Saturday, 31 December 2016

NI DA YAYA HABEEB 61_70

[31/12 9:14 am] aliyujeeddah: [15/11 8:03 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```70```

~~I'm sorry yaya Habeeb lokacin da ka Kira ina sallah.
 A Canada kuma Habeeb na kwance akan kujera a bakin swimming pool na takatafare Hotel d'in da yasauka ya shafi lallausar suma kanshi idanunshi a rufe yacigaba da magana da Haleesa _ranar Monday Mus'ab zai zo ya kai Imaan school ki shirya mata da wuri_
okay Haleesa tafad'a cikin siririya murya
_I hope ba wani matsala"?_
Haleesa tace nop
_Good Ina Imaan"?_
''Tana parlour tare da Hannah
_okay ki bata waya_
Haleesa ta mik'e da sauri tanufi parlour bara na kai mata
_karki yi hanging up yafad'a a kasalance_
''Imaan zo ki yi magana da Daddy da gudu Imaan ta taso ta k'ar6e wayan daga hannun Haleesa tasoma zubawa Habeeb surutu    ''Daddy kasiyo min biscuit da chocolate da elephant da kuma snake.
Murmushi Habeeb ya yi my Angel bara ki bari mu gaisa, ba kin fara wannan lissafi naki da baya k'arewa to naji duk abunda kike so zan siyo miki _promise to me za ki yi karatu sosai banda wasa kinji my Angel"?_
"Yes Daddy I promise you kai ma Daddy karka manta da alk'awalina
 "By God great bara manta ba ki gaida aunty Hannah ya yi hanging up.
Imaan ta mik'awa Haleesa wayarta ta kuma Isar da sak'on Habeeb wurin Hannah.
*********************
_4 Day's later_
Haleesa da Hannah na tsaye cikin kitchen Haleesa na yanka cabbage Hannah kuma, tana yanka albasa.
''Imaan tashigo da gudu rik'e da wayan Haleesa aunty ankira wayanki
Da sauri Haleesa ta k'ar6i wayan daga hannun Imaan, ganin sunan yaya Habeeb akan screen ya yi mugun jefata cikin rud'ani hannunta na rawa ta yi "received
_Hello_
Cikin tsawa yace ke! Dallah ki ba wa Imaan waya duk lokacin da na Kira ki sai kinyi wasting time d'ina yak'arasa magana had'e da Jan dogon tsoki.
Jikinta a sanyaye ta mik'awa Imaan waya tace yi ki magana Daddynki ne tajuya tacigaba da aikinta duk abunda ke faruwa Hannah na tsaye rik'e da wuk'a tana, kallonsu.
Ta tayi shiru tana nazari yanayi sauyin fuskar Haleesa alama ce da ke nuna akwai abunda Habeeb yafada mata Wanda yayi sanadi sauyawarta a lokacin d'aya tajuya wurin Imaan da ke ta fama zuba wa Daddy ta surutu.
 tace Imaan ki je parlour ki yi waya da Daddy, Imaan tafice tadafa kafad'a Haleesa karki 6oye min Haleesa domin ko kin 6oye min a matsayin shekaru da nakeda su zan iya fahimtar wani abu kinga kenan 6oyewa batada amfani, kuma na tabbata a halin da kike ciki kinada buk'atar abokin shawara.
Ta d'an dakata domin ta ji ta bakin Haleesa
''Hawaye suka cika idanun Haleesa cikin murya da ke nuna tanaso yin kuka tafara magana me zan 6oye miki Hannah''?
Iya sanina kinsan duk abunda ke faruwa tsakanina da yayanki har izuwa yanzu bata chanza zani ba.
    ''I known Haleesa but kema yakamata ki yi amfani da baiwar da Allah yabaki, ta 'ya mace ki janyo hankalin mijinki zuwa gareki.
A yatsine Haleesa take kallon Hannah daga bisani tace akan wane dalili zan 6atawa kaina lokacin in janyo hankalinshi gareni angaya miki ina sonshi ne"?
  ''Hannah ta girgiza Kai ko bakya sonshi nasan bara ki so aurenki ya mutu ko za ki so ki shiga layin k'anana zawarawa"?
       "Jikin Haleesa ya yi sanyi ta yi shiru tana kallon Hannah had'e da nazari kalamanta daga bisani tace Hannah ya kike so nayi shi da yake d'an namiji bai nuna ra'ayi akaina sai nice zan nuna gaskiya ni bara iya ba ke ni fa ko k'amshin turare yaya Habeeb naji sai gaba na yafad'i tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
 ''Hannah ta yi dariya tace ni kuma me ye laifi na da kike murgud'a min baki daga ke har yaya Habeeb bara Ku ta6a iya gujewa k'addarar da ''Allah ya yi nufi akanku duk wannan noke-noke za Ku gama ne kudawo kan hanya.
  ''Haleesa ta tabe baki kanki akeji na fahimce cewa bakida aiki yi shiyasa kike yunk'uri cusa mini d'an uwanki ba kuma zai ta6a samun matsayi anan wuri ta nuna k'irjinta da yatsa.
  "Hannah ta girgiza kai bata k'ara cewa da ita komai ba tacigaba da yanka albasa.
******************
_1 week later_
Around _2:00  o'clock_ na dare flight d'in su Habeeb yayi landing sa'eed ya zo ya yi picking nasu da yake part d'inshi yanada tazara da na Haleesa har washe gari  batasan yadawo ba.
 "Tun da asuba Haleesa ta falka bata k'ara komawa bacci ba saboda za ta shirya Imaan zuwa school _7:20am_ ta gama shirya Imaan
"Haleesa ta dube imaan tace bara naje na dauko miki launch box d'inki.
 Imaan tace aunty ba ki bani Chocolate ba
Na saka miki a schoolbag d'inki''
 a kitchen ta tararda Peter yana had'a breakfast peter ina lunch box d'in Imaan''?
Ya nuna mata da yatsanshi da sauri ta sunkuce lunch box d'in ta kuma rik'o hannun Imaan tanufi compound da ita saida suka kai parking space Imaan tasa rigima tana magana had'e da bubbuga k'afafu a k'asa _Allah aunty ni yau bara je school uncle Ezekiel duka na yake yi_
  ''Haleesa ta dafe goshi tasoma rarrashinta haba imaan a kullum za ki tafi school sai mu zo mota kike saka rigima kinga shiga mota Ku tafi zan kira uncle Ezekiel a waya ba zai dake ki ba kinji"?
Cikin jin dad'i Imaan ta daka tsalle sa'eed na ta fama yi musu Haleesa ta bud'e mata k'ofa oya zo ki shiga kada ki yi latti Imaan tashiga mota sa'eed ya ja _bye bye aunty ki had'a mini chocolate cake kafin nadawo_
Haleesa na dariya tace _bye babynaa zan had'a miki ke kuma ki yi karatu sosai_
Saida ta ga motarsu tafita gate sannan tajuya cikin gida.
Duk abunda ke faruwa tsakanin Haleesa da Imaan Habeeb Lamido na tsaye a balcony da ke sama yana kallonsu idanunshi na kan  Haleesa har ta6acewa ganinsa ya ja iska had'e da lumshe ido.
  ''Haleesa na shiga parlour taci Karo da Hannah sanya da sports wear's ke nake jira mu fita exercise
  Haleesa tabe baki bacci nakeji bara iya zuwa ba
Wane irin bacci Dan Allah ki zo mu je banaso "fat ya yi miki yawa kada yaya Habeeb ya auro 'yar shila.
  Mtww...Haleesa ta ja tsoki had'e da shigewa bedroom da kyar Hannah ta ciyo kanta ta amince suka fita compound bayan sun gama jogging suka nufi wurin snooker tun da suka fara buga wasan Hannah ce take winning saboda Haleesa ba iyawa ta yi ba in ta daki ball da stick sai ya yi tsalle yafad'i Hannah ta kwashe da dariya.
Habeeb yadawo daga jogging Bala na biye da shi tun daga main gate ya hango Haleesa da Hannah kaitsaye yanufi wurinsu Hannah nagani shi, ta washe hak'ora tuni Haleesa ta nemi natsuwarta rasa sai gumi ke tsatsafo mata.
Yaya Habeeb saukar yaushe"?
_Jiya da dare yafad'a chan k'asan mak'oshi_
Haleesa tasauke ajiyar zuwa wance ta janyo hankalin Habeeb yasoma yi mata kallon da ta tsana......

Jeeddah Aliyu🌹
[31/12 9:17 am] aliyujeeddah: [13/10 6:02 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```61```

Matuk'ar na kirga 3 ba ki fito ba wallahi zan kira Baffa a waya na Fad'a mishi abunda ki ke shirin aikatawa nasan duk iya shegenki kina tsoro Baffa"
Sosai Haleesa ta tsorota da jin furucin Aunty Juwairiyya ba shiri da mik'e ta bud'e k'ofa suna had'a ido da Aunty Juwairiyya wance ta cika ta yi fam cike da takaici ta gallawa Haleesa uwar harara d'auke kai Haleesa ta yi kamar ba ta ga Aunty Juwairiyya na harara ta, ta ra6a gefen ta za ta wuce cikin Zafin nama Aunty Juwairiyya ta fisgota ta  igizata cikin "bathroom koma ciki don gidanku ki yi Wanka ko kina nufi bara ki yi Wanka ba"?
Idanuta taf da kwalla tace to ni Wanka me zan yi"?
"Bansaniba Aunty Juwairiyya tafad'a a zafafe tacigaba da magana ta hanyar nuna tsanani 6acin ranta wallahi Haleesa ki kiyaye ni sai na yi mummuna sa6a miki idan ki ka sake kwatata irin Wannan shashanci so ki ke mutane duniya su zage mu ace mu yi miki Aure dole.
"Haleesa ta shar6e hawaye had'e da k'argame k'ofa kuka takeyi sosai har ta gama Wanka tana kuka, idanuta sun yi luhu-luhu tana fitowa Aunty Funke tafara aikin nata na tsatsara mata Make-up ta kece raini ta yi matuk'ar kyau Aunty Funke ta fito da "Wedding gown ash& black colour ta mik'awa Haleesa tace ga wannan ki saka Yatsine fuska Haleesa ta yi ta Wani turo baki da ya masifar K'ara mata kyau tace me zan yi da Wannan abar"?
Galala Aunty Funke ta yi da baki tana duban Haleesa "OMG! Ni kan banta6a gani "Bride da irin wannan hali ke da yakamata ki yi farin ciki  wannan fa ranar ki ce "Humm Haleesa tafad'a had'e da kyabe baki bata k'ara bin ta kan Aunty Funke ta juya tasanya inner wear's daga bisani tasanya gown d'in Aunty Funke ta rufe mata zip ta daura mata "black colour head sai ga Haleesa ta yi dass da ita tubarakallah masha Allah" Zainab da wasu school mate d'inta suka take mata baya har Zuwa "compound d'in da za'a yi kamu gidan yacika taf ba masaka tsinke yayinda 'yan "police bands su ka k'awata wurin da kid'ansu mai matuk'ar dad'i da ratsa Zuciya Hannah tayi "Parking motar ta ta fito ita da k'awaye ta ta nufi "high table wurin Amarya Haleesa ta d'a yi hugging in ta Haleesa tasaki Murmushi yak'e Hannah tace "Wow! Ki yi matuk'ar kyau matar yaya Habeeb bara na d'auke ki "Pic's na turawa yaya Habeeb nasan dole yarud'e ya nemi natsuwa da kwaciyar hankali shi yarasa tana magana had'e da haska Haleesa da camera wayarta yayinda Fad'uwar gaban Haleesa ta yawaita Jin takeyi kamar za ta kurma ihu har Hannah ta gama budirinta Haleesa na bin ta da ido, "2 minutes matar yaya Habeeb Hannah tafad'a had'e da juyawa tana dannar wayarta tabar Haleesa cikin halin k'unci da tsoron yadda zata rayuwa da Wani d'a namiji ba yaya Habeeb d'in ta ba.
Cikin Salon tafiyar k'asaita da son nuna ita d'in 'yar wani ce ta tunk'aro "high table wurin Haleesa yayinda muk'arabanta suka take Mata baya a yadda tashigo da kuma yanayi tsarin Make-up in ta za ka yi tsanmani ita ce Amarya tun kafin tak'araso Haleesa ta gane ta a zuciyarta tace me kuma wannan 'yar iska ta zo yi anan"?
Maryam da Zeely suka k'arasa wurin Haleesa sauran muk'arabanta suka nemawa Kansu matsugunni daf da kunne Haleesa ta kai bakinta kamar za ta Fad'a mata abun arziki duk da Haleesa ta tsorata amma sai ta dake ba na zo nan ne don na tayaki murna nassara auren d'an masu kud'in da ki ka yi na zo ne na yi miki albishir da mummuna tanadi da na tanada  miki zan bi kowace hanya domin gani na nisanta ki da duk Wani farin ciki da kike  kwad'ayi samu a gidan Yaya Habeeb nayi alk'awali sai na mayarda rayuwarki, tamkar ta kare da ke yawo akan bola yana neman mushe sai kin yi danasani aure abunda na ke ```SO``` tak'arasa magana had'e da Murmushi ta wani kwanto a jikin Haleesa tace Zeely haska mu da camera Zeely ta saita camera wayarta dauke su photo Maryam ta shafi checks d'in Haleesa da d'an yatsata tajuya tana Murmushi Wanda da Haleesa za ta k'ura mata ido kaitsaye za ta gano na yak'e ne ga kuma zafafa hawaye shinfid'e a eye's ball in ta Zeely ta Mara mata baya suka fice daga gidan dama ba kamu suka zo yi ba sun zo ne don su aiwatar wa da Haleesa gargad'i mai cike da barazana  Haleesa ta bi Mutane da ke Wurin da kallo tasauke ajiyar Zuciya mamaki da tsoro suka lullu6e ta k'irjinta na duka uku-uku kamar zai tsage gida biyu tafara zance zuci to ita wannan mai kama da "snooker stick me ta ke nufi da ni ne humm"?
Ba shakka wannan mugun nufi ta kala d'aya ne da na Habeeb Lamido a duk lokacin da ya yi nassara lullu6e Zuciyata da zazafa kalamai daga karshe sai ya wanke ni da Murmushi mugunta ita ma Wannan girl friend in shi haka ta yi min Wannan ke nuna tafiyar su d'aya lallai kuwa akwai kwaram tsakanina da ita in har shi Habeeb Lamido ina tsoronshi ae ita bana tsoronta zan nuna mata cewa ni ma ba kanwa lasa bace, sai na tabbatar mata kalamanta duk burgace da rashin samu nassara Haleesa ta yi kyaci cike da buri k'ara aragama da Maryam.
Sai daf da sallah magariba aka watsi daga kamu Hannah na manne da Haleesa sai faman zuba mata surutu take cike da gajiya da surutu Hannah Haleesa tace ni kuwa Hannah in tambaye ki mana"?
Hannah ta washe hak'ora had'e da daga kai''
Haleesa ta gyara zamanta ta yi k'asa da murya Hannah wacece doguwar yarinya nan mai sanye "dark blue lace wance na hango ki tsaye da ita ina nufi Ku na da alak'a da ita"?
Murmushi Hannah ta yi tace ta yi miki Wani laifi ne"?
A'a kawai na tambaya ne saboda na ga tana da kirki da son mutane kuma ga ta da saurin sabo Haleesa tak'arasa magana tana kyabe baki kafin Hannah tafara magana saida tasauke ajiyar Zuciya tace k'anwar marigayiya Salma ce matar yaya Habeeb wance tarasu.
Shiru Haleesa ta yi tana nazari kalman Hannah daga bisani tace amma ba wata alak'a tsakaninta da yaya Habeeb"?
Hannah ta tsorata da wannan tambaya da Haleesa ta yi mata nazari take yi irin amsa da za ta bata shigowar Aunty Juwairiyya ce ta yi sanadi katsiwa Hannah nazari da sauri Hannah ta mik'e tsaye Matar yaya Habeeb zan wuce gida me ye sak'onki a wurin yaya Habeeb"?
"Haleesa ta ja 'yar siririya tsaki karaf ta had'a ido da Aunty Juwairiyya gani irin mugun kallon da ta watsa mata batasan lokacin da tace "My regear to him"
Bata fuska Hannah ta yi haba! Haleesa gaskiya gaisuwa ta yi kad'an ki d'an k'ara da wata kalma wance za ta hana shi bacci ta k'are magana tana 'yarfe hannu  shiru Haleesa ta yi tarasa abunda za ta furta ga Aunty Juwairiyya ta kafe ta da ido jira take ta ji abunda za ta Fad'a chan dabara tafad'o mata ta rok'o hannun Hannah zo mu je na rakaki a hanya na gaya miki abunda za ki fada masa suna fitowa Haleesa ta mitsine mata hannu ashe bakida kunya Hannah a gaban Aunty Juwairiyya kike irin wannan Zance"?
Hannah ta kyalkyale da dariya tace cab! Lallai kuwa Haleesa kinada aiki domin yaya Habeeb mutum ne mai son rayuwa jin dad'i gaba d'aya tsarin rayuwarshi ta turawa ce gwara tun wurin ki koyi yadda ake tarairaya miji a gaban kowa ki yi fatali da wannan kunyar taki cike da takaici Haleesa ta ja tsoki "You know what"?
Hannah ta girgiza kai "Bana son yayanki Hannah babban wulak'anci da zan yi wa kaina na yi sake Zuciyata ta kamu da sonshi ballatana ina da yak'ini cewa Zuciyata bara ta6a son wani d'a namiji a dalilin na mallakawa marigayi Yaya Habeeb ita zan aure yayanki ne saboda Mahaifyarku ba wai don ina sonshi ba kamar yadda shima banida muhalli a zuciyarshi tana k'are magana ta juya cikin zafin rai da tafarfasa zuciya Hannah tasha gabanta karki biyewa Zuciyarki Haleesa tasa ki aikata abunda zai sanya mutane su gano cewa ba aure soyayya Ku ka yi ke da yaya Habeeb hakan wata dama ce da za ta ba wa mak'iyaki nasara akanki''
Yatsine fuska Haleesa ta yi daga bisani tace " I don't care what's they people say oll I know banaso Habeeb Lamido kamar yadda shima baya sona na tsane shi kamar yadda ya tsaneni that's oll tana kare magana ta ra6a ta gefen Hannah tashige cikin gida Hannah ba ta yi mamaki jin wad'annan zafafa kalamai daga bakin Haleesa, domin tasan za'a yi haka ta yaya mutane da ke jinyar Zuciyoyinsu ace za'a had'a su aure da wannan zance zuci ta ja motarta ta nufi gida saukin ta d'aya tuni ta sallame k'awayeta da yanzu a gabansu Haleesa za ta furta wad'annan kalamai masu zafin gaske.

```HABEEB LAMIDO ```

Habeeb da Mus'ab na Zaune a parlour madam Hindu da ke upstairs ga kuma tarin invitation card's na dauri aure zube a gabansu, Habeeb ya ja tsoki Mus'ab yad'ago ya galla masa harara wannan wane irin iskanci ne tun d'azu ka ke ta fama yi wa mutane tsoki aure nan fa ba dole bane ko yanzu za ka iya tunk'ara Mom ka fad'a mata ba ka yi har Mus'ab ya dasa aya Habeeb yana kallonshi ya tabe baki had'e da Shafa sumar kanshi kaitsaye Hannah tashigo ta nufi  kujera da Mus'ab yake Zaune shima yana ganinta yafara zabga Murmushi Yaya Mus'ab dama kana gidanan ba ka tafi ba"?
Ke ji ki da wani Zance Hannah ina zan tafi in bar wannan shashasha, yak'arasa magana yana nuna Habeeb da yatsa Hannah ta rufe bakinta tana dariya tasan  Mus'ab ne mutum na biyu da ke tilasawa Habeeb ya yi abunda bashida ra'ayi akai tana dariya tafito da wayarta ta yi "scrolling pic's in da ta yi wa Haleesa tace yaya Habeeb "take a look ta mik'a masa phone in  yana daura idanushi akan screen d'in wayar yaci Karo da fuskar da yatsana wawa tsoki ya ja had'e da cillawa Hannah wayarta saura kiris tafad'i Hannah ta chafe ya mik'e cikin angry face yace "how dare you show me dis nonsense" wannan ya kasance shine na farko na kuma karshe da za ki k'ara nuna mini fuskar wannan mummuna yarinya tashi ki bar parlour nan
Jiki na rawa Hannah ta tashi saboda ta tsorata da yadda Habeeb yataso mata kamar zai cinye ta Mus'ab ya tabe baki Habeeb yakoma mazauni shi zuciyarshi sai fama tafarfasa ta ke.

```2:45am```
Da gudu Haleesa tafito daga bedroom tana rik'e da k'asan wedding gown d'in da take sanye da ita tanufi parlour Habeeb na zaune akan 3 Star yana duba magazine kaitsaye tafad'a K'irjinshi ba bu shiri ya jefar da "Magazine  hannunshi yasaka ya matse ta gam har ya bud'e bakinshi zai yi magana  Ta had'e bakinta da nashi tana tsotsa tsawon lokacin tadauka tana rikita mishi "brain da salonta daga bisani ta kamo hannye shi tadaura a bayanta "very slowly take magana yaya Habeeb ka zuge min zip yana bud'e mata zip d'in ta cire gown in ta yi flinging da ita ta rage daga ita sai inners wear's tak'ara shigewa jikinshi idanu ta na lumshe take 6alle masa bottoms har ta yi nasara raba shi da rigar jikinshi Cikin zumudi manna bakinshi cikin nata daga nan Komai yacigaba da wakana Haleesa ta yi matuk'ar gigitashi ta rikita masa lissafi bayan komai ya kamalla yana k'ank'ame da ita kuka yake yi tamkar k'aramin yaro _"I love you leesa you are the only woman I loved "Tell me leesa you love me_ yafad'a yana lek'e fuskarta yatsine fuska ta yi yak'ara marairaice murya  "please leesa say it's you love me....kai! Habeeb wawa dukan da Mus'ab ya narka masa ya falkar da shi daga baccin sa mai cike da mafalki Haleesa  Habeeb ya mik'e zaune ya shafi fuskarshi  a tsorace yabi tafin hannnunshi da kallon " Habeeb Wacece leesa"?
Tambayar da Mus'ab yajefa masa kenan kallon mamaki Habeeb yake masa a kasalance yace ''I don't know''
"Look malam karka rena mini hankali ya kana mafalki yarinya har da saduwa da ita a mafalki kana mata kuka gaba d'aya ni ka hanani bacci   ita ya akayi tayi winning heart in ka har kana mata kuka wannan ke nuna you are already in love with her c'mon dude tell me who is this lucky girl"?
Habeeb ya share zufa had'e da hawaye a zafafe yace "I don't know anything About whats you are saying yana kare magana yadiro daga bisa bed yanufi "bathroom yabar Mus'ab sake da baki dama akwai wance Habeeb yakeso shine tsawon wannan lokacin bai ta6a Fad'a mini ba"?
"Huh! Habeeb shu'umi ne ko me yasa ya amince da za6in Mommy bayan akwai wata a zuciyarshi"?
Wacece Leesa me yasa Habeeb ya sadaukar da soyayya da yake mata ya amince zai aure Haleesa"?
Amma kuma a mafalki shi naji yana rok'o ta tace   Sonshi "which means bata sonshi shi kadai ke hauka shi Mus'ab ya kyalkyale da dariya Habeeb ya bud'e k'ofar bathroom yafito ya yi tsaye yana kallon yadda Mus'ab ke kwasa dariya a tsakiyar dare ya girgiza kai yanufi wardrobe yasanya jallabiya ya haye bed ya yi kwanciyarshi tun yanaji dariyar Mus'ab har bacci ya yi awo gaba da shi....

 Jeeddah Aliyu
[31/12 9:21 am] aliyujeeddah: [15/10 4:53 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```62```

Note:- _na yi kuskure a wurin fadar sunan garin a farko labari mai karatu zai ji nace yola a wani wurin kuma zai ji nace Yobe to yola ne ba Yobe da fatar za'a gafarce ni_

_10:30am_

"Habeeb na tsaye gaban "dressing mirror yana sharce suma shi da "Comb Mus'ab ya murda handle ya shigo ta mirror ya had'a ido da Habeeb ya kyalkyale da dariya da sauri Habeeb ya had'e rai ya d'auke kai yace banaso iskanci Mus'ab hali yanzu ka fara kaini bango tun dare jiya ka ke ta fama yi min dariya shin akwai uban da baya mafalki ne da za ka sakani a gaba kana dariya, Mus'ab yak'ara kyalkyalewa da dariya har yana dukan gefen bed abunda yak'ara harzuk'a Habeeb ya jefa masa comb in hannunshi ka ga Mus'ab na rok'e ka da ka had'a "luggage in ka ka bar min gidana Mus'ab ya tsagaita da dariyar da yake yi au abin har da su kora to ba ida zan tafi ina nan tare da kai har sai Amarya ta zo''
Amma kuma kaima kana da gida sai ka je gidanka ka tare ka jira zuwan Amarya ni kan bara iya cigaba da zama da mahaukaci"
Kyalkyalewa da dariya Mus'ab sake yi yace to ae ni narasa gane tsakanin ni da kai waye mahaukaci ko ka manta kuka ka ke yi wa mace a mafalki wannan ke nuna cewa kai d'in zarare ne Mus'ab bai jira me Habeeb zai ce ba ya juya yafi ce daga d'akin yana dariya shak'iyanci Habeeb ya bi shi da kallo daga bisani ya ja tsoki kai amma yarinya nan ta gama da ni me  ke shiri faruwa da ni da na ke mafalki na sadu da ita"?
Lallai sai na musgunawa yarinya nan sai ta yi danasani zuwa mini a mafalki cike da takaici ya murd'a handle yafi ce Mus'ab ya tarar akan dining table yana breakfast batare da ya dube ida yake zaune ba ya ja kujera ya zauna, chef Peter ya yi masa "saving har suka gama breakfast ba Wanda ya tankawa d'an uwanshi Habeeb ya dube ida yake zaune yadauke kai in ka ga dama katashi mu tafi Mus'ab ya yi murmushi had'e da cewa gaskiya tsarin gidanan ya burgeni matuk'a ba k'aramin more rayuwa za Ku yi kai da Amarya Haleesa wai... Ina nufi dream girl domin Haleesa bata kai matsayin da za'a more rayuwa da ita ko ba haka bane aboki na"?
Ran Habeeb yak'ara 6aci jin yake kamar ya zabgawa Mus'ab mari ya ja tsoki ya fice daga parlour Mus'ab ya Mara masa baya yana dariya har suka iso gidan Madam Hindu Mus'ab yana tsokanar Habeeb tun yana jin zafinshi har yagaji ya zuba masa na mujiya.

_8:00pm_

```HALEESA```

Duk lokacin da Haleesa ta tuna cewa saura kiris ta zama mallaki Habeeb Lamido sai ta zubar da hawaye ta yi nisa a tunani Aunty Juwairiyya tashigo Haleesa ki tashi ki je wanka Aunty funke na jiranki za ta yi miki makeover na tafiya _Dinner_ Haleesa ta kwa6e fuska wai ni Aunty dole ne sai na je dinner"?
"Dole ne Haleesa sai kin je don haka ki tashi ki je ki yi abunda na umurce ki Karki 6atawa mutane lokacin''
Haleesa ta shar6e hawaye na fahimce cewa Aunty Juwairiyya ko tausayi na bakyaji ta kare magana had'e da mik'ewa Aunty Juwairiyya ta tabe baki sai anan a gaba za ki gano alkhairi da ke cikin wannan aure"
Tun da zuciyata bataso
 Ya za'a yi na fahimce akwai alkhairi a wannan aure kawai zan yi biyayya da dukkan Umarni da ki ka bani domin banida mafita bata jira jin abunda Aunty Juwairiyya za ta fad'a ba tashige "bathroom.
"Aunty Funke tsantsarawa Haleesa kwalliya wance tafi ta jiya kyau da tsaruwa Amarya Haleesa ta yi matuk'ar kyau cikin wedding gown "golden colour" da head blue colour kafarta sanye da blue hill's hannaye da k'afafuta sun sha Zane k'umshi ja da baki Haleesa ta nemi gefen bed ta zauna ta zabga tagumi gani take wannan abun kamar almara hawaye suka wanke mata fuska da sauri Aunty Funke ta rik'o hannunta haba! Haleesa me yasa bakya gajiya da kuka"?
Haleesa ta sada kai k'asa had'e da ja majina da k'arfi tana k'ok'ari danne hawayeta  Aunty Juwairiyya tashigo d'akin ta yi turus ya akayi ne sarkin kuka"?
Ki sausautawa kanki Haleesa wannan kuka bara ya K'ara ki da komai ba kullum kuka abu yak'i ci yak'i cinyewa sai hawaye ki sun kare a wofi tashi mu tafi karki 6atawa mutane lokacin''
Da kyar Haleesa ta mik'e hawaye na ta ambaliya akan fuskarta Aunty Funke ta rik'e ta Haleesa ki daina kuka karki 6ata kwalliyarki kinji"?
Saida tak'ara Jan majina sannan tad'aga kai Aunty funke tayago tissue ta yi wiped in hawaye fuskarta ta k'ara Shafa mata powder sai ga fuskar Haleesa na kyalli kamar ba ita ne tagama kuka Aunty Juwairiyya ta wuce gaba Haleesa da Aunty Funke suna biye da ita har zuwa "Compound Aunty Funke ta bud'e mota kirar "Lexus 2016 model'' ta zaunar da Haleesa cikin dusashiya murya Haleesa tace Aunty bara iya tafiya ni kadai ki kira Zainab da khadeejat mu tafi tare'
"Aunty Juwairiyya ta kya6e baki tace tuni Zainab da khadeejat suka tsofa a "Hotel in da za'a yi dinner in kin je kya had'u da su Aunty Funke ta rufe mata k'ofa driver ya ja mota yayinda Aunty Juwairiyya da Aunty Funke suka shiga ta su mota had'e da marawa motar da Haleesa take baya.

```HALL```

Motar su Haleesa ta yi parking har driver ya bud'e mata k'ofa ta zuro k'afarta d'aya Hannah ta dakatar da ita karki fito Haleesa koma ciki sai yaya Habeeb yak'araso za ki fito"
Yatsine fuska Haleesa ta yi batare da tace komai ba ta mayarda da k'afarta tsawon _6-7 minutes_ ta dauka zaune a mota tana jiran k'arasowa Habeeb sai gashi ya iso tare da Mus'ab"
Hannah ta bud'ewa Haleesa k'ofa tafito Haleesa na kyalla ido ta sai akan Habeeb Lamido yana sanye da suit "sky blue ya yi matuk'ar kyau yafito balarabe sak gabanta ya yanke yafad'i jikinta yafara "sharking kamar wance "electric shock ya ja da sauri ta d'auke kai a Zuciyarta tace shi wannan wai bashida kayan ne hatta da ranar Aurenshi suit zai saka "huh! Ta tabe baki jin ta yi an rik'e hannunta tad'ago da sauri Hannah ta gani damk'e da hannunta ta nufi wurin Habeeb Lamido da ita shima ta rik'o hannunshi ta had'e da na Haleesa ba yadda ya iya dole ya rik'e hannunta a lokacin d'aya wani shock ya ja su Wanda ya yi sanadi dagowarsu suka had'a ido kallon k'asan ido yake mata yayinda Haleesa takasa jure kallon ta d'auke "eye's ball in ta k'awaye Haleesa da friends in Habeeb Lamido suka fara haska su da camera wayoyinsu hannaye su na sark'e suka fara tattak'i bisa lallausar blue carpet Habeeb ya lalla6o yatsu Haleesa ya matse su da k'arfi tsanani zafin ratsa ta wabi irin zufa ya karyo mata jin take kamar za ta saki fitsari ta bud'e baki da kyar cikin wahalaliya murya da ke nuna ba k'arami zafin take ji tace it's hurt yaya Habeeb Dan Allah kadaina ko kallonta bai yi ba sai ma 'kara matse ta da ya yi a haka har suka k'arasa akan high table da aka tanada domin su a tunani Haleesa in suka zauna Habeeb zai sake mata hannu sai taga sa6ani hakan cigaba ya yi da murza mata yatsu da k'arfi yake murza su
 Haleesa tad'ago idanu ta taf da hawaye ya kalle Habeeb fuskarshi a had'e ya dank'ara mata harara da sauri ta sunkuyar da kai, Mus'ab yak'araso yadafa kafadar Habeeb yakai bakinshi dai-dai kunnenshi ya yi mishi rad'a haba! Ango na Haleesa da leesa ka Saki ranka mana duk yawan jama'a da ke wurinan saboda Ku suka zo amma kai wani had'e fuska "Habeeb yatsine fuska ya k'akaro murmushi dole Mus'ab ya yi dariya maras sauti ya d'an daki kafadar Habeeb "Good job abokina ya juya wurin Haleesa yace Amaryamu ya haka naga kin wani had'e fuska Dan Allah ki saki ranki ki k'awata kyakyawa fuskar nan taki da sanyaye murmushi Haleesa tasaki murmushi yak'e mai kama da mai so yi kuka "Ma'aruf MC ya umurce ango da Amarya su fito su d'an taka rawa Jikin Haleesa yadauki rawa tsawon rayuwarta bata ta6a rawa ba Habeeb, ya mik'e yad'an rankwafa dai-dai kunnen Haleesa kamar zai rada mata abun arziki ke! Villager tashi mu je karki yarfa ni a gaban jama'a ace Habeeb Lamido ya auro 'yar Daji tad'ago dara-dara idanuta masu d'auke da kwalla tasauke su akan fuskarshi alama ya yi mata da girar idonshi tadaina kallonshi da sauri ta d'auke idanuta yana rik'e da hannuta suka nufi tsakiyar fili Haleesa kan tsaye ta yi k'ik'an yayinda Habeeb Lamido yake juyi da hannaye Haleesa tuni filin ya rikice sai ruwan naira ake musu Maryam ta ratso tsakiyar filin ta nufi wurin Habeeb ta 6alle pose in ta taciro bundle na N1000 tasoma yi masa lik'e ta fakaci idanu mutane ta bangaje Haleesa ta matsa daf da Habeeb kamar za ta shige k'irjinshi kallo d'aya Haleesa ta yi musu ta dauke kai nan take ta ji wani bak'o yanayi na shigarta Mus'ab ya ankara da waina da ake toyawa ya yi wa Habeeb rad'a wani shegen murmushi yasake yarik'o hannun Haleesa su ka koma wurin zamansu sai misali k'arfe _12:15am_ aka tashi daga dinner har izuwa lokacin  Habeeb na rik'e da hannun Haleesa yana Gana mata azaba ta hanyar matsi mata yatsu har wurin mota Habeeb yaraka Haleesa ya matsa daf da k'ofar mota ya yi k'asa da murya kamar mai rad'a Ina fatar za ki k'ara jajircewa ki zama jaruma domin zama da Habeeb Lamido sai jarumar mace ya wani dage girar sama oh! Kina mini kallon marigayi saurayinki koh"?
To ki yi gaggawa ki fitarda da hakan daga ranki na barki lafiya Amarya taa yak'arasa magana had'e da sakin tsadad'e murmushinsa yabar Haleesa sake da baki tana mamaki shu'umanci sa.

```ON FRIDAY ```
_2:30:pm_

Tun daga farko layin su Haleesa har zuwa karshe sa d'an mutum ne ba matsaka tsinke tarin jama'a 'yan dauri aure ne Habeeb Lamido na hango cikin farar shadda d'inki babbar Riga kanshi d'auke da farar hula kum6e Mus'ab da khaleel sun saka shi tsakiya sai fama washe hak'ora dole yake k'arfe _2:40pm_ dai-dai dunbanni jama'a suka sheda daurin auren Habeeb Lamido da Haleesa Usman akan sadaki naira dubu d'ari ana Shafa fatiha gaban Habeeb yafad'i a zuciyarshi yace shikenan yarinya nan da tsana ta zama mallaki na ya yi murmushi had'e da Shafa gajerar gemun shi.

_5:00pm_

Aka gudanar da walima inda aka gaiyyato malama Hafsat Umar ta yi Nasiha akan zamantakewar Aure tafad'i irin azabobi da Allah tanardawa duk mace da bata biyayya ga sunnah ma'aiki s.a.w bayan gama wa'azi yaran Aunty funke su dinga raba katuwar jakka mai d'auke da pic d'in Amarya da ango in ka bud'e jakka za ka tararda 'yan uban kaya daga ciki har da atamfa mai kyau gaske tun lokacin da aka tashi daga walima Haleesa keta faman rusa kuka ta tsorata murtuk'a da Nasiha da malama Hafsat Umar ta yi nan take ta k'udiri anniya yi wa Habeeb Lamido biyayya koda ace zai dinga yanka naman jikinta bara ta ta6a tsalleke umurni sa.

_9:44pm_

Haleesa na durk'ushe a gaban iyayyeta suna kora mata Nasiha duk akan zaman aure yayinda Haleesa ke kuka kamar ranta zai fita Baffa yarik'o hannunta yanufi k'ofar gida yasanya ta cikin mota ya mik'a mata Al-qur'ani da pray mat had'e da casbaha yace Haleesa ki rik'e wannan domin shine magani kowace matsala ta d'an Adam Allah yabaku zaman lafiya yabaku zuri'a dayyaba Haleesa tak'ara fashewa da wani sabon kuka Baffa ya umurce driver yaja mota su tafi har aka fita daga unguwarsu tana kuka kamar ranta zai fita....

Jeeddah Aliyu
[31/12 9:25 am] aliyujeeddah: [20/10 11:06 am] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

Note:- _Ina ba Masoya ni da yaya Habeeb hankuri a dalilin rashin post da ba nayi akai-akai har wasu na k'orafi na cika Jan rai yakamta ku yi min uziri ni ma ba'a son raina hakan take faruwa_


              ```63```

"Har suka k'araso unguwar Haleesa bata saniba domin kanta na tsakiyar cinyoyita tana shassheka kuka, katsaye direban yanufi had'ad'e gate d'in gidan Habeeb Lamido ya yi tsaye ayarin motacin da ke bayan shi suka bi sahunshi saida suka share tsawon _10 minutes_ a tsaye saida security camera in da ke manna a gida suka gama "screening in motaci daga bisani gate d'in ya bud'e kanshi tafiya mai d'an nisa sukayi kafin su tararda k'aramin gate anan "gate man yake zaune yataso ya bud'e musu gate bayan driver ya gama parking yafito ya bud'ewa Haleesa k'ofa inna mairo ta rik'o ta gaba d'aya jikin Haleesa  lullu6e yake cikin white colour lafayya ko fuskarta ba'a gani inna Mairo ta rad'a mata ki yi addu'a kafin mu Shiga ciki sannan kuma ki shiga da k'afar dama Aunty Mami ce ta jagorance su inna mairo zuwa bedroom d'in Haleesa inna mairo ta zaunar da ita a gefen bed tak'ara yi mata nasiha gani yadda Haleesa take ta rusar kuka ta yi matuk'ar ba inna mairo tausayi take ta tuna da d'ata Marigayi Habeeb da yanzu gidanshi za'a kai Haleesa ta kuma tabbata cewa da ace gidanshi za'a kai Haleesa da ba abunda za ta yi wa kuka idanu inna mairo suka ciko da hawaye da sauri ta fice Zainab da khadeeja suka saka Haleesa a tsakiya suna lallashi kamar suna k'ara zugata ne domin wani sabon babi ta bud'e na kuka k'arfi _10:20pm_ dai-dai Su Zainab suka ce za su wuce yayin da Haleesa ta k'ank'ame Zainab tana kuka "Zainab karki tafi ki barni ba zan iya rayuwa da Habeeb Lamido saboda Zuciyata har yanzu yaya Habeeb takes....da sauri Zainab tarufe mata baki haba! Haleesa me yasa bakyaji magana"?
Ko kin manta cewa a yanzu kina matsayi matar wani Dan Allah ki yak'i zuciyarki ta daina ambato yaya Habeeb gudun daukawa kanki zunubi Haleesa ta zare jikinta daga na Zainab tafad'a bisa bed ta cigaba da shasshek'ar kuka har Zainab ta yi yunkuri nufar wurinta Khadeejat ta dakatar da ita ki kyalleta kawai domin na tabbata kowace kalma za ki furta mata halin da take ciki bara su yi tasiri akanta ae ita ba jahila bace tanada ilimi   tasan abunda yadace ta kuma San abunda bai dace ba tana k'arasa magana tarik'o hannun Zainab suka fice gidan ya yi tsit gaba d'aya 'yan rakiya amarya sun kama gabansu.

_11:15pm_

```HABEEB LAMIDO ```

Bala yadanno hanci mota a farfajiya gidan ya nufi parking space ya yi "parking ya za gaya ya bud'ewa Habeeb k'ofa yafito yana sanye da "black colour Jeans da blue colour long sleeve shirt yasha stocking cikin yanayi da ke nuna ya kwaso gajiya yanufi cikin gida a main parlour ya tsaya ya yi switch off in light ko kallon bedroom d'in Haleesa bai yi ba ya hura upstairs yanufi dak'inshi bayan ya yi wanka ya sanya pajamas ya haye bed Sam ya manta da wata aba Haleesa tsanani gajiya da ya kwaso yasa bai d'auki dogon lokacin bacci ya yi awo gaba da shi.

```HALEESA```

Tun tana kuka da hawaye har tadawo kukan zuci ko kayan jikinta kasa cirewa ta yi sai fama juyi take zance ta rufe k'ofa bai ma taso ba saboda tasan ko kare hauka ya cije Habeeb Lamido ba yadda za'a yi ya shigo d'akinta sai  kawai ta cigaba da zance Zuci sai kusan asuba bacci ya yi nassara kwasheta.

```WASHE GARI ```
_10:08pm_

Haleesa ta falka daga bacci a gauggauce ta gyara "bedsheet ta jona "burned a "socket ta zuba turare wuta d'akin ya gume da sanyaye k'amshi daga bisani tashiga wanka bata d'auki dogon lokacin ba tafito ta shirya cikin atamfar "Super Sheraton blue da touch in pink ta yi matuk'ar kyau tafito amarya sak batare da ta daura Dan kwali ba ta yane kanta da d'an siriri "veil pink colour tanemi gefen bed ta zauna ta rakka d'an uban tagumi k'ugi da  cikinta yake yi yasa babu shiri ta mik'e ta murde handle ta bud'e k'ofa kad'an ta lek'a wayam ta hangon parlour ba kowa a hankali take sand'a kamar barauniya ta  dafe da kwakwaso tana kallon tsarin parlour ya yi matuk'ar yi mata kyau "everything's da ke  parlour red & yellow colour ne tasauke numfashi a baiyane tace "amazing that's my favourite colour" daga bisani tanemi d'aya daga cikin "Royal chairs d'in da suka k'awata parlour ta zauna tunani take ina za ta nemo abinci za ta sakawa hanjinta tun, kafin yunwa da takeji ta yi mata illah 'kamshi turare "intense men da ta shak'a ya haddasa mata fad'uwa gaba  karar "footsteps da taji ana saukowa daga upstairs yak'ara jefata cikin matsananci tsoro cikin d'an k'ank'ani lokacin zuciyarta ta motsa yayin da hankalinta yatashi tasoma fargaba had'uwa da Habeeb Lamido ko wace irin tarba zai yi mata sanye yake ciki "three quarter red colour da white armless shirt k'afarsa rufe cikin white combat boot hannaye shi na zube cikin aljihu wandon fuskarshi a had'e yak'araso cikin parlour a wulaqance ya dube inda Haleesa take zaune ya Ja 'yar siririya tsoka yanemi nesa da ita ya zauna tsawon "4-5 minutes da zaman shi ya d'ago ya kalleta har yanzu kanta na k'asa tana wasa da yatsuta ranshi ya yi mugun b'aci wannan 'yar k'auye tana nufi bara ta gaishe ni ba yafad'a a cikin zuciyarshi Cike da izza yace ke! A rud'e Haleesa tad'ago idanuta suka firfito alama tsoro ke! Ba da ke nake magana ba"?
"Na"am ta Fad'a tsoro shinfid'e a fuskarta kina nufi bara ki zo bane"?
Jiki na rawa ta mik'e tanufi gabanshi tayi tsaye had'e da sada kai k'asa ta k'asan ido yake kallonta kamar Mai rad'a ya furta ba ki iya gaisuwa ba koh"?
Sam Haleesa ba tayi zato jin wannan kalma daga bakinshi ba ta hadiye yawu da kyar tace na iya mana''
Yad'ago eye's in shi yana tsotsa bakinshi kamar mai tsotsa sweet daga bisani ya ja iska kamar Wanda ya ci yaji da sauri Haleesa tadauke kanta da bari kallonshi "tsabar iskanci ne da yacika miki ciki yasa kika kasa gaida ni koh"?
Girgiza kai Haleesa ta yi
"A fusace Habeeb yace you are not dump or deaf so open your bloody mouth & talk to me"
Cikin sarkewa halshe tace dan..Allah.. Yaya Habeeb ka yi hankuri ni banaso fitina
Ya galla mata harara kina nufi ki ce ni ne fitinane lallai kuwa zan nuna miki cewa ni cikkake fitinane, ne ya mik'e tsaye saida ya yi mata kallon wulaqanci yace "Follow me
Haleesa tadafe k'irji ta zaro ido tace na'am"
Ko kallonta bai yi ba yanufi wata k'ofa ta glass cikin sassarfa ta bi bayanshi yana shiga tana shigowa batare da ya dube ta ba yanufi gym mat machine" yasoma motsa jikinshi sai uban gumi yake had'awa yayin da Haleesa tacigaba da tsayuwa jin ta yi k'afafuta sun fara d'auke wuta ta yi nufi ta zauna akan d'aya daga cikin chair's d'in wurin tun kafin d'uwawu ta su kai bisa kujerar yadaka mata tsawa ke! Wa ya baki izzini zama"?
A tsorace Haleesa ta mik'e chak ta yi narai-narai da ido hawaye suka tsiyayo mata wani irin dad'i ya lullu6e Habeeb Lamido sakamako hawaye da yagani sunanta fita daga idanuta, ya wani kada kai cikin d'agawa da nuna isa yace kad'an daga cikin k'anana wulaqanci da kika fara gani daga gareni kafin na fara baiyana miki manya-manya da ke jiranki amma in har kika dinga bin umurni na zan iya rankwata miki saboda ni mutum ne da bayaso shiga harka wani kamar yadda ni ma banaso a Shiga nawa yak'arasa yana Jan iska a zuciya Haleesa tace kai amma guy nan d'an air ne dube yadda yake ja iska kamar Wanda yaci yaji ta sauke numfashi muryarta na rawa tace zan kiyaye da duk wani umurni da za ka dinga ba ni.
Kamar bai ji abunda tafad'a ba ya yi switch off in machine d'in yasauko yadauki fari towel ya goge gumi fuskarshi har zuwa dokin wuyanshi yajuya yafice Daga room d'in da kyar Haleesa ta ja k'afutata kafin tak'ara sa tuni har Habeeb yarufo k'ofar ta tura k'ofa amma ta ji ta gam tacigaba da tura k'ofar iya k'arfinta har tagaji ta yi tsaye turus wani irin gumi ya tsiyayo mata me Habeeb yake nufi na rufe a cikin wad'annan k'arafe dole tanemi wurin ta zauna a hankali take rera kuka ga wani irin murd'awa da cikinta ya ke yi ta mik'e da kyar gaba d'aya jikinta ya jik'e da zufa tasoma dukan k'ofar da k'arfi had'e da kiran sunan Habeeb tsawon lokacin ta d'auka a haka daga karshe ta sulala k'asa tadafe kanta tasoma tambaya kanta, wannan wane irin aure ne rana farko na a gidan Habeeb na fara fuskantar k'alubali Habeeb yana sane yarufe Haleesa saboda yasan bara ta ta6a iya bud'e k'ofar domin k'ofar da code take using saida 6ata "long time a bathroom duk don ya wahalarda Haleesa ya shirya cikin brown Jean's da yellow t-shirt yasauko k'asa fuskarshi a murtuk'e ya bud'e ta Haleesa nagani K'ofa ta bud'e tak'ara fashewa da kuka Habeeb ya ja tsoki ya yi tafiyarshi tafito tana Jan k'afa ta hango shi a dining area peter yana saving in shi nan take yunwa da takeji tadawo sabuwa wata zuciya tace ki je Haleesa ki cika cikinki saboda bara ki iya cigaba da jure zama da yunwa "with full confidence tanufi table d'in a lokacin har Habeeb yafara cin abinci shi peter ya ja mata kujera ta zauna ya yi mata saving tsanani yunwa da takeji yasa tafara cin Chip's bata ko taunawa sosai take hadiyewa abunda ya yi mugun ba wa Habeeb haushi ya tsane ya ga ana cin abinci haka domin shi komai a yangance yake yi da k'arfi ya jefa  spoon in hannunshi cikin plate yature kujera ya yi tafiyashi Haleesa ta bi shi da kallo ta tabe baki saida ta yi narkat sannan ta tashi tanufi cikin "main parlour Habeeb na hakice akan two star fuskar nan a had'e kamar tsoho soja cikin sanyin jiki Haleesa ta zauna a k'asa "rugs carpet ta sunkuyar da kai a fakace Habeeb yake satar kallonta, Haleesa tad'ago da sunan ta sace kallonshi karaf suka had'a ido ya galla mata harara ya kuma k'ara  d'aure fuska da sauri ta d'auke idanuta phone in shi ta yi ringing ya yi picking _mtwww....ya ja tsoki look Mus'ab ni fa banaso iskanci in za ka shigo to bissmillah in kuma za ka tsaya munafuci ka ne ka kyalle khaleel ya shigo_ ya yi hanging up
A zuciya Haleesa tace kai wannan anyi masifafe, da kowa masifa ya ke"
Mus'ab da khaleel suka shigo sai fama kyalkyatar dariya suke kowanesu yanemi wurin zama Haleesa ta gaida su cikin tsokana Mus'ab yace Amarya bakya laifi ko kin kashe d'an masu gida murmushi yak'e Haleesa ta yi tak'ara sada kai k'asa Habeeb ya ja tsoki cike da takaici yace sanin kanka ne banida d'a a gidanan bansaniba sai in kai za ta kashe Mus'ab ya yi dariya yace to ae ni ba d'a ka bane a yatsine Habeeb yace wannan kuma matsalar ka ce "Haleesa ta mik'e tsam tanufi bedroom d'inta Mus'ab ya gyara zamanshi yace Habeeb yakamata ka sakawa zuciyarka salama ka, zauna lafiya da yarinya nan domin ni banga wata matsala a tare da ita, Habeeb ya yi tsoki had'e da mik'ewa khaleel tashi mu tafi banida "time in sauraro surutu wannan duk yadda Mus'ab ya so ya lurar da Habeeb amma yak'i bashi had'in kai.
Bayan fitar Su Habeeb Haleesa tafito parlour bata jima da zama ba Hannah tashigo suka bud'e shafi na fira Hannah tarik'o Hannun Haleesa shawara zan baki Haleesa ba wai a matsayina na k'anwar mjinki ba matsayina na k'awarki kuma 'yar uwarki a musulunci Haleesa ki yi hankuri ki bi mijinki sau da k'afa domin samun aljannarki kada ki biyewa ta yaya Habeeb domin shi mutum ne mai wuyar sha'ani a wani gefe kuma yana da matuk'ar saukin kai, Haleesa ta yi murmushi na gode da wannan shawara ta ki Hannah zan yi k'okari na rinjaye zuciyata na bi yaya Habeeb insha Allah ba za'a ta6a samun matsala daga gareni zan bi shi ta yadda yakeso, sai misali k'arfe _2:30pm_ Hannah ta yi sallama da Haleesa.

_5:00Pm_
Haleesa na zaune a parlour har zuwa lokacin Habeeb bai dawo ba Maryam da zeely suka fad'o parlour ba ko sallama sai kace tumakai Haleesa tad'ago tana musu kallon mamaki daga bisani ta sauke idanuta akan wata kyakyawa yarinya da ke rik'e da hannun Maryam da shekaru ta basu haura 5-6 yrs nan take Haleesa tagano cewa ita ce imaan domin tana kama da Habeeb "sannu Ku da zuwa bissimillah ga wurin zama Haleesa tafad'a cikin 'yar gajeriya fara'a maryam ta yi mata kallon sama da k'asa ta yi tsoki tafinciko hannun zeely suka haura upstairs suka soma zagaya gidan kowane bedroom da parlour saida suka shiga part d'in Habeeb  ne kadai basu samu damar shiga saboda yana rufe Haleesa ta juya wurin imaan da ke tsaye tana kallonta ta rik'e hannunta baby ya sunanki"?
Da k'arfi imaan ta fincike hannunta ta wani 6ata fuska cikin 'yar muryarta mai cike da yarinta tace "don't touch me ni bana sonki kuma aunty Maryam tace ke ba mommy na bane ke 'yar talakawa ce gidanku na jar k'asa ne irin gidansu hajjo mai aiki tak'arasa magana had'e da murguda d'an k'aramin bakinta Haleesa tasaki baki da hanci tana kallon Imaan a hankali ta dinga ja da baya tafad'a bisa kujera da6ass ta yi zaman 'yan bori cabdijam! Ana wata ga wata lallai ina da Jan aiki a gabana Maryam da zeely suka dawo cikin parlour Maryam tace, zeely yanzu kin gansu da abunda na ke Fad'a miki"?
"Kwarai kuwa k'awata ga zahiri nagani tajuya wurin Haleesa tace ke! Figa tsiyo kaza mayu wannan wane irin talauci da zallan kwad'ayi Ku ke da shi ke da iyayyenki"?
Ace ko allura ba su kawo ki da ita duk fad'in gidanan bakida tsinke naki na kanki Maryam ta kar6e zance ta hanya cewa wallahi, wallahi sai na yi nassara raba ki da yaya Habeeb domin bai dace da 'yar talakawa irinki mai k'ashin tsiya sai na sa kin yi kuka da hawayenki, masifa da bala'i da zan haddasa miki sai sun sanya ki fita gidanan da k'afarki haka su ka cigaba da yi wa Haleesa cin mutunci da yanka k'auna Haleesa na hakince tana kallonsu daga bisani ta yi murmushi tace kun gama"? Inaso ki bud'e kunnenki da kyau Maryam ki saurare ni kin riga kin tafka babban kuskure da ki ka yi sake na shigo gidan yaya Habeeb Wannan ne ya tabbata min da cewa ke d'in bakida Sa'a a rayuwa kuma da ki ke zance kayan d'aki tsabar na nunawa duniya ni nake juya yaya Habeeb yasa na zo ni kadai batare da ko tsinke, banda ke dak'ik'iya ce Maryam ae so ba ruwanshi da kyalekyale duniya ```NI DA YAYA HABEEB ``` nan gani nan bari dukiyar uban wani 'yar talakawa ta riga ta mallake zuciya abunda ki ke so.
Ran Maryam ya yi matuk'ar sosuwa da jin furuci Haleesa sai fama huci take kamar kubunbuwa motsin shigowar Habeeb ce ta janyo hankalinsu, da gudu Imaan tanufi wurinshi "Daddy oyoyo yad'aga ta chak had'e da mannata a k'irjinshi "how you my Angel"?
Am fine "Daddy
Ya yi pecking nata a cheek ya nufi kujera da Haleesa ta ke kai ya zauna daf da ita har jikinshi yana guga nata rass! Gaban Haleesa yafad'i ta wani d'id'ice Maryam ta mak'e murya tace "sannu da zuwa yaya Habeeb
Batare da ya dube ta yace sannu ya mayarda hankalinshi wurin Haleesa yarik'o hannunta "baby ba dai fushi ki ke yi da ni ba"?
Tsanani tsoro ya lullu6e Haleesa tad'ago had'e da tsura masa ido shin me Habeeb Lamido yake nufi da wad'annan kalamai nashi....??


Jeeddah Aliyu
[31/12 9:29 am] aliyujeeddah: [04/11 7:06 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

              ```64```

Da sauri-sauri Haleesa ta sauke numfashi ta hadiye yawu Habeeb yak'ara dank'e yatsunta yana wani lumlumshe idanu "am sorry baby bara k'ara fita na barki ke kadai kinji"?
Haleesa tayi murmushi yak'e tasada kai k'asa zuciyarta cike da mamakin Habeeb lalle Habeeb Lamido cikakken d'an duniya ne, kallo d'aya tayi mashi ta gano duk abin da yakeyi mata"pretending ne, muryar imaan ce ta katsi mata zance zuci "Daddy aunty Maryam tace "new mommy da ka kawo min 'yar talakawa ce bata dace da kai ba kum..."shut up Imaan bana hanaki irin wannan surutu maras kan gado ke fa da bakinki ki ka ce kinaso na kawo miki "new mommy ba"?
"Imaan ta gyad'a kai
Duk ranarda na K'ara jin irin wannan magana a baki ki bara k'ara siya miki "Ice cream
Rau-rau da idanu Imaan ta yi kamar za ta yi kuka tace, "Daddy na daina Habeeb ya shafi cheek in ta ya juya wurin Maryam da ke tsaye tana fama da tafarfasa zuciya ya dank'ara mata harara mai dauke da gargad'i ya mik'e tsaye ya sunkuce Imaan ya dube Haleesa yace baby in kin sallame visitors in ki ina jiranki a sama bai jira amsar da Haleesa za ta bashi ya haura upstairs cikin d'aga murya Maryam tace kadawo da imaan tafiya za mu yi batare da yajuyo ba yace za ki iya tafiya Co's imaan tadawo gidan ubanta
A tsoroce Maryam tace wannan wane irin d'aye hukunci ne yaya Habeeb"?
Cikin isa da tak'ama yace saboda ni nake iko da imaan
Maryam tak'ara harzuk'a Duk tsawon wannan lokacin da imaan ta dauka a tare da mu baka ta6a nuna kanada iko da ita sai yanzu ba yadda za'a yi muna raye imaan ta zauna a hannun kishiya uwa in har kai baka sonta to mu munasonta matuk'ar ka ga imaan ta zauna a gidanan ka tabbata cewa ka rataya mini igiyoyi aurenka Inda har hakan bata kasance ba wallahi imaan bara ta zauna a hannun wannan 'yar Matsiyata, Habeeb ya bud'e baki da d'ibin mamaki yana kallonta cike da takaici yadawo cikin parlour ya sauke Imaan yanuna Maryam da yatsa yasoma magana cikin b'aci rai banaso iskanci banza da wofi maryam har ni za ki fadawa magana banza zai fiye miki alkhairi ki tattara k'afafu ki ki bar min gida tun kafin ki kaini bango nayi miki rashin mutunci nasha Fad'a miki bana sonki na tsane ki da yake ke dak'ik'iya ce kin kasa gane hakan zeely ta janyo hannun Maryam tace zo mu tafi Maryam sannu-sannu bata hana zuwa saidai ajima ba'a kai ba lokacin na zuwa da za kiyi fatali da gwannati 'yar Matsiyata ki mulki yaya Habeeb son ranki "Habeeb yak'ara harzuk'a yanufi wurinsu da gudu suka fice daga parlour da Ku tsaya na nuna mu Ku yadda za Ku yi mulki na 'yar Matsiyata nan da Ku ka rena tafi Ku daraja da k'ima a wurina'yan iska tarkace tsiya marasa tarbiyya, kuma duk ranarda na k'araji d'aya daga cikinku ta kira matata da suna 'yar Matsiyata dai na gwaje mata baki Haleesa ta tsura masa ido tana mamaki yadda kalamai nan suke fitowa daga bakinshi yana juyowa suka had'a ido ya watsa mata harara ke! daina kallona kin wani tsareni da idanu sai kace mayya da sauri ta sada kai k'asa yak'araso daf da ita saida yak'are mata kallon wulak'anci ya ja tsoki ke! Ina son ki bud'e fakanfakan kunneye ki masu kama da na zomo ki saurare abunda zan Fad'a miki domin banaso asami akasi ki ce baki fahimce abunda nake nufi duk magana da Habeeb yakeyi Kai Haleesa na sunkuye tana murza zobe yatsanta saida yaja iska sannan yacigaba da cewa ina matuk'ar son imaan banida buri da yawuce naga rik'o ta yadawo hannuna musanmman da na fahimce irin rik'o sakainiya kashi da akeyi mata a duk lokacin da na je ganin Imaan raina na matuk'ar sosuwa a yadda nake tararda ita Sam bata samu kyakyawa kulawa gaba d'aya tarbiyyar ta na wurin 'yar aiki Imaan na buk'atar wance za ta maye mata gur6i mahaifiyarta da tarasa, dalili da yasa lokacin da mom ta yi min tallarki na amince zan aure ki, ina fatar za ki rik'e Imaan da amana sai lokacin Haleesa tad'ago tasauke ajiyar zuciya, cikin sanyi murya tace insha Allah zan bawa Imaan kyakyawa kulawa bara ka ta6a samu na da aikata ba dai-dai a gareta ae d'a na kowa ne yadda zan kula da 'yar da na haifa haka zan kula da ita tak'arasa magana had'e da sada kai k'asa "Habeeb Lamido ya ja wawa tsoki ya wani zare idanu ke! Ba dai ni kike tunani zan miki ciki har ki haihu"?
A tsorace Haleesa tak'ara d'agowa tasauke "eye's ball d'inta akan fuskarshi yadda ya murtuk'e fuska ya yi mugun kad'a anta cikinta cike da takaici yace kidaina yaudara domin ni ba abunda zan tsinta a jikinki yanuna jikinta da yatsa shi yana yatsina yacigaba da cewa na mafalki ma da kike samu da ina da yadda zan datsi shi da tuni na taka miki birki da fatar kin fahimce inda na dosa"?
" Batare da Haleesa ta fahimce abunda yake nufi ba ta gyad'a kai ya tabe baki had'e da cewa ki bani aro hankalinki na karato miki dokoki zaman gidana idan kika kiyaye su za ki ji dad'i zama da ni doka ta farko na tsani k'azanta shiyasa bana sha inuwa d'aya da k'azami  in har bakida tsafta ki fara koyo in kuma kinada sai ki k'ara bisa ga wance kike da saboda ni mutum ne mai tsanani kyakyame gaske doka ta biyu ya zame miki dole duk wani abu da kika yi amfani da shi ki mayarda shi a muhallinsa hatta da "toothpick yana da muhallinsa a gidanan, sai kuma doka ta uku dole ki girmama ni domin ni mutum ne mai matuk'ar so girma daga yau za ki dinga gyara mini sitting room da kuma bedroom dole ne kullum ki wanke mini bathroom amma ban amince ko "Noodles ki dafa da sunana, da sauri Haleesa ta dube shi fuskarta d'auke da d'inbi mamaki yak'ara zare mata shegu idanunshi masu masifar tsorata ta kidaina mamaki domin ba ki kai matsayi da ki za ki dafa mini abinci shi ma gyara rooms in da kika ji nace kidinga yi min ba wai kin Kai matsayin shiga d'akina bane kawai banaso kidinga cinye min abinci a wofi sai ki kiyaye dokoki da na  shinfida miki domin shine kwaciyar hankalinki a gidanan ya sunkuce Imaan suka haura upstairs yabar Haleesa sake da baki hawaye masu masifar zafi suka wanke mata fuska tasaka bayan hannunta ta goge, bayan "10 minutes da fitar Habeeb sai gashi yadawo yana rik'e da hannun Imaan jin karar footstep in shi yasanya Haleesa tajuya yasauya kaya zuwa dark blue Jean's da white shirt ya sha stocking da belts mai tambari D&G ko kallon gefen da Haleesa take zaune bai yi ba yafice yayin da Haleesa ta bi su da kallo haka tacigaba da zama a parlour tana sak'e-sak'e kiran sallah magarib ne ya mayarda ita bedroom in ta ta yi wanka had'e da alwala ta yi sallah tana gama sallah tasoma lazimi har akayi kiran sallah isha'e ta mik'e ta gabatarda sallah bayan tagama sallah tanufi "dressing mirror ta yi simple make up tasanya yaloluwa night gown pink colour  ta fashe jikinta da designer perfume ta tufke gashin kanta da k'ato ribbon pink colour kaitsaye tanufi downstairs parlour peter ta hango a dining area yana jera abinci a table tanufi wurinshi peter na ganinta ya rusuna ya gaida ta cikin sakin fuska ta amsa masa ya ja mata kujera ta zauna cikin gur6ataciya hausar shi yace mah me za'a zuba miki"?
Haleesa ta yi shiru daga bisani tace zan yi serving da kaina za ka iya tafiya Peter yajuya yafice ta bud'e warmers pounded yam ta zuba had'e da egusi soup ta sha smoked fish tana ci tana gyada kai alama abinci ya yi mata dad'i bayan ta cika cikinta tanufi parlour ta kwanta akan 3 star tasoma tunani wance irin rayuwa za ta yi da Habeeb Lamido.

_9:00pm_

Sai misali k'arfe 9:00pm Habeeb yadawo yana sa6e da Imaan a kafad'arsa ta yi bacci, yana shigowa parlour Haleesa ta mik'e da sauri tanufi wurinshi sannu da zuwa yaya Habeeb Imaan ta yi bacci ne"?
Kallon sama da k'asa ya yi mata ya ja d'an siriri tsoki cikin husky voice in shi, yace ba ki ga alama bane ko ke makauniya ce"?
Murmushi ta yi ta lamgwabe kai dallah matsa ki bani wuri ki yi wani tsare da tambayoyinki na shirme Allah ya ba ka hankuri kawo ta na kaita bedroom kamar ba zai mik'a ta ba saida ya yi mata kallon da ta tsana sannan ya mik'a mata Imaan garin amsa ta hannushi ya goge k'irjinta saura kiris Haleesa tasaki Imaan cikin zafin nama yarik'e Imaan jikin Haleesa yadauki rawa sai fama zarar ido take wani mugun kallo ya watsa mata had'e da daka mata tsawa ke! Wance irin mahaukaciya ce"?
Don kawai hannuna ya goge k'irjinki shine za ki sake min yarinya Allah yaso ki da tafad'i Allah da sai na 6arar da ke Humm! Haleesa tasauke ajiyar zuciya cikin tsanani jin kunya tasada Kai k'asa ya ja tsoki ya ra6a gefenta ya haura upstairs bedroom in shi ya wuce da Imaan ya shinfid'e ta had'e da sauya mata kayan jikinta zuwa sleeping dress ya kwa6e kayan jikinshi yadaura "bathrobe towelling yanufi bathroom yacika bathtub da ruwa masu dumi-dumi ya zuba bath perfumes masu k'amshin gaske ya yi kwance cikin bathtub ya d'auke remote control ya yi switch on in TV ya murd'o BBC channel ya murza liquid soap mai k'amshin "guava fruit a skin in shi saida ya share "20 minutes yana wanka sai kace zai sauya skin colouring d'inshi daga bisani yafito daga bathroom d'in ya yada zango a gaban dreesing mirror ya shafe jikinshi da lotion ya bi lungun da sak'o na jikinshi da perfumes yasaka pajamas sky blue colour ya fice zuwa downstairs parlour Haleesa na zaune ta rafka tagumi kallo d'aya ya yi mata yadauke kai yanufi dining area Haleesa tad'ago ta sace kallonshi ta tabe baki ga ni zai yi serving in kai shi yasa ta tuna da nasiha da baffa da Ammi suka yi mata akan ta bi Habeeb lamido sau da 'kafa domin aljannata tana k'ark'ashi k'afarshi bai kamata furuci shi yayi tasiri akanta tak'i yi masa biyayya da sauri ta mik'e tanufi dining area har ya yi nufi ya bud'e warmers kamar daga sama ya ga hannun Haleesa ta dafe murfi ta wani lamgwabe kai tadawo kala tausayi "please yaya Habeeb ka bani dama nasamu wannan lada kallon hadari kaji ya yi mata ya murtuk'e fuska ya janye hannunshi ke! Ban Fad'a miki a rayuwa na banaso shishigi ni za ki yi wa kilinbibi da kissa da kisisina shine don tsabar iskanci har da su saka "transparent night gown don ki ja hankalina wallahi ki yi a banza ki yi yawo nicked  a gidanan ko dar bara ji ba Co's bana kallonki a matsayin mace, ki gaugauta ki bace mini  da gani na tsani kallon wannan "ugly face naki duk k'ok'ari Haleesa ta yi ta danne hawaye ta ta k'asa shar hawaye suka tsiyayo akan fuskarta ke! Dallah bace min da gani banza 'yar k'auye  "classless kawai da gudu Haleesa tanufi bedroom in ta tafad'a bisa bed tasaki kuka mai tsunma zuciya dama ga Haleesa da kuka banza marigayi yaya Habeeb ya riga ya sagarta ta abun d'a k'ank'ani ya isa yasaka ta kuka har da su majina ta bangare Habeeb kuwa yana gani tafice ya ja tsoki ya Ciro phone ya yi dialling number Bala P.A  kai! In ka ga dama ka zo mu ci abinci bai jira amsar da Bala zai bashi ya yi "hanging up after 4-6 minutes sai ga Bala yashigo direct yanufi "dining area cikin zolaya yace "Boss na yi zato Amarya ta ture gwanati na kadaina cin abinci da ni ashe har yanzu matsayina na nan bai sauya ba yak'arasa magana yana dariya shak'iyanci Habeeb ya wani dage gira sama ya cize lips in shi yana yi wa Bala kallon k'asa ido daga bisani yace wallahi Bala ka kiyaye ni karka ga kamar bara iya firing naka kanemi ka raina mini hankali Bala yadafe baki yana dariya k'asa-kasa ya bud'e warmer ya yi musu "serving Habeeb yad'an tsakare abinci ya mik'e batare da ya dube Bala ba yace bacci nakeji zan kwanta inda ka gama ka rufe mana k'ofa "Bala yacika baki da katuwar loma pounded yam don tsabar k'arfi hali irin na shi saida ya furta abunda ke ranshi "Boss bacci tun yanzu kwata-kwata 10:08pm sai naga kamar ka yi sauri kwanciya yak'arasa magana had'e da tand'e yatsunshi wani mugun haushi yak'ara turnuk'e Habeeb rasa abunda zai ce da Bala ya ja tsoki yajuya kawai yanufi bedroom d'inshi ya gyarawa Imaan kwanciya ta ya yi pecking nata a goshi yanufi doguwar kujera kwara d'aya chal da ke cikin room d'in da alama had'e take da bed yaciro System d'inshi da ke soke a socket tana charging ya zauna a tsakiyar kujera ya langwashe k'afafu shi yasoma kallon pic's d'in motoci  a wani Company motoci da ke Japan suna turo masa simple na new models na car's har 2:00 o'clock ta buga yana zaune sai fama zabga hamma yake bacci yakeji sosai ya mik'e tsaye da kyar ko rufe laptop d'insa bai yi ba yafad'a kan bed ya karato addu'a kwanciya bacci ya tofe Imaan ya dauki remote yak'ara gudun Ac al'ada Habeeb ce Sam baya iya kwanciya sai yaji sanyi Ac na ratsa k'assa jikinshi sosai, ya jawo blacket ya lullu6e su ya lumshe sexy eye's d'inshi bai d'auki "long time bacci ya yi nassara kwashe shi ta 6angare Haleesa kuma ta ci kuka ta ita kadai ba mai rarrashinta gani kuka ba zai amfane ta da komai ba ta mik'e tashiga bathroom ta daura alwala tasoma Nafilla saida ta yi raka'a 11 ta d'aga hannaye ta sama hawaye na zuba akan fuskarta tasoma kai kukanta wurin Ubangiji da baya bacci _ya Allah ina tawasali da kyawawa sunaye ka masu girma da d'aukaka Allah Kaine_ _masani sirri da ke boye da sirri da ke baiyane ya Allah ina rok'o ka idan har aure na da Habeeb Lamido akwai alkhairi a cikin sa Ya Allah kabani_ _hankuri da juriya cinye wannan jarabawa ya Allah ka tausaya mini ka cire min son marigayi yaya Habeeb a zuciyata, ka maye mini zuciyata ka mini zuciyata da son mijina_
_Ya Allah kabani iko yi biyayya a gareshi Ameen_ ta Shafa addu'ar ta mik'e had'e da linke pray mat tanufi bed ta kwanta sai kawai ta ji duk wani b'aci rai da takeji yafita bacci mai dad'i gaske ya yi awo gaba da ita.

```HABEEB```
Zaune yake akan resting chair yana shan ice cream yashak'i k'amshin turare "musk Al-ghazal, bai Sam lokacin da ya lumshe idanushi daga bisani ya bud'e su yasauke ganinshi akan pretty face d'inta sai fama zuba masa murmushi take cikin tafiya kassaita tanufi wurinshi tashige jikinshi ta lafe kamar magge Habeeb yasaki sanyayar ajiyar zuciya, chan k'asan mak'oshi sa ya kira sunanta _leesa_ shiru ta yi bata amsa ba ya daura bakinshi akan kunneta ya maimaita sunan nata ta sigar Jan suna iska bakinshi ya ratsa dodo kunnenta ba bu shiri tad'ago dara-dara idanuta ta dube shi kallon-kallon mai cike da tsan-tsan so suke yi wa junansu daga bisani leesa ta d'auke kanta had'e da kar6e roba ice cream d'in hannunshi ta ciko spoon tasaka masa a baki bai ankara ba yaji bakinta akan nashi a hankali take shan ice cream d'in da tasaka masa a baki saida tashanye shi tass sannan ta debo tasaka a nata baki ta turawa Habeeb bakinta ta lumshe idanuta ga bakinta a bud'e Habeeb ya dube ice cream d'in da ke shinfide akan halshenta ya matsa face d'inshi daf da nata ya zura  bakinshi cikin nata firgigit Habeeb ya zabura ya mik'e zaune daga mafalki da yakeyi yadafe goshi zufa ya tsatsafo masa yajuya ya dube Imaan da ke ta fama sharar baccinta
"Ya sauke ajiyar zuciya yafi a kirga yasoma aikawa brain d'inshi zafafa tambayoyi _meke faruwa da ni"?_
_miyasa nake yawan mafalki yarinya nan"?_
_iya sanina bana sonta batada muhalli a zuciyata amma a duk lokacin da na kwanta bacci sai nayi mafalkinta to me hakan yake nufi"?_
Ya ja iska mai zafin gaske ya furza Haleesa tanaso ta zamewa rayuwata karan tsaye ya lumshe idanushi mafalki da ya yi yasoma yi masa shawagi sai kawai ya tsince kanshi da sakin dogon tsoki, ya shafi sumar kanshi had'e da lashe lips d'inshi wani irin haushi da tsanar Haleesa suka mamaye masa zuciya cike  da takaici ya gyara zaman pillow ya kwanta.

```WASHE GARI ```

_10:00am_

Haleesa na zaune a gaban dressing mirror tana Shafa lotion, ta d'a Shafa powder had'e da kwalli ta mik'e tanufi tarin trolley's d'in da ke jere tasauke guda d'aya tasoma kallon kayan da ke ciki duk tari kayan da ke ciki rasa na sakawa ta yi domin ganin take yi, matsayinta bai kai na saka wad'annan tsadadu kaya tsohuwar trolley d'inta tadauko ta zuge zip karaf idanuta suka sauko bisa wata fitted gown na shacking material a sanyaya tadauki rigar nan take kwakwalwa ta tasoma tuno mata da abunda yawuce ba za ta6a manta ranarda marigayi yaya Habeeb ya kawo mata d'inki rigar nan daga d'akinta tafito sanye da rigar zip yak'i rufewa sai fama gunguni take yayin da yaya Habeeb ke tsaye a k'ofar kitchen suna fira shi da Ammi tun kafin tafito daga d'aki take kwada masa kira yaya Habeeb! Wannan wane irin d'iki ne ka yi min zip yak'i rufewa"?
"Yaya Habeeb yadafe bakinshi yana dariya tak'araso daf da shi yaya Habeeb ina magana ka kyalle ni tafad'a cikin shagwa6a ya sauke hannunshi daga dafe bakinshi da ya yi ya k'ura mata ido ba ko kiftawa a shagwa6e tace me ye haka yaya Habeeb ya ina maka k'orafi akan zip d'in riga na yak'i rufewa kai kuma kana aikin kallona"?
Ya yi murmushi had'e da cewa babylove rigar nan ta yi masifar yi miki kyau, muddin nayi sake kika fita da ita ba k'aramin "accident za ki had'a dad'i ya lullu6e Haleesa ta kada kwayar ido ta kyalkyale da dariya Ammi da ke kitchen tace Allah yaraba mu da masifa duk abunda kyau shi ya zama masifa abun gudu ne yaya Habeeb ya dube Haleesa suka kyalkyale da dariya Ammi tace au ni ku ke yiwa dariya to maza ko bace min da gani gaba d'aya kun toshe k'ofar kitchen kun hanawa iska shigowa sai fama shak'ar hayaki nake Yaya Habeeb yarik'o hannunta zo mu je d'aki mu yi sirri banaso Ammi ta ji abunda za mu fad'a a bakin k'ofar d'akin Haleesa ya ja birki ya yi k'asa da murya kada Ammi ta ji abunda yakeso fad'a babylove ina matuk'ar sonki shiyasa nake kishinki wallahi banaso kowane d'a namiji ya kalli kyakyawa surarki na rok'e kada ki saka rigar nan ki barta sai mu yi aure ki yi min kwalliya na dinga gani ni kadai kinji babylove"?
Murmushi Haleesa ta yi tace yaya Habeeb rigima ina lissafi kusan kala 4 ka yi min d'iki kana hanani sakawa kace na ajiye sai mu yi aure ni fa hijab nake sakawa ba haka zan fita ba tak'arasa magana had'e da turo baki yaya Habeeb yak'ara narkewa sai kace manshanu na amince ki sakawa wad'anchan amma wannan ki ajiye ki yi min kwalliya amarci dariya sosai Haleesa ta yi daga bisani tace shikenan amma bana iya rufe zip din rigar da kaina cikin sigar jin dad'i yace wannan ba matsala bane ranarda da duk kika saka rigar ni da kaina zan k'arasa rufe miki zip da sauri Haleesa tarufe fuskarta da tafin hannunta yaya Habeeb yayi dariya yace bara na koma shago salman yana jira na in nadawo da dare zan ji dalilin wannan rufe fuska yajuya yafice Haleesa tadawo daga dogon tunani da ta afka tafashe da matsananci kuka "Allah sarki yaya Habeeb Allah ya yi nufi bara maka kwalliya da wannan rigar wance na d'auki tsawon lokacin ina adana ta kuka sosai Haleesa ta yi mutuwar yaya Habeeb tadawo mata sabuwa dal tsawon lokacin tadauka tana kuka duk ta6ata kwalliya da ta yi saida tagaji don kanta ta yi shiru, cikin sanyi jiki tanufi bathroom ta wanke fuskarta tasake Shafa powder da kwalli duk da haka kallo d'aya za ka yi mata kagano ta yi kuka har ta linke rigar ta mayar a trolley sai kuma tafasa domin bata ga amfani ajiyar ta da take yi tasaka inner wears ta zura rigar ta yi tsaye gaban dressing mirror tana kallo yadda rigar ta yi matuk'ar yi mata kyau hawaye suka ciko mata ido da sauri ta mayarda su ta rufe zip amma yak'i rufewa duka kamar yadda ya yi a wance lokacin kasancewa Haleesa bataso d'a kwalli shiyasa ta yane kanta da d'a k'aramin mayafi zuciyata a chukushe tafice tunawa ta yi da dokokin da Habeeb Lamido ya gindaya mata gabanta na fad'uwa tasoma haura upstairs karon na farkoda k'afarta ta ta6a takawa bedroom d'in shi......


Jeeddah Aliyu
[31/12 9:32 am] aliyujeeddah: . [09/11 12:02 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```65```

~~Hannunta na rawa ta rik'e handle sai ta yi niyar ta bud'e k'ofar sai kuma tafasa yayin da gabanta yacigaba da fad'uwa, tak'ark'arewa ta yi ta danne numfashinta ta yi ta maza ta murd'a handle d'in kutt...sautin da k'ofar ta bayar kenan ta wangale saura kiris numfashinta ya fita daga gangar jikinta sakamako hango Habeeb Lamido ta yi yafito daga bathroom yana sanye da bathrobe yana goge sumar kanshi da d'an 'karamin towel Haleesa ta yi mugun tsorata da ganinshi domin bata yi zato yana cikin d'akin ta juya da sauri da nufi ta koma inda tafito har ta riko handle ta bud'e k'ofa, yadaka mata tsawa ke! Ta tsaya chak saboda tsabar tsoro numfashinta yafara Kara kaini, ke! Ba magana nake da ke ba ne"?
Yafad'a azafafe a hankali Haleesa tajuyo ta dube shi, ta yi narai-narai da idanu kamar za ta fashe da kuka ta d'an rusuna cikin rawar murya tace _ina...kwana...yaya Habeeb"?_
Tagwaye harara ya watsa mata had'e da 'yar k'aramar tsoki, a dak'ile yace da ban kwana ba kya ganni meye dalilinki na dako samako ki shigo min bedroom batare da izzini na ba"?
"Ka yi hankuri Dan Allah da ma na zo ne nayi maka gyaran d'akin kamar yadda ka umurce ni, duk magana da ke yi kanta na sunkuye a k'asa bata yarda sun had'a ido ba tabe baki ya yi amma shine don wulak'anci kina ganina za ki koma kina nufi tun da ina ciki bara ki gyara ba koh"?
Ba haka bane yaya Habeeb na ga kafito daga wanka kana buk'atar "privacy shiyasa zan koma in kama abunda ka ke yi sai na shigo kallon k'asan ido yake mata ya ja iska kamar yaci yaji gaban Haleesa yafad'i a zuciyata tace kai Habeeb Lamido mugun shu'umi ne dube yadda yake ja iska sai kace d'an air ya lashe lips d'inshi batare da yatanka mata ba yanufi "dressing mirror d'auki robar mai yasoma shafawa yayin da Haleesa tacigaba da tsayuwa Imaan da ke kwance akan bed tana sharar bacci ta falka "Daddy na tashi
'Yar k'aramar muryarta ce tadawo da tunani Haleesa ta juya tana kallonta, Habeeb ya dire robar mai yanufi wurinta yad'aga ta sama "Morning my angel kintashi lafiya"?
Imaan ta wangale d'an k'aramin bakinta tana dariya Haleesa ta tsura musu ido sunyi matuk'ar bata sha'awa ya bata peck a kumatu mu je ki yi brush na yi miki wanka da sauri Haleesa ta tari numfashinsa ta hanyar cewa yaya Habeeb kawota na yi mata yatsine fuska ya yi bar shi kawai yafad'a adak'ile ta girgiza kai  wannan aikina ne zai fi kyau ka barni nayi mata ya tabe baki yadire Imaan k'asa yajuya yacigaba da abunda yakeyi Haleesa ta sunkuya tadauki imaan tanufi bathroom da ita tana jefa k'afarta a bathroom d'in ta yi turus mamaki ya baiyana akan fuskarta tasaki baki da hanci tana kallon tsarin bathroom d'in babban abunda ya yi mugun bata mamaki bai wuce gani katuwar plasma manne a jikin bango takara yadda ganinta akan stool na farin glass madauke da tarin news paper da magazines ikon Allah lallai in baka mutu ba kasha kallo wannan, ae dabi'ar nasara ce ko miye abun sha'awa da burgewa da har Habeeb zai dinga koyi da su  d'ayan 6angare zuciyata yace Haleesa kenan kinmanta da Habeeb half caste ne {ruwa biyu}, ta tabe baki tanufi bathtub ta tara ruwa ta darje imaan tass wurin wanke fuska ne suka fara artabo Imaan ta yi tsaye kai da fata bataso a wanke mata fuska cikin sigar rarrashi Haleesa tace haba! Imaan ki bari na wanke miki fuskarki kinga da hannu zan wanke miki ba da soso ba"
Imaan ta mak'e kafada banaso ni ki kyalle ni Haleesa ta zare mata ido tace Allah ba ki isa ba sai na wanke miki fuska, ta goga sabulu a hannunta tana murzawa akan fuskar Imaan ta kwala d'an uban ihu za ka yi tsanmani idanuta ne Haleesa ta kwakwale "Wayyo Daddy ido na wayyo za ta cire min ido"!
Habeeb da ke tsaye yana rufe bottoms d'in rigarshi jin ihun Imaan yakarade gida yasa cikin hamzari yanufi bathroom, d'in _ke! Menene"?_
_Me ki ka yi mata ne"?_
A tsorace Haleesa tad'ago ta dube k'ofa inda Habeeb yake tsaye cikin sark'ewa halshe tace wai bataso na wanke Mata fuska "Habeeb ya ja tsoki yace Imaan ki bari aunty ta wanke miki fuska miye amfani wanka ba'a wanke fuska ba Imaan ta turo baki yayin da Habeeb yajuya  yafita Haleesa tadauko towel karamin ta rufa mata koda Haleesa tafito Habeeb yafice daga d'akin bayan ta Shafa mata mai tace imaan je ki tambayo Daddy ina ya ajiye kayanki, Imaan tace aunty nasan Inda ya ajiye ta bud'e wardrobe tasoma kacaniya janyo wata k'atuwa Leda Haleesa ta dakatarda ita ta hanyar cewa bara na dauko miki ta bud'e Leda kayan sawa ne birjik Imaan ta yi karaf tace aunty jiya "Daddy yasiyo min su yace nadawo gidanan da zama zai dinga siya mini chocolate da ice cream kuma ya......dariya da Haleesa ta yi ne ya katsiwa imaan surutu ta Haleesa ta tsagaita da dariya da ta ke yi tariko hannun Imaan uhm....Imaan sarki surutu irin wannan zuba ba "comma balle full stop Imaan ta washe hak'ora aunty miye comma da full stop"?
Dariya Haleesa ta yi tace zan fad'a miki amma ba yanzu ki zo nasaka miki kaya ki je ki yi "breakfast ta Ciro wando Jean's blue had'e da White top mai Zane teddy bear kayan sunyi matuk'ar kar6a Imaan Haleesa tace oya ki je parlour ganinan zuwa kinji"?
Imaan tad'aga kai tafice da d'an gudunta  "A hankali Haleesa ta bi room d'in da kallo idanuta suka sauka bisa bedside a hankali ta taka zuwa wurin ta mik'a hannun tad'auki d'an k'aramin frame mai d'auke da photo Habeeb da salma suna manne da juna ga annuri shinfid'e akan fuskoki su Haleesa batasan lokacin da ta tsintsire da dariya a zuciyata tace kalli wannan luk'ek'iya mata ace ita ce matar Habeeb da ganinta za ta girme mishi, wannan shi ake kira to match takara kyalkyalewa da dariya da sauri ta rufe bakinta ta dube bakin k'ofa daga bisani tafara wurwurga idanuta kamar tana neman wani abu a sannu ta ajiye frame d'in tafara karkade bed ta tattara kayan da yacire ta zuba a laundering basket nan take ta gyara d'akin ya yi fass ta fesa air freshener masu k'amshi gaske tanufi bathroom ta wanke shi tass duk ta bi ta jek'a k'asan, rigarta a hakan tafito kaitsaye ta doshe downstairs parlour Habeeb da Imaan na zaune a 2 sitter Imaan na ta fama zuba masa, surutu yayin da shi kuma yake zabga murmushi, a zuciya Haleesa tace uba kurma 'ya parrot ta tabe baki da sallama takarasa shiga parlour ta zauna a 1 sitter da ke facing d'in Habeeb ta talabe kumatu ta da hannunta na dama ta sukunyarda kai kallon k'asan ido Habeeb ya watsa mata ya yatsine fuska peter yashigo parlour ya dan rankwafa cikin girmamawa yace "Boss breakfast is ready"
Chan k'asan mak'oshi ya amsa masa "okay yarik'o hannun Imaan suka nufi dining area peter ya yi musu serving dai-dai lokacin da Bala P.A yashigo fuskarshi d'auke da murmushi yace _ina kwana amaryar boss"?_
Haleesa ta yi dumm" takasa amsawa gani haka yasa Bala ya yi murmushi yanufi dining area _Good morning Boss_
Bala yafad'a had'e da Jan kujera ya zauna kallon banza Habeeb ya yi masa yacigaba da cin abinci shi Bala yace Imaan ba gaisuwa"?
 Imaan ta turo baki had'e da cewa nayi fad'a da kai tun da ka k'i siya mini goriba, Bala ya kyalkyale da dariya kai Imaan har yanzu baki manta da zance goriba nan ba"?
Imaan tad'aga kai
"To shikenan zan nemo duk inda goriba yake na siyo miki Habeeb ya mik'e yanufi parlour har yanzu Haleesa na zaune idan yabarta, ya zauna had'e da murtuk'e fuska a wulaqance yace ke! A nutse tad'ago ta amsa da na'am"
Saida yadauki tsawon dak'ik'a uku yana mata kallon da ta tsana, ki je bedroom d'ina a cikin bedside drawer akwai file's ki dauko min kiyi sauri Karki bata min lokacin.
"Haleesa ta mik'e tanufi stairs Habeeb ya rakata da ido sai lokacin idanunshi suka hasko masa rabin zip d'in rigarta a bud'e har yana iya hango brown colour bra d'inta ga wani dingo bak'i a bayanta{Mole} cike da takaici ya girgiza kai tuni Haleesa ta yi nisa domin har takai last stairs ya ja tsoki yadauke kanshi kamar Wanda aka mitsina ya mik'e da k'arfi ya haura stairs Haleesa na shiga d'akin tafara bubbud'e bedside drawers gaba d'aya ta duba a tafarko ba komai a ciki ta nufi gudan d'ayan wance ke d'auke da frame akai tana bud'ewa taci karo da tarin file's tana daukowa Habeeb na murd'a handle yashigo ya jigina jikinsa a jikin k'ofa ya hard'e hannaye shi a k'irji a firgice Haleesa ta dube shi ta ware idanu ta tsanani tsoro ya lullu6e ta, zuciyata tasoma yi mata wasi-wasi me yashigo da Habeeb"?
Ko dai wani tuggu ne ya had'a mata"?
Kafin ta lalla6o amsa tambayoyinta Habeeb ya yi mata alama da yatsanshi ta zo tak'ara rud'ewa 'yan hanjinta suka hautsine takasa bin umurninshi ganin haka yasa yafara dunfaro ta a tsorace tafara ja da baya yayin da Habeeb bai fasa tunk'ara ta jin ta yi karo da bango yasa tagano ba bu saura wurin gudu, kawai ta sadakat hannunshi yasa a bayanta yadafa bango ya rankwafa dai-dai bakinta da sauri Haleesa ta runtsi idanuta a tunani ta Habeeb sumbata ta zai yi hakan yasa jikinta yadauki rawa, ke! Banaso iskanci bud'e idanuki yak'arasa magana cikin d'aga murya ba bu shiri Haleesa ta bud'e idanuta ya dank'ara mata uwar harara nasan kwakwalwa ki yabaki cewa zan sumbace ki, in har tunaninki yabaki hakan kin yi kuskure, domin da na sumbace wannan bakin naki gwara na sumbace bakin akuya yak'arasa magana yana Shafa lips d'inta da yatsanshi ya ja iska a bakinshi jikin Haleesa yacigaba da rawa kidaina wannan karkarwa da ki ke yi ni tambaya ki zan yi
Haleesa tad'ago idanu ta fuskarta shinfide da mamaki, wance irin tambaya ce Habeeb Lamido zai yi mata da har sai ya matsita a jikin bango
_Miye dalilinki na barin zip d'in rigarki a bud'e"?_
_ko kinaso ki nuna min wannan abun ya Shafa mole in bayanta"?_
_Ko kuma  colour din brazier da kika saka ki keso nagani"?_
Haleesa tarasa bakin magana sai fama girgiza kai take
Abunda yak'ara harzuk'a Habeeb yadaka mata tsawa ke! Bara ki bud'e baki ki bani amsa ko sai na yi miki wulaqanci"?
Cikin rawar murya Haleesa tace duk abubuwa da ka lissafi banida manufa da su kawai zip d'in ne yak'i rufewa tak'arasa magana had'e da sunkuyar da kai
"Habeeb ya yi shu'umi murmushi yad'ago fuskarta yace karki yi min k'arya Co's nasan duk wannan abu da ke yi kina yi ne saboda ni kuma kin yi a banza domin ni ba burgeni za ki yi, yafisgo ta da k'arfi ya murd'e hannayeta da hannunshi d'aya yasaka d'aya hannunshi ya rufe mata zip yadaura bakinshi dai-dai kunnenta ya rad'a Mata wannan ya kasance na farko na karshe da zan K'ara ganin zip d'in rigarki a bud'e ya wulgar da hannunta da k'arfi ya duk'a ya kwashe file's d'in da ta zubar yafice Haleesa ta zauna k'asa dabass tadafe saitin zuciyata da ke barazana fita daga k'irjinta saida ta share tsawon _10 minutes_ ta na jiyar zuciya da gangar jikinta daga bisani ta mik'e jiki a sa6ule tafita tun kafin ta k'arasa saukowa ta idanuta suka hasko mata Habeeb tsaye yabawa k'ofa baya hannunshi guda cikin aljihu wandonshi d'aya hannu yana rike da waya ya kara a kunnenshi, a nutse tashiga parlour Bala da  Imaan na zaune Imaan nata zuba masa surutu yana dariya Bala yace amarya kina fama da surutu Imaan koh"?
Haleesa ta yi murmushi Habeeb ya kamalla wayar da yakeyi fuskar nan a had'e yace Bala tashi mu tafi in ka biyewa Imaan za Ku kai gobe tana zuba batare da tagaji bakinta Sam baya ciwo Bala ya yi dariya yasauke Imaan yayin da Imaan tasaka rigima "Daddy zan bi ka
"Habeeb yarik'o hannunta my angel office zan tafi ki zauna ki taya aunty hira zan siyo miki ice cream kinji"?
Imaan ta washe hak'ora "Daddy hadda chocolate da teddy da Ku....da sauri Habeeb ya katsita my Angel irin wannan lissafi ba ko numfasawa to naji duk abunda kike so zan siyo miki
"Uncle Bala karka manta da goriba na
Bala ya yi dariya yace to babyn Daddy insha Allah ba zan manta ba tak'ara juyawa wurin Habeeb Daddy yaushe za ka fiddo min Rahul da Rita mu yi wasa Habeeb yatafe goshi surutu Imaan yafara kai shi bango ya sumbace kumatu ta yace Bala mu tafi yajuya da kyar Haleesa ta iya sarafa halshenta ta furta _adawo lafiya Allah ya tsare_
Ya juya ya galla mata harara da sauri tadauke fuskarta.
Kamar jira take su fita ta mik'e tanufi dining table tacika tumbinta Imaan tadame ta da surutu _aunty Dan Allah ki kunna min cartoon_
Haleesa ta chanza mata channel zuwa Nickelodeon Imaan tadinga ihu Haleesa na dariya shirme ta daga bisani Haleesa ta kwanta a 3 sitter kwakwalwarta tasoma yi mata backward d'in abunda yafaru tsakaninta da Habeeb a haka baccin ya sace ta, Imaan ta d'auki katuwar tissue tadinga yagewa tana zubarwa ta wargaza wata kyakyawa flowers da ke sama stool ta yi daidai da remote cikin d'an k'ankani lokacin ta sauyawa parlour kamanu yayin da Haleesa batasan abunda take aikatawa sharar baccinta kawai take.
Habeeb na fita direct gidan madam Hindu yawuce yana shiga parlour gidan house maids {'yan aikin} suka dinga kwasan gaisuwa, ya amsa adak'ile ya dube yarinye a yatsine yace mom fa"?
Tana sama tafad'a cikin rawar murya a natse ya haura stairs cikin sand'a yashiga d'akin madam Hindu na tsaye gaban dressing mirror tana fesa turare taciki mirror ta hango shi yana zuwa ya yi hugging nata yadaura kanshi a kafadarta _Good morning sweetheart_
Madam Hindu ta yi murmushi _morning son me yafito da kai da sanyi safiya nan"?_
Habeeb yak'ara narkewa kamar Imaan cikin shagwa6a yace _just to see you sweetheart are you not happy"?_
Madam Hindu ta girgiza kai son baka girma abunda ka ke yi ko Hannah da take Auta bata yi shi yasake ta ya zauna a gefen bed nafi Hannah matsayin a wurinki domin ita gidan wani za tafi ni kuma _Ina tare da ke_
Murmushi madam tayi ta ajiye kwalba turare ta zauna kusa da shi _ina Haleesa da fatar ba wata  matsala a tsakaninku"?_
Ras-ras gaban Habeeb yafadi nan take yafara tunani k'arya da zai sharawa madam ya
Wani karkace kai yace.......

Jeeddah Aliyu
[31/12 9:33 am] aliyujeeddah: [10/11 6:19 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```66```


~~lafiya lau take ba wata matsala yak'arasa magana yana mai shigewa jikin mom"
Madam tace madallah amma bai kamata kafito ka barta ita kadai ae sai kewa ta dameta
"A fakace Habeeb ya tabe baki mom Imaan na nan za ta d'ebe mata kewa
Madam ta 6ata fuska wannan ba dalili bane yaushe surutu Imaan zai barta ta huta, katashi maza ka koma gidanka
 "Habeeb ya yatsine fuska mom wannan fitowa da nayi sabon company zan tafi ina da meeting da workers
Wane irin meeting Habeeb kwata-kwata yau kwananki uku da yin aure sai ka buge da zuwa office"?
To ban amince wannan ae shirme ne ko so ka ke ka Jan min surutu jama'a"?
Ni a tunani za ka yi Hutu angwaci ko da na _1 month_ ne
Habeeb ya gyara zaman shi ya dube mom kamar zai fashe da kuka mom _in zauna gida na tsawon wata d'aya ae sai ciwo yakamani_
"Kai banaso shirme zama cikin iyalinka ne zai sanya ciwo yakama ka kadai ka riga ka biyo halin mahaifinka, na neman kud'i murmushi Habeeb ya yi sweetheart kenan ba ki ji bahaushe yace kyau d'a yagado ubansa madam ta yi dariya had'e da dungure masa kai sun dauki tsawon _15 minutes_ suna fira daga bisani ya mik'e sweetheart ni zan wuce
"Son ka koma gida ban amince ka yi attending d'in wani meeting kana matsayin ango ko ba komai ka yi _1 week_ kafin kafara fita"
"Habeeb ya yi shiru yana kallon mom kamar yau ne yafara ganinta yasan duk wani bayani da zai yi mata bara gansarda ita ba yadda ya iya dole ya bi umurni ta tare suka fito zuwa downstairs parlour Hannah na zaune tana amsa waya tana ganin Habeeb ta katsi wayar cikin dariya tace mom me wannan ango ya zo yi a gidanan"?
"Harara Habeeb ya galla mata na fahimce zama da Mus'ab yasa kin rena ni koh"?
Hannah ta yi dariya _sorry bros kaima kasan ka fi gaban reni ko yaya Mus'ab da ke Shiga gonarka k'arfi hali yake yi domin yana jin tsoro kada kafasa ba shi aure na_
"Habeeb ya ja tsoki yace kin shiga uku Hannah a gaban mom ki ke zance aure sai kace ba'a jinsi Fulani kika fito ba rashin kunyarki ya yi tsanmari Hannah ta kyalkyale da dariya
 umhh...yaya Habeeb karka had'ani da mommynaa na ga kaima aure aka yi ma gashinan har kafara tada komad'a gaskiya Haleesa ta yi iya kiwo
Duka ya kai mata tagoce ta ruga ta boye bayan madam tana yi mishi dariya, madam na tayata sai fama dariya suke masa a fusace yanufi k'ofar fita
 "madam ta d'aga murya kaga agogo sarki aiki ka tabbata ka  yi cancel schedule d'inka na yau saboda ba wani meeting da za ka je banda abin ka son akwai meeting d'in yafi ka zauna da iyalinka don haushi ko juyowa Habeeb yakasa yi kuma bara iya fatali da umurni mom da ba abunda zai hanashi zuwa company saboda akwai workers d'in yakeso ya yi wa rashin mutunci tun kafin yakarasa parking space Bala da ke zaune a bakin gate yana fira da gateman ya mik'e da hamzari yanufi wurinshi ya bud'e masa mota fuskarshi a had'e yashiga Bala gida za ka kaini yafad'a a kasalance
Bala ya gyara zama madubi ta yadda zai iya hango fuskar Habeeb "Boss ba company za mu tafi ba"?
Nafasa kawai ka kaini gida
Bala yadane dariyarshi yace "boss ba dai har amarya tafara hanaka zuwa office ba"? yak'arasa magana cikin dariya.
"Habeeb yak'ara harzuk'a zuciyarshi na tafarfasa yarasa kalma da zai furtawa Bala sai kawai ya tsunduma tunani yadda zai huce haushi akan Haleesa domin ita ne ummul abasi hadasa komai har suka isa gida yana cika yana batsiwa Bala na yi parking Habeeb ya balle k'ofa yafita yanayi tafiyarsa kadai zai tabbatar maka, da ranshi a b'ace yake yana shiga parlour ya yi tsaye turus yasoma wulwulga idanu yana kallon yadda parlour ya yi kace-kace ga kuma Haleesa kwance tana sharar bacci hankalinta kwance Imaan na zaune a k'asan rugs carpet ta k'urawa TV ido ran Habeeb yak'ara b'aci cikin zafi rai mai cike da k'unar zuciya yanufi wurin Haleesa ya dagargaje iya k'arfinshi ya narka mata mahaukaci duka a ciya kamar daga sama Haleesa ta ji saukar duka a ciya ta a firgici ta falka idanu suka sauka akan fuskar Habeeb ras-ras gabanta yafara lugude mahaukaciya ta yi tsuru-tsuru da idanu
"Ke! Yadaka mata tsawa wannan wane irin sakarci ne"?
Don tsabar samun wuri kina kwance kina sharar bacci kalli yadda Imaan ta rikita parlour ke, ko kunya bakyaji kin wangame baki kina bacci wani yashigo yatarar da parlourn ki a haka yak'arasa magana had'e da nuna parlour da hannunshi
Haleesa tasauke ajiyar zuciya cikin tausasa halshe tace _Dan Allah yaya Habeeb Ka yi hankuri basan lokacin da bacci ya yi awo gaba da ni insha Allah hakan bara ta k'ara faruwa_
Kanki za ki ba wa hankuri ba ni ba domin bara lamunci k'azanta a gidana, kin k'arya min doka kuma sai na hukunta ki na ba ki _5 good minutes_ ki gyara parlour nan ki same ni a upstairs parlour yana k'arasa magana ya haura stairs yabar Haleesa sake da baki tadafe goshi kamar za ta fashe da kuka ta mik'e jiki a sa6ule, tanufi socket in kayan kallo ta yi switch off Imaan tace aunty me yasa kika kashe min kallo"?
 ni ki kunna min na kalli "Dora
Haleesa batasan lokacin da ta galla mata harara, Imaan tafashe da kuka ta mik'e tanufi upstairs Haleesa ta girgiza kai tasoma aikin da ke gabanta, cikin d'an k'ankani lokacin ta gyara barna da Imaan ta yi parlour ya yi fess da shi saidai tana tsoron yadda za ta tunk'ari Habeeb domin batasan irin hunkuci da zai yi mata tsawon lokacin tadauka tana shawarwari ta je ko kada ta je, daga bisani ta yanke shawara ta je a natse ta shiga parlour ta yi sallama yana zaune a 2 sitter Imaan na kwance a jkinshi tana cin chocolate
Adak'ile ya amsa mata sallama
"Yaya Habeeb gani tafad'a cikin sark'ewa halshe
Banza ya yi Mata kamar bai ji abunda tafad'a
Saida ta share kusan _10 minutes_ a tsaye yayin da shi kuma hankalinshi na kan movie d'in da yake kallo
Yaya Habeeb gani tak'ara fad'a
A d'age yad'ago ya had'e girar sama da ta k'asa ya dube ta ya wani yatsine fuska ya ja tsoki ke! Banaso iskanci banza da wofi angaya miki ni makaho ne da za ki dame da ga ki karki sake ki kaini bango na yi miki wulaqanci ki cigaba da tsayuwa har sai zuwa lokacin da naga dama kulla ki
Tsawon _1 hour_ Haleesa tadauka a tsaye zuwa lokacin k'afafu ta sun d'auke wuta jin take kamar k'afafunta za su cire ga wani irin zogi da tafin k'afarta ke yi
Habeeb yad'ago ya dube ta a wulaqanci yace za ki iya tafiya
A sanyaye tajuya da kyar take iya ja k'afafuta da ke barazana fita daga gangar jikinta tafice daga parlour tana zuwa kan stairs takasa sarafa k'afafuta ta yi zaune tafara gurgura duwawu ta a haka takai karshen stairs da rerafe tak'arasa bedroom d'inta tana Shiga ta zube k'asa tafashe da matsananci kuka mai had'e da sambatu marasa ma'ana _wayyo Allah yaya Habeeb me yasa katafi ka barni gashinan wannan mugun maras tausayi da imani zai kashe ni_
Tun kafin tafiya ta yi nisa yafara gallazawa rayuwata na tabbata nan da d'an k'ank'ani lokacin zai gama da ni haka tacigaba da kuka da sambatu..

_2 hour's later_

Haleesa na kwance akan pray mat d'in da tagama sallah azhar, hannunta rik'e da casbaha idanuta sunyi luhu-luhu alama taci kuka Imaan ta turo k'ofa tashigo aunty ki zo Daddy na kira ki Imaan tafad'a had'e da juyawa
Haleesa ta kwa6e fuska tuni hawaye suka fara tsiyaya daga idanuta a baiyane tace to ni me zan masa Fissibillah wannan mutumi so yake ya kashe ni yana ci zarafi na ni fa ba baiwa bace ballatana yace siyo ni ya yi ko angaya mishi aure k'iyayya hauka ne
Gani wannan tsoki burutsu bara fishe ta ba ta mik'e da kyar tafice tun daga nesa ta hango shi zaune bisa dining table ya wanke ta da mushiriki murmushi zo nan amarya Habeeb Lamido ki ci abinci yak'arasa magana yana mai k'ara fad'ad'a murmushinsa
Wani irin k'ugi ciki Haleesa Ya yi tsanani tashin hankali ya baiyana k'arara akan fuskarta hawaye suka soma anbaliye akan fuskarta, domin zuciyata ta hasko mata wannan ta yi da Habeeb Lamido ya yi mata akwai wata manufa a k'asa
Ya mik'e chak yana murmushi yanufi wurinta ba zato balle tsanmani ta ji..........


Jeeddah Aliyu
[31/12 9:36 am] aliyujeeddah: [11/11 5:24 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```67```

~~Ya dank'i hannunta kaitsaye yanufi dining table ya ja kujera ya zaunar da ita, yayin da Haleesa ta ke rarraba idanu takasa boye mamakinta
 ya bud'e food flask yadauki plate ya zuba white Rice saida ya yi kusan cika plate ya zuba tomato stew akai ya kuma lullu6e stew d'in da had'in con slow ras-ras gaban Haleesa yafadi sakamako kwalba "Bama cream da taga yadauko ya dube ta ya sake haske ta da tsadade murmushi spoon 4 ya zuba na Bama cream ya ja kujera da ke facing d'inta ya zauna yana mai cigaba da murmushi mugunta k'amshin Bama cream kadai da Haleesa tashak'a yafara hautsine mata 'yan hanji tashin zuciya ya turnuke ta, hawaye suka cika mata idanu saboda ta hal6o mugunta da Habeeb yakeso yi mata
Tana kallo yana juya abinci da spoon ta yadda Bama cream zai gauraye abinci yace _yauwa Amarya Habeeb Lamido yau da kaina zan yi feeding naki kinsan me"?_
Bai jira jin ta bakinta yacigaba da cewa banaso sweetheart ta zargeni da rashin baki kulawa, shiyasa na yi decided yau da kaina zan cika miki tumbinki
Hawaye suka wanke mata fuska cikin tashin hankali tace _yaya Habeeb banaci Bama cream amai yake sani ka tausaya min karka tilassata ni cin shi_
Tak'arasa magana tana mai goge hawaye da bayan hannunta
Ya zare mata ido ya wani murtuk'e fuska Allah ba ki isa ba kice bara ki ci abunda nakeso  tun da kika shigo rayuwata bakida za6i dole sai abunda na za6a miki yaciko spoon da abinci yanufi bakinta _oya bud'e baki_
Yaya Habeeb banaso zai sakani amai tafad'a cikin marairaice murya
Ranshi a b'ace ya galla mata harara ya mik'e ya dank'o bayan wuyanta za ki bud'e bakinki ko sai na tsinka miki mari
 Haleesa tak'ara rud'ewa _wayyo Allah wuyana you're hurt Me yaya Habeeb please have mercy on me_
Ba zan taba tausaya miki saboda ke kika fara Shiga gona ta, alfamar d'aya zan miki ki ci abinci nan
To ka sakeni zan ci
Yasake ta ya koma ya zauna spoon d'aya yabata tafara kakari Amai ke! Karki sake ki yi min amai anan wuri yak'arasa magana cikin shouting"
Tsanani tsoro ya lullu6e ta batasan lokacin da ta hadiye abincin tsabar mugunta irin na Habeeb sai yaciko spoon yadank'ara mata a baki, a wahalce ta ke hadiyewa
Yaya Habeeb zan sha ruwa tafad'a cikin rawar murya
Mugun kallo ya watsa  wuta za ki sha ba ruwa ba dallah! Malama bud'e baki saida ta cinye fiye da rabin abinci sannan ya kyale ta tashi ki b'ace min da ganin in yaso ki je ki amayar da 'yan hanjinki ba abunda yadame ni Burina yacika na daura miki abunda bakyaso wannan kad'an daga cikin hukunci da zan dinga yi miki a duk lokacin da kika karya mini doka tashi mana yadaka mata tsawa ta mik'e a firgice ta kwasa da gudu tanufi bedroom d'inta agigice ta afka bathroom tafara kwara amai, saida ta amayar da abinci da taci duka ta cire kayan jikinta tasakarwa kanta shower tsawon lokacin  ta d'auka ruwa na sauka akanta ta kashe shower ta daura towel tafito ta zube akan bed tafashe da kuka mai cike da k'unci _me na yi wa wannan d'an taliki ya za6i ya dinga kuntatawa rayuwata"?_
_ashe dama haka rashin so yake"?_
Wani irin ciwo kai yarufe ta da kyar take iya bud'e idanuta
Ta mik'e zaune ta share hawaye fuskarta ba komai Habeeb Lamido zan cigaba da yi maka biyayya akwai lokacin da zan ci riba biyayya da na yi maka tun da narasa yaya Habeeb nasan na yi bankwana da farin ciki
Ta 6angare Habeeb yana ganin Haleesa tafice daga gudu ya ja tsaki yafara zance zuci, narasa dalilin da yasa a duk lokacin da na kalli yarinya nan nakan ji tsanarta na k'ara tasiri a zuciyata ya lumshe idanu mik'ewa ya yi yadauki Imaan suka fice daga gidan.

_9:30pm_
Haleesa na zaune a main parlour ta yi zurfi cikin tunani, Habeeb yashigo duba d'aya ya yi mata yadauke fuska  _sannu da zuwa yaya Habeeb_
"Habeeb ya mata wani mugun kallo mai k'unshe da tsana ya ja tsoki ya haura sama Haleesa ta tabe baki ta nan zaune har yadawo yadda ya bar ta haka yadawo ya tarar da ita
Ranshi a 6ace yadaka mata tsawa ke!
Tad'ago a tsorace
Wai ke wace irin bagidajiya ce"?
Haleesa ta hadiye b'acin ranta ta kud'iri aniyar Zata yi hak'uri ta shanye wulaqancinsa
"Ke ba magana nake da ke ba kin wani tsare ni da idanunki masu kama da na mujiya narasa wace irin k'addara ce ta hau kaina na aure ki ba ki da amfani a rayuwata, na tsane ki bana k'auna na bud'e ido na ganki daga yau karki kuskure na sake ganinki a main parlour kidinga zama a parlour ki tashi ki bani wuri
 "Haleesa ta mik'e tsam tanufi part d'inta ta haye bed ta k'undudune cikin blanket tana kukan zuci bacci ya k'aurace wa idonta da rufe ido fuska Habeeb Lamido take gani b'akin ciki da b'aci rai suka lullu6e ta komai ya dagule mata kanta ya dau zafi tana mamaki irin wannan zazzafa k'iyayya da Habeeb yake nuna mata sai kusan asuba baccin ya yi awo gaba da ita.
********************
_1 week later_
Tun daga lokacin Haleesa ta datse duk wata hanya da za ta had'a ta da Habeeb sai ta tabbata yafita sannan ta ke Shiga part d'inshi ta gyara masa suna ciki wannan yanayi yasami urgent call daga Canada a wani company da yakeda hannun Jari"
Haleesa na zaune a falonta tana tsifewa Imaan kai Habeeb, yashigo fuskarshi a had'e da sauri ta d'auki mayafinta za ta lullu6e jikinta saboda rigar da ke jikinta transparent ce rabin k'irjinta a bud'e bata manta da wulaqanci da ya yi mata ranar da yaganta da transparent night gown shiyasa ta yi wa kanta k'iyamunlaili tun kafin ya ci zarafinta
Ta yi mugun ba Habeeb Lamido haushi da k'arfi yaficike mayafin ya jefar
Haleesa ta yi galala da baki tana kallonshi
Ya dube imaan yace
Imaan tashi ki je room d'ina akwai chocolate akan bedside ki d'auka
jikin imaan na rawa ta mik'e tafice da gudu yak'arasa kusa da ita yadaura k'afarshi akan kujera da take zaune yad'ago fuskarta daf da ta shi numfashinsa yana sauka akan fuskarta k'amshinsa ya baibaye ta ya tsareta da manyan idanunshi "eye's ball d'inshi masu kama da na magge suka k'ara jefa Haleesa cikin rud'ani ya matsi mata baki ya ja iska duk ranar da ki ka sake ganina ki ka rufe, wannan busashe k'irji naki sai na yi miki wulaqanci ko mata kirki ba su ishe ni kallo ballatana ke mai kirge dangi yak'arasa magana had'e da Jan tsaki ya dungure mata kai cikin isa da tak'ama yanemi 2 sitter ya k'ame ya yi crossing legs d'inshi saida yagama shan k'amshi yafara magana a yatsine _zan yi tafiya gobe in da akwai abunda ki ke buk'ata you should tell me_
Haleesa ta yi ignoring nashi saboda batasan abunda za ta ce da shi
_ina magana da ke kin yi shiru yana d'aya daga cikin abunda yake k'ara mini tsanarki_
Tad'ago da kyar kamar za ta fashe da kuka muryarta na rawa tace bana buk'atar komai
Ya tabe baki gobe mom da Hannah za su wuce Abuja na yi magana da mom za ki bi su da fatar ba ki manta da dokoki da na shinfid'a miki"?
"ki tashi yanzu ki had'o kayan Imaan da ke bedroom d'ina har ta mik'e tsaye yadakatar da ita oh! I forgot to tell you chef peter da direba da zai dinga kai Imaan school tomorrow morning za su wuce so that ki had'a takarce ki su wuce miki da shi saboda a flight za Ku tafi
Cikin muryarta mai sanyi tace _toh_ tafice yayin da Habeeb ya bi ta da kallo Half gown ne sanyi a jikinta mai spaghetti hands idanushi suka sauka bisa hip's d'inta, da sauri yadauke kai ya ja iska had'e da lumshe idanu ohh! Gosh ashe baby nan mai zafi ce "she has Good body structures ya lashe lips d'inshi ina ma yanda jikinta yakeda zafi ace tana da gurbi a zuciyata, ina ma auren soyayya mu ka yi ya ja tsoki cike da jin haushin kanshi to wai me zai sa na dinga wasting time d'ina ina wannan tunani tun da ba sonta nakeyi ba asalima a tsarina banaso k'aramar yarinya yaushe wannan kwaila za ta iya da ni"?
Har Haleesa tadawo janye da trolley d'in Imaan yana zaune da waya a hannunshi yana buga game, ke! Ya kirata batare da ya dube ta very slowly yake magana kamar mai ciwo hak'ora ki shirya ke da Imaan za mu fita unguwa kuma karki bata min lokacin ta amsa masa a sanyaye tana shiga bedroom ta daka tsalle _yeee yau zan fita na shak'i iskan duniya tun da na zo gidanan ko k'ofar gida ban ta6a zuwa ba_
A gurguje ta shirya cikin Arabian gown orange colour da ado white stone's ta gyara fuskarta ta feshe jikinta da turare mai sanyi k'amshi ta yi rolling da d'an siriri white veil"
Imaan ta shigo da gudu _aunty Daddy yace ki yi sauri_
Jikinta na rawa ta sauyawa Imaan kaya suka fito main parlour yana tsaye a tsakiyar parlour yana ganinsu yafice Haleesa na rik'e da hannun Imaan ta Mara masa baya zuwa parking space
Bala na tsaye yana jiransu ya washe hak'ora yace
_Barka da fitowa amaryar Boss yau za'a fita evening show'?_
Murmushin yak'e Haleesa ta yi Habeeb ya ja tsaki ya bud'e seat d'in gaba ya zauna Bala ya bud'ewa Haleesa da Imaan seat d'in baya tun lokacin da suka d'auki hanya Bala ke ta fama zuba yayin da Habeeb ya yi banza da shi wani kyakyawan gate suka nufa Imaan tasa ihu _Daddy yau bara fita gidanan sai mom ta biyani gyad'a na da ta zubar_
Habeeb ya yi murmushi mai sauti yadauke ta yanufi cikin gida Haleesa na biye da shi har cikin parlour Hannah ta taso da gudu ta rungume Haleesa _amarya yaya Habeeb oyoyo_
Habeeb ya haura sama yabar su a parlour
  "Humm....Hannah 'yan mata mommy ae ni na yi zato kin koma school
_ina nan ba idan na je bari kawai na matsu na gama karatu nan aure nakeso_
Haleesa ta zaro ido da tsanani mamaki take kallon Hannah
   "Me ye haka amarya yaya Habeeb"?
Kafin Haleesa ta bata amsa tafisgo hannunta zo mu je ki gaisa da in-law d'inki kada tafara nuna miki halin uwar miji suka kyalkyale da dariya Haleesa tace kai amma wallahi Hannah bakida kirki, sai na gayawa mom abunda kika ce
  "Madam na hakice akan 3 sitter Habeeb na kwance ya yi matashi da cinyoyinta su Haleesa suka shigo har k'asa Haleesa ta duk'a ta gaidata cikin fara'a ta amsa ta ture kai Habeeb d'agani magge sarkin son jiki Habeeb ya kwa6e fuska
     "Madam ta janyo Haleesa ta zauna a gefen ta Nasiha ta shiga yi musu Kan Haleesa na sunkuye daga bisani madam tace Son tashi Kai Haleesa ta yi bankwana da su Ammi shiru ya yi kamar ba zai tashi ba ya mik'e madam da Hannah su ka yi musu rakiya har wurin mota Bala ya ja mota suka nufi unguwar su Haleesa Bala ya yi parking a k'ofar gidan su  Habeeb ya dube ta a yatsine saura kuma in kin Shiga gidanku ki manta da mu a k'ofar gida
Batare da Haleesa tace da shi komai ba ta bud'e k'ofa tafita tana fitowa idanunta suka hasko mata Yaya Habeeb sanye cikin kayan ball ya tunk'aru ta fuskarshi d'auke da murmushi nan take kwakwalwa Haleesa ta d'auki zafi _dama ana mutuwa a dawo tambayar da tafara aikawa kanta_
      "A lokacin d'aya tsanani tsoro da rud'ani suka lullu6e ta numfashinta yafara k'okari barin jikinta yana daf da yak'aroso wurinta ta kwaso da gudu tashiga zaure gidansu duk abunda ke faruwa Habeeb Lamido na tsaye a jikinsa mota yana kallonsu..........

Jeeddah Aliyu
[31/12 9:39 am] aliyujeeddah: [13/11 7:17 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```68```

~~Ammi na zaune tsakiyar gida Haleesa tafad'o kamar daga sama, ta fad'a jikinta tak'ak'ame ta _lafiya ki ka shigo min a firgice daga ina kike"?_
A lokaci guda Ammi ta aikawa Haleesa tagwaye tambayoyi
   _Ammi yaya Habeeb na gani a k'ofar gida yana sanye da kayan Ball dama Ammi ana mutuwa adawo ko yaya Habeeb fatalwa ya yi"?_
Mtwww.....Ammi ta ja dogon tsoki cike da jin haushin ta yakice Haleesa daga, jikinta Anyya Haleesa mutuwa Habeebu bata ta6a kwakwalwarki ba"?
  Haleesa ta yi duru-duru da idanu hawaye da majina suna ambaliya akan fuskarta Allah Ammi yaya Habeeb na gani tak'arasa magana cikin shasshek'a
Gafara chan shashasha banza da wofi yadda kwakwalwarki ta toshe kina tsanmani kowa haka yake Habeebu yatafi Haleesa bara yata6a dawowa ki sawa zuciyarki salama ki rungume mijiinki kada ki 6ata rawanki da tsalle.
 Haleesa ta share hawaye da gefen mayafinta
A k'ofar gida kuma Hasheem na gani Haleesa tashiga gida da gudu zuciyarshi ta tsinke musanmman da ya ga mijinta tsaye ya hard'e hannaye fuskarshi babu annuri, cikin rashin k'uzari yanufi wurin Habeeb a zuciyarshi yana addu'ar Allah yasa Haleesa ba matsala tasamu da mijinta, sallama ya yi wa Habeeb had'e da mik'a masa hannu
  Bala ne ya amsawa Hasheem sallama, a maimako Habeeb ya bai wa Hasheem hannu sunyi musabaha sai kawai yad'aga masa hannu da sauri Bala yad'anki hannun Hasheem suka gaisa a mutunce sa6ani Habeeb da ke tsaye k'ik'an yana operating phone d'inshi kamar bai Sam da tsayuwa Hasheeem a wurin
   "Jiki ba lakka Hasheem Yajuya yashiga gidansu Haleesa zuciyarshi na aiyana masa Haleesa matsala tasamu da mijinta, da sallama yashiga gidan a firgice Haleesa tad'ago tana kallonshi, tasauke k'arfafa ajiyar zuciya ba shakka yaya Hasheem ne nagani zuciyata tabani yaya Habeeb ne
Tuni Ammi tagano Hasheem ne Haleesa tagani ba Habeeb domin tsanani kama Hasheem da shi yake da Habeeb sai ka kwatar da hankalinka za gano banbancinsu
   _Ammi lafiya wannan bak'auya amarya ta zo mana gida"?_
Idanun Haleesa na tsiyaya hawaye ta galla masa harara Ammi ta sanarda shi tabargaza da Haleesa tashigo da ita dariya sosai Hasheem ya yi gaskiya Haleesa Yakamata zuwa wannan lokacin ki fitarda yaya Habeeb daga ranki a dalilin ka sa cire shi daga zuciyarki yasa yafara yi min gizo
  ''Haleesa ta galla masa harara da jajaye idanunta har da laifinka yaya Hasheem me yasa ka sanya JC d'in da yaya Habeeb yake amfani da shi baya kuma kasan kun yi kama saida yafika kyau tak'arasa magana tana murgud'a baki
Hasheem yarufe baki yana dariya bisa wannan dalili naki zai sa na fasa amfani da JC da raina yakeso"?
  Ammi ce takar6e zance ta hanyar cewa rabuda ita kawai Hasheemu tsabar shirme ta ne, ya motsa
Hasheem yana dariya ya mik'e Ammi ni zan wuce gida na ji amfara kiran sallah magariba har ya juya yak'ara dawowa Ammi ba fa Haleesa ita kadai bace tare take da Habeeb Lamido yana k'ofar gida''
A tsorace Haleesa tad'ago sai lokacin ta tuna da Habeeb Lamido nan take gargad'i shi yafad'o mata a rai.
   "Ammi ta girgiza kai had'e da cewa Allah yaye miki wannan matsala Haleesa don lamarinki sai addu'a Hasheemu kace da shi yashigo Hasheem yafice a k'ofar gida ya tarar da Habeeb yana alwala da roba ruwan faro Hasheem yadanne zuciyarshi yace "Yalla6ai da ka bari na kawo maka buta
Fuskar nan a had'e yad'ago karka damu abokinaa na gode
Bala ya yi karaf yace ni  ka kawo min a matse nake ina so in kama ruwa
Wani mugun kallon Habeeb ya watsa masa da sauri Bala yadauke kai tamkar bai ga kallon da Habeeb yake masa Hasheem yashiga gida bai jima ba yafito sanye da jallabiya hannunshi d'auke da buta ya mik'awa Bala
Habeeb yace abokinaa ina zan sami masallaci mu je na nuna maka yana farko layi watakila don ba ka lura bane da za Ku shigo da ka ganshi
  Humm....Habeeb yafad'a a takaice
Ammi ta dube Haleesa tace har tsawon wane lokacin za ki dauka kafin ki dawo mutum"?
Haleesa ta sada kai k'asa tarasa amsa da za ta ba Ammi
Wannan ya ba Ammi dama tasoma yi mata fad'a mai had'e da Nasiha daga bisani tace tashi ki je ki yi sallah Haleesa ta tashi jiki a sanyaye Imaan tashigo da 'yar sallama ta Haleesa tariko hannunta
Ammi na ganinta tagane ita ce 'yar Habeeb Lamido
Akan hanyar su Habeeb na zuwa masallaci idanunshi suka sauka bisa symbol na ```Ni da yaya Habeeb tailoring center ``` rubutu ya ja hankalinshi har yatuna da zobe Haleesa da ta ta6a yarwa a Lagos yatsinta, a zuciyarshi yace _Humm..... Wannan Habeeb d'in yana da matuk'ar mahimanci a rayuwa Haleesa ya riga yagama da zuciyarta shine ni kuma mom ta had'ani da ita yaushe na ke da lokacin soyayya da k'aramar yarinya ae sai ajina ya zube_
Ya wani tabe baki a haka suka k'arasa masallaci saida ya jira akayi sallah isha'e sannan yafito, a k'ofar masallaci yatarar da Bala da Hasheem sai kuma salman da yazama ciko na ukunsu suna fira, yadda a kullum abinci Kara tsada yake rayuwa talaka Nigeria tadawo abar tausayi, abunda ya ji Bala yana fad'a kenan Habeeb ya girgiza kai a zuciyarshi yace su Bala an sami abunda akeso kalli yadda ya karkace baki yana zuba yak'arasa wurinsu ya gaisa da yaya salman daga bisani suka dunguma zuwa gida akan hanya Habeeb yake sanarda yaya salman tafiyar Haleesa abuja cikin sigar zolaya yaya salman yace _yalla6ai kace za ka k'ara nisantani da k'anwataa"?_
 Murmushin k'arfin Hali Habeeb Lamido ya yi a cikin zuciyarshi yace dama za ka rabani da ita da ka taimakawa rayuwata, a baiyane kuma sai yace mafi yawa hark'oki na nafi yi su a abuja da Lagos ka ga bai kamata ina abuja k'anwarka tana yola ae sai ka zargeni da rashin bata kulawa yaya salman ya yi 'yar dariya had'e da cewa wannan gaskiya ne yalla6ai da haka suka k'arasa k'ofar gida, yaya salman ya yi wa Habeeb iso zuwa cikin gida har k'asa Habeeb ya durk'usa ya gaida Ammi yaya salman yace Ammi ina Haleesa"?
Ammi tace tana d'akinta
Yaya salman yanufi d'akin ya tarar da ita tana sallah yajuyo yace Ammi sallah ta ke yi in tagama ki ce da ita zan kirata a waya saboda sauri nake zan koma shago akwai Wanda yake jirana yaya salman ya sake mik'a wa Habeeb Lamido hannu sukayi musabaha salman yafice
Imaan da ke zaune a gefen Ammi tana ci tuwo tace Daddy Ammi tabani tuwo mai dad'i
Habeeb ya yi murmushin yak'e yace to yi maza ki cinye karki ragewa Bala
Ae kuwa da sauri Imaan ta yaki katuwar loma Ammi na mata dariya
"Shiru-shiru Haleesa bata fito ba yayin da Habeeb yake duba wrist watch d'in ke daure a hannunshi Haleesa kuwa tana gama sallah ta haye mattress tana kwance rub da ciki ganin Hasheem da ta yi yataso mata da tsohu mik'i na rashin yaya Habeeb a hankali take rera kuka
Habeeb yak'ara duba agogo hannunshi ya ga _9:00pm_ ta yi ga shi kuma yanada appointment da manager company shi sun yi da shi za su had'u k'arfe _8:30pm_ duk duniya ba abunda Habeeb ya tsana irin sa6a alk'awali yana matuk'ar girmama lokacin yawan duba agogo da yakeyi ya ankarar da Ammi tace wai wace irin sallah ce Haleesa take yi"?
Da sauri Habeeb yace Ammi bara na duba ta ya mik'e yanufi d'akin a dai-dai k'ofa ya tsaya kamar mai shawara daga bisani ya yanke shawara shiga ya bankad'ala curtain{lubulle} yana shiga idanunshi suka sauka bisa bango d'akin hotuna marigayi yaya Habeeb ne birjik kowane hoto Haleesa ta yi rubuta kalamai soyayya masu zafi a k'asa shi a hankali Habeeb Lamido yake karanta rubutu _I love you yaya Habeeb I can't live without you_
_you are d only men I love live without you is miserable_
_I love you yaya Habeeb more than my own life I will continue to love you for d rest of my life_
Da sauri Habeeb Lamido yadauke idanunshi ya mayarda akan mattress ke! Ya kira Haleesa shiru ko motsi bata yi ba jin yake yi kamar ya narka mata mugun bugu a gadon bayanta, amma yana ji tsoro kada ta kurma ihu Ammi ta ji sannu a hankali yakai hannunshi kamar Wanda zai ta6a kashi ya d'an bubbuga bayanta ke! Bacci ki ka yi ne"?
A firgice Haleesa ta mik'e zaune rigarta ta yaye cinyoyinta suka baiyana ta ja baya ta jigina a bango ta yi duru-duru da jajaye idanuta
Habeeb ya kafa wa cinyoyinta ido take ya tuna da mafalki da yata6a yi ya ja iska yayin da Haleesa ta kafe shi da ido yad'ago yana tsotsa bakinshi kamar mai tsotsa sweet kallon ido cikin ido su ka yi wa junansu Haleesa ce tafara d'auke idanunta saboda bara ta jure cigaba da kallo eye's ball d'in shi yana mata kwarjini matuk'a a zuciyarta tace ina mamaki wannan d'abi'a ta yaya Habeeb sai dinga Jan iska kamar Wanda yaci yaji ga wani tsotsa baki da yake kamar mai sha sweet kuma da alama wannan d'abi'a ta bi jikinsa amma fa wannan d'abi'ar tashi tana burgeni kuma tak'ara masa kyau kai Habeeb Lamido kyakyawa ne ajin farko     "Habeeb Lamido yak'ara yadda ganinshi akan jela gashin kanta da ke reto a bayanta a cikin zuciyarshi yace _ashe yarinya nan 'yar duniya ce hadda attachment take sakawa na tsani mace mai saka gashin doki_
Ya ja tsoki yak'ara murtuk'e fuska ke ki tashi mu tafi mana gaba d'aya Haleesa ta rikice jikinta na rawa ta d'auki mayafinta yana gaba tana biye da shi a bakin k'ofar Ammi ya tsaye ya yi mata sallama yaciro bundle na 'yan N1000 ya ajiye mata yafice da sauri domin yasan halin Ammi za ta iya cewa bara ta k'ar6a ba Haleesa tadauke imaan wance tuni ta yi bacci Ammi tak'ara gargad'i Haleesa ta bi mijinta sau da k'afa a k'ofa gida Haleesa ta tararda Habeeb da baffanta suna fira ta runsuna ta gaida baffa a gurguje tashiga gidansu marigayi yaya Habeeb ta gaida inna mairo zainab ta yo mata rakiya sai fama tsokana ta take yi ita ma kyautar kud'i Habeeb ya yi mata Ya kuma bata bundle gudu biyu yace bayan yatafi ta ba wa baffa da baba Audu domin yasan matuk'ar ya basu da kanshi bara su k'ar6a ba Bala ya bud'e musu k'ofar mota Haleesa ta zauna a seat d'in baya tana rungume da Imaan tun lokacin da suka d'auki hanya sanyi Ac ya ratsa Haleesa tafara gyagyadd'i a k'ofar gidan Alhaji bashir manager Bala ya yi parking Habeeb yafice yanufi cikin gidan yabar Haleesa da Bala a mota Bala yana ta zubawa Haleesa surutu tun tana bashi amsa har bacci ya yi nasara d'auke ta sai misali  karfe _10:30pm_ Habeeb yafito daga gidan Bashir manager a lokacin tuni Haleesa ta yi nisa da bacci "Bala ya dube Habeeb yace Boss mutane nan naka gaba d'ayansu sun yi bacci
Habeeb ya mak'e kafad'a alama I don't care har suka isa gida Haleesa batasaniba tana ta sharar bacci Bala ya yi parking Habeeb yafito dauke Imaan daga jikin Haleesa yasoma tayar da ita ke tashi mu iso gida Haleesa ta yi wani juyi ta gyara kwanciyarta
Bala yayi karaf yace Boss yadda ka ga amarya ta gyara kwanciyata za Ka iya kai gobe kana tayar da ita bata tashi ba kawo Imaan na shiga da ita ciki ka dauki Haleesa Habeeb ya galla masa harara angaya maka ni d'an dako ne da zan d'auke ta"?
boss ba fa yau kafara daukarta ballatana nace abun zai zo maka banbarankwai
Cike da jin haushi Habeeb ya ja tsoki ya sunkuya yadauke Haleesa ya ji kamar yadauki Imaan Sam bata da nauyi a parlour ya shinfid'e ta bisa 3 sitter ya karbi Imaan yakaita bedroom Bala ya yi masa sai sa safe yafice Habeeb ya yi tsaye yana kallon Haleesa nan take ya kudurta wani Abu a cikin zuciyarshi yasaki murmushi mugunta...........


Jeeddah Aliyu
[31/12 9:42 am] aliyujeeddah: [14/11 5:46 pm] Jeeddah Aliyu```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa Shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```69```

~~kitchen ya shiga ya bud'e fridge ya d'auko roba ruwan Mr V masu sanyi gaske, fuskarshi d'auke da wicked smile yadawo wurin Haleesa.
 ''Baiwa Allah tana ta sharar baccinta ya balle murfi ruwan ya juye mata su a jiki Wani irin zillo Haleesa ta yi kamar za ta shed'e ta mik'e zaune bakinta d'auke da kalma shahada, tasauke ajiyar zuciya mai k'arfi ta tsurawa Habeeb ido sosai ranta ya b'aci da wannan wulaqanci da Habeeb ya yi mata.
Habeeb ya yi flinging da empty roba ruwa saida yak'are mata kallon wulaqanci, yace ke wannan kallon na menene ko za ki rama ne"?
"Girgiza kai ta yi A'a ta furta a sanyaye amma inaso kasani wulaqanta d'an Adam ba abu ne mai kyau d'an Adam yanada matuk'ar daraja bai kamata ya zama abun wulaqantawa a gareka musanmman ni da nake matarka ta sunnah tak'arasa magana had'e da sada kai k'asa.
"Habeeb ya ja iska jikinshi ya yi sanyi sai kawai ya tsince kanshi da rashin jin dad'i abunda ya yi mata kalamanta sunyi masifar ratsashi amma bayaso ya nuna mata kada ta yi tsanmani tafara samun matsayi a zuciyarshi.
''Ke wannan dad'i bakin naki bara sa nafasa yi miki abunda na yi niyya _so you better keep quiet & listen to me_
Idanu Haleesa suka ciko da hawaye bata yi k'ok'ari hana su zubowa saboda ita ma tana buk'atarsu a wannan lokacin.
D'aya bayan d'aya yafara magana kamar Wanda aka yi wa dole _Do you think zan yi dakonki tun daga compound har izuwa parlour a banza"?_
Sai lokacin Haleesa tafara raba-raba idanu har ta yi nasara gane Inda take tasauke eye's ball d'inta a fuskarshi ta yi k'asa da murya tace ka yi hankuri yaya Habeeb bansan lokacin da na yi bacci a mota ba.
  "Yakara had'e fuska kin ga malama ni ba hankuri nace ki bani kawai ki biyo ni a bedroom d'ina, ki sauke Hakke na da yarataya a wuyanki
"Numfashin Haleesa yadauke chak tana wani muzu-muzu da ido tsoro ya baiyana k'arara akan fuskarta
Cikin gadara ya daka mata tsawa ke! Bara ki tashi ba"?
Babu shiri ta mik'e zubur ruwan da zuba mata suna d'iga daga jikinta, wuce mu tafi yafad'a chan k'asan mak'oshi Haleesa tana gaba yana biye da ita a rud'e take haura stairs ta zame saura kiris ta fad'i ta rike karfe.
    ''Habeeb ya ja tsoki yace ke ki yi hankali fa karki je wurin tunaninki na banza ki illata kanki a wofi.
  Haleesa ta kasa gane inda kalamansa suka dosa hannunta na, rawa ta bud'e k'ofa  ta jigina a wardrobe tana muzurai.
Habeeb ya dube ta ya tabe baki ya matsa daf da ita a rikice ta matsa yak'ara matsa ''very close to her har ya na ji  heartbeat d'inta ya yatsine fuska k'asa-k'asa yafara magana kamar mai rad'a ke wace irin bad thinker ce ga ki 'yar ta tsutsuwa amma sai d'an banza tunani ke me kike tunani za ki yi min a wannan k'anana shekaru naki"?
Haleesa ta yi shiru gabanta na cigaba da fad'uwa Dallah! matsa ki bani wuri yafad'a had'e da tureta Haleesa ta koma gefe tana kallonshi ya bud'e wardrobe yace ke dama luggage d'ina nakeso ki had'a min gobe around _7:30am_ flight d'inmu zai tashi in nace da safe ki had'a za ki iya b'ata min lokacin saboda na fahimce siririta a jininki yake yak'arasa magana had'e da kallon fuskarta.
    ''Haleesa tasauke sanyayar ajiyar zuciya tanufi wurin wardrobe da sauri Habeeb ya matsa yace ke kafin na fito daga bathroom ki tabbata kin cire wannan rigar naki karki jik'a min rugs yanuna rugs carpet d'in da hannunshi Haleesa ta yi masa kallon mamaki a zuciyata tace dube shi dallah sai kace bashi bane ya jik'a ni tana kallonshi har yashige bathroom ta Ciro d'aya daga cikin jallabiya shi ta cire rigar jikinta tasaka 'yar k'aramar trolley ta janyo ta loda masa kayanshi tana yi tana gyangyad'i bacci yaci k'arfinta a hankali ta sulala k'asan rugs bacci mai dad'i ya yi awo gaba da ita Habeeb ya gama wanka yafito ya yi tsaye sororo yana kallon Haleesa yadda ta yi kwance ta dunk'ule a wuri d'aya ya yi bala'e bashi dariya da shi gwanin dariya ne da abunda zai hanashi kyakyatawa, kawai ya yi murmushi a zucyarshi yace kai wannan yarinya akwai bacci tsiya ya gyara mata kwanciya sai lokacin ya lura da jallabiya shi a jikinta yak'ara sakin murmushi mai sauti ya bud'e wardrobe yadauko blanket ya rufa mata ya sanya kayan bacci ya haye bed.
*********************
Kiran sallah asuba ne ya falkar da Habeeb ya yi mik'a had'e da addu'a tashi daga bacci, ya zuro k'afafu shi har ya tsallake Haleesa sai kuma yadawo ya shiga  bubbuga hannunta ke, ke ki tashi asuba ta yi a hankali ta bud'e idanunta ta ware su akanshi a tsorace ta mik'e zaune.
 "Habeeb yashige bathroom da sauri ta mik'e tanufi bedroom d'inta sai da ta sauya kayan jikinta sannan tashiga bathroom ta yi brush had'e da alwala tana gama sallah ta bud'e Qur'ani ta yi tillawa.
_7:15am_
"Habeeb Lamido yafito cikin shirin tafiya yasha black suit sunyi matuk'ar yi masa kyau jikinshi na fitarda fitinane k'amshi kaitsaye ya murd'a handle bedroom d'in Haleesa tana kwance akan pray mat d'in tagama sallah ga Qur'ani ajiye a gefenta.
   "Habeeb ya girgiza kai sleeping sickness yafad'a a baiyane chan k'asan mak'oshi yasoma kiran sunanta da yake baccin nata baiyi nisa ba nan take ta falka yana tsaye hannaye shi zube cikin aljihu.
Muryarta na rawa tace _ina kwana yaya Habeeb"?_
   Tafad'a had'e da d'an runsunawa.
_Lafiya lau_
Yafad'a a takaice
Tsawon _10 second's_ yadauka yana nazari daga bisani ya aza briefcase d'inshi a gefen bed d'inta ya zuge zip yaciro 2 bundle na 'yan N1000 ya mik'a mata zaro idanu ta yi ta k'asa k'ar6a''.
K'ar6i mana yafad'a ciki angry voice ya za'a yi na baki abu ki ce bara ki k'ar6a ba"?
Jiki a ma ce Haleesa ta mik'a hannun biyu ta k'ar6a.
  "Ajiye su a hannunki koda buk'ata ta taso miki sai ki yi amfani da su yak'ara Ciro ATM ya ajiye a gefen gado  yaciro farar takarda ya rubuta code d'inshi yadaura akan ATM wannan ATM d'ina ne inda k'udin Hannunki suka k'are sai ki je bank ki ciro in kuma bakisan yadda ake yi  Hannah ta rakaki tanuna miki yadda ake yi.
Har ya dasa aya kan Haleesa na sunkuye Yaya Habeeb duk me zan yi da wad'annan kud'i gaskiya sun yi yawa katafi da ATM d'inka wad'annan da kabani har kadawo bara iya kashesu. harara ya galla mata ba shawararki nake nema ba abunda nakeda ra'ayi ne, _11:30am_ flight d'inku zai tashi ticket d'inki yana wurin mom ki had'a kayanki driver da zai wuce da su shi zai sauke mu a airport kafin yadawo kin had'a.
   "Haleesa tad'aga kai har Yajuya yasake dawowa ina phone d'inki"?
Haleesa ta yi duru-duru da idanu tace tana ciki wardrobe mamaki ya lullu6e shi me kuma waya yake yi a ciki wardrobe"?
  ''cikin sanyi murya tace basan yadda ake operating d'inta  shiyasa na ajiye.
   "murmushi Habeeb ya yi yace village girl kawai je ki dauko nagani ta bud'e wardrobe taciro kwalin wayar ta mik'a masa ya bud'e yaciro charger ya jona wayar a charging.
Yace ki bawa Hannah wayar za ta koya miki yadda ake operating d'inta kinji"?
Haleesa tad'aga kai had'e da cewa _Allah ya kiyaye hanya_
"Ameen Habeeb yafad'a yadauki briefcase da sauri Haleesa tace kawo na rik'a maka jakkar batare da yace komai ba ya mik'a mata ya wuce gaba tana biye da shi a compound suka ci karo da Bala.
Habeeb yace Bala sa'eed ya iso kuwa"?
"Eh Boss tun da asuba ya iso yana main gate yana jiran fitowar ka
"Shiyasa nakeso aiki da sa'eed Sam baya wasa da lokacin
   Gaskiya ne "Boss
Habeeb ya juya wurin Haleesa yace kawo briefcase d'in ki koma  Imaan tana bedroom d'ina tana bacci ki dauko ta ki rufe min d'akin.
Jikin Haleesa a sanyaye tajuya kaitsaye tanufi bedroom d'inshi ta tayarda Imaan ta yi mata wanka ta gyara masa room d'in tarufe k'ofa tanufi d'akinta ta had'a kayanta.
*******************
_11:30am_
Flight d'in su Haleesa yad'aga zuwa Abuja lokacin da flight d'insu ya yi landing driver madam Hindu ya zo, ya yi picking nasu zuwa gidan madam da ke "Wuse 2.
_3 Hour's later_
Madam Hindu na zaune a parlourn ta Haleesa da Hannah na gefenta ta dube Haleesa cikin kulawa tace Haleesa ki tashi ki had'a luggage d'inki driver ya kai ki gidanki ga Hannah nan ta tayaki zama kafin son yadawo.
Haleesa kamar za ta fashe da kuka ta mik'e saboda taso madam ta kyalleta ta yi zamanta anan.
_3 day's later_
Yammaci ne mai cike da ni'ema ga iska mai sanyi yana kad'awa Haleesa da Hannah na sanye cikin farare sports wear's suna buga basket ball a filin wasa da ke cikin gidan da yake Haleesa bata iya ba Hannah na ta yi mata dariya yayin da Imaan ke wasa bisa bicycle d'inta sai daf da magariba suka koma ciki gida.
Haleesa na cikin sallah phone d'inta ya yi ringing kafin ta sallame ya katsi bayan tagama sallah ta dauki wayan ta tsurawa number ido tana cikin nazari number kira yak'ara shigowa, nan take ta tsince kanta da fad'uwa gaba.
A hankali ta zauna a gefen bed ta yi picking ta kara a kunnenta cikin muryarta Mai dad'i tace
_Hello_
_ke wannan wane irin wulaqanci ne ina kira ba ki d'agawa ko har yanzu ba ki iya operating d'in wayar bane"?_
Gaban Haleesa yak'ara fad'uwa ta dafe k'irjinta a zuciyata tace na shiga uku yaya Habeeb ne da kyar ta bud'e bakinta tace.........

Jeeddah Aliyu
[31/12 9:46 am] aliyujeeddah: [15/11 8:03 pm] Jeeddah Aliyu: ```NI DA YAYA HABEEB```

_the sweetest love_

Na Hauwa shehu Aliyu

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


              ```70```

~~I'm sorry yaya Habeeb lokacin da ka Kira ina sallah.
 A Canada kuma Habeeb na kwance akan kujera a bakin swimming pool na katafaren Hotel d'in da yasauka ya shafi lallausar suma kanshi idanunshi a rufe yacigaba da magana da Haleesa _ranar Monday Mus'ab zai zo ya kai Imaan school ki shirya mata da wuri_
okay Haleesa tafad'a cikin siririya murya
_I hope ba wani matsala"?_
Haleesa tace nop
_Good Ina Imaan"?_
''Tana parlour tare da Hannah
_okay ki bata waya_
Haleesa ta mik'e da sauri tanufi parlour bara na kai mata
_karki yi hanging up yafad'a a kasalance''Imaan zo ki yi magana da Daddy da gudu Imaan ta taso ta k'ar6e wayan daga hannun Haleesa tasoma zubawa Habeeb surutu    ''Daddy kasiyo min biscuit da chocolate da elephant da kuma snake.
Murmushi Habeeb ya yi my Angel bara ki bari mu gaisa, ba kin fara wannan lissafi naki da baya k'arewa to naji duk abunda kike so zan siyo miki _promise to me za ki yi karatu sosai banda wasa kinji my Angel"?_
"Yes Daddy I promise you kai ma Daddy karka manta da alk'awalina
 "By God great bara manta ba ki gaida aunty Hannah ya yi hanging up.
Imaan ta mik'awa Haleesa wayarta ta kuma Isar da sak'on Habeeb wurin Hannah.
*********************
_4 Day's later_
Haleesa da Hannah na tsaye cikin kitchen Haleesa na yanka cabbage Hannah kuma, tana yanka albasa.
''Imaan tashigo da gudu rik'e da wayan Haleesa aunty ankira wayanki
Da sauri Haleesa ta k'ar6i wayan daga hannun Imaan, ganin sunan yaya Habeeb akan screen ya yi mugun jefata cikin rud'ani hannunta na rawa ta yi "received
_Hello_
Cikin tsawa yace ke! Dallah ki ba wa Imaan waya duk lokacin da na Kira ki sai kinyi wasting time d'ina yak'arasa magana had'e da Jan dogon tsoki.
Jikinta a sanyaye ta mik'awa Imaan waya tace yi ki magana Daddynki ne tajuya tacigaba da aikinta duk abunda ke faruwa Hannah na tsaye rik'e da wuk'a tana, kallonsu.
Ta tayi shiru tana nazari yanayi sauyin fuskar Haleesa alama ce da ke nuna akwai abunda Habeeb yafada mata Wanda yayi sanadi sauyawarta a lokacin d'aya tajuya wurin Imaan da ke ta fama zuba wa Daddy ta surutu.
 tace Imaan ki je parlour ki yi waya da Daddy, Imaan tafice tadafa kafad'a Haleesa karki 6oye min Haleesa domin ko kin 6oye min a matsayin shekaru da nakeda su zan iya fahimtar wani abu kinga kenan 6oyewa batada amfani, kuma na tabbata a halin da kike ciki kinada buk'atar abokin shawara.
Ta d'an dakata domin ta ji ta bakin Haleesa
''Hawaye suka cika idanun Haleesa cikin murya da ke nuna tanaso yin kuka tafara magana me zan 6oye miki Hannah''?
Iya sanina kinsan duk abunda ke faruwa tsakanina da yayanki har izuwa yanzu bata chanza zani ba.
    ''I known Haleesa but kema yakamata ki yi amfani da baiwar da Allah yabaki, ta 'ya mace ki janyo hankalin mijinki zuwa gareki.
A yatsine Haleesa take kallon Hannah daga bisani tace akan wane dalili zan 6atawa kaina lokacin in janyo hankalinshi gareni angaya miki ina sonshi ne"?
  ''Hannah ta girgiza Kai ko bakya sonshi nasan bara ki so aurenki ya mutu ko za ki so ki shiga layin k'anana zawarawa"?
       "Jikin Haleesa ya yi sanyi ta yi shiru tana kallon Hannah had'e da nazari kalamanta daga bisani tace Hannah ya kike so nayi shi da yake d'an namiji bai nuna ra'ayi akaina sai nice zan nuna gaskiya ni bara iya ba ke ni fa ko k'amshin turare yaya Habeeb naji sai gaba na yafad'i tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
 ''Hannah ta yi dariya tace ni kuma me ye laifi na da kike murgud'a min baki daga ke har yaya Habeeb bara Ku ta6a iya gujewa k'addarar da ''Allah ya yi nufi akanku duk wannan noke-noke za Ku gama ne kudawo kan hanya.
  ''Haleesa ta tabe baki kanki akeji na fahimce cewa bakida aiki yi shiyasa kike yunk'uri cusa mini d'an uwanki ba kuma zai ta6a samun matsayi anan wuri ta nuna k'irjinta da yatsa.
  "Hannah ta girgiza kai bata k'ara cewa da ita komai ba tacigaba da yanka albasa.
******************
_1 week later_
Around _2:00  o'clock_ na dare flight d'in su Habeeb yayi landing sa'eed ya zo ya yi picking nasu da yake part d'inshi yanada tazara da na Haleesa har washe gari  batasan yadawo ba.
 "Tun da asuba Haleesa ta falka bata k'ara komawa bacci ba saboda za ta shirya Imaan zuwa school _7:20am_ ta gama shirya Imaan
"Haleesa ta dube imaan tace bara naje na dauko miki launch box d'inki.
 Imaan tace aunty ba ki bani Chocolate ba
Na saka miki a schoolbag d'inki''
 a kitchen ta tararda Peter yana had'a breakfast peter ina lunch box d'in Imaan''?
Ya nuna mata da yatsanshi da sauri ta sunkuce lunch box d'in ta kuma rik'o hannun Imaan tanufi compound da ita saida suka kai parking space Imaan tasa rigima tana magana had'e da bubbuga k'afafu a k'asa _Allah aunty ni yau bara je school uncle Ezekiel duka na yake yi_
  ''Haleesa ta dafe goshi tasoma rarrashinta haba imaan a kullum za ki tafi school sai mu zo mota kike saka rigima kinga shiga mota Ku tafi zan kira uncle Ezekiel a waya ba zai dake ki ba kinji"?
Cikin jin dad'i Imaan ta daka tsalle sa'eed na ta fama yi musu Haleesa ta bud'e mata k'ofa oya zo ki shiga kada ki yi latti Imaan tashiga mota sa'eed ya ja _bye bye aunty ki had'a mini chocolate cake kafin nadawo_
Haleesa na dariya tace _bye babynaa zan had'a miki ke kuma ki yi karatu sosai_
Saida ta ga motarsu tafita gate sannan tajuya cikin gida.
Duk abunda ke faruwa tsakanin Haleesa da Imaan Habeeb Lamido na tsaye a balcony da ke sama yana kallonsu idanunshi na kan  Haleesa har ta6acewa ganinsa ya ja iska had'e da lumshe ido.
  ''Haleesa na shiga parlour taci Karo da Hannah sanya da sports wear's ke nake jira mu fita exercise
  Haleesa tabe baki bacci nakeji bara iya zuwa ba
Wane irin bacci Dan Allah ki zo mu je banaso "fat ya yi miki yawa kada yaya Habeeb ya auro 'yar shila.
  Mtww...Haleesa ta ja tsoki had'e da shigewa bedroom da kyar Hannah ta ciyo kanta ta amince suka fita compound bayan sun gama jogging suka nufi wurin snooker tun da suka fara buga wasan Hannah ce take winning saboda Haleesa ba iyawa ta yi ba in ta daki ball da stick sai ya yi tsalle yafad'i Hannah ta kwashe da dariya.
Habeeb yadawo daga jogging Bala na biye da shi tun daga main gate ya hango Haleesa da Hannah kaitsaye yanufi wurinsu Hannah nagani shi, ta washe hak'ora tuni Haleesa ta nemi natsuwarta rasa sai gumi ke tsatsafo mata.
Yaya Habeeb saukar yaushe"?
_Jiya da dare yafad'a chan k'asan mak'oshi_
Haleesa tasauke ajiyar zuwa wance ta janyo hankalin Habeeb yasoma yi mata kallon da ta tsana......

Jeeddah Aliyu