari numfashina.
Dad'i ya baibaye Basmah ta k'ank'ame Ansar tana zuba mishi godiya ita dama ta tsani Zuhra Sam basu shan inuwa d'aya saboda d'an banzan girman kanta da d'agawa ta dauki kanta wata tsiya alhali ita d'in ba kowa bace.

Ansar yacireta daga jikinshi ya mik'e had'e da rik'o hannunta, a tare suka Jera zuwa cikin gida a parlour suka iske mum fatee suna had'a ido da sauri Ansar ya sukunyarda kai zo nan Boy!
Kanshi na k'asa yak'arasa wajenta zai zauna k'asa ta katse shi zauna anan tanuna kusa da ita Cikin laushin murya Mum tafara magana Boy meyasa ka biyewa son zuciyarka kayiwa 'yar mutane duka?
Shin ko kasan Hajiya saudat takirani sai abunda bakinta ya manta?
Boy banaso harka da tashin hankali maganin bari kar afara tun farko bason wannan al'amarin nakeyi ba. kanace sai ita dama shine burin Mahaifinka shi a dole mai son zumuncin ba wani kwakwaran bincike halayen yarinya ya goyi bayanka, alokacin duk ilolin da nake zaiyana masa akan zuhra sai ya yi biris! Da ni daga karshe sai ya yi min kashedi muddin inason zaman lafiya na iya bakina akan aurenka da zuhra, wannan yasa najawa bakina linzami domin fad'a da yafi k'arfinka tilass! Ka mayarda shi wasa.
Gashinan tun kafin tafiya tayi nisa kafara dukan 'yar mutane.
Sai lokacin Ansar yad'ago zai yi magana Mum ta katseshi ta hanyar d'aga masa hannu, banason jin komai daga bakinka wane irin nuni ne ban maka ba? kana tsirowa da zance zuhra ka keso, daga ni sai kai sai ubangijin da ya halicemu nasaka d'akin nasawa k'ofa key don kada kowa yajimu nace, da kai zuhra batadace da kai ba. Kaje kanemi saleema 'yar gidan former controller 'yar abokin Mahaifinka kuma 'yar aminiyata Hajiya Maryam duk duniya banida aminiya kamar Maryam amma ka watsa mun k'asa a ido kace bakasonta tacika fari kamar zabiya  zuhra ita ce dai-dai kai.

''Don haka wallahi ba ruwana duk tsuntsu da yakira ruwa shi ruwa kan doka, yanda kaje har gida ka dake 'yar mutane haka za ka wanke k'afa kaje ka bata hak'uri ita da mahaifiyarta, domin ina ji maka tsoro wannan maganar taje kunnen tijarare ubanka, wallahi ba zai maka da dad'i ba.
''Ansar yarik'o hannunta ya yi k'asa da murya Mum ki yi hak'uri ki bani dama na fad'a miki dalilai na nason barin zuhra ba wai don banasonta ba
Har yanzu da raguwar sonta a zuciyata.
Mum ta dubeshi ta tabe baki toh! Tunda da raguwar sonta a zuciyarka ba sai kacigaba da hak'uri da ita ba.
Mum ba zan iya ba wallahi tsanar da nake mata tafi son da nake mata yawa a zuciyata. Mum zuhra ba matar aure bace kuskure ne nariga nayi tun farko da nakasa karanta halayyenta.

Ba wani kuskure da kayi Boy tun asali son zuciyarka ka bi lokacin da nake zaiyane maka munanan d'abi'unta me kace da ni?
Ansar ya yi shiru yakasa amsawa.
Nace me kace da ni?
Saida yasauke ajiyar zuciya yadawo kalar tausayi sannan yace cewa nayi _*SO* ba ruwanshi da hali ko d'abi'u muradi zuciya tasamu amincewa zuciyar da takeso_
A nawa shirme Mum tunda inaso zuhra ita ma tanasona fiye da son da nake mata d'abi'u da halayyamu za ta iya dawowa d'aya ashe ba haka bane.
     ''Boy ni ba abinda zan maka karka manta a tsarin Mahaifinka da d'an uwanshi suka yi, kafin azumi ko kuma bayan sallah za su aurarda Ku bakin al'kalami yariga ya bushe.
   "Ansar yadafe kai jin yake kamar ya kurma ihu, Basmah ta kalli Mum tace Mum bakin al'kalami bai bushe ba domin Ya Ansar shi yakeyi auren a yanzu kuma yace bayayi a wannan zamani ko 'ya mace andaina yiwa auren dole balle d'a namiji, Mum ansha taro za'a daura aure ango yace yafasa dole a hak'ura jama'ar da aka tara a basu hak'uri shikenan kowa yakama gabansa ballantana wannan ba'a tsayarda takamame lokacin ba.


Jeeddah Aliyu
[08/05 8:17 pm] Jeeddah Aliyu: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*19*

Mum ki fahimcin inda Ya Ansar yadosa a halin yanzu bayason zuhra sonta yafita daga, zuciyarsa ke ce mutum ta farko da yadace ki goyi bayansa yanemawa 'ya'yansa uwa tagari amma wallahi mum zuhra Sam bata cancancin zama matar Ya Ansar ba kaddara ce tasa ya furta mata Kalmar so.

Ke! Dallah rufemin baki in har ke kinmanta da waye ubanku ni ban manta ba, in har ke bakya guje masa masifar da bala'in mahaifinku ni ina guje masa, Boy karka bari shed'an ya yi tasiri akanka har Mahaifinka yaji wannan maganar wallahi zai yi masifar sa6a maka watakila har tashafe ni karufawa kanka asiri karufa mini ni uwar da na haifeka.
''Da kyar Ansar yafurta shikenan Mum komai yawuce zan je na basu hak'uri, cike da farin ciki Hajja fatee tashiga sa masa albarka.
Ansar yafad'i haka ne don kawai ya kwantarwa Hajja fatee da hankali ba wai hakan ne har cikin ranshi ba.
Ya mik'e jikinsa a mace yanufi part d'inshi yayinda Basmah tanufi kitchen ta had'a mishi abincin Hajja fatee tabisu da kallo tana mamakin irin tsananin shak'uwar da ke tsakanin Ansar da Basmah.

_Anaal_
*9:33pm*

Tana zaune a parlourn Granny abin duniya yataru ya yi mata yawa, rashin ganin Ansar ba k'aramin halin damuwa yajefata ba, gashi har _9:33pm_ tayi tasan kuwa a irin wannan lokacin mayuwacin abu ne Ansar ya zo tadauki wayarta tayi checking balance taga ko na plashing batada sai kawai ta haddace digit d'inshi tayi masa please call me''
Alokacin yana kwance a parlour yajingina rabin jikinsa a kujera yaji shigowar text a wayarshi da ke ajiye akan ''center table kallo d'aya ya yi mata yadauke fuska, yawan kawo haske da takeyi tadauke yabashi haushi Basmah tayi sallama tashigo d'auke da tire mai d'auke da foodflask ta ajiye a gefen center table a kasalance yafurta Basmah miko min wayata.
Wance daga ciki tafad'a tana kallonshi da yatsa ya yi pointing d'in wance yakeso ta tadauko masa.
Tadauko ta mik'a masa yana yadanna text d'in yaga Anaal ce tayi mishi please call.

Hannunshi har makyaryata yakeyi wajen kiranta, Anaal har tafitarda ran zai kira unexpected taji phone d'inta yadauki k'ara cikin zumud'i ta amsa kiran _Hello_ tafad'a cikin sanyi murya mai cike da damuwa.
   "Saida ya lumsashe idanunshi daga bisani ya bud'e su yakike my Lucky?
Lafiya lau tun d'azu nake baza idanu zuwanka gashi har 10:00pm ya kawo jiki banganka ba hope lafiya ce ta rik'eka?

Huh! Abubuwa ne sukayi min yawa amma gobe insha-Allah zan shigo ya Granny?
Granny tana d'akin watakila tayi bacci  naga tasha magani, kuma bacci yakesata sosai.
Ke kadai ce kenan?
Eh!
Ya gyara kwanciya can! K'asan mak'oshi yafurta nayi missed naki sosai sai kace ba d'azu da rana mu ka rabu ba.

''Anaal ta rausayarda kai ta kalli bakin k'ofar d'akin Granny taga ba kowa, tace nima haka Ya Ansar yau rana d'aya da ba ka zo da dare ba duk sai naji ba dad'i ko abincin nakasa ci.
Ansar ya yi k'ayatatcen murmushi had'e da cewa nima bancin abincin ba ban fahimci inajin yunwa ba, saida ki ka ce ba ki cin abincin ba kitashi kije ki zubo abincin ki zo mu ci tare.
Mamaki ne ya lullu6e Basmah ta yi zugun tana kallon Ansar sai aikawa kanta tambaya takeyi da wacece ya Ansar yake waya, da har tayi saurin gusarda b'acin ranshi da wuri haka?

 "Zaro ido Anaal tayi Uhm! Ya Ansar karka tsorata ni kadai ka ke nesa da ni ta wace hanya za mu ci abinci tare?
Ke dai kawai ki je ki d'ebo kuma karki kashe waya.
Uhm!
Anaal tashiga kitchen ahankali tafurta nashigo kitchen
Toh! Ki yi mana saving
Na bud'e foodflask.
Menene a ciki?
Tuwon semo ne da miyan kubewa.
Wow! Delicious ashe za mu ci dad'i?
Uhm! Haka dai kafad'a.
 ta zuba tuwon semovita Leda d'aya da miya ta bud'e roban man shannu Granny ta tsiyaya tadauko plate d'in da hannu d'aya d'ayan kuma na dafe da waya tadawo parlourn, kasan me?
A'a sai kinfad'a
Har da man shannun Granny na zuba.
_iyeee lallai yarinya nan za ki ci dad'i_
Zan ci ko za mu ci kana nufi kafasa cin ne?
Dariya ya yi no! Banfasa ba sai lokacin ya dube Basmah wance mamaki yahanata motsi, Basmah yi min saving mana.

Ajiyar zuciya Basmah tayi tad'auki plate tasa mishi ledan tuwon shinkafa fari fat! da shi tak'ara d'aukar plate mai zurfi ta zuba mishi miyan agusi taji stockfish.

''Ta6angare Anaal kuma bayan ta ajiye plate tanufi fridge tadauko ruwa had'e da cup tadawo ta zauna gaban plate tana sauraron Ansar da ke zayyano mata kalan nashi abinci.
Narke fuska tayi Wanda hakan yasa ta manta da wa take waya, tasa shagwa6a Allah Ya Ansar naka yafi nawa dad'i ni ba zan ci nawa ba naka zan ci.
Tashi zaune ya yi yana dariya da ke nuna tsantsan nishad'i da yake ciki, shikenan ki jirani zan zo yanzu nan na kawo miki nawa na kar6i naki.
Uhm! Uhm! Yi zamanka nima zan ci nawa ko ba komai nawa da man shannu, naka ba bu tak'arasa magana tana dariya mai ban sha'awa.

Huh! Kinsa yawuna ya tsinke amma ba komai nima zan yi manage da nawa, sai kifara ci kinsan kinfini k'atuwar loma.
''Tasa dariya na dai ji d'in.
shiyasa nafika kwari sai da safe.
Da sauri yace ina za ki tafi?
Zan ci abinci mana.
Karki kashe waya ki ci ahaka inaso naji karar shigar loma bakinki.
Dariya sosai Anaal tayi daga bisani tayi Bismala tafara cin tuwonta.
Jin tayi bismillah! Yasa Ansar ya wanke hannunshi yafara cin nashi, tariga shi k'oshi amma sai tayi mishi wayo sai da ta tabbatar da yacinye nashi tass! Sannan ta ture nata plate tana dariya tace _yeee nai maka wayo ko rabi bancinye ba_
Shima dariya ya yi ya tara hannunshi a robar wanke hannu Basmah ta zuba mishi ruwa ya wanke hannunshi.
Tayagi tissue ta goge mishi hannu _thanks my 'yar lukuta_ yafad'a kamar Mae rada duk da haka saida Anaal ta ji _wacece 'yar lukuta?_ ta watsa masa tambaya.

Saida ya yi murmushi kafin yabata amsa Basmah ce bara na bata Ku gaisa, ya mik'awa Basmah waya had'e da cewa Anaal ce za Ku gaisa.
Wani zaro ido Basmah tayi za ka yi tsanmani kwayar idonta zai yi tsalle yafad'o k'asa cikin kid'ima tafurta A....Anaal?
Ita ce mana kiyi magana kudaina k'ona min credit a banza yak'arasa magana yana harararta.

Cikin rawar murya ta gaisa da Anaal daga bisani ta mik'a masa waya yacigaba da magana da Anaal cikin nishad'i da Annashuwa sai kusan around 10:44pm, ya yi sallama da ita yajuya yana kallon Basmah wance ita ma shi take kallo ba ko kiftawa.
Ya yi murmushi yadai 'yar lukuta naga kina kallona kamar bak'auye yashigo birnin?
Huh..ba dole na kalle ka ba ka zo min da abin mamaki Mae rikitarda kwakwalwa. Yaushe alaqa Mae k'arfi irin wannan tashiga tsakanika da Anaal?
Saida ya yi ajiyar zuciya ya ajiye wayar da ke hannunshi ya rik'o hannayen Basmah yana kallon cikin idonta, wannan yakasance sirri tsakanina da ke ba za ki fad'awa wani ba.
Har sai lokacin da yadace ya yi da zan bankad'o sirri kowa yaji.
        ''Basmah tayi murmushi karka damu Ya Ansar tsakanina da kai sai Allah, wannan alqawalin ne na d'aukarwa kaina insha-Allah wannan maganar ba za ka ji ta a bakin kowa ba.
Basmah!
Na'am''
_Tun daga ranar farko da nayi tozali da Anaal zuciyata ta kamu da sonta so mai tsananin gaske har, nakanji a jikina sanadin sonta zan iya aikata koma menene domin na mallaketa ni kadai. Kada kiyi zaton kyakyawar fuskarta ce tajani wallahi ba ko d'aya domin ranar da na fara ganinta fuskarta na lullu6e da niqabi abu d'aya zan iya ce miki kyakyawar tarbiyyarta, kamun kanta, uwa-uba iliminta sune suka k'ara jefa zuciyata a tarkon sonta._
Basmah inason Anaal Sosai fiye da tunaninki rasata tamkar rasa wani sasshe ne a jikina, Babban farin cikina na kasance tare da ita har k'arshen numfashina.
Anaal ita ce ta dace da tsarina ita ce mace da nake mafalki na, mallaka ba zuhra ba. Kurciya da rashin sani su suka debeni har na furtawa zuhra kalmar so a yanzu nayi nadama had'e danasani marar adadi.

Zufa ya karyowa Basmah bata damu da ta goge ba saboda hannayenta na danke da na Ansar, ta rankwadar da kai tana kallonshi saida tagama karantarshi tass! Sannan tafara magana.

Jeeddah Aliyu

16 comments:

  1. Enter your comment...pls continue

    ReplyDelete
    Replies
    1. dan.allah.asmau.a-inakikaga.2o-din.pls

      Delete
  2. Pls sis ki taimaka ki turo nxt part,wani abun mamaki shine na ci karo da part 20~21 a wani page bayan babu anan da Allah kiyi wani Abu akai.

    ReplyDelete
  3. Healrun is a health news blog we provide the latest news about health, Drugs and latest Diseases and conditions. We update our users with health tips and health products reviews. If you want to know any information about health or health product (Side Effects & Benefits) Feel Free To ask HealRun Support Team.

    ReplyDelete
  4. Supplements For Fitness drugs. Since they are not classified as medicines, there will be no regulation of their distribution or production process. In general, there are no strictly scientific studies that assess their effectiveness and

    ReplyDelete
  5. Pilpedia is supplying 100 percent original and accurate information at each moment of time around our site and merchandise, and the intent is to improve the usage of good and pure health supplement. For More Info please visit Pilpedia online store.

    ReplyDelete
  6. For the purpose of learning digital marketing you have come to the right place my friend. You, yes you my friend can be the first person to join this amazing program and then learn about the ins and outs of digital marketing. Digital marketing is a growing field in the economy and the people in this Academy are experts at producing other experts who will master this subject and then start their own business by joining the facebook advertising page. This Quit 9 to 5 Academy Review will let you know everything there is to know about this subject and then you too can start a business.

    ReplyDelete
  7. This is another must read and one of the best hausa Novel HUBBUL YAQEEN http://share4world.com.ng/2019/03/24/hubbul-yaqeen/ enjoy free readings

    ReplyDelete
  8. Thanks for all your effort that you have put in this, It's very interesting Blog...
    I believe there are many who feel the same satisfaction as I read this article!
    I hope you will continue to have such articles to share with everyone!

    918kiss
    holiday palace
    red dragon
    pussy888

    ReplyDelete
  9. 6 Incredibly Easy Ways To Nd10x Review Better While Spending Less https://www.reviewengin.com/nd10x-review/

    ReplyDelete
  10. However, once you're familiar with all of your options, you can start narrowing down the types of marketing strategies that might work best for your business. A goal-oriented marketing plan to implement these strategies will help you determine the best ways to reach your audience and convert leads into paying customers. Social Media Marketing - The term 'Digital Marketing' has a number of marketing facets as it supports different channels used in and among these, comes the Social Media. The journal offers an important and critical platform for researchers, practitioners, entrepreneurs, policymakers, and educators to present and discuss their experiences and perspectives on important issues and current trends related to marketing activities and research in an online context. A business that uses ambush marketing will attempt to associate its products or services with an event that already has official sponsors. However, although SEO once involved adding keywords to your site for search engines to find, SEO in 2018 is far more complex and involves a much broader scope of considerations.

    In reality, it's very rare that a customer views an advertisement or visits your website for the first time and then immediately converts into a customer. Branded media is media that your company produces for the purposes of informing, entertaining, and engaging your audiences. Hubspot defines inbound marketing as a marketing strategy aimed at attracting customers through relevant and helpful content. As a small business, the most important thing to figure out is how you can get more prospects to convert into customers. Beyond that, there are a number of marketing strategies that can indirectly affect how your site ranks, such as Pay Per Click advertising and email marketing. Many of them may prefer to take things slowly and to stick with one or two basic forms of advertising, assuming that their business will evolve as time passes. 10 However, the more recognisable period as being the start of Digital Marketing is 1990 as this was where the Archie search engine was created as an index for FTP sites. Whether you're creating new site pages or firing up a few Twitter posts, you should use the same brand voice and tone to help create a more seamless experience for your target audience.

    As summer 2019 approaches, the digital marketing landscape that encompasses SEO, social media, PPC, content marketing and more is witnessing a dramatic shift. As marketing has evolved, though, brands are segmenting customers and displaying pages that more closely target their needs. From email marketing to content marketing, take advantage of Kajabi's advanced features to make your products more appealing to your target demographic. What's essential about content marketing is that you need to make your content valuable, relevant, and consistent to make it worth the time of those consuming it. But even if you operate a local-focused business, gaining more customers from foreign markets can increase your income and reputation. Customers today expect brands to cater to their needs with reliable information. Your individual blog posts are the branches that reach out into the corners of the internet and search engines. Every ecommerce store should consider blogging regularly to connect with customers and to rank better in search engines. https://www.reviewengin.com/5-best-online-marketing-tactic-with-no-or-very-minimal-expenses-in-2019/

    ReplyDelete
  11. That is true, regardless of who you are. I will cowl Weight Loss Diet Pills during this post. Fast Weight loss probably comes low on the list. Keto Power Boost This can be merely mind over matter. I said solely the truth. You must avoid the plain lose fat . I, externally, do not comprehend slim body. This is a manner to require advantage of obtaining slim body. I'll try this if I have to. It wasn't insightful.

    http://www.sharktankdiets.com/keto-power-boost/

    http://www.sharktankdiets.com/

    ReplyDelete
  12. 50 Pips A Day Profitable Forex Strategy

    Forex System Trading
    As a result, the Quantum Fund made billions of dollars and Soros grew to become often known as the person who broke the Bank of England. His feat can simply be featured within the list of the best foreign exchange merchants to follow. The forex market is present process steady evolution, and because the years go by, it is clear that the state of forex trading in nations will continue to endure change that may influence the markets. Have easy access to the major buying and selling hubs, with ability to open foreign currency trading accounts with brokers in these hubs.
    Using Technical Indicators To Develop Trading Strategies
    He can easily be considered as probably the greatest day merchants on the planet. A final ditch attempt to hike UK charges that had briefly hit 15% proved futile. When the UK announced its exit from the ERM, and a resumption of a free-floating pound, the foreign money plunged 15% against the Deutsche Mark, and 25% towards the US greenback.
    Trained by none apart from Ed Seykota, Marcus would later go on to mentor one other great dealer, Bruce Kovner. During the Ronald Reagan era of presidency, Marcus held positions of just about US$300 million in German marks. It may be said that together with banks, he was the biggest foreign money dealer in German marks at that time. Turning down a possibility to go to Harvard Business School, Tudor Jones went on to work as a commodities dealer in the NYSE. In October 1987, when the markets had been crashing, he managed to make a revenue of 62%, simply by holding brief positions.
    Babypips
    The foreign exchange market lends itself particularly well to automated trading, which is another excuse it has attracted a growing number of participants. Trading platforms at many brokerages permit for trades that can routinely be implement when certain value or market situations occur. "Swing merchants" might trade on market tendencies inside a interval of one day to every week. Traders may use a wide range of styles, relying on what's most snug for them.
    Trade Example: Sell Eur/usd
    Druckenmiller says that his buying and selling philosophy for constructing long-term returns revolves around preserving capital, and then aggressively pursuing profits when trades are going properly. and it shouldn't come as an excessive amount of of a surprise that this successful Forex dealer has ties to the subsequent trader on our list. In fact, Mr. Druckenmiller labored alongside him on the Quantum Fund for more than a decade. But Druckenmiller has established a formidable reputation in his personal right, efficiently managing billions of dollars for his personal fund, Duquesne Capital.
    Generally, these might affect the amount of time and depth of the activity they dedicate to trading during their week. Typically, the ratios might range from 1-to-1 to 1-to-5 (or extra), depending on the dealer's threat tolerance.
    Lipschutz also agrees with Stanley Druckenmiller's view that when you're considering tips on how to be a profitable trader in Forex, it is not dependant on being proper, and it is extra usually that you're wrong. Instead, he stresses that you should work out how to generate income when being proper only 20 to 30 p.c of the time. As well as being part of Soros' well-known Black Wednesday trade, Mr Druckenmiller boasted an incredible document of successive years of double-digit features with Duquesne, earlier than his eventual retirement. https://www.reviewengin.com/learn-how-to-do-affiliate-marketing-basics-of-affiliate-marketing/

    ReplyDelete
  13. it's now not private. i am thinking about setting up a personal discussion internet site on well-being. you could count on that i'm trying to deceive you here. we'll begin with this part first. I do distrust that I would love to mention more within the count of wellness. Matt wrote me in advance this week to ask if i have carried out any updates to my health critiques. well being is a common factor.
    https://www.nutrahealthpro.com

    https://www.facebook.com/nutrahealthpro

    https://twitter.com/nutrahealthpro

    ReplyDelete